Showing 132001 words to 135000 words out of 186041 words

Chapter 45 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53906

girgiza kai Junaid yayi sannan yace "makaranta takeyi yanzu! kuma ai bani ne mai bayar da ita ba.." Judan yace "Ni ko ainane zanje a bani ita idan ta kammala karatunta..."
murmushi kawai Junaid yayi ba tareda ya kuma cewa komai ba,
Judan yakai kusan minti biyu bai ce komai ba idonsa a gefe guda sai faman zuba murmushi yake shi kaɗai, Junaid ganin zama shurun ya ishe shi haka yasa yayi masa gyaran murya tareda faɗin "toh baban love yanzu dai a sanar mun saƙona kafin ka shiga tunanin ka..."
Dasauri Judan yasa hannu a aljihunsa ya ciro wata takarda ya miƙa masa tareda cewa "gashi saƙone daga ƙasar california Chief of Army's yana son ganinka next month..."

Junaid cike da mamaki yace "meyasa Chief of Army's California yake son ganina alhalin ga manya-manyan sojoji ba'a nemesu ba sai Ni da nake Captain kuma zuwa yanzu kam na ajiye aikin..."
Murmushi Judan yayi sannan yace. "kai kafi cancanta a nema basu ba, sannan bakada labarin kowa an ƙaƙƙara masa matsayi acan california? nima yanzu haka miƙamin Angel aka bani,
yanzu dai ka buɗe takardar ka karanta saƙonda yake ƙunshe a ciki..."
Jinjina kai Junaid yayi tareda yin Bismillah ya fara warware takardar yace "Allah yasa muga Alkhairi"
Idonsa ya kafa akan rubutun ko ƙibtasu bayayi lokaci guda kuma ya miƙe tsaye a zabure yana zazzaro dara-daran idanuwansa dasauri yakai idonsa kan Judan yana masa kallon rashin fahimta,
Murya na shaƙewa yace "wai dagaske ne Judan kodai tsokana kazo yi?..."
Murmushi Judan yayi yace "haba Ogah yanzu saboda tsokana saina taso tin daga California nazo Nigeria? ka duba signing ɗin manya-manyan mutane ne da kuma manyan sojoji a jikin takardar, yanzu ka zama babban soja mai faɗa aji..."
"toh amma meyasa sai ani za'a bawa wannan matsayin hakan ma a ƙasar da ba namu ba?..."
a cewar Junaid wanda gaba ɗaya ya ruɗe ganin wannan letter.
tashi yayi shima Judan yazo har gabansa ya tsaya suna fuskantar juna yace "Ogah a duk faɗin ƙasar california da China da Pakistan da Italian da indian da Nigeria da duk sauran sojojin ƙasashe babu mutum ɗaya wanda aka samu ya iya yaƙar Babban matsafi kamar Munafurr ba sai kai, babu wanda ya iya yaƙar namun daji na tsafin Munafurr sai kai da kuma marigayiya Angel, sojoji waran trillions duk mun rasasu a sanadin yaƙin nan iya kai kaɗai ne kawai ka tsira da rayuwarka, kai ka cika babban jarumi! a duk ƙasar california da sauran ƙasashe duk suna alfahari dakai da kuma jarumtarka, yanzu haka kana shiga headquarters na ƙasar california zaka ga mutum mutuminka a mashigar facility, saboda haka ne yasa aka yanke shawarin zaka zamo General na sojojin california, wannan shine takardar shaidar...."

Junaid kawai binsa yake da kallo gaba ɗaya ya kasa cewa komai tsabar farin ciki sai cewa yayi "yanzu saboda wannan yaƙin da akayi ne yasa aka bani matsayin General? hakan ma na ƙasar california?..."

"ka cancanci haka ne shiyasa..."
jin muryar mutum ata bayansu ne yasa suka waiwaya da sauri suna son ganin ko waye wannan,
ganin sarki Raamud ne yasa Junaid ya nufi waransa da fara'a yana faɗin "Abbah saƙon ƙarin matsayi aka kawo mun..."
sarki Raamud yana murmushi yace "Junaid kenam ai nafika sani tinda nima saida aka kawo mun takardar nasa hannu..."
Junaid baki ya gagara rufuwa yace "kenam kaima harda signing ɗinka acikin takardar?..."
Jinjina kai kawai sarki Raamud yayi tareda ƙarasowa cikin falon ya nemi kujera ya zauna, suma Junaid da Judan zama sukayi kowa da Annuri a fuskarsa,
sarki ya kalli Judan da fara'a a fuskarsa yace "sannu da isowa Judan kaine ɗan aika kenam, kazo kuma matan gidan basa nan gashi ko lemo ba'a kawo maka ba..."
sai a lokacin Junaid ya tuna ashe dai ba'a kawowa baƙo ruwan sha ba, da hanzarinsa ya miƙe tsaye ya nufi kitchen cikin sa'a kuwa ya samu abinci a flask da miyan ferfesun chicken ya ɗora plate da spoon akai ya kawo masa kan dinnig table sannan yaje ya buɗe frig ya ɗauko lemon juice da farro na ruwa sannan ya haɗo masa da kayan fruits yazo ya jejjera kayan abincin, ya ɗauki wuƙa yayi slice ɗin kayan fruits akan glass tray,
saida ya kammala haɗa komai tukun ya ɗago masa hannu yayi masa alama da yazo yayi lunch, tasowa yayi da murmushi akan fuskarsa ya nufi wajen dinnig yanda Junaid ya haɗa
masa kayan food,
har ya fara cin abincin ya dakatar tareda cewa "kashhh ..."
Junaid har zai bar wajen yaji sautin Judan da sauri ya juya tareda tambayarsa "lafiya kuwa?..."
Ɗan turo bakinsa yayi yace "banga wannan ruwan tea ɗin da mommy take haɗawa ba,
cikin rashin fahimta Junaid yace "wani tea kenam, oh tea kakeso a haɗa maka?.."
Judan yace "No no nooo akwai wani tea wanda mommy take haɗawa ba tareda tasa milk da sauran haɗe haɗe ba, kuma akwai daɗi sosai domin ban taɓa shansa ba sai randa nazo gidan nan..."
Ɗan tsuka Junaid yayi sannan yace "kace empty tea kake so mana"...
Judan rufe idonsa yayi tareda faɗin "Kashhh ka kasa fahimta ta..."

Sarki Raamud yana daga kan sofa yana jin draman da suke yi sai faman ƙunshi dariya yake, shi Junaid ne yafi bashi dariya da har baƙo ma yasan kalar girke girken Hajia Fateema amma shi har yanzu ya kasa gane wani irin shayi Judan yake masa magana akai ba,
ganin Junaid bazai gane ba yasa yayi gyaran murya tareda faɗin. "Junaid tsawon shekaru kana tareda mahaifiyarka amma baka san wani irin shayi takeyi mai daɗin gaske ba..."
Junaid yace "toh kunata cewa tea marar milk toh ai Ni bazan iya sha ba tareda milk ba.."
Sarki yace "yana nufin shayin na'a-na'a kasan akwai wasu saiwowi da take sawa masu daɗin gaske, sai sugar amma duk wanda yasha saiya manta ƙofar gidansu ....?

"Okayyy na tuna, wannan haɗin kam sai mommy don ni bansan yanda takeyi ba, saidai ka jira ta dawo tinda ba yau zaka koma ba..."
a cewar Junaid!
Girgiza kai Judan yayi tareda faɗin "gaskiya I can't wait, a ƙira Hafzat tazo ta haɗa mun..."
Sarki yace "ehh tinda tana nan ita saita zo ta haɗa maka, ai naga duk wacce ta zauna agurin Hajia saita koyi komai na girki da sauran abubuwan zamani..."
Junaid yace "ok bari na ƙira maka ita.." ya wuce yana jinjina kai shidai yasan wayon Judan kawai so yake ya kalleta shiyasa ya fake da hakan...
kai tsaye ɗakin Hafzat ya wuce,


Hafzat tana ƙwance asaman katafaren gadonta tana lumshe da ido kamar mai yin bacci ƙwatsam taji bugun ƙofa a hankali, tana son tambayar ko waye amma hakan ya gagara daƙer ta tashi jiki a mace tana jan ƙafa taje ta buɗe ƙofar,
ganin Junaid yasa ƙirjinta yayi wani rass dasauri taja da baya domin tinda tazo gidan nan bai taɓa zuwa koda bakin ƙofar ɗakinta ba sai yau,
Junaid tsayawa yayi yana kallonta cike da mamakin irin tsoron da take masa, baisan dalilin da yasa take jin tsoronsa ba,
nafarko shi ba wani haɗe mata rai yake yi ba, har yanzu bai nuna mata asalin kansa ba amma duk da hakan tana nuna tsoronta akansa, hakan kuma yana shirin sosa masa zuciya,
ƙarasa shugowa yayi ya nemi guri ya zauna a bakin gadonta idonsa akanta yace "zo ki zauna"
jiki na ɓari ta soma girgiza masa kai alamar a'ah,
ƙara maimaita mata yayi kuma du ta sake girgiza masa kai, ransa ne yayi matuƙar ɓaci yakai hannunsa saitin goshinsa yana murzawa cikin zafin nama ya zaburo ya cabko hannunta sannan ya janyo ta dab dashi yana zaro mata ido yace "zauna nace..."
ba shiri ta ɗosana ɗuwawunta a bakin gadon tana ajiyar zuciya,
ba tareda ya kalleta ba yace "me kike tunani akaina ne?..."
shuru tayi masa ba tareda ta bashi amsa ba, ya kuma cewa "nayi miki kama da dodo ne ko kuma kina tunanin zan cutar dake ne?...."
kanta a sunkuye ta kasa ɗagowa balle ta iya bashi amsa,
ransa ne yayi matuƙar ɓaci a fusace ya daka mata tsawa tareda faɗin "I hate dis nonsense, idan ina miki magana kina sharar dani wata rana zanyi ball dake ..."
Hafzat a gigice ta ɗago tana kallonsa lips ɗinta na kakkarwa tama rasa mai zata ce masa,
. haka kawai Junaid yake mata ƙwarjini tin daga lokacin data fara ganinsa ta soma jin shakkarsa domin ta juma bataga namiji dirarre ƙarfaffa mai faffaɗar ƙirji irin na Junaid ba, gashi asalin kyakykyawa ne ga lips ɗinsa kamar na mace ƙarami dashi ga yaci launin maroon colour, ga sumar kayi baƙi ƙirin lallausa a ƙwance luf² har zuwa sajensa zuwa gemun, haƙiƙa duk macen data haɗa ido da Junaid bazata taɓa sanin Lokacin da zata shiga wani hali ba,
Hafzat ko kaɗan bata ƙaunar Junaid yazo yanda take domin bazata iya juran ganinsa ba, shiyasa idan tana gabansa kanta yake ƙasi bata son ɗagowa ta kalleshi,
a yanzun ma bata san lokacin da idonta suka kafu akansa ba, ko ƙibtasu bata yi, wani dogon tunani ta faɗa ciki still idonta akansa,
ganin kallon da take masa ne yasa shi mamaki yana tunanin meye dalilin da yasa ta zuba masa na mujiya har haka, hannu yakai saitin idonta yana karkaɗasu yanason ganin shin a hayyacinta take ko sumar zaune tayi,
firgit tayi a tsorace ta soma faɗin "innalillahi wayyo Allah mijin Aljanna..."
kallonta yayi cikin rashin fahimta yace "kin haukace ne?..." girgiza masa kai tayi tareda cewa "a'ah..."
jinjina kai yayi sannan yace "kin iya shayin na'a-na'a?..." dasauri ta ɗaga masa kai alamar ehh, yace "aina kika iya?.." cikin sanyin murya tace "agurin Mommy.." jinjina kai yayi yace "ok kizo ki haɗa mana yanzu" yana kaiwa nan ya tashi yayi ficewarsa, ita kuwa bin bayansa tayi da kallo cikin wani irin yanayi data tsinci kanta a ciki...

Around 10 O'clock pm.
Sarki Raamud yana nan yanata kai kawo a falo ya kasa zama gaba ɗaya yana cikin damuwa na rashin ganin mommy, sai tambaya yaketa yi "wai shin har yanzu bata dawo bane? kuzo ku kaini asibitin nan naje na dubo ko lafiya tinda safe har zuwa yanzu dare.."

Shima Junaid yana zaune akan hannun kujera sai faman ƙiran wayan Ayush yake amma ba'a picking, gaba ɗaya ransa a ɓace yake domin basuyi akan zata kai wannan lokacin bata dawo ba, sai tsaki yake ta ja shi kaɗai..

Ita kuwa Hafzat da Judan suna saman dinnig suna night lunch su biyu, sai jan hankalinta yake da hirar masoya ita kuwa hankalinta yana kan su Junaid, shi yana damuwa akan rashin dawowar Yushert ɗinsa shi kuma Sarki Raamud yana damuwa akan Mommy toh abunda yafi bata mamaki shine "shin meye alaƙar Abbah da Mommy? Bayan ance su ba ma'aurata bane, gaskiya akwai ƙaƙƙarfar alaƙar soyayya a tsakanin mommy da Abbah..." a cewar Hafzat da take ta maganar zuci,
duk gidan nan ita kaɗai ta fahimci akwai soyayya a tsakaninsu domin ita take kusa da mommy akoda yaushe inhar tana gida, kuma suna yawan waya, yana daga part ɗinsa itama tana part ɗinta amma haka zasu ɗau lokuta suna waya, wani lokacin kuma sukan haɗu a guest room dake can wani part na gidan, tsararren waje na baƙi idan za'ayi wani ɗan taro! acan suke haɗuwa su sha lovayya, kuma Mommy takan tashi cikin dare misalin ƙarfe 12 ko 1 taje kitchen ta haɗo shayin na'a-na'a takai part ɗin sarki Raamud, saboda shi indai bai tashi yasa wani abu a cikinsa dadaddare ba akwai matsala, hakan yasa mommy take ɗauka masa wannan ɗawainiyar, soyayyarsu suke sha ba tareda kowa yasani ba a cikin gidan, amma ita Hafzat tana bibiye dasu itace CCT ɗinsu, kuma tana yawan ɗaukar wayar mommy da cewar zatayi Game ko kallo haka zata shiga gurin saƙonni taga duk saƙon soyayyar da sarki yake turo mata itama tamayar masa da reply na soyayya, wayan yana hannunta sarki yasha ƙiran mommy amma bata ɗauka saboda bata son su gane cewar ita tasan alaƙar dake tsakaninsu har sai sune suka bayyanar da kansu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login