Showing 42001 words to 45000 words out of 186041 words
da kuma kukan data sha,
murya ciki-ciki tace "Yaya Junaid kayi haƙuri waɗannan tambayoyin bazan iya amsa maka su ba,
Kamar yanda na gaya muku ni marainiya ce..."
da sauri Junaid ya juyo yana kallonta cike da takaici yace "ƙarya kike Yushert, ki faɗa mun gaskiya karki raina mun wayo..."
Ayush tace "Yaya Junaid mai kake so nace maka..."
Junaid wani irin kallo ya watsa mata yace "Yaushert bana son shirme fah, nace ki gaya mun wacece ke? banason munafurci da iskanci nasan akwai abunda yake cikin zuciyarki..."
Ayush ranta ne ya ɓaci ta zare allurar jinin da aka ɗaura mata ta sauƙa daga kan gado tace "wai shin Yaya Junaid kai ka kawo ni gidan nan ne? meyasa kake son takura mun ne? dan Allah ka rabu dani na roƙe ka, idan kuma baka son zama na agidan nan to ni yau zan bar muku gidan, na gode Allah tinda har ka samu lafiya...."
tana kaiwa nan tayi ficewar ta,
ga sauran jinin da ta bar masa.
Junaid buɗe baki yayi yana kallonta har ta fice,
yayi mamakin jin kalaman nan daga bakin Yushert,
dafa kansa yayi yana hura iskar bakinsa tsabar tsananin ciwon kai da yake damunsa,.
Maimaita maganar ta yayi cewa "kin gode Allah tinda na samu lafiya?..."
Abunda ya tsaya masa arai kenam...
Ita kuwa Ayush tana zuwa ɗakinta ta ɗauki hijab ɗinta ta saka ta jawo jakarta tana kuka ta fice a ɗakin,
Daman kayanta a shirye suke dasauri ta sauƙa daga down stairs, ta fice a falon!
gudu-gudu sauri-sauri haka Ayush ta nufi gate tana jan akwatinta,
Shi kuwa Junaid yana tsaye ta window yana kallonta....
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 23 ➡️ 24
Doctor Hasheem ne ya shiga falo da sallama a bakinsa gani yayi falon yayi tsit ko motsin mutum babu, haka ya wuce ɗakinsa yaje ya rage kayan jikinsa ya shige toilet yayi wanka ya fito ya sanya ƙananun kayansa na zaman gida tukun ya fito falo ya wuce kitchen domin ba ƙaramin yunwa yake ji ba, haka yaje ya samu kitchen wayam ba'a yi girki ba,
taɓe baki yayi yace "wato yarinyar nan tana can tana ta faman shan baccinta bata samu damar yimana girki ba kenam, zanje na sameta dan ƙaniyarta..."
ficewa yayi daga kitchen rai a ɓace ya nufi ɗakin Lailah!
yana zuwa kuwa ya buga ɗakin da ƙarfin gaske ya buɗe baki zaiyi masifa yaga abu a sama yanata lilo, sake baki yayi yana kallon ikon Allah, saida yasa hannu ya murƙusa idanuwansa sosai yana kallon Lailah wacce take rataye a saman fanka ga kuma jikinta duk ya farfashe dake daga ita sai breziya...
A tsorace ya furta "Lailah?..."
Shuru bata amsa ba sakamakon sumar datayi, a ruɗe ya jawo kujerar mirror ya hau ya sinco ta ya sanya mata riga, da gudu ya fice a ɗakin yaje ya ɗauko box na magani tareda bottle na ruwan sanyi ya dawo ɗakin Lailah, harda hawayensa sam baiji daɗin ganin Autarsu a cikin wannan halin ba, haka ya shiga yayyafa mata ruwa a gigice kuwa ta farfaɗo tana faɗin "dan girman Allah Ogah Junaid kayi mun rai, wallahi bazan sake ba, dan Allah ka ƙyaleni haka wayyo mutuwa zanyi..."
Doctor Hasheem jin abunda Lailah take faɗa ne yasa ransa yayi matuƙar ɓaci yace "Junaidd ne yayi miki wannan aikin?.."
Lailah tana fitar da numfashi daƙer ganin Yayanta ne yasa ta rungumeshi tana kuka sosai tareda faɗin "Yayana wayyo Allah, Ogah Junaid ne..." kuka ne yaci ranta sosai, haka Doctor Hasheem yake bubbugar bayanta a hankali yana rarrashinta, shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin da yake ji aransa...
yana sharar ƙwalla haka yayi treatment ɗin jikin Lailah ya bata magani tasha, gaba ɗaya ta zamo kalar tausayi, idanuwanta sunyi lufu-lufu,
kwantar da ita yayi tareda faɗin "bari naje na sama miki abunda zaki ci ko?.."
tashi yayi a fusace ya ƙudurta a ransa cewa wannan karan kam bazai ƙyale Junaid ba, saiya je har gida ya sameshi akan abunda yayi wa Lailah...
******
Ayush tana tsaye a bakin gate tanason fita saidai maigadi ya hanata fita sakamakon nunin da Junaid yayi masa daga saman window ya masa alamu da hannu na kada ya barta ta fita,
Ayush tayi-tayi akan ya barta ta fita amma maigadi yaƙi, Ayush ce ta lura da yanda maigadin yake kallo, itama ɗaga kanta tayi sama taga Junaid ne ashe ya hana shi buɗe mata,
Ayush kamar zatayi kuka haka take jumping da ƙafafunta a cikin ranta tace "wayyo na shiga uku indai ban bar gidan nan ba toh tabbas asirina saiya tonu, kuma ba ƙaramin hukunci Yaya Junaid zai ɗauka ba, nafison kafin su ankare da sanin ko wacece ni nabar gidan kawai..."
tana cikin wannan tunani sai ta jiyo Muryar Angel ta nufo gurinta tana faɗin "Ayush yana ganki da akwati lafiya kuwa?..."
Girgiza kai Ayush tayi ba tareda ta furta komai ba,
Angel ce ta sake yin magana tace "kodai Junaid ne ya koreki?.."
Girgiza kai tayi tace "a'ah babu komai.."
Angel tace "toh tinda babu komai ki shugo ciki, kin manta zaki rakani gurin malamin da kikace zan musulunta a hannunsa.."
Murmushi Ayush tayi tace "a'ah ban manta ba Aunty Angel"
Angel tace "to yanzu kuwa zaki rakani muje mu kinga bamuda isasshen lokaci.."
Ayush ta amsa mata da "toh.."
ta furta hakan tareda ƙara ɗaga kanta sama tana kallon Junaid dake tsaye a window ɗakinsa shima binta yake da kallo...
Mommy bayan ta kammala yiwa Sauro magani fito dashi tayi har zuwa bakin gate ta tura maigadi akan yaje ya dubo mata mai keke napep, Sauro zama yayi domin bazai iya juran tsayuwa ba, ita kuwa Mommy sai haƙuri take bashi tana "sannu maza bawan Allah, kana ji kana gani akasa ƙarfe aka cire maka yatsa tsabar rashin tausayi irin na Junaid..."
Bayan wasu ɗan mintuna saiga maigadi acikin napep ya ƙirawo shi, daƙer Sauro ya shiga ciki ya zaune, mommy ce ta biya kuɗin napep sannan ta bawa sauro kuɗin kashewa har Naira 100k!
Juyawa Mommy tayi zata koma ciki saiga Angel da Ayush sun fito a tare suna shirin shiga mota,
Mommy tace "yanzun sai ina?.." Angel tana yamutsa fuska tace "mom zamu je unguwa ne da zarar mun dawo zan sanar miki yanda muka je..."
Mommy tace "toh shikenam sai kun dawo Allah yasa muji alheri..." tana kaiwa nan ta shige cikin falo..
Su kuma Angel tada motar tayi ta karya ƙwana ta miƙi hanyar gate, ita Angel tana sanye da Abaya da ɗan gyalensa tasha makeup sosai tayi kyau,
ita kuma Ayush dogon hijab tasa mai hannu irin hijabi jalbab ɗin nan amma har ƙasi yake ja, fuskarta a koɗe ba kwalliya, haka maigadi ya buɗe musu suka fice a gidan gaba ɗaya, kai tsaye gidan malam lawan suka miƙa...
Suna fita kuwa saiga motar Doctor Hasheem sun ganshi amma basu tsaya sauraronshi ba, parker motarsa yayi daga waje sannan ya fito a fusace ya fara knocking, maigadi ne ya buɗe ganin Doctor Hasheem ne yasa shi faɗin "sannu da zuwa Doctor ka shugo mana.."
Doctor Hasheem bai nuna wa maigadi cewa akwai matsala ba sai cewa yayi "yawwa Baba! Junaid kuwa yana ciki?.."
Maigadi ya amsa masa da "eh yana nan"
Dasauri Doctor ya shige yana sauri har ya iso compound, tsayawa yayi yana knocking ƙofar falo ba jumawa aka buɗe, Mommy ganin Doctor yasa ta murmushi tace "wata sabon gani, wato sai yau aka tuna dani ko.."
Doctor yana sosa ƙeya ya gaida mommy sannan ya tambayeta Junaid, Mommy tace "toh ka shugo mana Junaid yana can ɗakinsa..."
Doctor Hasheem bai tsaya jin abunda Mommy zatace ba haka yayi saurin haura upstairs yana zuwa kuwa ya tura ɗakin Junaid cikin sa'a kuwa ya sameshi yana kwance,
Shima Junaid ɗin ransa ne ya ɓaci domin ko wayene ba'a shugo masa ɗaki kai tsaye ba tareda excuse ba,
Doctor Hasheem ne yaje gaban Junaid ya tsaya yana nuna shi da yatsa tareda faɗin "amma kai Junaid wallahi bakada mutunci, kuma ka ban mamaki domin yin faɗa da mace ba jarumta bane hauka ne zalla da kuma rashin ilimi..."
Doctor Hasheem a fusace yake maganar domin ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba, shi kansa bai san abunda yake faɗi ba domin idonsa ya rufe...
Junaid yana kwance bai samu damar tashi ba haka yana jin yanda Doctor Hasheem ya tsaya masa akai yana gaya masa maganganu marasa daɗin ji!
Doctor Hasheem ne ya cigaba da cewa "saboda kai bakada wata ƙanwa ko ƴan uwa shiyasa zakana musgunawa ƴaƴan mutane, toh yau kam na zo maka warning ka fita a harƙar ƙanwata, idan kuwa ka sake sa hannu ka dakar mun da ita toh wallahi tallahi za'a kwashi ƴan kallo domin zan gaya maka maganar da har ka mutu bazaka daina tunaninsa ba, ni ƙanwata tanada mutunci da daraja kuma tanada ƴanci tana kuma da asali da tushe ba kamar kai ba, kai da har yanzu ba wanda yasan tushen mahaifinka balle azo kanka, saboda haka Lailah ta fika a idon mutane, yanzu bana fargaban tunkararka domin a bayane kake tiger amma yanzu you are a real person bana shakkar ka Junaid, abunda kake yiwa Ayush kar ka sake kace zakayiwa Lailah domin ita Lailah tanada wanda zai tsaya mata, ita kuma Ayush rashin gata ne yasa ba'a bi mata hakki, amma a juri zuwa rafi,
Ni dai abunda nazo sanar maka shine idan ka sake dukar mun da ƙanwa wallahi saina maka ka a kotu ayi mana shari'a
ai dai kasan hukuncin dukan mace, kuma yanzu ma inda ace zan shigar da ƙara akan abunda kayiwa Lailah toh tabbas da saika shiga gidan yari domin ita kotu ba ruwanta da sanin ko kai wayene da kuma matsayinka, kuma idan wani abu ya sake faruwa dani ko ita Lailah kotu zan nufa direct...."
Doctor Hasheem yana kaiwa nan ya juya zai tafi...
*****
Mommy tana ɗakinta tana waya da wani babban malami akan wani tsararren masallacin data gina,
Mommy tana faɗin "Masha Allah naga masallacin ya tsaru sosai, abunda nakeso yanzu inaso a yau ɗin nan a buɗe masallaci da taron ɗaurin Aure..."
daga ɓangaren malamin kuma cewa yayi "hakan ma yanada kyau amma Auren wa za'ayi kuma?..."
Mommy tace "gaskiya Auren ne ana so ayishi cikin sirri, mutanen da za'a tara ba wani masu yawa ba, guda goma ma sun isa, masallacin ne da ɗaurin Aure nake so a buɗeta bayan an kammala ɗaurin Auren sai a fara amfani da masallacin,
zan gayyaci dattijan unguwar nan da abokan marigayi mijina da kuma malam lawan shima duk su halaci gurin ɗaurin Auren..."
Malamin yace "toh shikenam ba matsala Hajiya Fatima mudai ba abunda zamu ce miki saidai Allah ya saka miki da gidan Aljanna, kuma kamar yanda kika ce za'a gayyaci malamai dasu halarci masallacin amma tinda kince a yau ake buƙatar ɗaurin Auren insha Allahu da yamma zuwa ƙarfe 5 za'a gabatar da ɗaurin Auren, yanzu dai ƙarfe 3 ne hajiya ki turo mana da sunayen waɗanda za'a ɗaura musu Auren da kuma waɗanda zasu zauna a matsayin wakilansu da kuma sadakin da za'a bayar..."
Mommy tace "duk ba abun tashin hankali bane yanzu zanje gidan Barrister Aminu babban abokin mahaifin Angon ne shi zai zamo maɗaurin Auren yaron,
Ita kuma yarinyar malam lawan ne zai karɓi Aurenta, don haka zan bada sadakin a Barrister Aminu, nidai malam dan Allah a tabbatar an tara shaidu..."
Yace "ba komai hajiya Allah ya sanya alkhairi.."
ta amsa da "Ameen.."
daga nan suka katse wayar..
Mommy da sauri ta yafa gyalenta ta ɗauki key ɗin mota ta fice a ɗakin..
*****
Angel da Ayush suna tareda Malam lawan sun kora masa bayani kuma ya gamsu yayi gyaran murya sannan yace "insha Allahu zaki musulunta yanzu, zan faɗi kalmar da zaki musulunta wanda idan kika faɗi kalmar shikenam kin shiga cikin musulunci dake da wanda yayi shekara 100 a cikin Musulunci kun zama ɗaya don haka duk abunda nace kema ki maimaita..."
Angel tace "toh Malam.."
Haka yake karanto mata kalmar shahada tana biyawa har suka zo ƙarshe...
Malam yace "yauwa ƴata Masha Allah yanzu kin zama musulma kema, yanzu abunda ya rage shine ki canzawa kanki suna daga Angela ki koma asalin sunan musulmai..."
Angel tana murmushi yanzu zuciyarta tayi wasar ta kalli Ayushert tace "meye asalin sunanki Ayush?.."
Ayush tace "kina son zama takwarata ne?.."
Angel tace "eh mana..."
Ayush tayi murmushi sannan tace "wow naji daɗi sosai toh ni sunana Ayshert.."
Angel ta turo baki cike da shagwaɓa tace "no no noo ba Aisha ba..."
Ayush tana dariya tace "wato sunana ba daɗi ko?"..
Angel tace "yess zan zaɓi suna ne mai daɗin gaske..."
Malam yace "toh muna jinki ki zaɓi sunan daya kwanta miki..."
Angel tajaa dogon numfashi sannan tace "Ni sunana Maryammm na zama takwarar mahaifiyar Annabi Isah..."
Sai malam ya ƙarasa mata da cewa "A.S.."