Showing 105001 words to 108000 words out of 186041 words

Chapter 36 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53947

da ƙasara maganar ba ta katse shi da cewar "saboda baka kishin mahaifiyarka? nifa da hannuna na kasheta har lahira..." zabga mata wani irin gigitaccen mari yayi saida ta kife akan gadon, ɗagowa tayi tana kuka tace "Ni ka sakeni, na haramtawa kaina zaman Aure, bazanyi rayuwar Aure da kowa ba, nifa ƴar ta'addace da hannayena nayi kisan kai...." ta ƙarasa maganar tana fashewa da matsanancin kuka harda majinar ta, ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin guduwa ya riƙota yana cewa "Yushert ki saurareni, idan kika fita yanzu kasheki zasuyi..." ita kuwa ƙoƙarin ƙwacewa take tana faɗin "Ni ka sakeni nafi son su kasheni daman na gaji da zaman duniya, ka sakeni ko na kashe kaina, wallahi zan kashe kaina, zan kashe kaina idan baka sakeni baaaa....". tana kuka tana maganganu marasa lissafi ganin taƙi dawowa hayyacinta ne yasa ya kuma zabgeta da mari a ruɗe ta hautsina saman gado ta kifu da cikinta, dafe cikinta tayi tana kuka haɗi da cewa "wayyo Allah nah cikinaaaa..."
a tsorace Junaid yayo kanta yana ƙiran sunanta a kiɗime "Yu Yu yuu yuushertt kina lafiya ko? Please am sorry, so so srrrry my Yushert...." ganin yanda take juyi tana riƙe da ciki ga kuka yaƙi tsayawa yace "Yushert kina so ki kasheni ne?..." wani irin ƙara yayi ya dafe saitin zuciyarsa ya dungura shima akan gado tareda ɗauke numfashinsa ido a rufe, Ayush jin Junaid yayi ƙara kuma ba motsi yasa tayi saurin ɗagowa ta nufi yanda yake da rarrafe akan gadon tana ƙiran sunansa da ƙarfi cikin tashin hankali "Yayaaa Junaid! Yaya Junaidd!! wayyo Allah Yaya Junaid karka mutu ka barni dan Allah, dan girman Allah Yaya Junaid ɗina ka tashiiiiii wallahi inasonka, ina ƙaunarkaaa zan zauna dakai a matsayin matarkaaa...." sake fashewa tayi da kuka tana jijjigansa da ƙarfi, kamar ranta zai fita haka take faman ƙiran sunansa cikin kuka, kifar da kanta tayi a saman ƙirjinsa ta rungumeshi sosai tana faɗin " shikenam tinda ka mutu nima rayuwata bata da wani amfani, gwara nasha poison nima na mutu inyaso azo a kwashi gawar mu a tare..." ta tashi cikin ƙarfin hali har cikin zuciyarta ta ƙudurta hakan, tana kuka taji an riƙe mata hannu da sauri ta kalli hannunta taga Junaid ne ya riƙe mata hannu sai faman tintsirewa yake da dariya yana kallonta, haushi ne ya isheta cikin ɓacin rai tace "daman wasa kake yi Yaya Junaid?..." ganin yanda yake mata dariya yasa takai hannu tana kai masa duka da hannu bibbiyu tana kuka daga ƙarshe ta rufu akansa tasa hannu ta rungume shi sosai tana kuka tareda faɗin "inasonka sosai Yaya Junaid, ka gafarce ni nima ba'a son raina na tafi na barka ba, inason kasancewa a tare dakai, duk da nasan yanzu hukuma nemana suke..." ta sake fashewa da kuka..
Junaid hannayensa biyu ya zagayo dasu ta bayanta ya rungumeta shima bakinsa a saitin kunnenta yake mata magana a hankali ta sigar rarrashi,
daga baya tayi shuru tana jin yanda yake ɗan bubbugan bayanta a hankali, saida sukayi kusan awa guda a haka tukun Junaid ya mirgino da ita ya ƙwantar ta idonsa cikin nata yace "wait for me bari naje na haɗa miki ruwan wanka koh..." ya ƙarasa maganar tareda yi mata sigina....
tashi yayi ya shiga cikin toilet can ya fito yazo ya ɗauki Ayush suka shiga ciki tare,
yayi mata wanka sosai da ruwa kala uku kuma ko wanne ruwa da kalar ƙamshin turarensa, haka ya wanke mata kayinta tass ya koma asalin yanda yake baƙi ƙirin sai sheƙi yake yana ɗaukar ido, yayi mata shevin gashin hammatar ta sannan shi da kansa yayi mata sheving farjinta, saida ya gama mata wanka tukun shima ya cire yayi wankansa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, a yayin da yake wanka ita kuma Ayush tana gefe tana brush....
A tare suka fito yana sanye da gajeren wando mai kama da pant, bayan shi babu komai a jikinsa ya fito yana ɗauke da Ayush a hannunsa wanda ita kuma towel ne a ɗaure saman ƙirjinta, ajiyeta yayi a bakin gado ya ɗauko creams kala² dana gyaran gashi duk ya mulmulka mata, yayi mata ƙwalliya sannan ya gyara mata gashin kanta yayi rolling da gashin saboda tsayin yayi yawa, ya feffesheta da turaruka kala² masu ƙamshin gaske, saida ya kammala shiryata tsab sannan ya nufi wardrobe ya ciro wata farar jallabiya na mata a cikin akwatinta da sauran ƙananun abubuwanta yazo ya sanya mata su ya ɗauki Hirami mai zanen fari da baƙi ya naɗa mata a kanta ya fitar mata da tsolon gashinta ta waje, ya kuma ƙara fesheta da turare, ɗakin duk ya kaure da ƙamshin turaruka kala-kala, a gaskiya Ayush ba ƙaramin kyau tayi ba, kamar wata kyakkyawar balarabiya ƴar ƙasar madina, Junaid tsayawa yayi yana kallonta kamar ba Yushert ɗinsa ba, sai faman murmushi yake baki yaƙi rufuwa,
daga baya shima ya shirya cikin wata danƙararriyar gizna water fruit, yasha hula kalar gizna takalmi jinin sarauta kalar gizna shima ba ƙaramin kyau Oga Junaid yayi ba,
Ayush sake baki tayi tana kallonsa ita tinda take da Junaid bata taɓa ganin shi acikin manyan kaya irin haka ba, saiya fito a mazannin Alhaji Junaid,
rufe bakinta tayi da hannunta tana dariya, shima tsayawa yayi yana kallonta yace "Ni kike wa dariya ko..."
tace "daman kanada shaddodi da giznoni ne?..."
Murmushi yayi har saida dimple ɗinsa ya lotsa sosai ga saje baƙi ƙirin a kwance saman fuskarsa zuwa gemunsa ba ƙaramin haɗuwa yayi ba yace "ke nifa yanzu na zama Baba dole na riñƙa shiga cikin manyan kaya yanzu, amma ba kullum ba domin har na fara takura wallahi, jikina yayi mun nauyi ni cire kayan zanyi ma..."
ya ƙarasa maganar tareda sa hannu zai cire rigar Ayush tayi saurin zuwa gabansa tana riƙe da hannunsa tace "a'ah dan Allah mijina kayi kyau sosai kar ka cire..."
dariya yayi tareda riƙe ƙugunta yace "toh shikenam matata na bari, yanzu jirani bari naje na nemo mana abunda zamu ci koh?..."
kaɗa masa kai tayi cikin shagwaɓa tace "ehhh Baby na jin hungry..."
hannu yakai yana jan dogon hancinta cikin wasa yace "haka itama mommin Baby na jin hungry..." yana kokkoyan yanda tayi shagwaɓa, cikin jin kunya takai masa naushi kan ƙirjinsa a hankali tace "uhmm uh uhmmm nasan Daddin Baby shima na jin hungry..." duk ɗinsu suka tintsire da dariya cikin zolayan juna suka rabu shi Junaid yayi waje zaije restaurant domin nema musu abunda zasu ci,
Ita kuma ƙwanciya tayi akan gado tana shaƙar A.C cikin ɗakin da murmushi saman fuskarta da haka bacci ɓarawo yayi awun gaba da ita....



A ɓangaren Doctor Hasheem kuwa yana ƙwance a bayan kanta sunyi masa jinajina har gagara tashi yayi, yana ƙwance ido a lumshe sai fitar da numfashi yake a hankali, domin ba ƙaramin wahala yake sha ba, wannan karan kam tsabar duka jini har ta hancinsa yake fita, ga sun cire masa haƙori ɗaya ta gefe, jibi kuma za'a shiga kotu.....

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 53 ➡️ 54




Bayan kwana biyar da yankewa Dr Hasheem hukuncin zaman gidan prison na tsawon shekara 25 akan yiwa yarinya fyaɗe...
a ranar da aka kai Dr Hasheem prison a ranar Maimoon ta santalo kyakkyawan yaronta, amma saidai mahaifinta yayi fushi da ita ko amsa sallamarta bayayi da zarar tazo yanda yake, haka idan ta gaishe shi baya amsa mata, amma saidai yayi halacci ɗaya daya siyo ƙaton rago yace a yankawa jariri sanna kuma shi ya bada umarni a sanyawa jariri sunan mahaifin Dr Hasheem wato Abubakar, Maimoon taji daɗin haka sosai saboda ko ba komai ya nuna yana son yaronta, Maimoon ta saka wa yaron sunan inkiya wato "Rapeekh", saidai ba'ayi wani hidimar suna ba...
yayin da shi kuma Dr Hasheem yana can cikin mawuyancin hali shi kaɗai kamar wani marar gata haka yake zaune yayi tagumi yanata nazarin abubuwa, gaba ɗaya duk ya rarrame ya fita hayyacinsa, suturar dake jikinsa irin na ƴan cikin prison ne kowa an rubuta masa number a bayan rigarsa...


******

Shi kuma Junaid ya kulle kansu a cikin gida saboda sojojin da suke yo masa zirga-zirga akan ya bada Ayush su tafi da ita amma sam yaƙi, yanzu baya fita aiki saboda wannan matsalar, koda yaushe suna cikin ɗaki a manne da juna yauma kamar kullum suna ƙwance akan gado a yayin da ita kuma Ayush take kwance saman ƙirjinsa, tace "Yayana.." ya amsa mata da "na'am ƙanwata ya akai?.." ɗagowa tayi ta zauna tana fuskantarsa tace "meyasa ka kasa cika alƙawari?.." shima idonsa akanta yana cije leɓɓen sa yace "Alƙawarin mai?.." ɗan turo baki tayi a shagwaɓe tace "ka ɗaukarwa sojojinku Alƙawarin zaka kaini gurinsu da hannunka yanzu kuma yau kusan sati guda suna binka amma kaƙi sauraronsu ka kashe wayanka gaba ɗaya, ai baka kyauta musu ba koh kuma zasu ɗauke ka maƙaryaci marar cika alƙawari kuma suna ganin girmanka..". ajiyar zuciya Junaid ya sauƙe yana lumshe ido yace "Yushert a halin yanzu bana ƙaunar rabuwa dake, bansan wani hukunci zasu yanke miki ba, bazan iya barinki ina ji ina kallo su hukunta ki ba..."
Ayush katse shi tayi da cewa "amma baka ganin abunda kayi zai iya shafar aikinka?..." yana kwance saida yayi jinkiri kaɗan kafin ya bata amsa da cewa "sosai ma hakan shi yafi sauƙi saboda na karya doka, bayan haka shuwagabanni nane suke son ganina amma naƙi zuwa, banaso wani abu ya taɓaki Yushert ga kinada juna biyu..."
kuka Ayush ta fara yi ta riƙe hannun Junaid duk biyun tana faɗin "dan girman Allah Yaya Junaid kada ka shiga matsala saboda ni, ka ɗauke ni ka kai musu ni kamar yanda kayi musu alƙawari, ni inada tabbacin babu abunda zasuyi mun na zalunci, hukunci ɗaya ne shine nasan za'a kaini kotu ne, kuma nasan duk hukuncin da za'a yanke mun a kotu baza ayi mun yanzu ba dole sai an bari na haihu tukun, ka kwantar da hankalinka, haka kaddara ta tazo mun, kuma kowa baya tsallake ƙaddararsa saboda haka dan Allah ka tashi muje mu gurin aikin nakun, dan Allah badan ni..."
shima binta da kallo yake kamar zaiyi kuka yace "Yushert ki barni dasu kawai".
"a'ah ni kawai ka tashi muje mu, idan ma bakaje ba ni zan kai kaina..." tana ƙarasa maganar ta tashi da sauri ta nufi wardrobe ta zaro hijab ɗinta har ƙasa, ta sanya sannan ta fidda hannayenta waje ga ciki kuwa ya fito sosai...
tashi yayi shima ya tsaya a gaban ta yana jinjina kai yace "shikenam tinda kin dage akan saina kaiki toh amma ki sani duk wanda yayi kokarin cutar mun dake wallahi wallahi saina ɗauki ƙwaƙwaran hukunci wanda kare ma bazai shanshana ba...". yana kaiwa nan ya riƙo hannunta ya kuma cewa "muje mu." yana janta a haka suka sauƙa falo shi kuwa yana sanye da baƙar jallabiya a jikinsa, suna fita out side na gidan suka shiga motar a hankali ya karya ƙwana sannan ya miƙi hanyar gate, kafin ya iso mai gadin ya buɗe musu suka fice da gudu..."

*****

A sashin mommy Kuma kulawa iya kulawa tana samu agurin sarki Raamud, ga mata zaƙa² dake mata ayyuka, ko ƙwaƙƙwaran motsi mommy tayi sai sun tambayeta ko akwai abunda take so, ga ta ɓangaren sarki Raamud shima babu abunda zata nema ta rasa, wani ƙyakykyawar alaƙa ne a tsakaninsu duk da har yanzu babu maganar soyayya a tsakaninsu amma kana ganinsu kasan akwai ƙauna, yauma kamar kullum tana zaune akan dadduma dake wajen lambu a bayan masarauta ta ɗan shigingiɗa kaɗan tana riƙe da apple a hannunta har ta ci rabi, a gabanta kuma ƙaton paranty ne yana ɗauke da kayan fruits a ciki duk anyi slaces ɗinsu, ga kuma kuyange a wajen su biyar suna taya mommy hira, wasu suna mata tausa wasu kuma suna zazzaune kawai, dake suma ƴan aikin suna son kasancewa da mommy domin tanada son mutane, bata son zama ita kaɗai, suna cikin hira saiga mai martaba sarki Raamud ya shugo filin lambu dake fakaice guri guda, yana zuwa ƴan aikin suka tashi suna gaishe shi tareda ficewa daga wajen, shima zama yayi akan daddumar yana fuskantar mommy da murmushi a fuskarsa yace "Rankiya daɗe sarauniya na gaisheki..." murmushi tayi itama ta tashi zaune tace "haba mai martaba nifa ban zama sarauniya ba..." dariya yayi yace "ai kin zama mah" ta ɗago tana kallonsa tace "taya kenam?..". yace "saboda kema jinin masarauta ce..". zaro kyakkyawar idanuwanta tayi tace "o-oh o-oh! yara nane jinin sarauta bani ba, ban haɗu da masarauta ba" sarki Raamud ido kawai ya kafa mata da ƙyakykyawan murmushinsa yace "gashi kuwa yanzu ta dalilin yaranki kin zamo ƴar sarauta..."
dariya tayi tana kawar da fuskarta gefe, yace "amma fah kinyi kyau sarauniya, alkebbar tayi miki kyau.." da sauri ta jawo mayafinta tana rufe fuskar, hannu yasa yana ƙoƙarin buɗe fuskar har yayi nasarar janye mayafin, ta sunkuyar da kanta ƙasi cikin jin kunya tace "dan Allah ka daina, mu ba yara ba..."
yace "yaran to me suka iya in banda shirme, ai iya soyayya sai tsofi.."
zaro ido mommy tayi tace "soyayya kuma?.." shima jin abunda tace ne yasa shi sosa ƙeyarshi yana faɗin "a'ah badai soyayya ba, wasa nake miki" tace "ohooo yanzu naji batu..."
daga nan kowa yayi shuru babu wanda ya ƙara ce wa kowa komai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login