Showing 57001 words to 60000 words out of 186041 words
tsaye toilet ta nufa ta tsaya a gaban mirror tana kuka tareda faɗin "Umma! Umma ki fito mana, meyasa bana ganinku a cikin madubi yanzun, dan Allah ki fito akwai mayaƙan da suke son ganin bayanku, ku gudu, ku gudu dan Allah banaso na rasa ku, ina Narasimha kuce ya ɗauke ku....."
Fashewa tayi da wani matsanancin kuka har saida ta durƙusa da gwiwowinta..
Bayan su Mommy sun isa headquarters itama kukan take sosai na tafiyarsu Junaid, Angel itama kukan take saboda basu san mai zasu tarar ba agurin yaƙin, Junaid ganin yanda Mommy taketa kuka yasa jikinsa yayi sanyi, murya a sanyaya yace "Please Mom ki koma gida zamuyi waya..."
Daƙer Junaid ya rarrashi Mommy ta hau mota ta koma gida.
Duk sojojin da za'a tafi dasu sun shishshirya kowa yana ɗauke da jakarsa na kakin soja, jirgi biyu ne suka tashi, jirgi na farko ya daɗe da tashi tin kafin su Junaid su iso,
suma yanzu jirginsu ya tashi...
Mommy tana komawa gida itama ta nufi ɗakinta ta kifu akan gadonta tana kuka tareda addu'ar Allah ya dawo mata da ƴaƴanta gida lafiya,
Ayush ce ta sauƙo daga upstair tayi wankan ta cikin doguwar riga na material idonta yayi lufu-lufu ya kumbura tsabar kukan da tayi,
waran dinning table taje ta zauna ta buɗe kula ta zuba abinci a plate don saida ta totsa plate ɗin da abincin tukun ta fara tura shi daman ba ƙaramin yunwa take ji ba,
*BAYAN WASU AWANNI JIRGIN SU JUNAID YA ISA ƘASAR CALIFORNIA...*
an tanadar musu da wani makeken hotel wanda zai iya ɗaukar duk sojojin da suka zo, sun ci sun sha saida suka ƙoshi tukun kowa yaje ya kama ɗakinsa,
Ita dai Angel ta tanadar musu da ɗaki ɗaya ita da Junaid, kafin a tafi yaƙin,
Misalin ƙarfe 12 na dare Junaid yana kan wata doguwar kujerar ɗakin yana ta faman danne dannen computer, ita kuma Angel tana kwance akan gado tana karatun littafi na English, babu wanda ya kula kowa a ciki sai sukaji ana Knocking Angel ce tace "waye ne?..."
daga waje aka bada amsa cewa "serjan Umar ne nazo gurin Ogah Junaid.."
Angel tace "toh coming..". buɗe ƙofar ɗakin akayi ya shigo da murmushi a fuskarsa ya nufi gurin Junaid yana faɗin "Ogah ga ƙaramin gun ɗinka ka manta dashi..." ya miƙa masa sannan ya juya yayi ficewarsa,
Angel ce ta ciro bread da bota a cikin jakarta tace "My man sauƙo muyi kumallo amadadin abun ƙaryawar safe..
Junaid ne ya kalli agogo yaga ƙarfe 12 da rabi yace "Ni ba abunda zan ci yanzu, ki ci abincinki.."
Tace "amma kasan da asuba zamu fita yaƙi koh? ba lokacin cin abinci, ka daure kaci dan Allah..."
cigaba yayi da danna computer ba tareda ya ce komai ba, ita kuwa sauƙowa tayi ta fara cin abincin ta cikin nutsuwa, lokaci guda kuwa sukaji an turo ƙofa da ƙarfin gaske saida Angel ta tsorata, shima Junaid ɗagowa yayi yana kallon bakin ƙofa fuska a haɗe, tsuka yayi ya girgiza kansa tareda faɗin "ai daman nasan ba wanda zaiyi wannan aikin sai ke..." ya ƙarasa maganar yana danna computer sa...
Aditi ce ta shugo a hanzarce tace "daman anan kuka fake, tinda na iso nake ta nemanka" ta juyo tana kallon Angel cikin fushi tace "ke kuma sarkin son maza kun zauna ɗaki ɗaya kamar miji ki mtts..."
Angel tana zaune tana cin abincin ta ko kulata batayi ba, acikin ranta tace "oh wannan bazata taɓa canzawa ba.."
surutun Aditi duk ya ishesu Junaid ne ya miƙe tsaye yana faɗin "meye matsalar ki ne Adity?..."
Adity tana huci tace "bazaka kwana da mace a ɗaki ɗaya ba..."
Yace "kina tunanin wani abu zai faru ne?.."
tace "eh zata koya maka kwartonci ne, nidai nasan Ogah na ba ƙwarto bane, amma naga sai shishshige maka take tayi..."
Angel ta tashi itama a fusace tace "wacece kwartuwa? ki shiga hankalinki wallahi..."
kafin Angel ta rufe baki Aditi takai hannu ta naushe mata baki!
Adity tana zaro ido tace "bana juran raini..."
Angel hannu biyu tasa ta toshe bakinta wanda tunin har ya fashe,
Junaid yace "Adity meyasa baza kiyi hankali ba? ku daina wannan shirmen kamata yayi kuje kuyita addu'a akan yaƙin nan gobe da asuba mah mun rigada mun tafi..."
Junaid bai ƙarasa maganarsa ba itama Angel ta kawo hannu ta zabga mata mari a fuska nan suka kaure da kokuwa,
Junaid tsuka yaja yabi ta gefensu ya fice a ɗakin kai tsaye ɗakin wani Abokinsa ya nufa yana zuwa kuwa ya shige ..
Angel da Adity faɗa suke yi sosai gaba ɗaya sunyi kaca-kaca da ɗakin saida sukayi mai isar su tukun suka rabu, Amma saidai Angel tafi jin jiki domin ita Adity naushi kawai take yi, Adity tashi tayi tana zage-zage ta fice a ɗakin, Angel kuwa kanta a kife ta gagara ɗagowa ma, sai can bayan fitar Aditi itama ta tashi daƙer ta shige toilet tayi wanka sannan ta ɗauro alwala tazo tayi sallah tareda addu'o'i tana zaune akan sallaya bata rintsa ba har asuba ta tashi tayi sallar asuba sannan ta miƙe ta shirya cikin kayan sojoji saida ta shirya tsab sannan ta ɗauki bindigarta ta fice a ɗakin tana mai fushi da Junaid akan ya barta yayi tafiyarsa, tana maganar zuci tace "mutumin da bai damu dani ba, a haka Mommy take cewa zata haɗa mu Aure, yanzu inda Ayush ce bazai barta tayi faɗa da wata ba har aji mata rauni...." ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye da haka har ta fita filin da zasu taru, duk safikonta saida ta samu sojoji da damarsu sun fiffito suma kowa yana riƙe da bindigunsa,
Bayan minti talatin saiga Ogah Junaid shima ya fito cikin kakin soja yana rataye da wata ƙatuwar bindiga shima layi ya shiga domin kafin a tafi sai anyi wasu jawabai, yana tsaye saiga Ogah Rumana tazo gabansa itama cikin kayan soja tana mai farin cikin ganinsa shima murmushi yakeyi suka gaggaisa daga baya ta koma gurin tsayuwarta, saiga Adity itama tazo tana faɗin "waini wannan jan ƙyallen goshinka na meye ne? ko asiri kayi ne na yaƙar matsafi?.. "
kallonta yayi sannan ya kawar da kansa gefe yace "ni ai babu ruwana dake tinda bakya jin magana..."
Ogan su Adity ne ya daka mata tsawa akan ta koma gurin tsayuwarta, turo baki tayi ta koma,
Angel kuma duk abunda sukeyi akan idonta ne ita kaɗai sai fushi take tayi,
tayi alkawarin bazata kula Junaid ba har su kammala yaƙin su...
*****
Sarki Raamud gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake yanda Munafurr ya kullesu a ɗaki, Uma Bara'at ba abunda take sai kuka, suna zaune akan gado tace "dan Allah Sarki ka nema mana mafita, na gaji da zaman kaɗaici, ka duba mana ɓoyayyar hanyar da zamu gudu dan Allah..."
Sarki Raamud yayi ajiyar zuciya sannan yace "kiyi haƙuri mu cigaba da zama har Allah ya kawo mana ɗauki, yanzu idan mukace zamu gudu Munafurr bazai barmu ba saboda yana kallon mu kinsan shi yana aiki da tsafi ne! kuma Damusa yana can a ɓoye guri guda fatana kar munafurr yasan da zaman Damusa Sujjur domin bazai barshi da rai ba, banaso na gudu nabar Damusa..."
tana kuka tace "bamuda mafita kenam?.."
yace "babu mafita sai abun da Allah ya tsara mana..."
Uma Bara'at gaba ɗaya ta zamo kalar tausayi ta kwanta akan cinyarsa, shima rarrashinta yake yana bata baki tareda kwantar mata da hankali, ga cikin twins a jikinta har ya girma domin cikin bazai wuce 7month ba...
Ta Ɓangaren Munafurr kuma sai zabga uwar dariya yake ganin yanda aka haɗa rundunar sojoji ta cikin madubi yake kallonsu, su sojoji tunaninsu shine zasu tarar da sarki Raamud ne,
Munafurr magana yake a tsawace yana faɗin "bazaku iya baaa, bazaku iya dani baa, nafi ƙarfinku ƙananun ƙwari Hhhhh..."
Shi Munafurr ko damuwa da zuwan sojojin nan baiyi ba saboda murƙusa ɗaya kawai zaiyi musu ya gama da rayuwarsu...
Zaman sarauta yayi sannan ya tura macijensa suje su buɗe babban gate yanda sojojin zasu ji daɗin shugowa,. cikin gaggawa kuwa macije sunfi million duk sun hallaru a harabar masarautar bayan sun buɗe gate ɗin layi sukayi domin dasu za'a fara yin yaƙin kafin azo kan ogan nasun wato Munafurr,
shi kam sarki Raamud bai ma san za'azo yaƙar shi ba...
Rundunar motor Egwa ne na sojoji sun kai dubu ɗari suka tunkaro masarautar...
(Egwa pah masu bindigu a saman mota, mota mai kakin soja wanda bindigarsu yake bada harsashin wuta😳😳)..
A bayan motocin Egwa kuma still motar sojojin ne suma sun tafo a jere zasu kai su ɗari biyu iya motoci kawai suma masu jikin kakin soja suna tattare da boma-bome masu tarin yawa,
Angel da Adity da Rumana su duk ɗin su suna daga cikin motocin indai macen soja ce toh tana cikin mota...
A bayan motocin kuma sai waɗanda suka hau Dokuna🐎🐎🐎🐎🐎!
wasu Dokuna ne masu ƙirar ƙarfi, ɓaƙaƙe dasu suma zasu kai su dubu ɗari, waɗanda suka hau Doki an ware ƙarfafan sojoji ne jarumai aciki kuwa har da Ogah Junaid, shima yana daga saman Doki....
A bayan Dokuna kuma taron sojojine waɗanda suke tafe da ƙafafuwansu, sai gudu suke ci da bindigoginsu a hannu....
Saman su kuma elekwabta🚁🚁🚁🚁 ne mai kakin soja zasu kai guda hamsin suma sojoji ne aciki
(Ikon Allah duk wannan gayyar a mutum ɗayane🤔🤔)
Shima Munafurr ya haɗa gayyarsa wato wani irin shiri yayi musu,
Manya-manyan Jegaru ya nemo masu aman wuta da fikafikunsu sun kai su ɗari biyu a jere a wajen masarautar,
Bayan jegarun nan kuma sai mikiyoyi masu carkwane idanun mutane suma sun kai su ɗari biyu ajere..
Bayan su kuma sai kadoji (corocodise) irin masu cinye mutane suma a jere suke sunkai su ɗari biyu..
Bayan su kuma sai Diragogi🦖🦖🦖🦖 suma sun kai ɗari a jere..
Bayan su kuma sai macije masu dafin bala'i, sara ɗaya suke yiwa mutum ya rasa rayuwarsa, suma suna nan a jere sun kai million....
daga su kuma sai a fafata da Munafurrr...
*****
Mommy daga Nigeria Alwala tayo sannan ta tsai da sallolin lafula tareda jero addu'o'i, tana faɗin
"Allah ya tsare sojojin da suka fita yaƙin nan, Allah ya dawo dasu lafiya, Allah ya basu nasara..."
Itama Ayush zuwa tayi tayo alwala itama ta fara sallolinta na neman kariya daga wajen Ubangiji...
tana addu'a Allah ya tsare mata iyayenta domin tasan yanzu mahaifinta bashida wani ƙarfin iko...
Munafurr Allah Allah yake sojojin nan su iso a fara fafatawa, domin ya tanadar musu da abubuwan mugunta, kamar yanda suma sojojin suka haɗa runduna guda...
Har yanzu kuma Damusa yana nan a ɓoye guri ɗaya ga kuma takobi a gabansa....
*Amm nace baa Ina masu fita yaƙi acikin readers nace how market🙌🙌*
*Masoyan Junaiduu ban hango ku ba👀 shin kunata inaa?*
*Cikin Egwa ne ko kuma kuna cikin motoci kodai kuma kuna kan Doki ko kuma kuna daga sama cikin elekwabta kodai kune a ƙasa masu gudu da ƙafafuwan ku?...*
*Masu cikin elekwabta kune gawar farko domin jegaru masu aman wuta furawa suke yi🤣🤣*
*Ga kuma mikiyoyi masu cire eyes😳😳😳*
Toh masu karatu anan zan dakata sannan na tafi hutun sati guda, na barku lafiya...
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 31 ➡️ 32