Showing 78001 words to 81000 words out of 186041 words
nufi ciki,
Lailah ce ta kara wayarta a kunne tace "kinga Maimoon zamuyi magana daga baya..." ta katse ƙiran tabi bayan Junaid da gudu...
A ɓangaren Maimoon kuma bayan ta sauƙe wayarta tana kuka sai ji tayi an turo ƙofa, da sauri ta ɗago tana kallon Ammy wacce ta shugo da hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskarta,
Maimoon a tsorace tace "Ammy meyasa kike kuka?.."
Ammy ta taho gurin Maimoon tana kuka tasa hannu ta cire dogon hijab ɗin Maimoon, saiga tumbin ciki har ya fito sosai,
Bazaka taɓa gane Maimoon tanada ciki ba indai ba lura kayi sosai ba, saboda kullum a cikin ɗakinta take, bata yadda taje falo saidai Ammy ta kawo mata abinci kuma kullum da hijabi a jikinta,
Anyi Anyi da ita amma taƙi fitowa cikin mutane, hatta mahaifinta shima yayi har ya gaji sun ƙyaleta..
Ammy ganin ciki a jikin Maimoon yasa taja baya da sauri tareda dafe ƙirjinta tace "nashiga uku Maimoonnn? yanzu abunda yake tare dake kenam? kike ɓoye mana? yanzun ma ji nayi kina waya da Lailah shiyasa na sani amma inbadan haka ba saidai idan naƙuda ne ya tarar dake, nashiga uku nah, yanzu har ciki yayi wata bakwai a jikinki ban saniba Maimoon?..."
Maimoon tana kuka tareda faɗin "dan Allah Ammy kuyi haƙuri ku gafarce ni, nasan nayi kuskure da ban sanar muku ba, inajin tsoron Daddy, bansan ya zanyi ba Ammy..."
Ammy itama kukan take tace "Maimoon waye ne ya miki ciki?..."
Shuru tayi Maimoon ta gagara bada amsa sai kuka,
Ammy ta sake yin magana tace "magana nake miki Maimoon ki ban amsa mana.."
Maimoon murya na kakkarwa tace "nima ban saniba Ammy, bansan inada ciki ba sai da naga ya fito.."
Ammy tace "kodai mutanen da suka sace ki ne suka ɗirka miki cikin?..". Maimoon tana kuka tace "ehh sune.."
Ammy cikin damuwa tace "Insha Allahu za'a ɗauki mataki akansu"
daganan Ammy tayi waje cikin ɓacin rai..
******
Junaid yana shiga cikin falo ya tarar da Ayush zaune tana fuskantar plasman ita kaɗai, juyowa tayi ta kalli wanda ya shugo ganin Junaid yasa ta miƙe tsaye da sauri tana kallonsa,
saiga Lailah itama ta shugo, kalle kalle suke yiwa junansu ba wanda ya kula kowa acikinsu, daga baya saiga malam lawan shima ya shugo ganin Ayush yasa shi faɗin "Ayshert daman kina nan a raye? taya kika bar gidan nan?.."
Ayush fashewa tayi da kuka ba tareda tace musu komai ba,
Junaid ne yazo gabanta ya tsaya suna facing juna yace "ki gaya mun gaskiya taya akayi gidan mu ya kama da wuta kuma mahaifiyata tana ciki?.."
wani irin kallo Ayush ta watsawa Junaid tace "wannan wani irin tambaya ne? shin inda nima na ƙone a ciki zaka samu kayi mun irin wannan tambaya ne?.."
Junaid kallonta yake cike da mamaki bai taɓa tunanin Ayush zata iya bashi wannan amsar ba, yace "shin kina farin cikin mutuwar mahaifiyata?."
kallon cikin eyes ɗinsa take ta maida masa amsa da cewa "kamar yadda kaima kayi farin cikin kashe mun mahaifiyata ba..."
Ba Junaid ba hatta malam lawan dake tsaye shima ya girgiza da jin kalaman Ayush, cikin ɓacin rai Malam Lawan yace "ke Ayshert wani irin magana kike yi haka ne?..."
Ayush ta kalli Malam Lawan sannan tace "malam wannan Junaid shine wanda ya kashe mun mahaifiyata da tsohon cikinta, kuma bazan taɓa yafe maka ba, mungu azzalumin bawa..."
Junaid idonsa ne sukayi jawur tsabar baƙin ciki ga duk ya fita hayyacinsa yace "Yushert a lokacin da nake tambayarki shin wacece ke, kasa bani amsa kika yi, shin meyasa kika ɓoye mun kanki? duk da baki gaya mun ba naji kuma an sanar mun ko ke wacece a guri na, ko ba komai nasan tushen mahaifina kuma na gano su waye ƴan uwana, Yushert ko ba soyayya zanyi alfahari dake a matsayin ƴar uwata kuma jinina, mahaifiyarki kuma bani na kasheta ba, ta ceci rayuwata ne...."
Kafin ya ƙarasa maganar Ayush ta kai hannu ta zabga masa mari asaman fuskarsa,
Lailah ce tayi wani irin firgita tasa hannu biyu ta toshe bakinta tana zaro ido waje,
Shima Doctor Hasheem dake bakin ƙofar ɗakinsa a tsaye saida ƙirjinsa ya buga,
Malam ne yayo kan Ayush yana faɗin "kin haukace ne Ayshert, shin kinada hankali kuwa?..."
Junaid haka yake bin Ayush da kallo cike da mamaki ya kasa aikata komai,
tana kuka tace "Ni ba abunda zaka gaya mun Junaid, ka riƙe ɗan uwantakar ka domin ni yanzu babu wata alaƙa dake tsakanin mu, na tsaneka wallahi bana ƙaunar ganin fuskarka, ka kashe mun mahaifiyata sannan kazo kana mun wani banzan shirmen maganarka,
zan gaya maka gaskiyar magana shine kamar yanda ka hallaka mun mahaifiyata toh haka nima na dasa gobara a cikin gidanku munyi two zero kenam, nima saidai ka kashe ni..."
tana ƙarasa maganar ta rufa da gudun gaske ta shige ɗakin da take tasa sakata...
Junaid jin furucin Ayush yasa yayi baya zai faɗi yana dafe da goshinsa Malam Lawan yayi saurin riƙoshi ya rungume shi sosai a jikinsa, haka jikin Junaid yake ɓari yana kakkarwa sosai ga duk gumi ya wanke masa ilahirin jikinsa, haka ƙirjinsa yake ta faman bugawa da ƙarfin gaske,
Malam Lawan shima kamar a mafarki yake jin kalaman Ayush domin yayi matuƙar tsorata sosai da abunda Ayush ta aikata kuma bata ji fargaban faɗa ba...
wani irin ihu Junaid ya rausa ya durƙusa ƙasi da gwiwowinsa yana dukan ƙasa da hannayensa biyu da ƙarfin gaske, yana ihu kamar ransa zai fita..
haka Malam Lawan yake rungume dashi a ƙasi yana rarrashinsa, kamar zaiyi kuka haka yake ji,
Doctor Hasheem shima yana tsaye yayi matuƙar tausayawa Junaid, Lokaci guda kuwa yaji Ayush ta fita masa arai kwata-kwata, a wannan lokacin ba ƙaramin haushi ta bashi ba,
Lailah itama fashewa tayi da kuka ta nufi ɗakinta da gudu,
tana zuwa ta zauna a bakin gado tayi dialing call number wata mutumiyarta ƴar jarida, bugu ɗaya kuwa ta ɗauki ƙiran,
Da sauri Lailah ta kara a kunne tana faɗin "Hello Sumaiya kina inane?..."
A ɓangaren Sumaiya kuwa cewa tayi "ina wajen aiki mana.."
Lailah tace "toh kar ki bar wajen gani nan zuwa akwai tattaunawar da zamuyi, kuma hanyar samun kuɗin ki.."
Sumaiya tace "Allah yasa rahotanni zaki kawo mun tsararru.."
Lailah tace "maganar akan Doctor Fateema ne, gobarar da ya tashi da ita ba haka kawai bane, yarinyar gidan ce ta ƙoneta, yanzu haka tana gidan mu.."
Sumaiya tace "amma kuma ance yarinyar itama ta ƙone a cikin gidan?..."
Lailah ta kuma cewa "duk shiri ne, yanzu haka tana ɓoye a gidan mu, a tunanin mutane sun ɗauka ta mutu.."
Sumaiya ta kuma cewa "Amma Lailah fatan dai kinada hujjoji a hannunki saboda bama aiki sai mun tabbatar da gaskiyar lamarin..."
Lailah tace "ni ce kuwa mai tattare da hujjoji, domin har recording ɗin maganar ta cewa ita ta ƙone gidan inada shi, sannan inada photonta da video duk maganganun da takeyi, inaso ku buga jaridu akanta sannan ku bubbuɗe duk wata kafar television ku tallata ta da duk wasu maganganun da tayi, inaso hukuma tayi aiki akanta, abi hakkin Doctor Fateema..."
Sumaiya itama ta gamsu da bayanan Lailah tace "shikenam zan sanarwa Ogan mu kuma zaiyi farin ciki sosai dajin wannan batun domin ba ƙaramin kuɗi zamu samu a kafar mu ba, mungode sosai Lailah,
yanzu kizo ki bamu duk wasu bayanai, inba sa'a ba sai anyi zanga-zanga akan a hukunta yarinyar..."
Lailah murmushi tayi sannan tace "shikenam saikin ganni..."
daga nan sukayi sallama..
Daƙer Malam Lawan ya rarrashi Junaid suka tashi har saida Doctor Hasheem yasa hannu suka fita da Junaid, domin kasa tafiya yayi ƙafarsa ta riƙe, ga zazzaɓin da yake kawo masa hari...
Ayushert tana daga cikin ɗakin tana jin ihun da Junaid yake yi gaba ɗaya ji takeyi kamar ta kashe kanta, itama kukan take sosai, tana cikin kukan sai taji murɗa yana damunta da sauri tasa hannu ta toshe bakinta tana yunƙurin amai! tashi tayi da gudun gaske ta nufi toilet,
haka take kwarara amai kamar ranta zai fita, duk abunda taci saida ta amar dashi, har ta koma tana aman zallar ruwa...
haɗagowa tayi tana maida numfashi sama-sama, domin ba ƙaramin wahala take sha ba, lokaci guda ta fita hayyacinta...
Narasimha tin tinin yazo ya ɗauke Damusa sun ɓace tare.....
*TOFAH KAR DAI ACE YUSHERT CIKI GARETA🤔🤔🤔*
*TAFIYAR OGAH JUNAID DA DAWOWARSA ONE MONTH...*
*TAYI 3 MONTHS A GIDAN DOCTOR HASHEEM...*
*4MONTHS KENAM🙄🤔🤔 NIDAI NA FARA LISSAFI..*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 41 ➡️ 42
Bayan Malam Lawan sun isa gida daƙer ya rarrashi Junaid, duk da har yanzu jikin nashin ba ƙwari, Junaid yana jan ƙafa ya shige ɗakin da yake a gidan Malam Lawan, yana shiga ya tarar da Damusa baya nan ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa daiden lokacin shima Malam Lawan ya shugo, da sauri Junaid ya waiwayo yana faɗin "ina Sujjur?.."
Malam Lawan yayi murmushi yace "kwantar da hankalinka Sujjur ya tafi yana can cikin ƙoshin lafiya" Junaid cike da mamaki yake kallon Malam Lawan yace "bangane ba, shin ina ya tafi?.."
yace "Junaid kenam ai masu masarauta bazasu bar Sujjur ya zauna a gefe guda ba, an bi ta hanyar tsafi an ɗauke shi..."
Junaid yace "toh amma waye yazo ya ɗauke shi?.."
Malam Lawan yace "Narasimha babban matsafine a cikin masarautar shine mai basu kariya akoda yaushe..."
Jinjina kai Junaid yayi sannan yace "ok na sanshi..."
ya ƙarasa maganar tareda zama a bakin gado yana dafe da kansa, maganganun Ayush ne suka fara masa yawo a ƙwaƙwalwa, lokaci guda kuwa saiga hawaye yanda yake ta gangaro masa, cikin sassanyar murya yace "why! why!! meyasa Yushert zata mun haka, mahaifiyata ta ƙona da wuta, saboda wani ƙudirinta da ban, meyasa zatayi wa mommy haka bayan tayi mata halacci a rayuwa..."
ya ɗago yana kallon Malam Lawan wanda shima tagumin yayi yana jinjina maganganun Ayush,
Yace "tabbas ba ƙaramin kuskure ta aikata ba, ban taɓa tunanin zatayi haka ba.."
Junaid dafe goshinsa yayi yana zubda hawaye, ji yayi malam lawan ya dafa kafaɗarsa yana rarrashinsa tareda faɗin "kayi haƙuri Junaid, kar ka biyewa zuciyarka ka aikata wani mummunan abu, inaso ka jirani ina zuwa yanzu..." yana kaiwa nan ya miƙe ya fice...
Bayan minti goma sai gashi da ƙaton littafi a hannunsa da wani ɗan ƙaramin akwati, Junaid ɗagowa yayi yana kallon Malam Lawan, yace "wannan littafin da na kawo maka kwanaki ne ai.."
Malam Lawan yace "ehh yanzu zan karanta maka tarihin rayuwar iyayenka da kakanunka sannan saika ɗauko mun ɗayan littafin da Narasimha ya baka, anan zaka gama fahimtar ko kai waye ne..."
Junaid shidai kawai kallon Malam Lawan yake da lufu-lufun idanuwansa waɗanda suka canza sukayi jawur...
Malam Lawan ne ya fara kora masa labari tin daga farkon haihuwar mahaifinsa har zuwansa Nigeria,
Malam Lawan kaf saida ya bayyana komai, da kuma silar kamuwa da ciwon Damusa har warkewarsa sannan ya bayyanar masa akan cewa Ayush ce tayi silar warkewarsa ta hanyar cire wannan zoben jikin cibiyarta...
Bayan Malam Lawan ya gama da littafi na ɗaya haka yasa Junaid ya ɗauko masa littafi na biyu nan ma ya fara bayyana masa labarai na tarihin rayuwarsa dana Ayushert,
Kamar yadda Narasimha ya bawa mommy labarin masarauta haka malam Lawan shima ya bada wa Junaid labarin kaf ba abunda ya bari,.
ya gama bashi labarin daiden lokacin anata ƙiraye-ƙirayen sallar mangarib,