Showing 15001 words to 18000 words out of 186041 words

Chapter 6 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53928

Angel tana ɗingishi, sai Rumana dake tafe duk goshinta an zagaye da bandeji, shi kuma Junaid yana biye dasu a baya, Ayush ganinsu yasa ta miƙe da sauri tana kallonsu tareda faɗin "sannunku ya jikin nakun?.." Angel ce ta amsa murya ciki-ciki, ita kuma Rumana ko ƙala batace ba haka ta wuce ɗakinta,
mommy da Angel da kuma Junaid neman guri sukayi suka zazzauna, itama Ayush ɗin zama tayi idonta akan Junaid domin bata gajiya da kallonsa, shima yana lura da kallon da take masa saidai baya bari su haɗa ido,

gaba ɗaya wajen yayi tsitt ba wanda ya kula kowa acikin su sai Angel ce data kalli yanda Junaid yake ta faman press phone ɗinsa tayi gyaran murya, murya a sanyaye tace "my Man ya batun sarki Raamud ne?.."
ɗagowa yayi yana kallonta yace "baki sanar mun komai akansa ba har yanzu.."
kallon yanda mommy take Angel tayi sannan tace "munyi bincike sosai akansa sannan mun gano cewa matar data zauna daku a matsayin ƴar aikinku matarsa ce, wato Bara'atu..."

a zabure Junaid ya miƙe tsaye tareda faɗin "whatttt...?"
itama mommy saida ta girgiza dajin wannan batun,
Ayush ido ta zaro waje tana binsu da kallo, zuciyarta kuwa haka yake bugun uku-uku,
Angel tana bin Junaid da kallo tace "ba abun mamaki bane dan ance matarsa ce, saboda bakinsu ɗaya kuma shi ya turo ta nan gidan domin ta shiga cikin rayuwarku ta misguna muku"
ta kuma cewa "ka zauna mana mu ƙarasa maganar..."
jiki a sanyaye ya zauna yana cewa "ina jinki Angel.."

ta kuma cewa "yarinyar da Bara'at tabar gidan nan da ita ƴarsu ce kuma sunanta Mayushat, a yanzu dai basa tareda yarinyar kuma gaskiya bamu gano a yanda take ba, amma guaranty Sarkin matsafa yana tareda matarsa Bara'atu a halin yanzu, sannan bincike ya nuna cewa yanzu babu wani tasirin da suke dashi na tsafi, zamu iya kai musu farmaki a koda yaushe, tawagar mu tana kan shirinta domin zuwa farmakar su, an sanar wa sojojin nan nigeria da kuma na pakistan da sojojin china da na UK da US duk akan su shirya ranar 5 ga watan November 2023, next week kenam, jirgin land army da kuma airpos na Nigeria zai tashi a ranar Monday, zamu fara shirin mu daga yau friday zuwa monday domin damu za'ayi wannan tafiyar, sai kuma mu dage da addu'a domin a tafiyar yaƙin namun bamu san mai zamu tarar ba, bamu san waye zai mutu ba waye kuma zai rayu..."

Junaid kallon Angel yake cike da baƙin cikin sarki Raamud a cikin zuciyarsa,
buɗe baki yayi yace "a shirye nake dana yaƙe shi, kuma ni zan zamo ajalinsa..."

Angel ce ta katse shi da cewa "a'a shuwagabannin mu basu bada umarnin a kashe shi ba, da ransa suke son ganinsa.."
Junaid miƙewa tsaye yayi yana darara wa Angel tsawa tareda faɗin " i will kill him with his wife, babu wanda ya isa ya dakatar dani, sai dai nayi sanadiyar rasa aikina da kuma rayuwata, amma saina kashe mutumin daya azabtar da rayuwata, saina kashe matar da tayi sanadiyar mutuwar mahaifina, sannan kuma bazan taɓa ƙyale ɗiyarsu ba, saina nemo ta a duk yanda suka ɓoyeta..." yana kaiwa haka ya bar falon ya haura upstairs...

Ayush tana zaune jikinta ne ya hau ɓari tana rawar sanyi, wani irin zazzaɓi ne mai zafin gaske ya rufeta, tinin hawaye har ya cicciko mata, zuciyarta yana bugu da ƙarfin gaske,
ganin kuka yana shirin kuɓuto mata yasa ta tashi da sauri itama ta haura upstair zata koma ɗakinta, tana shiga kuwa ta danna sakata a ɗakin ta faɗa saman katafaren gadonta tana rera kuka na gaske..

Junaid kuwa toilet ya shige, ruwa ya kwara a kansa yayi wanka shap-shap ya fito ya shirya cikin wandon soja da farar t-shirt, ya zura takalminsa sahu ciki irin na sojoji, ya feffesa turare sannan ya fice da sauri ya sauƙa down stairs,

Mommy da Angel ne suka miƙe tsaye a zabure ganin Junaid yana shirin ficewa,
Mommy tace "ina zaka je Junaid?..."
juyowa yayi yace "zanje headquarters ne domin na tantance ƙarfafan sojojin da za'ayi tafiyar dasu ba lusarai ba..."
yana kaiwa haka yayi ficewarsa, a gigice yaje ya shige motarsa ya fizgeta da gudun gaske,
maigadi daman tin fitowar Junaid yayi saurin buɗe masa gate...

Mommy tana daga tsaye ta kalli Angel da damuwa a fuskarta tace "wallahi Angel ina tsoro kar wani abu ya cutar mun da yarona, har ina ne ƙasar da zakuje?..."

Angel ta sauƙe ajiyar zuciya tana hura iskar bakinta tace "ki kwantar da hankalinki mom insha Allahu ba abunda zai faru da Junaid, ai jarumin namiji ne ba'a yaƙarsa sai dai ya yaƙi mutum, kuma ƙasar da za'a hallaru acan domin gudanar da yaƙin can ƙasar California ne, toh masarautar babu kowa yanzu haka sai su, babu mutane ko ata gefensu ne, waran dai ya kasance daji ne..."

Mommy tace "toh shikenam Allah dai yasa aci nasara akan su, a kamosu dumu-dumu..."
Angel tana murmushi tace "ai zamu ci nasara tinda sojojin da zasu hallara ba kaɗan bane, sojoji ƙasashe daban daban ne zasu zo domin gudanar da farmaki...

Ayush tashi tayi daga kwance tana zazzagaya cikin room ɗinta tareda faɗin "innalillahi wa inna'ilahi raju'un, shikenam iyayena nashiga uku nah, Allah ka karemun iyayena, taya zan sanar musu cewar su tafi? ta ina zan sanar musu cewar su gudu kafin ranar? ga yanzu babu tsafin da zanyi magana dasu ta cikin madubi, meye ake shirin aikata wa iyaye nane?..."
tana magana tana kuka sosai gaba ɗaya ta susuce..

Around 6 o'clock bayan anyi sallar mangrib
Angel ce ta fito ta gama shirya musu dinner na kayan abinci, sai data kammala tsab tukun taje ɗakin mommy ta tarar da ita akan sallaya ta idar da sallah,
Angel ta mata magana akan ta fito su ci abinci, mommy ta amsa mata da "toh"

sannan ta fice a ɗakin ta nufi upstairs taje tana kwankwasa wa Ayush, saida ta ɗan juma a tsaye kafin Ayush tazo ta buɗe mata, idon duk ya kukkumbura,
Angel tana ganinta tace "subhanallah Ayush meya sameki ne haka?.."
tana motsa baki daƙer tace "babu.."
Angel tace "kin fiye kuka da yawa, zakije ki sawa kanki ciwo ne, ke kullum kina cikin damuwa ba wargi, toh idan kika ce zaki biyewa Junaid ne mutuwa zakiyi murus domin Junaid asalin miskilin namiji ne, baya nuna damuwa akan abu, shawarar da zan baki shine ki zamo mace mai class, idan yaga bakya shiga harkarsa to shida kansa zai nemeki, amma yana ganinki kullum a haka duk saboda shi toh ya ringa gallaza miki kenam, ai namiji ba'a nuna masa tsananin so, kuma ma ai ke kika jawo agun baiko kika fetsare ido kika ce bakya sonsa alhalin son sa da kikeyi yafi wanda yake miki, ai yanzu ba maganar kuka, ki fito muyi night dinner..."

lips ɗinta ne yake kakkarwa daƙer tace "ni akawo mun cikin ɗakina..."
Angel tace "a'a wallahi ki fito yanzun nan muci acikin mutane, Allah ciwon zuciya zai kamaki Ayush, na gaya miki ki fito yanzun nan, mommy tana jira..."
tana kaiwa karshe tayi tafiyarta, saida ta duba room ɗin Junaid taga bai dawo ba har yanzu tukun ta sauƙa downstairs, ta tarar da mommy har ta fito,
mommy tace "me kikeyi ne tin ɗazu?.."
tace "wallahi mommy na tsaya agurin Ayush ne, tana nan fitowa itama.."
Mommy ta kuma cewa "Junaid ya dawo?."
tace "a'ah mommy.."
Mommy tace "toh shikenam kibi ɗakunan sauran kice su fito.."
ta amsa mata tareda nufan ɗakin Rumana tana kwankwasawa cikin ƙanƙanin lokaci saiga Rumana ta buɗe daga ita sai gajeran wando na sojoji ajikinta da black t-shirt, tana hararar Angel tace "ya akayi?.."
Angel juyawa tayi tareda faɗin "ki fito aci abinci inji mommy..."
Rumana bata koma ciki ba haka ta fito gaba ɗaya ta nufi gurin dinning table tana press ɗin wayanta, goshi kuwa duk anzagaye da bandeji...

Angel zuwa ɗakin Aditi ta nufa itama ta kwankwasa mata! da sauri aka buɗe ƙofar tana masifa ganin Angel yasa ta turɓune fuska tace "menene kodai dukan ne bai isheki ba?.."

Angel tace "ni ba masifa ce ta kawo ni ba, kizo inji mommy aci abinci..."
tana kaiwa nan tayi juyawarta itama waran dinner ta nufa ta zauna a kujerar kusa da mommy, itama Ayush fitowa tayi saida ta wanke fuskarta tukun ta zauna a kujerar kusa da Rumana, saiga Aditi itama tazo ta zauna a ɗayan kujerar gefen Angel ta toshe da earpice a kunnenta,
Angel ce ta buɗe kulolin gurin tana zuzzuba musu alokacin ne Junaid shima ya dawo, yana shugowa shima ya nufi gurin cin abincin domin wani irin yunwa yake ji, zama yayi a kujerar da yake fuskantar Aditi...

suna cikin cin abinci ba wanda yake kula kowa, ita kam Ayush bata ci sai faman juya spoon take, Mommy ce ta ɗago tana kallonta tace "Ayush lafiyarki kuwa, tin ɗazu nake nura dake ba wani abincin kike ci ba, meya faru dake?.."
girgiza kai tayi tace "babu komai.." ta fara tusa abincin daƙer a bakinta tana ci kamar bazata ci ba...

suna cikin wannan yanayin sai wayar Rumana ta fara rurin ƙira, ganin screen ɗin wayar tayi tace "oh god.."
duk kallonta sukayi daiden lokacin ta kara a kunne tana faɗin "hello Ogah Sir..."
saiji sukayi tana cewa "okay Sir, yes Sir, yes Sir, Okay Sir, thank you Sir..." ta sauƙe wayar tana sauƙe numfashi, tana kallon mutanen wajen ɗaya bayan ɗaya,

Junaid ne ya kalleta yaga yanayinta har ya sauya yace "what's wrong with you?.."
ta kalle shi tace "yanzu zan tafi airport zuwa cikin dare zan isa Australia, ana neman mu agurin aiki wai akwai yaƙin da zamu fita next week zamu je mu fara shirye-shirye..."

murmushi Junaid yayi sannan yace 'ai daman nasan daku za'a fita yaƙin nan.."
ta kalleshi da blue eyes ɗinta tace "kaima harda kai?.."
ya nuna Angel yace "tare zamu tafi da Angel ranar monday, tinda daman can ne gurin aikinta.."
Rumana kamar zatayi kuka tace "za'ayi asarar rayuka fa sosai, nayi weak da yawa..."
Angel ce ta tsomo baki tareda faɗin "dajin da kika sani a baya toh yanzu babu wannan tsafukan, babu aljanu a cikin ta, saidai bamu san ƙarfin ikon da yakeda shi ba.."

sake ƙiran wayar Rumana akayi a karo na biyu azabure ta tashi tana faɗin "sun sake ƙirana, bari naje na shirya.."
da gudu ta nufi room ɗinta tana zuwa ta tuttusa kayanta a cikin akwatinta ta rufe da sauri ta fito tana jan akwatin, haka ta faɗo falo kamar daga sama ko canza kayan jikinta batayi ba,
gajeren wandon nan ne ajikinta mai kakin soja sai baƙar t-shirt, ta saka takalmin ciki irin na sojoji ta fito tana musu sallama..

Mommy da Junaid da kuma Angel nufowa gurinta sukayi da sauri, mommy tana cewa "toh ki tsaya mana, wani irin gaggawa ne haka.."
Rumana girgiza kai take tana cewa "mom sun bani time ne, sunce nan da awa biyu suke son ganina a Australian Headquarters..."
tana kaiwa karshen maganarta ta rungumi mommy tana mata bankwana, ta juyo ta rungumi Angel tareda sumbatarta a kunci, ta nufi dinning table ta rungumo Ayush itama ta manna mata kiss a gefen fuska, taje yanda Aditi take itama ta rungumeta tareda mata kiss a kuncin ta, tukun ta tafo ta rungumi Junaid sosai tana kuka, shima rungumarta yayi sosai yana rarrashin ta, daga bisani suka rabe da juna, Junaid ɗaukar mata akwati yayi suka fita a tare domin shi zai kaita airport da motarsa...

Aditi kam sumar zaune tayi jin za'a fita yaƙar sarki zalimu, tasan dole suma harda sojojin ƴan ƙasarsu kuma harda ita za'a sako,
a matuƙar tsorace take domin shekarar data wuce sojojinsu sun kai farmaki can dajin amma ba soja ɗaya daya fito da rai, tana cikin wannan tunanin saiga hawaye zurzur asaman fuskar Aditi, daga yanzu itama zata fara tsammanin ƙiran waya daga wajen aikinsu na ƙasar china....




*WANNAN PAGE ƊIN NA SADAUKAR DASHI A WAƊANDA SUKE MUN COMMENT*

*NAGODE MUKU SOSAI DA ƘARFAFA MUN GWIWA WARAN YIN TYPING, COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR NISHAƊARTAR DANI, INA SONKU SOSAI....*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 11 ➡️ 12


washe garin ranar saturday da safe Mommy da Angel da kuma Ayush suna zaune a falo suna kallon film a Arewa 24, ita Ayush tana kallon ne amma tunaninta yana can gurin iyayenta,
Aditi tana ɗakinta a kwance itama gaba ɗaya ta suƙure jin farmakin da za'akai ƙasar california tasan babu wanda zai rayu haka taketa tunanin nan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login