Showing 45001 words to 48000 words out of 186041 words

Chapter 16 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53923

gaba ɗayansu sunyi farin ciki sosai dajin sunan da Angel ta zaɓawa kanta..
Malam yace "toh bari na ƙira matata kuje ta gwada miki yanda ake wankan shiga musulunci..."
Angel ta amsa da "toh malam.."

Malam yana shirin tashi kenam saiga ƙiran wayar Mommy ya ɗaga ƙiran yana faɗin "Assalamu alaikum Hajjajo ykk?.."
Mommy ta amsa masa cikin farin ciki sannan ta sanar masa cewa "zuwa ƙarfe 5 na yamma akwai ɗaurin Aure a masallacin data buɗe, ta sanar masa Auren waɗanda za'ayi sannan kuma shine maɗaurin Auren yarinyar..."
Malam yaji daɗin wannan batun sosai yayi hamdala sannan yace "ba damuwa Allah ya kaimu lokacin yanzu ma tashi zanyi nayi wankan shirin tafiya don yanzu haka ƙarfe huɗu ne kuma kinga sauran mana awa ɗaya, zan gayyaci mutane sosai..."

Mommy ta katse shi da cewa "a'ah malam bana buƙatar wasu mutane da yawa an rigada an tanadar da dattijai basu fi mutane goma zuwa ashirin ba saboda Auren sirri nake son yi wanda banaso ko su yaran su sani balle.."
Malam ya jinjina kai tareda faɗin "toh amma Hajiya meyasa? ko basa son junansu ne?.."
Mommy tace "a'ah kawai dai akwai abunda nake tsarawa ne, hatta shi yaron bai san da Auren ba balle ita yarinyar kuma banaso a sanar musu dan Allah malam.."
Mallam yace "toh shikenam Hajiya ba damuwa Allah ya sanya musu Albarka acikin Auren nan..."
Mommy ta amsa da Ameen sannan ta kuma cewa "yanzu haka ina gidan Barrister Aminu shima na sanar masa zaku haɗu a masallacin na bashi sadaki million ɗaya da zoben gwal..."
Malam yayi hamdala tareda nuna farin cikinsa daga nan suka katse wayar..."

Angel duban malam tayi cike da mamaki tace "malam kamar da Mommy kukayi wayar koh?..."
Malam yace "eh hakane Maryam.."
ta kuma cewa "toh amma naji kuna maganar Aure shin Auren wa za'ayi?..."

Ayush ce ta katseta da cewa "haramun ne shiga shirgin da ba naki ba Aunty Maryam..."
Ajiyar zuciya Angel tayi sannan tace "toh na daina ƙanwar Maryam.."
Duk sukayi dariya
Malam kam girgiza kai yayi yana murmushi sannan ya tashi ya nufi ciki ya sanar da matarsa Malama Zainab akan ta koyawa Angel yanda ake wankan shiga musulunci da duk wani abunda ya shafi Addinin Musulunci.."
Malama Zainab ta amsa masa cike da farin ciki itama....



🗣️🗣️🗣️🗣️ *SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*
*DAN GIRMAN ALLAH KU DAINA COMMENTS A CIKIN WANNAN PAID GROUP, KU RINƘA ZUWA CAN OLD GROUP KUNA COMMENT ACAN SABODA KAR WANCAN GROUP ƊIN YA MUTU KUNGA BA TURA LITTAFI NAKEYI ACAN BA, AMMA YIN COMMENTS ƊINKU ACAN ZAI ƘARA ƘARFAFA GROUP ƊIN...*

*NI INA BUƊE GROUP ƊIN NAN NE SABODA ANA ƊANYIN HIRA IDAN AKWAI MASU BADA SHAWARWARI AKAN LITTAFIN SU BADA, AMMA BANDA SHARHI DAN ALLAH ACAN GROUP ZAKUNA YI*

*SANNAN WAƊANDA BASA MUN COMMENTS NI BAZANCE MUKU KOMAI BA SABODA KUƊI KUKA BIYA KUKA SHUGO AMMA ZAKU NA GANIN DELAY ƊINA WAJEN YIN NEW UPDATE, DALILIN DAYASA BANA MUKU UPDATE KENAM AKAN LOKACI SHINE RASHIN COMMENTS ƊIN WASU DAGA CIKIN KU...*

*WAƊANDA BASA CIKIN WANCAN GROUP ZAN TURO DA LINK KU SHIGA KUNA COMMENT ACAN ƊIN....*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 25 ➡️ 26


Junaid yana kwance ya rufe idonsa sosai har wani zaƙami yake yi tsabar ɓacin rai, abunda ya tsara daman a ransa shine idan ya tashi bazai bar Doctor Hasheem da ransa ba, domin babu abunda zai hana shi ya murɗe masa wuya!

Doctor Hasheem yayi dace sosai tinda har ya bar ɗakin yayi tafiyarsa Junaid bai buɗe eyes ɗinsa ba,
Jikin Junaid ne ya fara kakkarwa, kansa yana juyawa inda ba'a kwance yake ba toh babu abunda zai hanashi faɗuwa, cije leɓɓensa yake da ƙarfin gaske...

Shi kuwa Doctor Hasheem sauri-sauri gudu-gudu haka yake tafiya har ya iso bakin gate ya buɗe da sauri ya shige motarsa yabar ƙofar gidan,

Ƙarfe 5:00 duk waɗanda aka buƙaci suzo gurin ɗaurin Aure duk sun zo kowa ya halarci gurin sai iya dattijai kawai ake gani dake su aka buƙaci suzo,
daga ƙarfe 5 zuwa 6 har an ɗaura Auren Junaid khan Maahmud da kuma Ayshert Máahmud akan sadaki million ɗaya da zoben gwal 🙏🙏
an kammala komai yanzu Junaid da Ayush sun zama ma'aurata a rashin saninsu,.
Mommy zuwa tayi ta buga cards na shaidar Auren su da date ɗin da aka ɗaura Auren da photunan ma'auratan a jikin katin,
waɗannan katinan ta bugosu ne badan ta rabasu ba sai dan ta ajiyesu ko wata matsala zata iya ɓullowa ga shaida nan,
Mommy tayi farin ciki sosai dajin an ɗaura Auren, tuƙin mota take amma bakinta a washe yake ta gagara rufesu tsabar farin ciki, da wannan farin ciki ta isa gida,
Horn tayi maigadi ya buɗe mata da sauri domin a lokacin ma ƙiraye-ƙirayen sallar mangarib ake yi, da gudu ta shige gidan kai tsaye wajen parking ta nufa ta ajiye motarta ta fito fuskar nan wasar!

Mommy tana shiga ta fara ƙiran sunan Angel! Angel!! Angel!!! "Ha'a kar dai ace yarannan basu dawo ba? kuma dare yayi ai zasu kamo hanya su dawo gida ko?..."
tana kaiwa nan ta haura upstairs tana faɗin "bari na dubo yarona ko shima ya fitan ne.."
tana zuwa ta fara knocking a hankali har saida ta jera kusan sau biyar tana buga ƙofar ba'a buɗe ba daga baya ta tura ɗakin,
ganin Junaid a zaune a bakin gado ya haɗe kansa da gwiwarsa yana rungume da kansa yasa ta cewa "wato kana jina inata faman knocking shine ko ka kulani koh my son..."

Junaid yana jinta bai ɗago ba, still ta ƙara cewa "kodai fushi ake da Mommy?..."
nan ma ko motsi baiyi ba, hannu mommy tasa tana ƙoƙarin ɗagoshi, ɗagowa yayi da wasu rinannun eyes ɗinsa waɗanda suka shashshanye juyowa yayi yana kallon Mommy ido kamar zai rufe kansa,
Mommy cikin nuna damuwa tace "lafiya kuwa Junaid? meya faru dakai haka, dubi yanda ka koma fa..."
Murya ciki-ciki yace "Please Mom my Headache..."
Mommy tace "subhanallahi ciwon kai kuma my son, meya jawo hakan? bari naje na ɗauko maka magani ko..."
tashi mommy tayi da sauri ta fice a ɗakin kai tsaye ɗakin magani ta nufa, ta jido maganunnuwa har kala uku aciki har da wanda zai sakashi bacci domin har da rashin baccin ma,
cikin ƙanƙanin lokaci mommy ta dawo hannunta ɗaya yana ɗauke da bottle na ruwa, ta sameshi a yanda yake a zaune itama zaman tayi tana ƙoƙarin ɓare masa maganin,

zuciyarsa ne yaketa harbawa da ƙarfin gaske, yana tariyo maganganun Doctor Hasheem, alokacin ne ya gaskaka maganganunsa na cewar bashida ƴanci tinda har ya rasa dangin mahaifinsa, akwai tambayoyin da yakeson yiwa mommy..."
yana wannan tunanin Mommy ta bashi maganin data ɓare, karɓa yayi ya watsa su a bakinsa sannan ya karɓi bottle ya korasu da ruwa, sauƙe ruwan yayi yana mai jan dogon numfashi..."

Mommy tace "sannu koh my son, Allah ya yaye maka..."
Jinjina kai yayi yana kallon ƙasa,
Mommy ta kuma cewa "Junaid shin akwai abunda kake ji a ranka akan Ayushert?..."
Ɗagowa yayi yana kallonta cike da mamaki yace "bangane ba"
Momy tace "ina nufin kana jin sonta a zuciyarka? dan Allah kar ka ɓoye mun ka faɗamun gaskiya..."
Junaid ɗan bubbuga goshinsa yayi ido a lumshe yace "kinsan fah a wancan lokacin ma saboda ke ne yasa na amince da baikon nan kuma tazo ta watsa miki ƙasa a ido" yaja dogon numfashi sannan ya kuma cewa "Mom kinsan duk abunda kike so ina ƙoƙarin ganin nayi miki shi, inason ganin abunda zai faranta miki rai..."

Mommy tana murmushi tace "Alhamdulillah naji daɗin wannan batu naka, toh amma shin kana jin sonta a zuciyarka? idan nace ka Aureta zaka Aure ta?..."

Junaid juyowa yayi yana kallon mommy fuska ba Annuri yana yamutsa fuska yace "wai kam Mom shin ita kaɗai ce mace aduk faɗin duniyan nan? kin nace a wannan yarinyar shin dole ne saina Aureta..."
Mommy ta ɗaga kafaɗarta alamar bata damu ba ta kuma cewa "Hmmm Junaid kenam nasan dai kana son Ayush, toh meyasa kake ɓoye mun?..."

Junaid yace "toh idan inasonta ita ɗin shin tana sona ne?..." ya ƙarasa maganar ba tareda ya juyo ya kalleta ba...

tace "Junaid kenam ai Ayush tafi sonka ma akan son da kake mata sai dai abu ɗayane yasa yanzu bata kula dakai shine ƙuntata mata da kake yi kana nuna mata zafin nama wanda duk son da take maka zata janye ne, tsorone ya hanata ayi muku baiko a wancan lokacin kuma kana dukanta taya zata amince da kai..."

Junaid ya ɗan sauƙe numfashi yana murmushi yace "koda ta amince dani ma bazan Aureta ba..."
Mommy tace "saboda mai kenam?.."
ya juyo yana kallon mommy yace "saboda batada asali kamar yanda nima banida asali toh amma gwara ni ai tinda ina da ke kuma ansan dangin mahaifiyata...."

Mommy jikinta ne yayi sanyi jin abunda Junaid ya faɗa, ɗagowa tayi tana kallonsa wanda shima kallonta yake, bata ankara ba taji ya sake jifanta da wata tambaya "shin su waye dangin mahaifina? sannan aina suke? meye asalinsu? duk bakisan wannan amsar ba, kawai kin Auri mutu bakisan ko shi wayene ba, baku tsaya kunyi bincike akansa ba, kunyi abunda yanzu nine nake jin zafinsa!
kuma haka kikeso ki sake aikata kuskuren da kika aikata a baya? kina so na Auri wacce ba'a San asalinta ba, koda danginta baki saniba, kinaso na Aureta ƴaƴana suzo suna kukan gorin da ake musu cewar ba'a San asalin dangin mahaifin ubansu ba haka kuma ba'a San asalin dangin uwarsu ba, haka kenam zasu tashi da wannan takaicin?
hatta ƴan uwanki ba sona sukeyi ba saboda basu san waye mahaifina ba, suma kansu ƴan uwanki gori suke mun balle azo cikin gari kan abokai da sauransu...."

Mommy tana zaune kamar wanda ruwa ya cinye, bakinta har wani kakkarwa yake maganganun Junaid sun ƙona mata rai tace "Junaiddd ka dakata haka, duk da ba'a San ko waye mahaifinka ba amma shi ɗin mutumin kirki ne, yanada kyakkyawan zuciya wanda hakan yasa mahaifina ya damƙa masa amana ta saboda yasan zai kula dani, kuma Alhamdulillah tinda mukayi Aure har muka haifeka har mahaifinka yabar duniya bamu taɓa samun matsalar zamantakewar Aure ba, har yau ban taɓa yin danasanin Aurensa ba, hakan ma ka gode wa Allah tinda shi yayi sanadiyar zuwanka duniya, koda bashi na Auraba ba lalle ne kazo duniya ba saboda wani baya taɓa haifan ɗan wani, bazaka taɓa fitowa daga cikina ba saidai na haifi wani daban domin kai ɗin jinsin mahaifinka ne, saboda duk wanda yasan mahaifinka toh tabbas idan an ganka anga suffarsa...."
Mommy ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye,
ta cigaba da cewa "Junaid bazaka taɓa tozarta ba a duniyan nan Insha Allahu koda bayan rai nane domin wannan dukiyar da muke sarrafa shi ya faro asaline daga mahaifina wato Alhaji Junaidu kafin rasuwarsa ya mallaka mun dukiyarsa da mahaifinka domin iya mu biyu kawai yake gani kuma ya yadda da mu duk da niɗin dole dukiyarsa nawa ne saboda ni kaɗai ya haifa,
dukiyata dana mahaifinka amfanuwarka ne na kai ɗaya...."

Junaid ne ya katseta da cewa "pleaseee Mommm it's okay ni ba maganar dukiya nake buƙatar ji ba, inason sanin su waye dangin mahaifina, daga wata ƙasar ya fito..."

Mommy tace "Junaid abunda kake son sani nima ban saniba, abunda na sani akan mahaifinka shine mahaifina ya haɗu da mahaifinka ne a titi yana yawon neman aikinyi saboda abincin da zaici ma gagaransa yake, wata rana mahaifina yaje office ɗinsa dadaddare yana kan hanyar dawowa gida kwatsam saiga ɓarayi sun tareshi kuma alokacin yana tareda maƙudan kuɗaɗe na kamfani wanda zaiyi kimanin Billion 100 acikin akwati, ɓarayin nan sun so su illata mahaifina sannan su karɓe kuɗin sai Allah ya turo mahaifinka a yawace-yawacensa yazo wajen ganin abunda ake shirin aikatawa ne yasa yazo da gudu ya ceci mahaifina sannan yayiwa ɓarayinnan dukan gaske wanda har kasa tashi sukayi daga ƙarshe aka ɗauke su aka kaisu hannun hukuma,
toh daga wannan lokacin ne mahaifinka ya shiga zuciyar mahaifina har ya ɗora shi akan kasuwancinsa, ansha tambayar asalinsa amma ya kasa gaya mana sakamakon ciwon mantau daya haɗu dashi duk ya manta daga inda ya fito, amma zubinshi ba ɗan Nigeria bane, irin bahindiyawan mutanen nan ne anfi tunanin daga ƙasar India yake, amma sai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login