Showing 75001 words to 78000 words out of 186041 words

Chapter 26 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53907

kallonsa ido cikin ido tace "daman kaima baka mutu ba?..."
Sarki Raamud shima hawaye ne suka fara cicciko masa saboda shima ya tuna da matarsa kuma sarauniyarsa Bara'at daƙer ya buɗe baki yace "ba nine mijinki ba, ni ɗan uwan mijinki ne..."
Mommy tana kuka tace "bangane mai kake nufi ba, kana nufin kace kaiɗin ba mijina bane? toh idan ka manta dani ai bazaka manta da ɗan ka Junaid ba koh?..."
Sarki Raamud bazai iya bata amsa ba sakamakon kuka da ya kuɓuto masa, ita ɗin ma kukan take...
Narasimha ganin baza su iya bawa juna haƙuri ba yasa yazo har gabansu yasa sukayi shuru ko wannensu ya maida hankalinsa kansa, Narasimha yana kallon mommy yace "kiyi haƙuri baiwar Allah wannan ba shine mijinki ba, amma kuma ɗan uwan mijinki ne wato sarki Raamud,
wannan shine mutumin da kike jin labarinsa a ko'ina kuma shine a baya yake cutar miki da yaronki Junaid, Amma yanzu ya rigada ya shiryu...."

Hankalin mommy ne ya fara dawowa jikinta anan ta fara tunanin ganin sarki Raamud da tayi a television lokacin da aka kamo shi,
tana kuka ta nuna sarki Raamud da yatsa tace "daman kaine sarki Raamud? Kuma ɗan uwan mijina?..."
Sarki Raamud jinjina kai yayi yana kallonta,.
Narasimha ne yace "kar kiyi mamaki domin yanzu zan baki tarihin rayuwar mijinki da kuma wannan sarki Raamud..."
Mommy juyowa tayi tana kallonsa,
Anan ya fara kora mata jawabai yana bata labari tin daga kakanun kakanun su sarki Raamud..."


*******


Shi kuwa Junaid shima yana zaune akan gado, har wannan lokacin yana gidan malam lawan sakamakon rashin lafiyan da yasha domin har yanzu baya iya cin komai kullum a cikin tunanin Mommy yake, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa duk yabi ya rarrame yayi fari sol dashi kamar ba jini a jikinsa,
Damusa yana ƙwance a ƙasin gadon da Junaid yake shima ba wargi a tattare dashi ganin Junaid a halin da yake ciki,
Malam Lawan ne ya shugo da sallama a bakinsa, daƙer Junaid ya iya amsawa, murmushi malam lawan yayi yana faɗin "Alhamdulillah yanzu ka fara samun sauƙi Junaid tinda yanzu kana iya amsa sallama.."
zuwa yayi ya zauna a bakin gadon shima ya riƙo hannun Junaid yace "Junaid Dan Allah ka zamo mai tawakkali a rayuwa, nasan kana jin raɗaɗin ciwon rashin mahaifiyarka da kuma Ayushert amma haƙuri zakayi, akwai yaran da iyayensu suka mutu suka barsu amma haka suke shan gwagwarmayar rayuwa, kaima kayi haƙuri, mahaifiyarka addu'a take buƙata a halin yanzu...."

Junaid tinda malam ya fara magana yake kallonsa har zuwa yanzu idonsa akan malam daƙer yake motsi da bakinsa yace "yaushe Yushert ta mutu?..."
Malam yace "eh mana har da ita wutar ta cinye..."
Junaid girgiza kai yayi sannan yace "Yushert tana nan a raye, ita ta sanar mun mutuwar mahaifiyata a lokacin da abun ya faru.."
Gaban malam ne ya yanke yace "Ayshert tana raye daman?..."
tashi Junaid yayi yana faɗin "Malam inaso ka rakani gidan Doctor Hasheem..."
ya ƙarasa maganar yana zaro jallabiya a jikin wardrobe ɗin ɗakin, ya sanya shi domin iya 3quater ne a jikinsa sai singlet,
Shima Malam tashi yayi yana mamakin ya za'ayi ace Ayushert tana raye kuma bata nemeni ba ko shi Junaid?..."
bin bayan Junaid yayi zasu fita,
Damusa ne shima ya miƙe zai bisu Junaid ya waiwayo yace "Sujjur zauna zan dawo yanzu.."
Damusa ya koma ya ƙwanta abunsa....



*MASHA ALLAH FATAN KUNA JIN DAƊIN LITTAFIN THE WIFE OF A TIGER*
*TO BE CONTINUE NEXT....

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 39 ➡️40


Narasimha a labarin da ya bawa mommy kam ba wanda ya tsallake hatta silar warkewar Junaid bai ɓoye mata cewa a silar Ayush ya warke ba...

Mommy kuka take sosai tace "Allah Sarki Ayushert daman wannan zoben data cire a cibiyarta shine maganin warakar Junaid? ta bayar da rayuwarta akansa, tasha jinya sosai, amma silar warkewar ta ai kaine, Muna godiya sosai..."
tana kallon Narasimha cike da farin ciki..

Narasimha yace "basai kin gode mun ba saboda su ɗin sun kasance jinin sarauta ne, kuma kakansu sarki Zaid mutumin kirki ne, ko dan shi zan temaki ahalinsa..."

Mommy tana girgiza kai cike da damuwa tace "Allah Sarki Bara'atu munyi mata mummunan fassara ashe itama ba'a son ranta tayi haka ba, anyi amfani da ita ne ta hanyar asiri, nayi tunanin Junaid ne ya kasheta ashe ita ta bada rayuwarta akansa, Allah ya gafarta mata, kuma Allah ne yasa mijina zai mutu ta hanyar nan, idan ajali yayi ƙira babu wanda ya isa ya tsayar da mutum, Allah ya jiƙanka mijinaaaa..." ta ƙarasa maganar tareda fashewa da wani irin matsanancin kuka...

Sarki Raamud shima yana zaune yana zubda hawaye cikin rarrashi yace da mommy "kiyi haƙuri Fateema duk laifi nane, ni nayi sanadiyar mutuwar ɗan uwana kuma mijinki, sannan inaso na nemi yafiyar Junaid akan abubuwan da na aikata masa na zalunce shi saboda son zuciyata, Mayushert ɗiyata ce amma itama na cutar da rayuwarta ta hanyar dasa mata abunda zai cutar da ita acikin cibiyarta, sauran kaɗan na rasata, dan Allah ku gafarce ni, ku yafe mun Fateema.."
Itama ɗagowa tayi tana kuka idonta akansa tace "kar ka damu Sarki mun yafe maka kuma Insha Allahu Allah zai yafe maka, ka cigaba da addu'a tinda Allah yaga zuciyarka, kazo ka rungumi ƴaƴanka hannu bibbiyu, suma zasu ji daɗin kasancewa tareda kai a matsayin mahaifi..."

Sarki Raamud share hawayensa yayi yana murmushin farin ciki tabbas yaji daɗin kalaman mommy, domin har cikin zuciyarsa ta ratsa, ɗagowa yayi yana kallonta yace "Nagode sosai mai kyakkyawar zuciya, haƙiƙa Junaid da Mayushert sunyi dacen uwa ta gari,
Amma sai daiii..."
ya ƙarasa maganar tareda shiga wani irin yanayi na baƙin ciki yace "haƙiƙannin gaskiya banji daɗin abunda Mayushert tayi miki ba, gobarar da ya tashi a gidanki ba haka kawai ya tashi ba, Narasimha yana gani yanda akayi kuma ya sanar mun, toh amma ni bazan ɓoye miki ba domin idan har kika ji daga baya ranki zai sosu matuƙa, toh amma ni nafison na gaya miki abunda ɗiyata ta aikata miki ba maganar ɓoye-ɓoye, wato Mayushert ita da hannunta ta tayar da gobara a gidanki tana so ki ƙone sakamakon tana tunanin Junaid ne ya kashe mata mahaifiya...."
Sarki Raamud ya ƙarasa maganar yana kallon mommy cikin tausayawa,

Mommy bata nuna alamar baƙin ciki ba ko kaɗan sai murmushin da tasau tana girgiza kai tace "Allah Sarki yarinta kenam, tana so nima ta kashe ni ne saboda Junaid ya ɗanɗani baƙin ciki shima kuma banga laifinta ba ko kaɗan wallahi, Allah Sarki ƴata Ayush tausayi take bani wallahi, ashe ma jinina ne ita ɗin..."
Babu wani alamar damuwa a fuskarta.
Sarki Raamud yace "kar kice haka Fateema domin Ayush butulci tayi miki..."
bai ƙarasa maganar bama ta katse shi da cewa "laaa kar kayi kuskuren faɗin haka domin nasan har yanzu ina cikin zuciyar Ayush, Ayush tanada kyakkyawar zuciya kuma ƴar baiwa ce, banaso ana aibata ta a gabana, domin duk wanda ya kushe Ayush toh maƙiyi nane ba masoyi ba saboda ta kasance jinin jikina ne..."
Sarki Raamud shima murmushi yayi yana sauraronta, ta cigaba da cewa "Ayush burinta Junaid ya shiga halin ƙunci a halin yanzu domin suna tunanin na mutu, toh kuwa zan cika mata burin natan, saboda haka bazan koma yanda suke ba har sai Ayush da Junaid sun daidaita kansu domin su ɗin ma'aurata ne, zan cigaba da zama a cikin wannan masarautar mai tarin albarka..."

Sarki Raamud yace "toh shikenam Insha Allahu za'a nemo miki mata waɗanda zasu tayaki zama kuma suyi miki duk wasu ayyukan da kike buƙata..."
Mommy murmushi tayi sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa tace "Nagode Sarki.."

Sarki Raamud shima murmushin yake ya kalli sama yace "mu godewa Allah,
nima yanzu banida wata matsala, domin an rigada an wanke ni a idon jama'a, duk laifukan da nayi an maida su kan Munafurr wanda ya sheƙa tintinin, duk ba kowa ne yayi mun wannan ƙoƙarin ba sai Junaid, kafin ya koma Nigeria shi yayi rubutu ya turawa shuwagabanni hukumomi, kuma an tabbatar bani aka yaƙa ba hasali ma har da ni muka yaƙi babban annoban,
yanzu dai nayi free, kuma wannan masarautar za'a ƙara tsara shi ne, a sako mutane a cikinta waɗanda zasu na hidimar aiki, da kuma fadawa, zan sauƙa akan mulkin nan Insha Allahu Prince Junaid da Princess Mayushert sune zasu cigaba da mulki a acikin masarautar nan...."

Mommy ta sauƙar da ajiyar zuciya tana kallon sarki Raamud tace "toh kenam kai baza kayi Aure ba? naga akwai part-part ɗin ɗakuna acikin masarautar nan sun kai 10 kuma manya-manya..."

Murmushi sarki Raamud yayi sannan yace "ehhh acikin part ɗin ɗakunan zan zaɓi ɗaya na zauna a ciki kafin rai yayi halinsa ba tareda matar Aure ba, domin ni na rigada na yanke cewar bazanyi Aure ba har ƙarshen rayuwata..."
ya ƙarasa maganar yana kallon mommy, itama ya tambayeta cewar "ina kema a cikin masarautar nan zaki cigaba da zama da yaranki?.."
Murmushi tasau tace "eh kamar yanda kaima kace haka nima zan zaɓi ɗaki ɗaya na zauna ni kaɗai, daman tinda mijina ya rasu na yanke cewa ba wanda zan Aura..."

Narasimha duk tattaunawar da sukeyi a junansu yana jinsu, yayi gyaran murya sannan yace "idan kun gama shiriritar takun ni zan koma yanda na fito kafin na sake dawowa..."

Sarki Raamud ne yayi saurin miƙewa sannan ya durƙusa ƙasi tareda haɗe hannayensa biyu yana roƙan Narasimha akan ya zauna dasu,
"Dan Allah Baba Narasimha kayi haƙuri ka cigaba da zama a tare da mu, inason ka kasance tareda mu domin zakana bamu duk wata kariya kuma zaka warkar mana da jinyar da ya gagare mu indai bana ajali ba, dan Allah..."
Narasimha yace "a'ah Raamud bazan iya zaman duniya ba, tafiya zanyi can wajen da nake zaune.."
Sarki Raamud hawaye ne suka cicciko masa yace "Baba Narasimha ka tuna fa mahaifina ya baka amanar mu, kar ka tafi ka barmu tinda yanzu ruhinka ya komo jikinka da temakon Damusa..."

Jikin Narasimha ne yayi sanyi yace "toh shikenam zan zauna daku...."
Daman akwai ɗakin Narasimha da ban wanda aka tanadar masa, ɗakin da ba kowa ne yake shigansa ba...

Sarki Raamud yayi farin cikin jin abunda Narasimha ya faɗa yace "Nagode Narasimha amma yanzu inaso kayi mun wata alfarma ɗaya..."
Narasimha yace "meye matsalar?.."
Sarki Raamud yace "Damusa nake so ya zauna dani, na tabbata a can Nigeria duk wanda yaga Damusa zaiyi ƙoƙarin tserewa ne, kuma kaga Damusan daman na masarauta ne, bazaiji daɗin zama a wajen Junaid ba.."
Narasimha yace "wannan gaskiya ne, zaman Damusa Sujjur a cikin masarauta shine zaman lafiyansa domin shi ba kamar sauran Damusa bane, abincinsa da ban ne, don haka yanzu zanje na ɗauko Damusa Sujjur..."
Narasimha yana kaiwa nan ya ɓace ɓatt...


********

Lailah tana zaune a harabar gidansu akan kujerar roba tana waya tana faɗin "kinga Maimoon ya zaki cemun kinada ciki? bayan sau ɗaya akayi amfani dake..."
Ata ɓangaren Maimoon kuwa cewa tayi "Laila nidai na gaya miki shi Allah babu ruwansa da sau ɗaya akayi, ciki ne Allah ya bani bansan ya zanyi ba, kuma muddin Daddy nah yaji wallahi saiya ɗauki ƙwakkwaran hukunci, gashi yanzu cikin har ya soma fitowa amma ban yadda an gane ba har yanzu..."

Lailah tace "yanzu cikin zaije wata nawa?.."
Maimoon tana kuka tace "yanzu fah yana shirin shiga wata na Bakwai.."
Lailah ta zabura tace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Maimoon ciki ai ya girma, kin kusan haihuwa, toh yanzu ya za'ayi? wallahi kinyi sakaci Maimoon meyasa tin da baki sanar mun ba sai yanzu, ai da an zubar yanzu kuwa babu halin zubar wa..."
Maimoon tana kuka tace "toh yazanyi, meye mafita.."

Lailah juyowa tayi zatayi magana kwatsam sai taga Junaid yana tsaye ata bayanta, shi kuma Malam Lawan yana cikin motarsa bai sauƙo ba,
Gaban Lailah ne ya yanke ta dafa ƙirjinta tace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un nashiga uku.."
Junaid yace "kinga babu ruwana da tattaunawar da kikeyi da munafukan ƙawayenki, shin ina Yushert?.."
Lailah hannunta na rawa ta nuna cikin falo tace "tana ciki.." juyawa yayi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login