Showing 156001 words to 159000 words out of 186041 words

Chapter 53 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53953

ɗari bibbiyu sannan yaja musu kunne akan baya son ƙazanta da nuna rashin gaskiya, saboda haka ne yasa akaje har ƙauyen suleja aka ɗauko su domin sunfi ƴan gari riƙon Amana kuma su basu fiye zalontoma kamar ƴan cikin gari ba, itama Hafzat saida ya bata kuɗi dubu ɗari biyar yace "kuɗin kashewarta ne idan tana buƙatar wani abu, kuɗin school fees kuma idan an buƙaci hakan tayi magana za'a turo mata...". Hafzat karɓa tayi tana godiya banda kuɗin da Judan ya bata Dollars goma, ko wani guda ɗaya dubu ɗari ne idan ta canza su sun zama one million kenam, mommy da Abbah suma suka bata two millions...

Ayush kuma shi kansa Junaid baisan adadin kuɗin daya ajiye mata ba, domin suna nan jaka guda a cike da kuɗi banda wanda mommy ta bata nan ma sunfi millions goma, ga Abbah yazo ya ƙara mata da Dollars domin shi baya amfani da Naira, waɗannan sun bata ne saboda idan madarar babies suka ƙare ta siya musu, sun faɗa mata hakane saboda sun san Ayush sam bata iya kashe kuɗi ba, yanzu dubu ɗari sai tayi shekara bata kashe su ba, madarar babies suna nan kamar ruwan randa, ba'a tunanin zasu ƙare a watanni kusa ba,
Da haka sukayi sallama suka tafi, juyawa Ayush tayi da gudu tana rera kuka bata tsaya ako ina ba sai a cikin ɗakinta, domin tasan bada wuri Junaid zai dawo ba, su Mommy kuwa sun tafi kenam...
Triplets kuma suna can waran masu rainon su, itama Hafzat ɗakinta ta shige tana kuka,
Gidan kuwa an zuba masu tsaro kam ba laifi dake iya mata ne kawai aciki, Bodyguards saida aka zuba guda goma, baƙaƙe da fararen fata kowa yana riƙe da manya-manyan bindigu, suna toshe da baƙaƙen glass, sunci boom kai kace tinda aka halicce su basu taɓa yin dariya ba,
Ga wasu karnuka na turawa da aka zuba suma sun kai biyar, waɗannan manya manyan karnukan Aikinsu zagaye duk faɗin gidan ne, daga sunji motsi su hau haushi, sai kuma wasu daga cikin Bodyguards su yo gurin....
Hafzat da direbanta mai kaita school, fitarta a gidan sai in za'a kaita skull idan kuma ta dawo shikenam ba sake fita sai washe gari kuma du, shiyasa duk tilin kuɗin da aka basu suna nan a ajiye basa kashewa saboda ba'a barin kowa ya fita haka kawai, kuma duk abunda zasu siya akwai shi a gidan, duk abunda suke so akwai a gida, saidai ita Hafzat dake tana da waya ta aika kuɗinta bank duk aka zube mata su acikin account duk sanda ta tashi takan turawa iyayenta kuɗi ta hanyar transfer...

(Tabb nikam duk kuɗin da aka ajiye mun bazan iya zama ba yawo ba yaciin🙄🙄🙄 anya kuma zaku iya kuwa Reader's?....)

Rayuwa tana tafiya yanda ya kamata, abubuwa suna chanzawa zuwa hanya mai kyau, akwana a tashi yau wata biyar da tafiyar su Mommy, kullum Ayush sai tayi waya dasu ta video call acikin computer, wani sa'in kuma a cikin ƙatuwar wayarta Iphone take waya dasu, especially Ogah Junaid kusan kwana suke suna waya ta video call, hakan yana rage mata kewa sosai, yanzu Ayush saita jera sati guda bata sauƙo falo ba, abinci saidai akai mata can upstairs, daga bacci sai kuma waya da Junaid ɗinta sai idan lokacin sallah yayi ta tashi tayi acikin ɗakinta, takan motsa jiki wajen gyara cikin ɗakinta domin bata yadda ƴan aiki su shugo mata bedroom sai iya Hafzat ce kawai ta lamince mata, itama sai idan zata zo ɗaukan yara takai su wajen raino, ba'a maiso mata dasu sai idan dare yayi, tin suna wata uku ta yayesu bata basu nono sai madara, ai kuwa yaran gwanin burgewa gasu ƴan ɓulɓul dasu duk da basa shan nono...
Itama Hafzat tin da safe idan ta tafi school bata dawowa Sai ƙarfe shida na yamma dake makarantar haɗe take da Boko da islamiyya, idan ta dawo tayi wanka taci abinci sai tayi waya da Judan tukun take ƙwanciya bacci bayan nan tayi sallar mangarib...
Kuma sa'in-sa'in Uncle Artaff yakan zo gidan dubasu ko akwai wacce bata da lafiya ko kuma akwai wata matsala.....


★★★ *AFTER 3 YEARS AGO* ★★★


Ogah Junaid aikinsa ya kankama a ƙasar California, yanzu aiki yake tuƙuru na aikin General, bai tashi dawowa Nigeria ba saida yayi shekara uku kafin, domin dayaje riƙeshi akayi aka hanashi dawowa, yanzu saidai ya rinƙa zuwa hutun ƙwana biyu saiya koma,
Dawowarsa ba ƙaramin farin ciki Ayush ta shiga ba, harda kukan farin ciki, Ogah Junaid ya ƙara kyau sosai yayi fari duk wanda ya ganshi yasan ya samu kyakkyawar kulawa da jin daɗin rayuwa, shima ba ƙaramin farin ciki yayi ba ganin iyalansa cikin ƙoshin lafiya, ga yaransa sun girma sosai yanzu duk sun wuce shekara uku² da haihuwa, Ayush itama ta ƙara kyau sosai ta samu hutu tayi ƙiba, jiki ya murmure....
Hafzat tayi candy ta samu result mai kyau, dake yanzu school of Nursing ta kammala ta karanci Pharmacy na shekara biyu...
Gaba ɗayansu suna zazzaune a falo suna kallon India Film na yaƙi Ayush tana zaune a kusa da Junaid ɗinta ga yaransu ɗaya tana can ƙwance saman cinyar Hafzat, ɗaya kuma tana kan cinyar Daddynta..

Junaid yana riƙe da little Angel akan cinyarsa yana wasa da ita tareda faɗin "Jaruma ta kenam, wannan ita ce jarumata kuma Soja ta...".
ta ɗago tana kallonsa cikin Muryar yara tace "Daddy nikam Soja zan zama idan na girma ko?..."
cikin so da ƙauna ya sumbaceta akan goshi yace "yawwa Jarumata shiyasa nake ƙara ƙaunarki ai, kinga takwararki ma Soja ce ta iya faɗa sosai..." tace "Daddy ai Mommy ta nuna mana photonta da kayan sojoji ajikinta tamun kyau sosai...". murmushi yayi yace "kema ai haka zaki zama, kiyi kyau acikin kayan sojoji..."
Little Angel cikin zaƙewa takai hannunta saitin goshinta tana faɗin "jinjina ga tutar sojoji..." daga nan ta sara wa Daddynta..
Gaba ɗaya kwashewa sukayi da dariya, Ayush hannu tasa ta maki gadon bayanta tana dariya, kuma daman Little Angel ta fisu surutu da iyeyi, Junaid ya kalli Ayush cike da mamaki yace "duk waye ya koya mata wannan?..."
Ayush ɗaga kafaɗarta tayi alamar itama bata saniba, Hafzat dake kujerar gefe dasu sosai tace "wallahi duk a Film take gani, kuma tafi kallon Film ɗin sojoji..."
Junaid ƙara rungumarta yayi tareda lumshe idonsa yana hasasho fuskar Angel marigayiya, gaba ɗaya ta dabaibaye masa ƙwaƙwalwa,
saida ya gama tunaninta tukun ya buɗe eyes ɗinsa a hankali ya maida kallonsa kan Amreesh yayi mata alamar tazo ta, tana can tana kwance saman cinyar Hafzat ta taso tazo gabansa tace "gani Daddy..."
Da murmushi akan fuskarsa yace "ke kuma pah idan kin girma wani aiki zakiyi?..."
Ɗan turo ƙaramin lips ɗinta tayi tana haɗe gira tace "Ni nikam Aure zanyi..."
Zaro ido Junaid yayi yana binta da kallo,
Ayush kuwa ruwa ta kora a bakinta amma jin abunda Amrish ta faɗa yasa ta burtso da ruwan tana kwashewa da dariya harda kama cikinta,
Junaid yace "Keee leave my front dalla dubeta, waii Aure kuttt..."
Kallon Ayush yayi ganin sai dariya take yasa ya haɗe rai tareda faɗin "ke kika ɗorata akan keken ɓera koh?.."
Ayush toshe bakinta tayi da hannu tana ƙunsar dariya tace "Ni kuma? wallahi ban taɓa musu maganar Aure ba...". yace "amma tayaya tasan ana yin Aure?.."
tace "taya bazasu sani ba bayan yaran sunyi wayo yanzu fah shekara huɗu suka nufa, kuma ko a makaranta ai zasu ji ana maganar..."
Yace "ƙarya kike babu yanda za'ayi ƴan Nursery school ayi musu maganar Aure, dole ma duk na tattara ku mu koma ƙasar waje saboda kar a lalata mun yara da maganar Aure..."
ya ƙarasa maganar yana kallon Amrish ya kuma cewa "ke kuma ko Takwarar ki Mommy saida tayi karatu ta samu Aiki tukun tayi Aure, Babbar likita ce don haka kar na sake jin kinyi maganar Aure kinji koh?..". dasauri ta ɗaga masa kai ganin ransa a haɗe, ya kuma cewa "wai ma waye yace miki kiyi Aure?.." tayi saurin nuna Ayush da yatsa tace "Mommy ce..."
zaro ido Ayush tayi tana kallonta a ruɗe tace "Ni kuma Amriish? yaushe nayi miki maganar Aure?..." Junaid wani irin kallo yake watsa mata yace "yaro ai bazai yi ƙarya ba"
ta juyo da kallonta kansa tana faɗin "wallahi tallahi bani bace, taya zanyi musu maganar Aure bayan nasan har yanzu basu datu ba, du Da du yaushe aka haifesu balle nace zan sakasu a gaba nayi musu....". kafin ta kai ƙarshen maganar ta yayi saurin ɗaga mata hannu tareda cewa "ya isa haka banson long story.."
Ayush hararar Amrish take da gwala-gwalan idanuwanta tana mamakin yaushe yarinyar nan ta koyi ƙarya haka...
Amrish kamar zata fashe da kuka, ta nufi gurin Hafzat daman itace uwar ɗakinta,
Amriish tafi kama da Ayush sosai kamar an tsaga kara, duk wata suffar ta irin na Ayush ce har tsayin gashi domin tafi little Angel sumar gashi, kuma tafi little Angel farin fata sosai duk da itama little Angel tanada haske amma bata kai Amrish haske ba,
Ita little Angel yanayin fuskarta irin na Junaid ne hatta launin haskensu, dan Junaid ko rabin ɗauko farin Ayush baiyi ba,
Shi kuma Areeph duk wani hali na Junaid ya ɗauko su, kwata-kwata an rasa kamannin wa ya ɗauko acikin Sarki Raamud da kuma Baban Junaid wato Máahmud takwaran Areeph..

Junaid ne ya fara waige-waige yana faɗin "Ni ina Areeph ne?...". Ayush tace "yana ɗakinsa.."
Yace "ha'a toh shi baya fitowa cikin mutane ne?.."
Little Angel tayi cabb ta tari bakinsa da cewa "Laaa Daddy shikam baya zama acikin mutane, daga ɗakinsa sai cikin ɗakinsa, kuma yana wasan game ɗin harbi da bindiga a cikin computer sa..."
Junaid yace "kenam shima soja zai zama ...".
Little Angel ta kuma cewa. "ehh mana ai we are together me and him...". Yace "wow my Jaruma Ina yinku over, jeki ƙira mun shi oyaaah..." ta sauƙa akansa da gudu ta nufi ɗakinsa, tana zuwa ta tura ƙofar ɗakin ta shiga ta tarar dashi yanata wasan game ɗinsa na sojoji da ƴan fashi, juyowa yayi yana kallonta up and down rai a haɗe yace "ke Ni abokinki ne zakina shugo mun ɗaki babu excuse?..."
tace "toh Daddy ne yake ƙiranka..." yace "yi mun kneel down a wajen"
turo baki tayi tace "cab ɗin wallahi bazanyi ba kai Uba nane..." Areeph tasowa yayi a fusace yana zuwa gabanta ya talleta da mari da ɗan ƙaramin hannunsa, yana faɗin "Ni ba abokinki bane...".
Da gudu little Angel tabar ɗakin tana kuka hannu riƙe da fuska, tana zuwa falon tace "Daddy ya mareni..."
Junaid cike da mamaki yace "ya mareki kuma?..." sai a lokacin Ayush tayi magana tana cewa "daman ai nasan hakan zata faru, shifa Areeph baya barin kowa ya shigar mar ɗaki sai iya Ni kaɗai..."
suna cikin maganar sai gashi ya fito yana kuncume da fuska ko alamar dariya babu, yana zuwa ya nemi guri ya zauna, yana fuskantar Ayush yace "Mommy ke kike ƙirana?..". girgiza kai Ayush tayi tana nuna masa Junaid da yatsa baki ya gagara buɗuwa tsabar ƙunsar dariyar da take yi a cikinta saboda ganin yanda Junaid ya ƙafe idonsa akan Areeph ko ƙibtawa baya yi gaba ɗaya yaron ya bashi mamaki ganin yanda yake abu kamar babban mutum,
Areeph kallon Daddynsa yayi sannan yace "gani toh, sauri nake ina uzuri...". Junaid ne ya danƙwale shi tareda faɗin "dan ƙaniyarka uzurinka yafi ƙirana muhimmanci?.."
Girgiza kai Areeph yayi tareda cewa "a'ah shiyasa na bar uzurin nazo Ni ai...". jinjina kai Junaid yayi sannan yace "meyasa ka mari Angel?..". kawar da kai Areeph yayi gefe yana mutsil-mutsil da baki daƙer ya iya furta "ta raina Ni ne kuma a ƙarƙashina take...". Zaro ido Junaid yayi yace "kai kake iko da ita?..."
Areeph yace "eh mana Daddy saboda duk gidan nan nine namiji, ni kuma bazan jure raini ba zan iya murɗe musu wuya..."
sake baki Junaid yayi yana kallonsa,
Ayush kallon Junaid tayi tana tuna yanda shima yake maganarsa a baya Abu kaɗan sai yace zai murɗe wa mutum wuya toh gashi yaronsa duk ya ɗauko irin halayensa da kuma yanayin maganarsa,
Jinjina kai Junaid yayi baiga laifinsa ba saboda shima yayi ire-iren waɗannan abubuwan, daƙer ya buɗe bakinsa yace "okay it's okay, daman tambayarka zanyi idan ka girma wani irin aiki zakayi ?..."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login