Showing 138001 words to 141000 words out of 186041 words

Chapter 47 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53905

yakamata kimun irin wannan maganar na rashin ɗa'a?...."
Ayush ko kula mommy batayi ba ta cigaba da tafiyarta harta ƙule wa ganin mommy,
Mommy ƙirjinta ne ya fara bugawa domin taga rashin nasara a idon Ayush ƙarara bazata yadda da maganar Auren nan ba, mommy jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba haka take jan ƙafa daƙer ta nufi part ɗin sarki Raamud.....

Ita kuwa Ayush pillow ta ɗauka ta ƙwanta akan doguwar sofa tana cikin tunani da nazari har bacci ya ɗauketa,
A daren yau mommy bata samu yin bacci ba saboda tsananin mamakin maganganun da Ayush tayi mata, kuma tana tunanin halin da zata shiga in har bata Auri sarki Raamud ba, gashi duk abunda Ɓingel take so shi Sarki Raamud yakeyi idan kuma tace bataso to kuwa ko ƙasa da sama zasu haɗe bazaiyi abun ba....


★★★★★★
Washe gari da safe bayan ta idar da sallar asuba tashi tayi ta fara kai kawo a cikin ɗakin, tana zirga-zirga ta kasa zama har gari yayi wasar a lokacin Junaid ya samu daman dawowa tin fitar sallar asuba ya zauna a masallaci ne domin karatun Alkur'ani,
Tana gani ya shugo amma ko kulata baiyi ba balle ya tambayeta dalilin yin zirga-zirgarta,
haka ya shige toilet har yayi wanka yayi brush sannan ya fito amma still tana wannan zirga-zirgar, abun yayi matuƙar ɗaure masa kai amma sai dai bazai kulata ba saboda rashin mutuncin data masa jiya,
Har cikin ranta tana son sanar masa abunda ke faruwa amma saidai tana fargaban abunda zaiyi mata saboda jiya da fushi ya ƙwana,
Shima har ya gama shirye-shiryensa yazo zai fita tayi saurin shige gabansa tana faɗin "Yaya Junaid dan Allah ka tsaya ka saurareni, akwai abunda zan gaya maka ne..."
kamar bazaiyi magana ba haka yake kallonta cikin fushi yace "idan baki ban hanya ba sai nayi ƙwallo dake awaran wallahi...."
Tace "dan girman Allah kayi haƙuri wallahi ina cikin matsala ne, ka gafarceni mijinaaaa..."
Jin ta ambaci girman Allah da kuma fashewa da tayi da kuka yasa yaɗan sauƙo yace "inajinki toh..."
dakatar da kukan tayi sannan ta kora masa jawabai akan mommy da Abbah ta ƙarasa maganar da cewa "yanzu haka ma har sun tsayar da maganar Aurensu...."

tinda Ayush ta fara magana Junaid ya kafa mata ido jin labarin da take bashi na soyayyar mommy da Abbah zaro da dara-daran idanuwansa yayi cike da mamaki yace "Whatttt! Aure kuma tsakanin mommy da Abbah?..."

Ayush ganin kalar reach ɗinsa yasa hankalinta ya kwanta domin tana tunanin zasu haɗu ne su wargaza maganar Auren,
Tace "yess of course abunda nake gaya maka gaskiya ne shiyasa tin jiya nake cikin damuwa ai"
Lokaci guda Junaid yasau ƙayataccen murmushi na farin ciki tareda faɗin "wow masha Allah, Allah na gode maka daka zaɓawa mahaifiyata mijin da zata Aura, na daɗe ina jiran wannan lokacin burina shine naga mommy tayi Aure itama saboda ba wuce yin Auren tayi ba amma ta kasa yi, nayi mamaki sosai jin mommy tana soyayya abun farin ciki ma wai sarki Abbah zata Aure, zan so Uncle Artaff yaji wannan Albishir...."
yana kaiwa nan yayi ficewarsa cikin nuna farin ciki...

Ayush kamar ta haɗiyi ranta tsabar ƙololuwar baƙin ciki bata san lokacin data fashe da kuka ba,
itama ta fice a ɗakin da haka ta sauƙo falon kai tsaye part ɗin Abbanta ta wuce,
tana zuwa kuwa ta samu Abbah yana zaune akan sallaya ga flask ɗin shayi da maganunnuwan da mommy ta kawo masa da daddare, tsayawa tayi ko zama bata samu damar yiba balle gaisuwa ga hawaye yanda yake mata go slow akan fuskarta,
Sarki Raamud ganin halinda Ɓingel take cikine yasa ya zabura shima ya miƙe tsaye yana faɗin. "lafiya kuwa Ɓingel mezan gani haka, kinaso ki ƙuntata mun koh? shine dalilin da yasa kika zo kina nuna mun hawayenki alhalin banason ganin hawayenki ko ɗaga indai bana farin ciki ba..."
Goge hawayen tayi tana jan zuciya tace "zan daina kuka ne da zaran ka gayamun gaskiya akan soyayyarka da mommy..."
Abbah yace "toh banda abunki Ɓingel tinda har kinsan gaskiya ai sake tambaya ma bai taso ba...."
Tace "kenam da gaske Aure zakuyi?..."
Dasauri ya amsa mata cikin ƙwarin gwiwa domin yana da tabbaci akan Ɓingel ɗinsa cewar zata yadda da maganar,
Dasauri ta katse shi da cewa "Tabb ɗin jamm kenam Amanar mahaifiyata za'a ciii?...."
tayi maganar cikin ɗaga murya tareda zaro manya-manyan idanuwanta waje tana huci ta kuma cewa "wallahi kar ma a fara wannan zance domin abu ne mai wuya na iya yadda, taya za'ace ka Auri mahaifiyata sannan kuma kazo ka Auri mahaifiyar mijina how comes, dis thing should never do abun baiyi tsari ba gaskiya wannan ai cin amana ne ƙarara da kuma rashin karaaa..."

Abbah gaba ɗaya shima jikinsa ya mutu yayi sanyi wani irin zazzaɓi ne ya ƙara rufoshi jin Ɓingel bata yadda da maganar Aurensa da mommy ba,
cikin harɗewar murya yace "Ɓingel shin mekike faɗa hakane? Kada kice zakiyi haka domin zaki cutar da zuciyata ne, na kamu da tsananin son Hajia Fateema kar kimun haka dan Allah...."
Itama tana kuka tareda faɗin "nima Abbah zaka cutar da zuciyata inhar ka Auri mommy domin bansan da wani ido zan rinƙa kallonta ba, wai ace surkuwata ta zama matar ubana? bantaɓa ji ba ko a Film, toh ma Abbah dole ne sai kayi Auren ? ka zauna mana haka mezai sameka ..."
Yace "Ɓingel koda banyi Aure dan kaina ba dole zanyi Aure dan masarauta na domin babu Sarkin da yake zama babu matar Aure, kuma kina maganar Mommy surkuwarki ce shin Addini ya haramta na Aureta ne? matar ɗan uwana ne pah dan na Aureta saboda bashida rai saiya zamo laifi?...."

Cikin yanayin damuwa tace "Ni kawai banasooo! na dantse alaƙar soyayyarku babu maganar Aure kuma idan har anason zaman lafiyata a gidan nan...."
Kafin Abbah ya ƙara cewa wani abu harta juya zata bar ɗakin tayi kucuɓuss da mommy a bakin ƙofar ɗakin tana tsaye duk taji maganganun Ayush daga A har Z,
Ayush burki tayi itama ta tsaya tana kallon Mommy....


Shi kuma Junaid yana can ɗakin mommy yana jiranta akan ya nuna mata takardar ƙarin matsayisa zuwa General a ƙasar california, sannan kuma sai su tattauna game da maganar Aurenta da Sarki Raamud kafin a sanarwa Uncle Artaff......




*DAN ALLAH NIMA INA BUƘATAR COMMENTS ƊINKU 🙏🙏🙏 INASON GANIN ZAFAFAN COMMENTS....*


𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 71 to 75


Mommy tana kuka tabar ɗakin sarki Raamud jin abunda Ayush take faɗi, kai tsaye ɗakinta ta nufa tana shiga ta tarar da Junaid yana zaune a bakin gadon yana jiran shugowarta, ganinsa yasa tayi saurin goge hawayen fuskarta cikin ƙarfin hali tace "my son yadai na ganka yau kamar kana cikin farin ciki..."
da murmushi ƙwance saman fuskarsa ya ɗago yana kallonta lokaci guda kuma ya haɗe ransa ganin yanda idon mommy yayi ja alamar tayi kuka sosai, dasauri ya miƙe tsaye ya riƙo hannunta tareda faɗin "why Mom, meyasa kike kuka ba tareda nasan dalili ba..."
Mommy daƙer take ƙwaƙulo murmushi saboda kar Junaid ya sakata a gaba da wasu tambayoyinsa, tace "babu komai ka kwantar da hankalinka ba wani abu bane.."
Junaid ƙura mata ido yayi tareda ɗago hannunsa ɗaya yana goge mata guntun hawayen da yake shirin gangaro mata, cikin sassanyar murya yace "Mom zauna kinji koh" ya zaunar da ita a bakin gadonta shima ya zauna yana fuskantar ta kamar zaiyi kuka haka yake ji saboda ya tsani ganin hawayen mommy ko kaɗan, shiyasa yake ƙoƙarin mata duk abunda takeso indai bana cutarwa bane,
yace "Mom bakya kuka akan abu saidai idan yakai maƙura, dan Allah kar ki ɓoye mun Mom..."

Mommy kamar bazata sanar masa ba kawai taji cewar gwara ta gaya masa duk halin da ake ciki, tana kuka ta soma kora masa duk abubuwan da suke wakana a tsakaninta da sarki Raamud,

Jinjina kai Junaid yayi yace "Okay shine dalilin da yasa Yushert tayi mun wulaƙanci jiya? okay I will teach her a lesson..."
a firgice ya miƙe tsaye zai fita mommy tayi saurin riƙo hannunsa tareda cemasa "yanzun ina zakaje "
yana huci yace "Mom haƙuri na yazo ƙarshe, bazan iya juran wulaƙancin Yushert ba, yanzu saboda iskanci irin nata duk rashin mutuncin da take mun ina shanyewa bai isaba har saita taɓo mun mahaifiyata, to wallahi mommy yau babu abunda zai hana na saki Yushert ko kuma na mata ɗan iskan duka..."
Mommy cikin lallami take roƙonsa tace "a'ah baza aje wannan gacin ba, kayi haƙuri komai zai zo cikin sauƙi, mu bita a hankali yarinta ke damunta..."

Junaid yana tsaye fuska a haɗe tsananin ɓacin rai ne ya bayyana akan fuskarsa sam baiji daɗin abunda Ayush tayiwa mommy da Abbah ba ta mayarsu kamar ƙananun yara,
Bai ankara ba yaji mommy ta jawo hannunsa tana cewa "zo ka zauna ka sanar mun abun farin cikin dake tafe dakai my son..."
jiki a sanyaye ya zauna sai faman tsuka yake tayi daƙer ya iya motsa hannunsa ya miƙawa mommy takardar ƙarin matsayinsa, karɓa tayi tana faɗin "wannan fah..."
buɗe takardar tayi ta soma karantawa lokaci guda ta miƙe tsaye dasauri tana zazzaro ido waje baki a sake ta juyo tana kallon Junaid dake zaune shima zuba mata ido yayi ganin yanda ta kasa yin magana tsabar farin cikin data shiga, lokaci guda ta durƙusa da gwiwowinta ƙasi ta ɗaga hannayenta sama tana faɗin
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah mun gode maka...." kasa ƙarisa maganar tayi takai hannu ta rungumo Junaid tareda fashewa da kukan farin ciki,
Junaid shima rungumar momminsa yayi yana faɗin "it's okay my mom bana son ganin hawayenki na gaya miki koh"...
ɗagowa tayi tana kallonsa cikin farin ciki tace "my son kukan farin ciki nake yi, sakamakon wannan gaba ɗaya Allah ya yaye mun duk wani ƙunci da nake ciki..."
Murmushi yayi sannan yace "Mom ki daina saka damuwa aranki, nayi miki Alƙawari duk abunda kike so a duniyan nan koda zan rasa rayuwata zanyi miki shi!.."
Mommy tace "Insha Allahu babu abunda zaisa ka rasa rayuwarka my son..." jinjina kai yayi sannan ya kuma cewa "yanzun gaya mun kina son Sarki har cikin zuciyarki kuma zaki Aure shi?..."
Mommy tace "meyasa kamun wannan tambayar?.." haɗe tafukan hannunsu yayi idonsa akan mommy yace "please tell me..." ya ƙarasa maganar kamar irin shagwaɓaɓɓun nan, mommy kamar zata fashe da kuka tace "har mun tsayar da maganar mu cikin sauƙi ina tunanin zakuyi farin cikin hakan shiyasa muka yanke cewar bazata zamuyi muku, toh sai akayi rashin sa'a Ayushert bata son Auren bansan dalili ba shiyasa yanzu zan yanke hukuncin warware maganar Auren banason ayi abu cikin ɓacin rai kaga mu ba yara ba balle..."
Girgiza kai Junaid yayi sannan yace "kar ku damu Mom Aure kamar anyi shi ne, kar ku yadda yarinya ƙarama ta juyar da ƙwaƙwalwarku, shin ita take da iko daku ne? ko kuma ita ta haifeku? ki kwantar da hankalinki komai zai zo cikin sauƙi Okay..."
Mommy ta jinjina kai tana murmushi tace "thank you my beautiful Son..."
ɗagowa yayi ya sumbaci Mom akan goshinta tareda faɗin "ina ji dake my Mom, take care..."
ya miƙe zai fita tayi saurin cewa "ya naga kana tafiya jiki ba ƙwari kodai yunwa? ooooh bari nayi saurin shiga kitchen banson barin yarona da yunwa ga itama Ayushert ciki ya tsufa dole nasan tana jin yunwa, ta ƙarisa maganar tareda ficewa daga cikin room ɗin,
a tare suka fito falo suna ɗan hirarsu mommy ta hango Hafzat sai faman shirya kuloli take akan dinning daman tare suke shiga kitchen,
cikin sakin fuska mommy tace "Hafzat kar dai ace har kin gama abincin breakfast?.."
Hafzat tace "na gama komai Mommy daman ai zuwa yanzu kam yakamata ace kin huta tinda ina gidan zan iya yin ko wani aiki..."
Mommy tace "a'a bazan iya bar miki komai kiyi ba, kema kina buƙatar hutawa..."
tana dariya tace "mommy kar ki samu damuwa Ni aiki ba komai bane a waraina saboda na rigada na saba baya bani wahala kasancewa ta a gidan talakawa na fito dole na motsa jikina, in banyi aiki ba jikina ciwo yake..."
Mommy cikin farin ciki take kallon Hafzat haka kawai yarinyar take burgeta, ga bata da matsala tace "shikenam Shalele nah Allah yayi miki Albarka..." Hafzat cikin nuna farin ciki ta amsa da"Ameen..."

Duk maganganun da suke yi Junaid yana zaune yana jinsu ɗagowa yayi ya kalli gurin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login