Showing 102001 words to 105000 words out of 186041 words

Chapter 35 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53912

ɗin kayin Junaid, duk ɗinsu haka suka tashi su ashirin suka nufo gurin Junaid suna kuka suna faɗin "Babaa! Babaaa!! Babaaa!!! Baban muuu!!!!..."
Junaid ja da baya yake sosai sai faman hashaska su yake, a firgice ya kalli yanda Ayush take a ƙwance yaga ta washe baki har zuwa kunne tana masa dariya ga babu haƙwarai a bakin sunyi ɓaɓurka.
Da gudun gaske Junaid ya miƙe ya fara gudu kamar zai fura sama haka yake wannan gudun ceton rai, torchin ma bai san lokacin da ya jefar shi ba,
yana zuwa saitin wani bishiya kawai ya kama yahau kan bishiyar nan, saida yaje kusan ƙarshen bishiyar tukun ya tsaya yana fitar da numfashi daƙer, yana ganin kamar ya tsere daga hannun jariran nan, haka ya ƙwantar da kayinsa kan bishiyar ya lumshe ido yana haki can yaji kamar ana taɓa shi da sauri ya buɗe idonsa yana buɗewa yaga wannan matar mai haihuwar nan ne a gabansa akan bishiyar, idanuwanta sun koma green ga yanda take wani irin dariya bakinta har kan kunnenta, ga babu haƙori ko ɗaya a bakin, bakinta kuwa duk jini a firgice Junaid yayi wani irin ihu a razane ya zamo daga kan bishiyar ya faɗo ƙasi, kansa ne ya bugu da wani dutsi nan take ya sume a wajen.....


******


A can headquarters kuma sunata ƙiran wayan Junaid akan a sanar masa cewar wani mutumi yazo ya sanar cewar shi da kansa yakai Ayush har jejin da take da mashin ɗinsa, amma basu samu wayarsa ba, wayar tana ringing amma ba'a picking dake a cikin motarsa yabar wayar,
Malam Lawan shima yakai sau nawa yana ƙiran wayansa amma ba'a picking har zuwa washe gari Sojojin headquartersu suka yi tracking wayarsa suka gano a yanda yake, abun ya basu mamaki ganin a dajin da akace Ayush take anan shima yake, anan suka fara shiri zasu je cikin wannan dajin, sojoji guda biyar aka ware waɗanda zasu je kuma acikin elekwabta zasu tafi saboda mota bazata shiga dajin ba,


Around 10:00AM Junaid yana ƙwance a cikin daji tin cikin dare har zuwa yanzu bai farfaɗo ba, ga hadari yanda ya haɗu sai walƙiya ake lokaci guda aka fara ruwan sama, wannan ruwan da yake sauƙa masa ne yasa ya tashi a firgice yana ambaton sunan "Yusherttt...." waige-waige yake ganin shi kaɗai a cikin daji yasa ya miƙe yana tangal-tangal kamar zai faɗi haka yake tafiya hajijiya na ɗibarsa ga kuma ruwan sama yanda yake jibgarsa, daiden lokacin saiga elekwabta na sojoji yanata yawo a sama, suna neman yanda zasu ga Junaid da Ayush! sunyi nasarar ganin Junaid sakamakon ɗaga musu hannu da yake yi, a hankali elekwabta ta sauƙo duk suka fito da bindigu a hannunsa suka zo gurin da yake suna faɗin "Ogah Junaid are you okay?..." wani irin matsanancin ciwon kai ne yake damunsa ga yunwan da yake ji da ƙishin ruwa haka suka rirriƙe shi suka saka shi a cikin jirgin, su kuma suka bazu neman Ayush acikin wannan ruwan ......




*TOH PAH 🤣 KU KUKE GANIN MU BA MU KE GANINKU BAA🤣🤣🤣*

*AUNTY HABIBA, AUNTY KHADIJA, AUNTY HAJJAJO NACE BAAA HOW MARKET🤪🤪*

*WANNAN PAGE ƊIN NA ALJANU NE BA NAMU BANE🤣🤣🤣🤣*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 51 ➡️ 52



_________________ Doctor Hasheem ƙwance yake akan sofa ya ɗora hannunsa ɗaya akan goshi yana fuskantar ceilling ido a rufe sai shan bacci yake a nutsu, baccin wahala, yana cikin baccin yaji anata buga ƙofar falo dake shima a falon yake a razane ya farka yana addu'a, bugu ake bana wasa ba haɗe rai yayi fuska a murtuƙe ga yayi wani irin muni bugu da ƙari ma sumar kansa da aka aske, sai fama tsuka yake tayi ya miƙe daƙer yana ɗingishi yayi bakin ƙofa yana faɗin "wai waye ne kam dallah.."
ya ƙarasa maganar daiden lokacin ya buɗe ƙofar ƙirjinsa ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin Police waran su biyar sunyi cirko-cirko suna kallonsa, a kiɗime Dr Hasheem ya fara ƙinƙina yana faɗin "la la lafiya kuwa na ganku?..."
ɗaya daga ciki ne yace "inda lafiya ne ai bazaka ganmu a gidanka ba..."
Dr Hasheem buɗe baki yayi yana shirin yin magana ƙwatsam idonsa ya sauƙa akan Daddy wato mahaifin Maimoon, juyawa yayi da gudu zai koma ciki ƴan sandan sukayi saurin riƙo shi suna cewa "Oh guduwa wai zakayi?.."
rantse² ya fara yi yana magiya haɗe da cewa "dan Allah ku temaka mun wallahi jiya na fito daga hannun sojoji, kuyi mun rai da Allah..." Baban Maimoon ne yazo gabansa ya tsaya yana huci shi alokacin bai ƙi yasa bindiga ya harbe kan Dr Hasheem bama, wani irin kallo ya watsa masa sannan yace "kai Kanada bakin magana ne Hasheem? shin ka tuno da yarinyar da kayiwa fyaɗe? wallahi kaban mamaki matuƙa, nayi tunanin kai mutumin kirki ne har na yarda dakai na baka amanar ƴata ashe kai ba ɗan goyo bane, kai butulu ne fool like you! wallahi albasa bata yo halin ruwa ba, mahaifinka mutumin kirki mai dattaku inda ace yana raye kayiwa ƴata fyaɗe toh wallahi babu abunda zai hana ya yageka daga cikin ƴaƴan daya haifa..."
Dr Hasheem kuka yake sosai ya haɗe hannayensa biyu yana roƙon baban Maimoon "dan Allah Daddy kayi haƙuri ka yafe mun, nayi kuskure babba nasan ban kyautawa Maimoon ba, amma wallahi har cikin zuciyata banyi niyar aikata mata haka ba saboda Maimoon macece mai mutunci kuma ta fito a gidan mutuntaka, har yau har gobe inason Maimoon, Ni ba mutumin banza bane saboda bana harkar mata, bana zuwa gidan club bana shaye-shaye kuma Ni ba ɓarawo bane...." kafin ya ƙarasa iddasa maganarsa Daddy yayi saurin darara masa wani irin gigitaccen tsawa tareda cewa "sai dai kai butulu ne, banason jin komai daga bakinka Hasheem domin kana ƙara hura mun wuta ne acikin zuciyata, ji nake kamar na murɗe maka wuya a yanzun nan, amma ba komai yau zakayi ƙwanan bayan kanta zuwa monday zamu shiga kotu daga nan za'a yanke maka hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 25, hukuncin fyaɗe kenam, na barka lafiya..." yana gamawa da Hasheem ya maida kallonsa kan ƴan sandan gurin yana ce musu "kuje dashi kuyi ta dukansa har saiya fita hayyacinsa kafin ranar da za'a shiga kotu, a tura shi prisoner yaje ya ɗanɗani kalar abincinsu har ya tsufa ya sheƙe...." cikin ɓacin rai ya ƙarasa maganar tareda wucewa a fusace yayi tafiyarsa, yana jin yanda Dr Hasheem yake roƙonsa da yi masa magiya amma ko sauraronsa baiyi ba,
Haka ƴan sandan nan suke jansa suna ƙwaɗa masa sandunan hannayensu, fashewa yayi da matsanancin kuka yana mai ƙara jinjina kansa a halinda ya tsinci kansa...


******


Junaid yana zaune acikin elekwabta yana dafe da goshinsa tunowa yake da abubuwanda suka faru dashi a daren jiya gaba ɗaya ya rasa sukunin sa, ga idanuwa sunyi lufu-lufu, yana cikin wannan halin yaji ihun Ayush ya daki dodon kunnensa da ƙarfin gaske, a kiɗime ya ɗago yana waige-waige, ihu na biyu ya sake ji a gigice ya sauƙo daga kan elekwabta da gudun gaske yake bin yanda yake jin ihun ga kuma ƙarar harbin bindiga da yake ji, ji yayi kamar furawa yake tsabar gudun da yake tiƙa yana haɗawa da tsalle, yana isowa wajen ya daina jin ihun sai harbi da yake ji, haka yake ratsa jeji yana kutsawa ciki ko waiwaye baya yi haka yake tiƙan gudu,
itama Ayush sai faman gudu take tana waiwaye, jin ta bugu da abu ne yasa tayi saurin kallon gabanta ƙara tasau tayi baya sauran kaɗan ta faɗi yayi saurin riƙo hannunta ya jawota jikinsa suna maida numfashi a tare,
da sauri yakai hannunsa biyu ya tallafo fuskarta suna kallon juna Junaid yana haki yace "Yushert ki ƙwantar da hankalinki ba abunda zai sameki..."
tana kuka cike tsoro da firgici ta ƙanƙame hannun Junaid tana faɗin "Yaya Junaid zasu kashe ni ne, na gansu da bindigu suna harbawa wallahi kasheni zasu yi..."
tana maida numfashi sama² tareda waige-waige ko sun biyota,
kafin kace me sojojin har sun iso yanda suke a tsaye duk sun kewaye su sun saita bindigunsu, ɗaya daga cikine yace "Ogah Junaid ka miƙo mana ita nan, saboda ance mana duk rintsi duk wuya mu tafi da ita..."
Ogah Junaid yana rungume da Ayush yace "ku jeku zan kai muku ita da kaina.."
suka ce "Please Ogah Junaid muna bin tsarin aiki ne, umarni ne daga shuwagabannin mu, idan kuma taƙi zamu harbeta ne..."
Ayush jin haka ta ƙara ƙanƙame Junaid jikinta na ɓari da ƙarfi tana kuka tace "dan Allah Yaya Junaid kada ka bari su tafi dani wallahi kasheni zasuyi.." ga tumbi kuwa ya fito sosai,
Girgiza kai Junaid yayi sannan ya ƙira sunan ɗaya daga cikin sojojin su murya a sanyaye yace "Commander inaso kamun wata alfurma please, ku bar mun ita a yanzu nace idan ta samu nutsuwa zan kai ta har quarters ɗin..." ya kalli sergeant yace "kuyi haƙuri nasan umarni ne daga sama amma kuyi mata uzuri saboda abunda ke cikinta, idan kun koma ku sanar cewa tana gurina amma nayi alƙawarin gobe zan kaita da hannuna pleasee my Man's...." ya marairaice yana musu magiya...
Sauƙar da bindigunsu sukayi suka ce "shikenam taci albarkacinka da kuma cikin dake jikinta amma badan haka ba babu abunda zai hana mu harbe mata ƙafa sannan mu kaita tinda ita tanada ƙafar guduwa...."
Jinjina kai Junaid yayi yana cewa "ok toh kuje ku zan isoku, motata tana bakin hanya..."
Commander yace "but ka cika alƙawari fa gobe ka kaita headquarter saboda kasan halin General, ga kuma marshal shima ya hura wuta a kai..."
Junaid kaɗa musu kai kawai yayi yana rungume da Ayush,
Sergeant yace "ok Ogah Junaid muje mu hau elekwabta sai mu sauƙe ka a bakin hanya ka shiga motarka, kasan akwai tazara mai nisan gaske daga nan zuwa bakin road..." Junaid ya amsa tayinsu yayi wa Ayush ɗaukar luɗa suka fara tafiya a cikin dajin nan, akwai ɗan nisa kaɗan kafin su je gurin da elekwabtarsu take...

Shi Junaid yana lallamin sojojin ne ba wai don yana jin tsoronsu bane sai don yasan suma bayin kansu bane, umarni aka basu daga wajen shuwagabanninsu gaba ɗaya shiyasa ya shugo da magiya a ciki saboda ya tseratar da Ayush....

Elekwabta suka shiga gaba ɗayansu still Junaid yana rungume da Ayush kamar wanda za'a ƙwaceta da ƙarfi, suna zuwa bakin hanya aka sauƙe su! su kuma sojojin suka yi gaba abinsu acikin elekwabta,
Junaid a seat back ya ƙwantar da Ayush yana faɗin "kwanta ki huta..." shima ya zagayo ya shiga ya fara tuƙin motar a hankali daga baya ya soma gudu da motar kamar zai tashi sama, Allah² yake su shiga cikin gari domin ba ƙaramin wahala yasha ba, duk jikinsa sai ciwo yake masa ga wani matsanancin yunwa da yake ji, tin jiya da safe rabonsa da abinci...

Around 2:30pm Junaid suka iso gida a wahalce, parking yayi a wajen space parker ya fito da saurinsa ya zagayo ya buɗe Ayush, hannu yasa ya kikkimeta suka nufi cikin babban falon da zai sadasu da ƙananun ɗakunansu na ƙwanciya, kai tsaye upstairs ya haura, yana zuwa ƙarshen stair ya sake shan ƙwana ya ƙara haura stairs na biyu, yana kaiwa ƙarshen nan ya kuma haura na uku ana ukun ne ɗakinsa da ƙafarsa ya tura ƙofar da ƙarfi ta buɗu, yana shiga ya zaunar da Ayush a bakin gado, gaba ɗaya duk ta rarrame ta fita hayyacinta, har tayi duhu kaɗan ga rigar jikinta tin data tafi bata canza ba saboda iya shi kaɗai take da duk yayi datti yayi baƙi ƙirin, sumar kanta shima ya cakurkuɗe babu gyara duk yayi ƙura da datti, haƙwaranta har sun canza kolo saboda datti, ita kanta rabon da tayi wanka tin data bar hospital gurin Junaid, sai hamami take tayi.
idanu sunyi lufu-lufu sun shanye kamar wacce tayi maye haka take bin Junaid da kallo, shima durƙusawa yayi a gabanta ya ɗora hannayensa biyu saman cinyarta haɗe da riƙo hannayenta yana murzasu, cikin takaici yake kallonta fuska ba Annuri daƙer ya iya cewa "Yushert shin abunda kikayi kin kyauta mun kenam? shin kinyi wa kanki adalci? dubi yanda kika koma fa kamar wata marar gata, kin cutar dani sosai kin ƙuntata mun matuƙa sannan kin wahalar mun da yarona wanda baiji ba bai gani ba why Yushert?...."
kuka ne ya kuɓuce mata tana ture hannayensa daga cikin nata tareda faɗin "Ni ka ƙyaleni! rayuwata a cikin dajin tafi mun komai daɗi, bana son kasancewa da kowa guri ɗaya..."
Girgiza kai Junaid yayi sannan yace "amma kina sane da igiyar Aurena akan ki?..."
ƙura masa ido tayi tace "daman tsawon watannin nan baka sakeni ba?.."
cije leɓɓensa yayi yana kallonta yace "meyasa zan sake ki? alhalin keɗin rayuwata ce"
katse shi tayi da cewa "duk da kashe maka mahaifiya dana yi?..."
rufe idonsa yayi sosai yana cije lips ɗinsa wani irin tafasa zuciyarsa take yi kamar wanda ake hura masa wuta a ciki ya danne yayi ƙarfin halin cewa "please Yushert ki bar mun wannan maganar, mahaifina ya mutu ata sanadiyar iyayenki, mahaifiyarki ta mutu ata sanadiyata, haka kuma mahaifiyata ta mutu ata sanadiyar ki, shin acikin mu wa akafi cuta? Yushert inaso ki sani cewa ƙaddara bata taɓa tsallake bawa, yakamata mu rungumi ƙaddarar mu muyi haƙuri mu zauna...." bai kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login