Showing 147001 words to 150000 words out of 186041 words
mu mukayi control ɗinta ta sanya gobara agidan da take ta hanyar amfani da maciji tinda shi ba Aljani bane, saidai munyi rashin nasara matar da muke so ta mutu an ceceta,
Kuma bazamu taɓa barinka kayi Aure ba shiyasa muke control ɗiyarka akan karta bari ayi Auren,
kuma matarka mu muka sanyata ta mutu ta hanyar Munafurr, munyi rashin nasara akan Junaiduu, wannan macijin da muka sanyawa ɗiyarka da zaran ta haihu zamu sheƙeta sannan mu ɗauke Jaririn, kuma munyi alkawarin kaima sai mun janye jinin jikinka...."
wani irin haɗiyar yawu sarki Raamud yayi duk ya haɗa gumi,
Artaff yace "Baƙin Aljani muna neman Alfarma daka bar alhalin nan tinda basuyi maka komai ba, sarki Raamud shine mai laifi kuma shima muna neman yafiyarka akan ka barshi haka..."
Baƙin Aljani yace "Artaff duk da nasan kaima acikin ahalin kake amma banyi garajen shiga rayuwarka ba sakamakon kayi karatu ne agurin babban malamin Aljanu kuma muna matuƙar jin maganarsa don haka kaima zamu saurari maganarka albarkacin babban malami..."
Artaff yace "Nagode Baƙin Aljani amma ka barshi yayi Aurensa sannan yarinyar nan ka barta haka, tanada zuciyar imani kar ka sanyata ta zamo munguwa,
Ata sanadiyarka ta zauna agidan kurkuku kuma karka taɓa mata yaran da zata haifa, na roƙeƙa idan har nima zakaji maganata to kabar mun Ahalina..."
Baƙin Aljani yace "shikenam! Shikenam zamu tafi mubar maka ahalinka amma kada a sake neman mu..."
Artaff yace "babu wanda zai sake hulɗa daku acikin Ahalina nayi maka alƙawari..."
Ayush tana kwance bata san awani duniya take ba Baƙin Aljani ya ɗagota sama da hannu ɗaya sannan ya ɓace da ita ɓatt!!!
Junaid a zabure yayo gurin da Baƙin Aljani ya tsaya sai ƙwalla ƙiran Ayush yake yana faɗin "Ina Yushert take, ina ya kaimun ita, Yushertttt! Yushertttt!! Yushertttt!!! ya tafi mun da ita, Uncle! Uncle!! kayi wani abu dan Allah kasa ya dawo mun da ita please 🙏 please 🙏...."
Uncle Artaff yazo gurin da Junaid yake ta surutai kamar wani taɓaɓɓe ya dafa kafaɗarsa yace "ka kwantar da hankalinka Junaid bawai ya tafi da ita bane, kaje ɗakinku zaka sameta cikin ƙoshin lafiya..."
Junaid yana jin haka ya ruga da gudun gaske ya haura Upstairs, yana zuwa yasa hannu da ƙarfi ya bankaɗa ƙofar kwatsam saiya tarar da Ayush kwance akan katafaren gadonsu sai sharar bacci take ga kuma cikinta shima yana nan lafiya, da sauri ya ƙarasa wajen gadon ya ɗale tareda rungumota jikinsa da ƙarfi kamar wanda za'a ɗauketa, yayi shuru yana rungume da ita ....
Shi kuwa Uncle Artaff masifa ya shiga yiwa Abbah yana faɗin "gashi yanzu duk saboda kai waɗannan bala'in suke faruwa akan ƴaƴanku, saboda abun duniya ka sadaukar da rayuwar ƴaƴanka haba wannan wani irin rayuwa ne, abu yaƙi ƙarewa tin shekarun baya, daga wannan masifa sai wannan, Aljanu ne suke ta bibiyan rayuwar ahalin mu duk saboda kai, gashi ka jefa rayuwar ɗiyarka cikin masifa badan anyi gaggawar dakatarwa ba, yanzu inda ban ankara ba sai ta haihu su kasheta kuma a rasa dalilin mutuwar ta sannan su ɗauke jaririn, ina fatan Allah ya kawo mana ƙarshen wannan abun daga yau,
Auren da kakeso kayi da bazasu taɓa barinka kayi ba kuma kuzo kuna ganin laifin yarinya alhalin ba ita take control kanta ba..."
Sarki Raamud tagumi yayi yana zubda hawaye kamar wani ƙaramin yaro,
Uncle Artaff ne ya nufi frig yaje ya ɗauko ruwan sanyi yazo kan mommy ya yayyafa mata a firgice ta farfaɗo tana addu'a, yazo kan matarsa itama ya yayyafa mata, har zai zauna ya hango ƙafar mutum ta bayan kujera zuwa yayi ya leƙa yaga Judan a zaune yana rungume da Hafzat wanda shima alamun a sume yake, suma haka yabi duk ya wawwatsa musu ruwan, a firgice suka farka suna jan numfashi, zuwa yayi ya zauna yana binsu da kallo, mommy ce tayi magana tareda faɗin. "wai meyake faruwa ne? wallahi bansan ya akayi ba muna cikin magana bacci ya ɗauke ni..."
Aunty Zainab itama magana tayi tana bubbuga goshinta tace "nidai kafin na fito nasha maganin mura ne, ina tunanin shine yayi mun aiki yanzu..."
Hafzat ganinta a jikin Judan yasa tayi saurin tashi tsaye a zabure tana faɗin "meye haka kuma, me kamun? na shiga uku yau nine ajikin ƙaton gardiii..." ta fashe da kuka tareda nufan ɗakinta da gudu cikin jin kunyar kanta.
Shima kansa bai san taya hakan ya faru ba, mamakin kansa ya shiga yi, jiki a sanyaye ya miƙe tsaye yana tangal-tangal kamar mai shaye-shaye haka ya nufi ɗakinsa,
Uncle Artaff ne ya miƙe tsaye tareda cewa ku jirani ina zuwa! haka ya haura upstairs ya nufi ɗakin su Junaid, yana zuwa ya tarar da ɗakin a buɗe ko tsaya rufewa Junaid baiyi ba, Uncle Artaff ne ya shiga ɗakin da sallama a bakinsa, tarar da Junaid yayi yana ƙwance ya rungumi Ayush a jikinsa, yaje har inda gadonsu yake yace "Junaid insha Allahu daga yanzu bazaku ƙara samun wata matsala akan Ayshert ba, abubuwan da tayi a baya ba yin kanta bane kuyi haƙuri, yanzu dai zamu tafi gida gobe kazo gidana zamu tattauna akan maganar Auren Mamanka da kuma sarki Raamud, kuma nasan yanzu Ayshert bazata farfaɗo yanzu ba sai zuwa cikin dare, idan kuma ta farfaɗo zata tashi da ciwon cibiya saboda wannan macijin tanan ya fito, ga wannan ka ɗiga mata a cikin cibiyar da zarar ta farfaɗo...."
ya ajiye wani ɗan ƙaramin ƙwalba kamar na miski akan drawer sannan ya fice daga ɗakin,
Junaid duk ya saurari abunda yace haka suka cigaba da ƙwanciyar yana rungume da ita...
Shi kuwa Uncle Artaff sallama yayi dasu Mommy akan zasu tafi,
Mommy tace "ku tsaya mana ku ci abinci yanzu zan girka, suka ƙi zama haka suka tafi,
Su Mommy duk abubuwan da suka faru sun mance an goge musu shi acikin kwakwalwarsu kuma ba kowa bane face Baƙin Aljani domin ba kowa bane yake kallonsa balle su bada labarin suffarsa...
Sarki Raamud shima jiki ba ƙwari haka ya nufi part ɗin sa, mommy ta ɗauka akan zazzaɓinsa ne ya dawo masa.......
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 76 to 80
Misalin ƙarfe 2Am cikin dare Junaid yana rungume da Ayush ɗinsa ko bacci bai samu damar yi ba, yaji Ayush sai mutsil-mutsil take tayi sai a lokacin ta farfaɗo, ba abunda take faɗin sai "Dan Allah ku ƙyale ni, ku maida Ni gida! shin ina zaku kaini wayyo mommy..." a ruɗe Junaid ya ɗagota tareda shashshafa fuskarta yana cewa "kinga Yushert ki kwantar da hankalinki babu inda zaki je, buɗe idonki Yaya Junaid ɗinki ne a gabanki..."
A hankali take kokarin bude eyes dinta ganin Junaid yasa tayi murmushi tareda fadin "kenam mafarki nayi?.."
Jinjina mata kai yayi tareda kai mata sumbata akan goshi, yace "are you okay?..."
'Daga masa kai tayi alamar babu komai, ta d'ago zata tashi zaune ta saki wani irin 'kara tare da kama saitin cikinta sai faman shushshutu take,
Ri'keta yayi yana fadin "sorry my dear kiyi a hankali.."
tace "cikina ciwo, inaso naje toilet ne". yace " ok let me carry you..." yasa hannu ya d'agota kamar wanda ya d'auki jaririya ya nufi toilet da ita, yana shigar da ita ta sau'ka tareda cewa "toh jeka waje ka jirani.."
d'an turo baki yayi yana binta da kallo yace "ok don't worry maman Baby..." murmushi tayi tasa hannu tana kare fuskarta cikin jin kunya...
shi kuwa ficewa yayi tareda rufe mata ƙofa, kai kawo ya fara yi a Cikin ɗakin yana jiran fitowar ta, ƙwatsam kunnuwansa suka jiyo masa sautin ihunta daga cikin toilet, Da gudun gaske ya tura ƙofar cikin zafin nama a rikice ya shiga ya sameta a tsaye sai ihu take tayi, rungumar ta yayi yana faɗin "kinga Yushert kiyi shuru ki sanar mun meya faru?..." ita kuwa babu bakin magana sai nuna masa cikin toilet take da yatsa.. ido ya zaro yana kallon wajen, cike da mamaki yace "fitsarin jini kuma?.."
ƙara rungumeta yayi tareda ƙwantar da kanta saman kafaɗarsa yana rarrashinta, murya ciki yace "muje bedroom.." suna takawa a hankali har suka fita!
jikin Ayush ne yake kakkarwa kamar wacce aka zuba mata ruwan ƙanƙara, zaunar da ita yayi a bakin gado sannan ya lalumi wayarsa yayi dialing call number Uncle Artaff, cikin ƙanƙanin lokaci ya ɗauka a ruɗe ya soma faɗin "Hello Uncle akwai matsala fah! Fitsarin jini take.."
Daga ɓangaren Uncle kuma cewa yayi "haba Junaid ka kwantar da hankalinka mana, sai kace ba namiji ba duk wannan ba matsala bane, in tayi kwana uku tana yi shikenam, amma ka shafa mata wannan ruwan ƙwalbar dana baka.."
Junaid ya amsa da "toh shikenam Uncle"
Uncle yace "miƙawa Ayshert wayan..". Junaid kara mata wayar yayi a kunne tareda faɗin "kiyi magana Uncle ne.."
Cikin fargaba da tsoro ta karɓi wayar tareda ƙara fashewa da sabon kuka, daƙer Uncle ya samu ya shawo kanta yana rarrashinta, shuru tayi tana sauraron duk maganar daya gaya mata sai yanzu hankalinta ya kwanta jin Uncle yace daman idan mace ta kusan haihuwa haka take fitsarin jini,
daga baya suka katse wayar, ta kalli Junaid tana sauƙe ajiyar zuciya tace "har naji daɗi a raina, amma na tsorata sosai..."
Murmushi Junaid yayi tareda shafar gefen fuskarta shi dai yasa Uncle ya gaya mata hakane saboda hankalinta yafi kwanciya, tashi yayi ya nufi toilet yaje ya wanke sannan ya haɗa mata ruwan zafi yanda zatayi wanka, dawowa cikin bedroom yayi sannan yasa hannu ya ɗauketa tareda nufan cikin toilet da ita yaje ya mata wanka tass ya fito da ita tana ɗaure da White towel, ya zaunar da ita akan kujerar gaban mirror yace "toh kiyi mun kwalliya mai kyau kafin na fito daga wanka nima..."
ya sumbace ta akan lips ɗinta sannan shima ya wuce cikin toilet ...
Kafin ya fito kuwa har tayi kwalliya kundai san kalar kwalliyar Ayush daga powder ne sai lips cream, shikenam sai turaruka data feffesa da gyaran gashin kanta tayi rolling dashi, sannan taje ta buɗe wardrobe ta ciro doguwar riga marar nauyi mai hannun breziya ta zura daga nan ta haura saman katafaren gadonsu tana jiran fitowar Oganta,
Can shima ya fito ɗaure da towel cikin rashin sa'a ya tarar da ita har tayi bacci,
kallonta yayi sannan yayi murmushi cikin so da ƙaunarta, shima ya shirya tsab kafin ya hau gadon saida ya shafa mata wannan maganin akan cibiyarta kafin ya kashe musu White light zuwa dark green lamp, ya ja musu mayafi...
★★★★★★
*TWO WEEKS AGO*
Sauran sati biyu ƙarshen month tafiyar Junaid da Judan ƙasar california,
Komai yana kan tafiya daidai,
Judan da Hafzat ƙullalliyar alaƙa ne ya shiga tsakaninsu, yanzu koda yaushe suna tare hatta kitchen ma tare suke shiga suyi girki, mommy data fahimci haka tabar musu girkin gaba ɗaya, Judan baya so yayi nisa da Hafzat inba sallah ba, sai kuma wajen kwanciya shima dole ne tasa suke rabuwa, sai idan zata tafi school..
Itama mommy An yanke ranar da za'a ɗaura musu Aure ita da sarki Raamud, ranar Jumma'at mai zuwa, sarki Raamud baiso akawo wannan lokacin ba'a ɗaura Aure ba, mommy ce ta dage akan cewa sai Ayush ta haihu tukun tayi Aure, yanzu kuma an tabbatar da cewa a cikin wannan satin Ayush zata haihu,
Duk wani kulawa Ayush tana samu daga ɓangaren mommy da shi kansa Junaid har Abba, tana jin daɗin kasancewa tare dasu, duk abunda take buƙata indai ata ɓangaren abinci ne toh shi ake mata...
Around 12 0'clock na dare Ayush tana zaune akan sallaya bayan ta idar da sallar dare tana jan carbi, shi kuma Ogah Junaid yayi shame-shame akan gado sai shan baccinsa yake, bai ma san Ayush ta tashi ba har tayi sallah daman kullum saita tashi cikin dare tayi sallah,
tana zaune kwatsam sai taji cikinta yanata juyawa da ƙarfin gaske, wani irin ƙara tayi game da kama cikin tana hura iskar bakinta a wahalce, wani ruwa taji yana ƙoƙarin zubo mata kamar meyin fitsari dasauri ta janye sallayar da take kai ta wurga gefe, nan danan rigarta ta ɓaci da jini, ga paya ta fashe wani irin murɗa take ji ga raɗaɗin ciwon ciki, gaba ɗaya ta fara fita hayyacinta, daƙer ta rarrafo bakin gado tasa hannu tana bubbugan Junaid dake ta shan baccinsa, shuru ko motsawa beyi ba, haka take kuka tana ta faman jijjigansa saidai yeyi juyi ya sake komawa bacci, ƙiran sunansa take a wahalce tana faɗin "Yaya Junaid ka tashi mana, cikina ciwo wayyo Allah, Yaya Junaid zan mutu ka tashi dan Allah, ka temaka mun cikinaaa..."
Junaid kuwa baima san tana yi ba, wani irin nannauyar bacci ne ya ɗauke shi,