Showing 33001 words to 36000 words out of 186041 words
ba amma idan bata gaya mun gaskiya ba zan harbeta agurin da zata jikkata,
Doctor Hasheem kaje ka zauna inajin kunyarka fah, banaso ka shiga lissafin da ba naka ba..."
komawa Doctor Hasheem yayi ya zauna domin yasa Angel wani sa'in batada Annuri idan Alluran sojan ta ya motsa...
Durƙusawa ƙasi Lailah tayi tana kuka tareda faɗin "dan girman Allah kiyi mun rai Aunty Angela wallahi banida laifi bansan komai ba, kuma bansan wanda ya tura video baaa.."
ta ƙarasa maganar tana kuka.
tsawa Angel ta darara mata tace "kiyi mun shuru, ai Lailah kin ƙara jefa kanki cikin masifa indai baki gaya mun gaskiya ba, taya kika san an tura video?..."
Shuru Lailah tayi bata ma san ta faɗin hakan ba,
ƙiƙƙina ta soma yi maganar ta na rawa ba'a jin abunda take faɗa ma, tsabar rikicewar da tayi..
A fusace Angel ta tashi taje har gabanta ta zabga mata wani irin gigitaccen mari tace "ki buɗe baki kiyi mun magana ko kuma na tafi dake headquarters su Ogah Junaid yanzun nan..."
Girgiza mata kai Lailah ta shiga yi tace "nine na tura video.."
Angel tace"ke ko? to meyasa kika tura? sannan wannan gayen da kuka haɗa baki dashi yazo kuka tozarta Ayush wayene shi?..."
Lailah tace "a'ah wallahi a ɓoye nayi musu basu sani ba, sunyi tunanin na tafi nikuma ɓuya nayi nayi musu, kuma na tura video ne saboda na ceci rayuwar Ogah Junaid domin Ayusher karuwa ce ƴar iska, tana bin yawon hotel..."
Kafin ta ƙarasa maganar Angel ta ƙara zabga mata mari tace "kiyi mun magana cikin ɗa'a, sannan a ɗaukar video nan bai nuna alamar a ɓoye akayi shi ba, a saitin gadon mai ɗaukar yake tsaye yake video..."
Shuru Lailah tayi bata ce komai ba,
tana tunanin mai zatace ne..
Angel tace "kinyi shuru Lailah ko dai kina jiran sauƙar wani marin?.."
A tsorace Lailah ta ɗago tana cewa "wallahi sune sukace na ɗauke su a video sai a turawa Ogah Junaid saboda Ayush bata son Aurensa, wai ita da wanda take so..."
Angel tace "ita Ayush ce tace ki ɗauketa a video?.."
Lailah tayi saurin ɗaga kanta tace "Ehhh..."
Angel tace "toh ita ɗin Ayush wa tace takeso?.."
Da sauri Lailah ta nuna Doctor Hasheem tace "Yayana wai take so..."
Angel girgiza kai tayi tana dariya tace "toh ita kuma mata mai liƙab fah?.."
Lailah tace "wata mata mai liƙab?..."
Angel ce ta danƙwaleta tace "kin ci ubanki, matar da kuka shiga kuka sameta a ɗakin Ayush fah?..."
Lailah ta ɗora hannayenta biyu akayi ta tace "nashiga uku wai meyasa ake son jefani cikin matsala ne, wallahi tallahi wuta bal-bal idan kika tuhumeni akan wata mata kumadu domin banganta ba wallahi ban sameta a ɗakin Ayush ba..."
Angel zaro ido tayi waje tace "Lailah ni ce wuta balbal? bani number mutumin da kika haɗashi da Ayushert munafuka kawai..."
Lailah tace "wallahi banida number saa.."
Kafin ta ƙarisa maganar Angel ta darara mata tsawa tace "ki bani number sa nace miki..."
A tsorace Lailah ta ɗauki wayarta ta lalumo number mutumin ta bawa Angel..
Angel tace "ki tabbatar ba wrong number kika bani ba.."
Lailah cikin kuka tace "wallahi tallahi numbersa ne..."
Angel ta karɓi wayar ta ɗauki number mutumin sannan tayi tracking wayar Lailah saboda duk wayar da tayi zata sani, in ma ta ƙira mutumin ne akan ya gudu Angel zata sani, domin Aikinta ne acikin aikin soja wato yin bincike, da kuma warware matsala,
Yanzu Lailah ta shugo hannu tinda har akayi tracking ɗin wayarta...
Tashi Angel tayi ta miƙa mata wayarta tace "kinji kunya wallahi Lailah, kin kasa haƙura da Junaid shi kuwa ba ke bace a gabansa ba, kina yarinya ƙarama amma kin iya munafurci, duka duka bazaki wuce shekara 18 ba a duniya amma kin iya salon munafurci,
Allah ya temakeki bana zaman Nigeria yanzu dana koya miki hankali wawiya kawai..."
Daga nan Angel tayi tafiyar ta...
Bayan fitar Angel da mintuna 30 Lailah ta ɗauki wayarta ta gudu cikin ɗakinta,
Shi kuwa Doctor Hasheem shuru yayi yana kallonta domin ya gano ko meke faruwa...
Lailah tana shiga ɗakinta ta danna ƙiran number mutumin da ake ƙira da sauro,
Itama Angel tana tuƙi acikin motar taji wayarta tana ring-ging dubawa tayi taga Lailah ce take ƙiran wayar mutumin da ta karɓi numbersa,
Murmushi Angel tayi tareda girgiza kai!
Bugu ɗaya kuwa mutumin ya ɗauki ƙiran Lailah,
Angel ta danna recording sannan tasa a speaker ganan muryar Lailah raɗau a wayar Angel tana faɗin
"Hello Sauro ka samu ka cire sim card ɗinka domin ana bincike akan video danayi muku kai da Ayush wacce Ogah Junaid yake son Aura.."
Cikin Muryar gardawa Sauro yace "kinga abunda nake gaya miki koh? daman nace miki wannan aikin bazan iya yinsa ba saboda bana shiri da a'halin sojoji domin riƙonsu ba kyau, kika sakani dole gashi yanzu kin sakani a cikin matsala.."
Lailah tace "toh naga na baka kuɗin aikinka, nidai yanzu kam ka gudu, shin kana inane?.."
Sauro yace "toh naji amma kafin na sanar miki yanda nake shin soja ta karɓi wayarki?.."
Lailah tace "eh mana ta ɗauki number ka"
Sauro yace "tirrr ƙaramar ƴar boko baki saniba ko tayi tracking wayarki, Ina wannan layin da kika tura video toh ki ƙirani dashi saina gaya miki..."
tace "toh shikenam.."
tana ƙatse ƙiran ta ɗauko ɗayan sim card ta ɗaura ta ƙira Sauro...
Wannan wayan kam kaf Angel taji duk tattaunawar su, murmushi kawai tayi amma saidai taso taji a yanda mutumin yake...
Ƙiran da Lailah tayi da ɗayan number shima Junaid yayi ƙirƙiransa ta yanda zaiji duk wayanda akayi da number ta computer,
yana zaune kuwa yaji ƙira ya shugo computer sa saida ya jira wanda aka ƙira ya ɗauka tukun Junaid shima ya danna record ya sanya abun sauraro a kunnensa yaji duk wayar da suka ƙarisa yinsa tsakanin Lailah da kuma Sauro,
Junaid jinjina kai yayi sannan yace "Lailah! Lailah!! Lailah!!! zaki shugo hannu na..."
Shi abunda ya ƙara rikirkitashi shine ɓacewar wannan matar da Ayush take ƙira da Uma, yana maganar zuci yace "kenam Yushert Aljana ce? daman da Aljana muke zaune? nima abun zai ban mamaki taya za'ace batada zuriya ko ɗaya..?"
Ɗaukar wayarsa yayi ya danna ƙiran wayar Angel bugu ɗaya ta ɗauka tareda cewa "Hello My Man..."
Yace "kina ina?.."
tace "yanzu zan shawo kwanar layin unguwar mu.."
Yace mata "toh ki juya baya yanzun nan Lailah ta ƙira wanda yayi video da Yushert zai tafi airport yace Ghana zai tafi a yau, but ki nemi wasu sojoji a headquarters Kamar guda biyu ko uku kuje tare..."
Tace "toh shikenam yanzu kuwa thanks for help..."
katse wayar yayi yana sauƙe numfashi, ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune ido a lumshe kamar maiyin bacci.....
Ita kuwa Lailah duk wayar da tayi Doctor Hasheem yana laɓe a bakin ƙofa yaji duk wayar da tayi...
*DAN ALLAH BAKWA COMMENT BEFI MUTANE UKU BANE MASU COMMENT, KUMA YAWAN COMMENT ƊINKU SHI ZAI ƘARFAFA MUN GWIWA WARAN TURO MUKU UPDATE AKAI AKAI....*
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 19 ➡️ 20
Sauro yana tafiya sauri-sauri gudu-gudu zai shiga jirgi har ya biya kuɗin jirgi yayi komai zai shiga kwatsam yaji an riƙe masa riga ta baya an jawo shi da ƙarfin gaske, a razane Sauro ya juya yana kallon wanda ya jawo shi ganin macece yasa ya ajiye jakarsa a gefe yana shirin naɗe hannun rigarsa yana dariyar mugunta yace "wato kece kike bin diddigi nah ko? toh yanzu zan sumar dake nayi tafiyata.."
Angel itama murmushi tayi tace "ni ba kalar macen daka raina bane, sai dai ka sumar da wacce kaga zaka iya amma not Angela..."
Da gudu sauro ya tafo zai kai mata naushi a kayi tayi saurin sunkuyawa ta girbe masa ƙafa ya faɗi ƙasi ta naushe shi a kunci...
Shima wuntsilar da ita yayi ya harɗe mata sawayenta da ƙafarsa,
Ganin yana shirin hawa kanta ne yasa tayi wani irin rigingine ta kama hannunsa ta murɗe da ƙarfin gaske saida hannun yayi ƙara, wannan hannun kam ya rigada ya gurɗe, tashi yayi zai gudu itama ta miƙe ta cabki kwalar rigarsa! juyowa yayi ya kirɓa mata naushi a saitin marar ta, Angel bata san lokacin data kurma ihu ba ta kama mararta ta faɗi ƙasi tana birgima,
Shi kuwa sauro har ya zari jakar sa zai shiga jirgi yana shirin tafiya, cikin ƙarfin hali Angel tana daga kwance ta zaro ƙaramin bindigarta ta saita ƙafar sauro ta harbe shi, shima lokaci guda ya faɗi ƙasa yaji shigar harsashi, kama ƙafar yayi yana sowa a wajen,
mutane kuwa suna tsattsaye suna kallonsu sai wani ne daga cikin mutane ya ƙira motar police ta sanar musu cewa ana faɗa a airport, nan danan saiga motar police da sauri suka zo zasu kama Sauro da Angel har sun ɗaga sauro zasu saka shi acikin motarsu, sukazo kan Angel zasu saka mata ankwa suna cewa "waya bata izinin yin harbi sannan suna tuhumarta da cewa waya bata bindiga inba ita ƴar fashi ba ce, duk basu san ko ita wacece ba, basu san ita soja bace, saida wani daga cikin police ya finciki hannunta zai sanya mata ankwa ta zamar da hannun ta zabga masa mari a fuskarsa ta hankaɗashi gefe, gaba ɗayansu police saida abun ya basu mamaki waran su uku sukayo kanta da sandarsu zasu kai mata duka duk su ukun ta girbe musu ƙafafuwa tana daga kwance domin ta kasa tashi tsabar ciwon da marar ta yake yi mata,
Ogan ƴan sanda ne yaje gabanta ya sunkuya yana busa mata hayaƙin tabar da yake zuƙa ya zaro ƴar ƙaramar wuƙa tareda kai hannunsa ya cafki sumar kanta ya ɗora wuƙar a saitin wuyanta yana faɗin "idan kika kuskura kika motsa saina yanke miki maƙogaro, shin ke ɗin ƴar fashi da makami ne? waye oganki? wannan bindigar aina kika samo shi, babban laifi kinyi harbi a cikin mutane...."
kafin ya ƙarasa maganar Angel tayi saurin murɗe masa hannu mai wuƙar ta karɓa ta caka masa akan takalminsa mai sahu ciki har saida wuƙar ta ratsa cikin takalmin ta samu ƙafarsa, ihunsa kawai ake sauraro a gurin tace "banida lokacin baku amsa ƙananun ƙwari kawai..."
suna cikin wannan halin saiga motar D.P.O da wasu ƴan sanda,
daƙer Angel ta miƙe tsaye idonta duk ya rine, wasu police ne sukazo gabanta zasu kai mata hari! ta ciro card a aljihunta ta nuna musu lokaci guda kuwa suka tsaya cak suna bin card ɗinta da kallo sai ɗaya daga cikine yace "Soja ce wallahi..."
kafin su rufe baki saiga motar Sojoji sun kai uku suka diddirƙo da manya-manyan bindigoginsu suka tsattsaya saiga Ogah Junaid shima ya fito yana sanye da wandon Soja da kuma farar riga t-shirt yaje gaban Angel ya yi mata ɗaukar luɗa yana ɗauke da ita yace wa D.P.O "she's a commander of soldiers, California Army..." yana kaiwa ƙarshe maganar sa yayi gaba da ita ya buɗe cikin mota ya kwantar da ita a back seat,
duk abunda ya faru akwai wani abokin Junaid wanda yake wajen yayi video ya turawa Junaid,
shiga cikin motar yayi shima yaja motar ya tafi da ita gida, har wannan lokacin cikin Angel bai daina ciwo ba,
saiji tayi yace "nace miki ki tafi da wasu Soja ku kamo mutumin amma kin tafo ke ɗaya ai dole ya raina ki..."
Sauran Sojojin kuma jawo Sauro sukayi daga cikin motar police suka sakashi a cikin motarsu suka tafi,
Ƴan sandar dake wajen basuyi mamaki ba saboda yanda sukaga Angel tana faɗa har cakawa Ogansu wuƙa tayi a ƙafa daman sunyi zargin tanada wani muƙami...
*******
Ayush sauƙowa falo tayi ta samu Mommy tana jera kuloli akan dinning daman yunwa take ji kuma saita fito a daidai,
Mommy tana ganinta tace "ha'a Ayushert kin fito ne, gashi kuwa na kammala girkin zo ki zauna ki ci ko.."
Ayush kasa magana tayi sai dai ta nufi dinnig ta zauna a kujera, ga tabo a goshi yanda Junaid ya buga mata shi ajikin bango, Mommy cikin tausayawa take kallon Ayush tana maganar zuci "kin kusa ki huta Ayush gobe Junaid zai tafi kafin ya dawo kuwa zan gama saita komai.."
ta zuba wa Ayush a plate tace "gashi nan Yarinyar kirki kici kisha magani ko saboda ciwon goshinki..."
Ayush ɗaga mata kai kawai tayi tareda ɗago da spoon zata sa abinci a baki,
Dai dai lokacin da Junaid ya shugo falo yana ɗauke da Angel,
Mommy na ganinsu a haka tace "subhanallahi meya faru da ita?.."
Kwantar da ita Junaid yayi akan doguwar sofa yace "rigima tayi da wani yayi mata duka.."
ya ƙarasa maganar tareda nufar gurin dinning domin yunwa yake ji,
har saida ya zauna zai zuba abinci ya lura da Ayush, ɗagowa yayi yana kallonta,
itama kallonsa take cike da fargaba da tsananin tsoronsa domin ta tabbatar yanzu Junaid ba ƙaunarta yake ba tinda har ya furta da bakinsa...
Kawar da kansa yayi gefe yana ɗan ƙwala spoon akan glass table sai yake ɗan bada sound yana ɗan cije maroon lips ɗinsa ya ambaci sunanta a hankali "Yushert..."
kallonsa kawai take domin tin zuwansa gurin ta dakatar da