Showing 108001 words to 111000 words out of 186041 words
shi sarki Raamud tunaninsa ya zai fara sanar wa mommy cewa yana sonta, kuma gashi yana da burin Auranta, shi ason ransa ko yanzu ta amince masa zai iya sawa a ɗaura masa Aure a gobe domin har sauran masarantu sun fara complain akan wai sarki Raamud yana zaune akan mulki ba mata, su a tsarinsu duk wanda zai zauna akan mulki sai yanada matar Aure, ansha kawo masa ƴaƴan sarakuna akan ya zaɓi matar Aure amma yaƙi zaɓa shi idonsa nakan mommy Kuma ya kasa sanar mata, a tunaninsa bazata yadda bane,
itama mommy gaba ɗaya hankalinta yana kan sarki Raamud, ganinsa take kamar mijinta, a duk lokacin da suka fake guri ɗaya kamar yanzu sai tayi tunanin kamar da mijinta take tare, har mantawa take da mijinta ya mutu saboda ganin sarki Raamud take kamar shi, domin kamar su ɗaya sakk kamar an tsaga kara, a duk lokacin da take kallon sarki Raamud bata sanin Lokacin da murmushi ke zo mata, kuma saita tsinci kanta a cikin farin ciki, ga kulawar da take samu a wajensa,
amma wasu lokuta idan ta tuno da yaranta saita ji ba daɗi a ranta, yanzu ma Junaid da Ayush ne suka faɗo mata arai, sarki Raamud ganin hawaye a fuskar mommy ne yasa shi firgita da sauri yasa hannu ya tallafo kanta yana faɗin "sarauniya lafiya kuwa? meya faru dake kodai na ɓata miki ne, dan Allah kiyi haƙuri! ki sanar mun abubuwan da bakyaso da kuma abunda kike so, ni kuwa insha Allahu zanyi ƙoƙarin ganin na faranta miki.."
murmushi tayi ganin yanda ya rikice akan ta, ta ɗago tana kallonsa tace " a'ah ba abunda kayi mun, kawai dai ina tunawa da yarana ne, bansan a wani hali suke ciki ba, dan Allah inaso naje garesu..." Sarki girgiza kai kawai yayi ba tareda yace komai ba, sai bayan ya ɗanyi jinkiri tukun yayi ajiyar zuciya yace "kuyi haƙuri sarauniya, insha Allahu zaki gana dasu! inaji ajikina suna nan cikin ƙoshin lafiya.."
mommy ɗagowa tayi kamar zata fashe da ihu tace "ni kawai inason sanya su a cikin idanuwana" murmushi yayi yace "shikenam ki ƙwantar da hankalinki zuwa end of the month zamu tafi Nigeria tare...". sai a wannan lokacin mommy tasau ƙayataccen murmushi ta ɗago suna kallon juna...
******
misalin ƙarfe 12 na rana motar Junaid ta ƙaraso cikin babban harabar cikin headquarter wanda yake zazzagaye da sojoji, parking yayi sannan ya fito jikinsa a sanyaye yasa hannu ya fito da Ayush jikinta sai faman kakkarwa yake ganin manya² sojoji suna riƙe da bindigu ga babu alamar wasa a fuskarsu, riƙo hannunta yayi suka nufi ciki, suna zuwa wasu sojoji suka tare hanyar shiga asalin cikin compound, tsayawa yayi yana kallonsu cikin ɓacin rai yace "Lafiya kuwa zaku tare mun hanya?.."
suka ce "Ance kada mu barka ka shiga ciki da zaran kazo..."
Junaid cike da mamaki ya kuma cewa "and what is your reason?.." haɗe baki sukayi waran cewa "Sorry Ogah umarni ne daga waran General..."
jinjina kai Junaid yayi tareda faɗin "okay fine.." har ya juya zasu nufi wajen motar suka ji daga sama ance "Captain Junaid come up we want to see you..." Junaid daidaita tsayuwarsa yayi yana kallon saman stairs ya amsa da "Okay Sir..." kallon Ayush yayi sannan yace "wait for me I'm coming back..." da sauri ya wuce ya fara taka matakala har saida yaje gidan beni mai hawa bakwai tukun ya shiga office ɗin da ake son ganinsa,
Shigarsa ya juma sosai aciki kafin ya fito hannunsa riƙe da farar takarda, fuska ba Annuri cikin fushi ya soma sauƙowa down stairs,
laifin da ya aikata zaɓi biyu aka bashi a matsayinsa na Captain, sanar masa akayi koya zaɓi zaman gadurum na tsawon kwana biyar ko kuma a bashi takardar sallama, already karɓar takardar sallama yayi saboda gani yake yafi ƙarfin zama a gadurum kuma bayan haka yaransa sojoji zasu raina shi ne, shidai ya karɓi takarda saboda yasan daga baya zasu mayar dashi bakin aikinsa domin Junaid yana musu aikin da ba kowani soja ne zai iya ba...
Bayan ya sauƙa ƙasi gani yayi an ɗauke Ayush babu ita a wajen, waige-waige ya fara yi yana tambayar sojojin wajen, da hannu suka nuna masa yanda marshal yake a cikin ƙatuwar motarsa yana ta faman danne² wayansa, da gudu Junaid ya nufi wajensa yana faɗin "please Sir where is my wife?..."
Marshal ko ɗagowa baiyi ya kalle shi ba, durƙusawa Junaid yayi yana roƙonsa akan ya sanar masa ina aka kai Ayush ɗinsa, marshal gajiya yayi da jin surutan Junaid haka yasa ya fusata yana ɗaga murya yace ",you will shut up? meya zaunar dakai bayan an sallame ka? shin baka zaɓi barin aikinka ba? ka kasa cika alƙawari, matarka nasa an kamata tana can cikin maƙarƙama a ɓoye, dole sai hukuma sun hukuntata...". Junaid kamar zaiyi ihu yace ", please officer inason sake sanyata acikin idanuwa na Please..."
Marshal yace "munga tana da juna biyu ne yasa muka sassauta mata amma badan haka ba sawa zanyi a kakkarya mata sawaye, saboda haka bazaka taɓa ganinta ba saidai ku haɗu a kotu...."
Zaro ido waje Junaid yayi duk yabi ya jiƙe jikinsa da gumi sai a yanzu yayi nadamar kawo Ayushh....
*DAN ALLAH KUYI HAKURI MATAR DAMISA FANS, WLLH INA WANI AIKI NE TIN ASUBA MUKE FITA BANA DAWO GIDA SAI DARE, TOH LOKACIN A GAJIYE NAKE GA DA WURI NAKE BACCI*
*AMMA INSHA ALLAHU DAGA YAU MUN GAMA, YANZU MAH WANI IRIN MASIFAFFEN BACCI NE YAKE DAMUNA SHIYASA NA HAƘURA DA YIN TYPING HAKA SAI ZUWA GOBE, GOBE BA KOMAI ZANYI BA ZANYI MUKU UPDATE AMMA GA WANNAN KU RAGE DUK DA NASAN YAYI KAƊAN SOSAI AMMA KUYI HAKURI 🙏🙏🙏*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 55 ➡️ 56
Junaid a fusace yake driving motor kamar zai tashi sama bai samu ganin Ayush ba da haka ya ƙariso gida,
ita kuma Ayush cikin wani ɗaki aka kaita na tsaro, ɗaki ɗaya ne amma saidai akwai katifa da wasu abubuwan da baza'a rasa ba, ɗakin yayi kyau, sai wani soja da yake tsaye ta wajen ɗakin yana gadinta! tana ƙwance ta haɗe kanta da gwiwa sai faman rera kuka take a haka ta wuni tana wannan kukan, ji tayi an buɗe ɗakin da sauri ta ɗago tana kallon bakin ƙofa a tunaninta Junaid ne sai kuma taga wani soja ne daban ya shugo da kular abinci, ya ajiye a gabanta yana faɗin "ki tashi ki ci abinci da zaifi miki.." bata kula shi ba saima ƙara ƙarfin kukan da take yi, shi kuwa miƙe wa yayi ya fice daga ɗakin...
washe gari Junaid ne yaje gidan malam Lawan ya kora masa bayanin abunda ke faruwa ya kuma cewa "dan Allah malam ka temaka mun Yushert ta dawo hannu na, matata ce kuma sannan tana da juna biyu bai kamata ace tana hannun sojoji ba, ni nariga da nasani akwai ƴan iska acikin su, banaso wani abu yazo ya faru domin nasan dole zanyi kisan kai duk wanda ya taɓa mun matata.."
malam Lawan idonsa akan Junaid yana girgiza kai yace "insha Allahu ba abunda zai faru, kuma ina tunanin sun shigar da ƙara a kotu tin ba yau ba, yau kuma za'a shiga shara'a, ni a halin yanzu babu abunda zan iya amma zan tura ka gurin abokin mahaifinka wato Barrister Aminu insha Allahu zai tsaya maka.."
girgiza kai Junaid yayi yace "ba lallai ba domin nasan bazai goyi bayan Yushert ba, saboda ba zarginta ake yiba ta tabbata da gaske ta kashe mahaifiyata, kowa yasan da hakan, dole nasan sai an yanke mata hukunci sakamakon hujjojin da ake dasu, ban san yazanyi ba .."
Malam dafa kafaɗarsa yayi sannan yace "ka kwantar da hankalinka insha Allahu za'a dace, amma Ayshert ta aikata babban kuskure sai dai kawai ka dage da addu'a ka kuma ƙara da haƙuri..."
Junaid miƙewa yayi da sauri yana faɗin "kafin a tafi da ita zanje na ganta, dole sai naga matata ko kuma ran kowa ya ɓaci domin bazan juri rainin hankali ba..." yana kai ƙarshen maganar yayi ficewarsa, kai tsaye headquarter ya nufa da motarsa..
Ayush tana zaune akan katifa ta haɗe kai da gwiwa kamar mai yin bacci amma sai dai akwai tunanin da take yi, wani soja ne ya shugo cikin ɗakin da saurinsa sannan ya mayar ya rufe ƙofar, tsayawa yayi yana ƙareta da kallo tareda cije lips ɗinsa, muryarsa kamar wanda yayi maye yace "ke ƴan mata ki shirya yau zaki haɗu da mutanen kotu, yanzu haka nazo tafiya dake ne ana jiranki, ki sani hukuncin ki kisa ne kamar yadda kema kika yi kisan kai amma kafin ki mutu zan ɗanyi koɗuma dake ko zanji sanyi², tinda aka kawo ki nake jin ƙwaɗayinki please kiban haɗin kai yanzu zan gama, bamai kallon mu..."
ita kuwa tana jinsa ko ɗagowa batayi ba, ita kaɗai tasan irin takaicin da take ji, yanayin maganarsa na rashin ɗa'a ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,
durƙusawa yayi a gabanta ya ƙara matsowa daf da ita yana mata wani irin kallo tareda fitar da harshensa yana lasan lips ɗinsa, hannu ya ɗago ya dafa kafaɗarta, ɗagowa tayi a fusace ta zazzaro manya-manyan idanuwanta tana kallonsa, ido yayi jawur duk da wannan kallon da take yimasa baisa ya janye hannunsa ba saima shafata da yake yi yana washe baki tareda faɗin "wayyo ƴar fara ƙyakykyawa, mai zubin halitta irin na ƴan aljanna...". yana shafata har zuwa wuyanta! Ayush idonta ta sauƙar kan wuƙar dake sokare cikin takalminsa da sauri takai hannu ta zaro wuƙar ta sauƙar da hannunsa wanda yake shafata dashi ta datsa masa wuƙar a hannun duk saida ta cire masa yatsun hannu guda huɗu, baisan lokacin da ya fara kurma ihu ba, kafin kace mai jini ta ko ina, ga kuma yatsun hannu a yaje a ƙasi, yana riƙe da hannu sai ihu yake yana neman agaji, ita kuwa kifar da kanta tayi kan gwiwarta kamar yanda take a farko ko sauraronsa bata yi ba saima toshe kunnuwanta datayi da hannu biyu,
da ƙarfin gaske aka bankaɗo ƙofar ɗakin sojoji ne waran su shida suka zo jin ihun da ake yi, abunda suka tarar ne ya basu mamaki, ɗago da majinyacin sukayi suna tambaya meya faru dashi ne amma ya kasa basu amsa sai nuna yatsunsa da yayi a ƙasi,
zaro ido sukayi ganin yatsu a ƙasi ga jini duk ya wanke wajen, kallon yanda Ayush take zaune sukayi ko ɗagowa batayi ba balle abun ya dameta...
ɗaya daga cikin sojojin ne yaje gaban Ayush a fusace yasa hannu ya riƙo damtsenta ya ɗagota tsaye a tsawace yake faɗin "kee me kika aikata masa? kin zamo ƴar ta'adda koh?..."
harararsa tayi fuska a haɗe tace "ka sakar mun hannuna ni matar Aure ce..."
ɗago hannu yayi zai mareta wani daga ciki yayi saurin riƙe hannun yace "a'a Commander ka ƙyaleta yanzu haka kotu za'a tafi da ita, zatayi bayani..."
Ayush tarar bakinsa tayi da cewa "kafin aje kotu ma zanyi bayani saboda wannan case bana kotu bane..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta wani soja yana biye da ita a baya,
Ƙwafa Commander yayi yana nuna ta da yatsa yace "wannan yarinyar wallahi badan Captain Junaid ba da ba abunda zai hana na buga mata bindiga a kayinta..."
ya ƙarisa maganar tareda riƙe abokin nasan wanda aka yankewa yatsu ya fita dashi, ɗayan sojan kuma kwashe yatsun yayi a farar leda shima ya fice..
Ayush ce a gaban General da Marshal da sauran sojoji masu manyan miƙami da kuma ƙananun sojaji duk suna tsaye bayan sanar musu da abunda Ayush tayiwa ɗaya daga cikin sojoji, a tsawace General yake tambayarta dalilin da yasa tayi haka, amma Ayush tayi shuru babu bakin magana kai a sunkuye sai faman kuka take, daiden lokacin da Junaid ya shugo da motarsa da gudu, da sauri yayi parking ya fito ganin yanda aka taru ga kuma Ayush a durƙushe a rana, da gudu ya iso gurin baiyi magana wa kowa ba sai nufan gurin da Ayush take yayi, yana zuwa yasa hannu ya ɗagota tsaye yana goge mata hawayen fuskarta da hannu,
ji yayi Marshal ya darara masa tsawa tareda faɗin "umarnin wa kabi ka ɗago da ita? shin meye matsayinka a yanzu da har zakayi mana wannan shishshigin...". Junaid bai kulashi ba yana kallon Ayush yace "Yushert what happened to you?.." kuka ne yaci ranta sosai tasa hannu ta rungume shi, shima rungumarta yayi rai a ɓace domin baiji daɗin ganin Ayush a wannan yanayin ba, General ne ya katse shi da cewa "Junaid mai kakeyi haka, waya baka izinin shugowa wannan quarters?..."
kallonsa Junaid yayi sannan yace "sorry Sir but what happen to