Showing 6001 words to 9000 words out of 186041 words

Chapter 3 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53933

yanzu, idan kinje falo ki buɗe frig zakiga ledar fruit saiki ci kafin ki kwanta, gana maimoon itama yanzu zan sakata taci natan..."
Lailah tace "toh my bros mun gode" yace "to bani key ɗin ɗakin nan" ta miƙa masa sannan tabar wajen da sauri, shi kuwa ya shige ɗakin.."

yana shiga ya tarar da maimoon kwance, riga a zame tana kallon saman ceilling rigarta ne kawai a ɗan ɗosane saman breast ɗinta, wanda ana zamar dashi shikenam, ga kuma breziya a gefe, binta yake da kallo cike da mamaki yazo daf da ita sannan ya zauna a bakin katifa yace "maimoon ya haka? meyasa kika cire rigar takin ga kuma rigar breast a gefe kuma ai ba zafi kike ji ba tinda ga iskar fanka ta ko ina.." tana daga kwance ko motsawa batayi ba tace "ka tambayi ƙanwarka mana.." saida gabansa ya faɗi yaji wani rass yace "ƙanwata kuma? bangane mai kike nufi ba." shuru tayi masa batace komai ba, ya ƙarishi maganarsa amma kota kulashi, ajiyar zuciya yayi sannan yace "ok tinda kin ƙi yin magana tashi kici abinci nasan kina jin yunwa ko?.."
mirginawa tayi tana kallon bayanta tace "bana buƙata"
murmushi yayi sannan yace ki temaka mun ki tashi kici.." miƙewa tayi ta zauna a fusace tace "kai malam taya kake son na rinƙa biye maka ne, nace banaso shin ana dole ne, idan nace banason abu to bana sonsa, kuma gwara yunwa ta kasheni indai ni zanci abun hannunka..." tana kaiwa ƙarshe ta tashi tana ɗingishi zata nufi toilet ga riga a hannu ta tare nonuwanta dashi, Doctor Hasheem riƙo hannunta yayi ya jawota jikinsa yana faɗin "meyasa kika raina ni ne maimoon? meyasa har yanzu baki yadda da ƙaddara ba, wannan abunda ya shiga tsakanin mu tsautsayi ne.." katseshi tayi da cewa "ni ka sakeni meyasa kuke mun hakane kai da Lailah kun mayarni tamkar jakar ku, na tsaneku wallahi"

gaba ɗaya ya kasa gane ina ta dosa sai cewa yayi "please maimoon ki nutsu mana, abinci...." idonsa ne ya sauƙa akan manya-manyan nonuwanta masu sheƙi dake farar fata ce, rigar data rufesu dashi ne ya zame, wani irin haɗiyar yawu yayi tinin har ya shiga taitayinsa, a hankali ya janyo rigar ya rufe mata su yakai idonsa saman fuskarta yaga itama shiɗin take kallo, ɗan yatsarsa yakai saitin bakinta yana faɗin "kiyi shuru ki zauna ki ci kayan fruit ɗinki.."
zaunar da ita yayi sannan ya buɗe ledar ya ɗauko ayaba ya ɓare sannan ya fara feeding ɗinta, a bata son haka ta haƙura take ci...


☆☆☆☆☆☆

Junaid bayan ya tambayi ɗakin da mommy take aka nuna masa ya shiga,
zama yayi a bakin gado ya zuba mata ido har ƙwalla ta soma cicciko masa, ya kamo hannunta ya rinƙe, ita kuma tana kwance bata farfaɗoba anyi covery baki da hancinta da oxygen, jinin da aka ɗaura mata ne yake ɗigowa da kaɗan kaɗan, yanzu ledar jini huɗu ta sha..

☆☆☆☆☆

bayan isar su Ayush gida, Rumana ce ta nemi guri ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana kallon plasman dake film ɗin turawa ake showing..
Aditi kuma wuce room ɗinta tayi tana faɗin "yunwa nake ji a nema mun abunda zanci kafin na fito.."
Angel ce ta kalli Ayush tace "to ki cire wannan ƙaton hijab ɗinki mana..." tasa hannu ta cire mata shi, itama Ayush ɗin zama tayi tana kallon, Angel kuma ta nufi kitchen zata dubo musu abun taɓawa,

cikin sa'a kuwa ta samu ferfesun chicken a cikin ƙatuwar kula da zafinsa, haka ta ɗauki kular gaba ɗaya ta fita dashi falo da plate guda huɗu, tazo ta zuzzuba musu ta ɗauko lemuka masu sanyi a cikin frig
Aditi fitowarta kenam ta tarar an shirya komai na abinci, ta zauna tareda janyo plate da lemon a gabanta, suma sauran ɗauka sukayi suna ci ba wanda ya kula kowa a cikinsu,
Ayush daƙer take cin domin bata jin cin komai saboda damuwar da ya sakota a gaba, kafin ɗan seconni Aditi ta gama da nata tace "ni saboda an raina mun wayo sai a sako mun chicken ɗan kaɗan kenam.." Angel ta kalle ta tace "yanda nasa miki haka na sawa kowa, acici mala'ikun tauna" a fusace Aditi ta tashi ta buɗe kular ta cika plate ɗinta dashi kafin ta zauna nan ma ta cinye tass, sauran kuma duk ba wacce ta iya cinye nata,
bayan sun kammala tsab Rumana ta cigaba da kallonta domin bata son draman ya wuce ta, Aditi ce itama ta zauna saman sofa tareda ɗaukar remote tana faɗin "mai zamu kalla a masu korayen idanuwa.." ta canza film ɗin da Rumana take kalla, ta sauya da film ɗin china.
Angel tazo gaban Rumana ɗaukar sauran chicken dake cikin kular! Rumana ta wani canki kular da ƙafarta sai ferfesun ya kwacaɓe a jikin Angel duk ya ɓata mata abaya gashi mai ruwan milk ne, ita a dole ta fusata ne yasa ta canki kular ta miƙe da sauri tayo kan Aditi zata karɓe remote ɗin,
tana faɗin "ba abunda zamu kalla a masu ƙananun idanuwa..." suka kaure da kokuwa suna dukan juna a tsakanin Aditi da Rumana, sai ga Angel itama ta miƙe a fusace tayo gurinsu, ɗago kafaɗar Rumana tayi ta zazzabga mata mari a fuska har sau huɗu tace "ke makahuwa ce kina kallo kin mun wanka da miya amma ko a jikinki?..."
Rumana hannu takai itama zata mari Angel tayi saurin riƙe mata hannu tareda ƙara zabga mata mari, daiden lokacin Aditi ta ɗago sawayensu gaba ɗaya ta wantsila su gaba ɗayansu,
daman haushinsu take ji gaba ɗayansu, a fusace Rumana da Angel suka taso suka cakumi Aditi, faɗa suke a junansu, wannan ta naushi wannan! Wannan ma ta kirɓa wa wannan naushi haka suka kaure gaba ɗayansu kuma kowa duka yake kaiwa ɗan uwansa, duk wanda ka samu zaka daka acikinsu...

Ayush kam kallonsu ta tsaya yi a tsorace, har jikinta ya soma ɓari yana kakkarwa sosai, ta kasa ce musu ƙala saboda tana tsoron kar suyo kanta tinda taga duka suke kaiwa junansu,

ɗakin yayi kaca kaca ga ferfesun kaji a kwance saman carpet, lemon da ba'a rufe ba duk sun zuzzube a ƙasin carpet,
saida suka sha dambensu suka gaji kowa jikinsa yaji masa, jiki duk ba ƙarfi Aditi ta miƙe daƙer ta ciro bindigarta daman koda yaushe basa rabuwa da bindiga,
kunna kunamar bindigar tayi ta saita kan Angel da shi daman tin ba yau ba tafi jin haushin Angel da kuma yawan shishigewa Junaid da take,

itama Rumana tashi tayi ta ciro nata ƙaramin bindigar ta saita kan Aditi dashi,

murmushi Angel tayi itama tasa hannu a aljihun abayarta ta ciro tata bindigar itama ta kunna kunamar ta saita goshin Rumana da shi,

kowa duk wanda yafi jin haushi akansa ya ɗora bindigar,

Rumana ta ɗora bindigarta akan Aditi,
Aditi ta ɗora bindigarta akan Angel,
itama Angel ta ɗora tata bindigar akan Rumana...

suna haki sosai duk sun bi sun gaji,
Ayush kam ganin kowa ya fidda bindigarsa ta zaro manya-manyan idanuwanta sosai, daga bisani tabi kan kujera ta kwanta sumammiya.....

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 005 ➡️ 006


Rumana ce ta fara sauƙar da bindigarta ƙasi tana huci ta nufi ɗakinta domin ba ƙaramin gajiya tayi ba, tana buƙatar hutawa, ganin Rumana ta tafi itama Angel ta sauƙe bindigarta tana kallon Aditi wacce har yanzu bindigarta akan Angel yake bata sauƙe ba,
Angel hararar ta tayi sannan tasa hannu ta ture bindigar tana faɗin "sha sha shaa marar aikin yi.." Aditi tana haɗe da gira ta sauƙar da bindigar tana huci itama ta nufi ɗakinta,
Angel gurin da Ayush take a sume ta nufa tana zuwa ta lanƙayo da hannunta ta wuyanta sannan ta riƙe kunkuminta ta ɗagata sama suka nufi upstairs a hankali suke taka matakalar har suka isa ɗakin Ayush,
kwantar da ita Angel tayi a saman gadonta, sannan ta rufe mata ƙofar d'aki ta sauƙa down,
ƙarewa falon tayi da kallo taga yayi kaca kaca, ɗago da kanta tayi tana kallon agogon bango ƙarfe 12 yanzu na dare, da haka Angel ta gyara falon nan tas, ga baccin da yake shirin kwasheta...


WASHE GARI
Junaid yana zaune a room ɗin da mommy take, kwatsam sai yaji mommy tana faɗin "burina shine naga na haɗa soyayyar Junaid da Ayush, inaso naga sunyi Aure sun hayayyafa, Allah ka cika mun burina ko bayan raina ne..." haka mommy ta rinƙa sambatun nan ido a rufe ga wasu siraran hawayen da suke faman gangaro mata, kamar wacce take mafarki..

Junaid ne ya tashi sannan ya koma bakin gadon ya zauna yana riƙe da hannunta yace "Mom! Mom!! Mom!!!..." haka yake ƙiran sunanta silently wannan ƙiran ne ya ratsa cikin dodon kunnenta a hankali take buɗe ido tana ganin dishi dishi har idon ya washe, juyo wa tayi tana kallon Junaid wanda shima ƙura wa mommy ido yayi, daga bisani ta sau masa murmushi tareda kai wa hannunta tana shirin cire oxygen dake kife a bakinta da hanci,
da sauri Junaid ya riƙe hannunta yace "karki cire, bari na ƙira doctor"...
yana kaiwa haka ya fice daga cikin room ɗin da saurinsa..

Doctor ne yazo duba mom, har ya cire mata oxygen, ya lanƙaye ledar jini a sama, ya gama tream ɗinta sannan ya tabbatar da yanzu ta ɗan samu sauƙi amma ba za'a sallameta yau ba..

suna cikin wannan halin saiga su Angel sun shugo su uku kowacce tana riƙe da kayan fruit a hannunta, kowa ya sha makeup sosai kamar ba su ba,
suna shugowa suka nemi guri suka zaune a kujerun ɗakin tare da gaishe da mommy da jiki,
Junaid ne yake lelleƙawa ko zaiga Ayush amma bai ganta ba, amma ya kasa tambayarta haka yaja baki yayi shuru...

Mommy ce take kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan tace "ina Ayushert?..."
Angel ce ta buɗi baki tace "Mom mun barta a gida saboda kanta ne yake mata ciwo..."
ajiyar zuciya tayi ta lushe idanuwanta sannan ta buɗesu a hankali murya ciki-ciki tace "nidai inason ganin Ayush ɗinta, buɗe ƙofar ɗakin akayi aka shugo tareda yin sallama, gaba ɗayansu waiwaya wa sukayi suna kallon bakin ƙofa, doctor Hasheem ne da kuma Lailah tazo ziyartar mommy, ƙarisa shiga ciki sukayi suna gaisawa da mutanen wajen tareda tambayar jikin mommy, neman guri sukayi suma suka zauna,
Lailah dai yanda take kallon ƴanmatan ƙasashen wajen nan da mamaki acikin ranta take faɗin "ni waɗannan su waye ne? kuma mai sukeyi a gidansu Junaid?..." da tarin tambayoyi a bakin Lailah still idonta akan su...

Mommy ce ta ƙara furta "Ina son ganin Ayushh ku kawo mun ita dan Allah"
Junaid yana riƙe da hannunta yace "don't worry mom, till tomorrow you will see Yushert..." mommy ta katse shi da cewa "till tomorrow? please go and find Ayush for me my son.."
Junaid kawai cewa yayi "okay..." ya miƙe tsaye yana kallon gurin da su Angel suke a zaune yace "ku zauna mun da mommy zanje na taho da Yushert.." Angel ce kawai ta amsa masa amma Aditi da Rumana kawar da kansu sukayi gefe suna haɗe rai, Rumana kam har idonta ya cicciko domin tana jin baƙin cikin rashin kulawar da Junaid yake bata, tinda tazo gidansu in banda ranar data zo ba bai taɓa fakewa da ita sunyi wasu maganganu na fahimta ba...

Junaid fice wa yayi daga cikin room ɗin zaije gida domin tahowa da Ayush, har zai buɗe murfin motar da su Angel sukazo da ita saiga Lailah ta fito da gudu tana faɗin "wait Ogah Junaid..." ta ƙaraso gabansa tana haki irin wacce tayi gudun nan ta gaji tace "dan Allah ka temaka ka tafi dani..."
kawar da kansa yayi yana shirin shiga cikin motar ta kuma cewa "dan girman Allah Ogah Junaid..."
katseta yayi da cewa "meye dalilinki nayin haka?.." har saida ƙirjinta ya buga ta zaro ido waje tace "menayi Ogah Junaid?"
ita a tunaninta abunda sukayi wa Ayush ne yake tambaya,
Kallonta yayi sannan yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login