Showing 114001 words to 117000 words out of 186041 words
mai nauyi duk Hafiza ke yinsu sakamakon cikin Ayush ya girma sosai, domin cikin yanzu watansa takwas, duk wasu ayyukan bauta da ake sakawa an bada umarnin kada a saka Ayush a ciki, yanzu hankalinta a ƙwance yake ba kamar farko-farkon zuwanta ba, kowa sai yace zai hantareta ita da Hafizat..
Damuwarta shine abu ɗaya wato Junaid tana mamakin yanda tsawon watannin nan amma baizo ya dubata ba, kuma sai take zargin anya lafiyarsa ƙalau, shine kawai damuwarta, amma malam Lawan yakan zo mata wasu lokuta, tana tambayarsa Junaid amma sai ya sanar mata cewa yana nan lafiya ƙalau, a yau ne daya zo yake sanar mata cewar tin lokacin da aka kawo ta prison Junaid yake kulle a gurin mutanensa sojoji,
Ayush tasha kuka sosai jin haka....
******
Duk tsawon wata ukun nan Junaid yana kulle a ɗakin dake quarters, Marshal yaƙi bari a fito dashi wai sai matarsa ta haihu a prison tukun, Abinci kuwa sai an daideci yana bacci tukun a buɗe a hankali a ajiye masa tukun a sake kulle ɗakin, shima haka rayuwarsa yake tafiya shi kaɗai a cikin ɗaki, zaman kaɗaici ya dameshi ga wayarsa tana hannunsu, yayi masifar! yayi barazana!! yayi magiyar!!! yayi kukan har ya gaji, ga yanaso ya sanya Yushert ɗinsa a ido amma babu hali, yayi matuƙar kewar matarsa Yushert, shi kaɗai yasan kalar raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyarsa, sannan ya ƙudurta a ransa cewar da zarar ya fito duk saiya ƙona headquarters ɗin gaba ɗaya, babu abunda zai rage a cikinta tinda har zasu masa wannan wulaƙanci da tozarci...
Malam Lawan yayi zirga-zirga wajen sojojin nan akan subar masa Junaid ya tafi dashi amma sun ƙi da haka har ya gaji ya daina zuwa,
******
Ata ɓangaren mommy da sarki Raamud sunata shirye shiryen dawowa Nigeria, duk da basu san abubuwan dake faruwa ba, Mommy murna kamar bazata mutu ba tana son dawowa gurin yaranta, ga tayi missing ɗin Junaid ɗinta, sun yanki Visa gobe da safe jirginsu zai tashi...
*TEAM ƊIN JUNAID DA TEAM ƊIN AYUSH NACE BAA HOW MARKET 🤪🤪🤪🤪🤪🤪🤪*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 57 ➡️ 58
Today is Monday Around 2pm jirgin su Mommy suka sauƙa a Nigeria,
Mommy murna kamar bazata mutu ba har ɗaukin ganin yaranta take kamar zata fura, Allah! Allah take ta isa gida, sarki Raamud ya fahimceta duk wannan saurin so take taje gida murmushi kawai yayi ba tareda yace komai ba, shima kansa mamakin kansa yake yana maganar zuci "wai yau nine a Nigeria? Allahu Akbar Aure mai haɗa zumunta...". suna tafe a motar haya domin babu motar a hannunsu, har suka ƙariso ƙofar gida, ganin yanda gidan ya rurrushe yayi baƙi ƙirin yasa mommy cewa "Yaa Salam haka gidana ya koma? kuma Junaid baiyi ƙoƙarin gyarawa ba? toh yanzun acikin gidajensa wanne ɗaya ya koma sai Allah...."
Sarki Raamud shima kansa abun ya bashi mamaki ganin yanda gidan ya ƙoƙƙone, baiyi tunanin har abun yakai haka ba yana jinjina kai yace "yanzu ya za'ayi mu samu Junaid?.."
Mommy ta juyo tana kallonsa cikin nuna damuwa tace "yanzu haka idan nace zan sauƙa nayi tambaya sai suce zasu firgita domin a tunaninsu na mutu ne, ni kuma nafison nabi abu a sannu har su gane cewar ba mutuwa nayi ba..."
Sarki Raamud shima idonsa akanta yace "hakane toh amma yanzu meye abun yi?.." da sauri mommy tace "ahh! muje gidan malam Lawan..". cikin rashin fahimta yace "waye malam Lawan kuma?..." Mommy tace "idan muka je zaka ganshi, daga nan sai in baka labarinsa"
murmushi yayi sannan yace "okay..."
suka sa mai motar ya juya mommy tana masa ƙwatance har suka isa gidan malam lawan...
Bayan isar su gidan suka tarar dashi shima ya fito daga cikin gidansa da motarsa alamun wani guri zaije, ganin mutane a tsaye da akwatunansu mata tana ɗaga masa hannu, cike da mamaki ya buɗe murfin motar ya fito sakamakon rashin gane kosu su waye ne, da sauri mommy ta nufi wajensa tana murmushin farin ciki, ganinta yasa malam Lawan tsorita da sauri yake ja da baya yana furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, wacece kamar Hajia Fateema?..."
Mommy tsayawa tayi tana kallonsa daman tasan hakan zata faru, kafin su yadda da ita sai ta fahimtar da su tace "please malam Lawan kar ka tsorita dani dan Allah, wallahi nice Doctor Fateema ban mutu ba da raina..." cike da mamaki ya sake maimaita cewar "baki mutu ba?..." ɗaga masa kai tayi tana murmushi, sauƙe ajiyar zuciya yayi sannan yace "toh amma ya akai kika tsira kuma?.." Mommy tace "kafin kamun waɗannan tambayoyin ka fasa zuwa ko ina mu shiga cikin gidan..."
Malam Lawan ya ɗaga kai yana kallon mutumin da yake tsaye gefe guda yace "wancan fah kice masa ya iso cikin gidan..." yana kaiwa nan ya buɗe gate suka shiga daga ciki kai tsaye babban falo ya nufa dasu, a falon ya tarar da matarsa ya sanar mata cewar ta haɗo kayan abinci da drinks, yana tsaye saiga Mommy ta shugo da sallama a bakinta ya amsa mata cikin kulawa sannan ya nuna mata waran zama tareda tsokananta yana faɗin " Allah dai yasa ba Aljana bace ta fito a suffar Hajiya Fateeman mu...". ya ƙarasa maganar tareda zaunawa shima, dariya abun ya bawa mommy tace "in ma Aljana ce ai baza a guji mai suffar Hajiya Fateema ba..."
Daiden lokacin da Sarki Raamud shima ya shugo da sallama a bakinsa, ganin sarki Raamud yasa malam Lawan miƙewa da sauri yana kallon sarki Raamud, a ruɗe yace "Raamud?...". shima sarki Raamud tsayawa yayi yana kallon Malam Lawan cike da mamaki shima ya ambaci sunansa da cewa "Artaf daman kana duniya?..."
malam Lawan kallon mommy yayi sannan ya maida idonsa kan sarki Raamud yace "za zauna mana, nasan ka juma baka ji labarina ba shiyasa kake tambaya ko ban mutu ba daman, amma ni nasan kana nan amma ban taɓa tunanin zaka zo Nigeria ba..."
Sarki Raamud zama yayi tareda bashi amsar "eh nazo Nigeria ne saboda ƴaƴana amma ba jumawa zan koma saboda masarauta.."
Malam Lawan yayi murmushi haƙiƙa yaji daɗin maganar sarki Raamud yanzu ya ƙara tabbatarwa da cewar ya shiryu ya kuma rungumi Junaid a mazannin ɗansa...
Mommy dai sake baki tayi tana kallon ikon Allah baki na kakkarwa tace "am am daman kunsan juna ne?..."
jinjina kai malam Lawan yayi yana kallon mommy yace "ata sanadiyar wa kika Sanni?.." tace "ata sanadiyar marigayi mijina..." ya kuma cewa "okay meye matsayin wannan agurin mijinki?.." ya ƙarasa maganar yana nuna sarki Raamud,
Mommy tace "shi ɗin ɗan uwansa ne" malam Lawan yasau ƙayataccen murmushi sannan yace "toh kinga kuwa akwai kyakkyawar alaƙa dake tsakanin mu, domin ni ɗin ma ɗan cikin masarauta ne..."
Mommy ta zaro ido waje cikin ɗaga murya a ruɗe tace "tayaya hakan zata faru?..." malam Lawan yace "ki ƙwantar da hankalinki zan sanar miki amma sai mun haɗu gaba ɗaya dasu Junaid..."
Mommy kallonsa take kai kawai ta ɗaga mashi gaba ɗaya ta shiga cikin zullumi,
Sarki Raamud ne yayi magana tareda faɗin "ina su Junaid ne?.."
sauƙe numfashi malam Lawan yayi yana girgiza kai yace "wato abunda ke faruwa shine!. duk abubuwan daya faru saida ya ƙwashe tas ya sanar musu,
Hankalin mommy ba ƙaramin tashi yayi ba jin irin ƙalubalen da yaranta suka shiga Kuma duk ata sanadiyar ta, dafe goshi tayi tana faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Ayushert tana prison shi kuma yana kulle a gurin aikinsu..." a zabure mommy ta miƙe tsaye tana faɗin "a gaskiya bazan bar yarana su ƙara ƙwana acikin wannan halin ba, dole zanje na karɓe su, daman ai saboda ni akayi musu haka koh? toh yanzu zanje na karɓo kayana...". tana kaiwa nan tayi ficewarta daiden lokacin da aka shugo musu da kayan abinci, mommy ko tsaya kallon abincin batayi ba, suma haka suka biyo bayan ta malam Lawan yace "ku tsaya na kaiku da motata, kamata yayi mu fara zuwa dubo Junaid daga nan sai mu wuce prisoner..."
haka kuwa akayi kai tsaye headquarters suka wuce,
★★★★★
Junaid kuwa yana ƙwance ga zazzaɓin da yake damunsa gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, duk ya rarrame sakamakon rashin cin abinci domin idan ya tashi yaga abinci ba ci yakeyi ba saidai ya ɗan kurɓi lemo shikenam, sumar sajensa zuwa gemu duk yayi tsayi harta suman kansa saboda tsawon wata uku babu gyaran gashi balle ya rarrage sumar sai fuskar tayi fiyau, shima babu maraba da wanda yake zaman gidan prison, sai dai shi Junaid ana kawo masa abinci mai kyau ne sannan muhallin da yake shima mai kyau ne, fita ne kawai aka haramta masa,
yana ƙwance ya lulluɓe kansa da mayafi kamar mai yin bacci, shi kaɗai yanata saƙe² aransa, tinda yake ba'a taɓa ɓata masa rai kamar na wannan karan ba, yana tunani aransa cewa "an raina mun wayo wallahi amma na yanke hukuncin koda sun nemi na dawo aiki wallahi bazan dawo ba, ni gurin da za'a rainani bana yadda na zauna a gurin, bansan kuma yaushe zasu buɗe mun ƙofa nayi tafiyata ba, waɗannan mutanen ba ƙaramin cutana sukayi ba dole naɗau fansan abunda suka mun, bazan ƙyalesu ba bansan a wani hali Yushert take ciki ba, ko sun kasheta ko tana gidan prison Allahu a'alamu, ya Allah ina neman agajinka! ya Allah ka temakeni banida wata mafita sai abunda ka zaɓa mun..." ya ƙarasa maganar yana kukan zuci..
bai ankara ba yaji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar ɗakin, a zabure ya tashi zaune yana sauƙe numfashi daƙer, wani daga cikin sojojin ne ya shugo ya sanar masa cewa "ya fito ana son ganinsa..." yana kaiwa nan yayi ficewarsa a ruɗe Junaid yabi bayansa gudun kar a sake ƙarƙame shi, yana fita kuwa kayinsa ya fara juyawa wani irin hajijiya ne yake shirin ɗaukarsa, yana dafe da kayinsa, ganin bazai iya tafiya da kansa ba dasauri yasa hannu ya dafe jikin gini yana shirin kaiwa ƙasi,
wasu sojoji ne su uku suka nufo kansa suna faɗin "lafiya kuwa Ogah Junaid, meyake faruwa ne?...". hannu suka kai suna shirin ɗago shi jin jikin yanda yaɗau masifar zafi yasa suka razana suka ce "wannan ai bashida lafiya ne, muyi saurin kaishi Office ɗin da General yake da iyayensa suna ciki.." a haka suka ɗaga shi yana jan ƙafa daƙer su kuma suna riƙe dashi,
A lokacin dasu Mommy suka bayyano kowa saida ya tsorita da ganinta wasu kuma suka guggudu daƙer aka fahimtar dasu suka dawo hayyacinsu, Allah ya temaka General yana nan domin baya zaman nan, saida yazo ya shigar dasu Officer ɗinsa sannan yasa aka je buɗe Junaid,
Bayan shigar dashi Officer mommy tana ganinsa tayi saurin miƙewa tsaye tana faɗin "subhanallahi meya samu yarona? me kuka masa?..." tayi saurin riƙe shi ta zaunar dashi,
General ya dubi waɗanda suka kawo shi yace "daman bashida lafiya ne? shine baku sanar ba?.." girgiza kai suka yi tareda faɗin "wallahi bamu sani ba muma yanzu muka tarar dashi a wannan halin, dake ba wanda yake shiga cikin ɗakin sai wanda yake kaiwa abinci da zarar yayi bacci..."
Jinjina kai General yayi tareda sunkuyar da kansa domin baisan mezai gaya musu ba, mommy durƙusawa tayi a gaban Junaid ta riƙo hannayensa tana kuka tareda faɗin "my son kayi haƙuri na aikata maka laifi, na tafi na barka ba'a son raina ba gashi na jefa ka a cikin mawuyancin hali ka gafarce ni my son...."
Junaid idonsa a lumshe kamar a mafarki yake jiyo muryar Mommy, a hankali yake buɗe idonsa kansa a sama yana kallon ceilling yana daga zaune ya sunkuyo da kansa idanuwansa suka sauƙa akan mommy, a razane yakai hannunsa biyu yana murza eyes ɗinsa ko mafarki yake ganin a zahiri yake kallonta yasa ya miƙe da sauri yana zazzaro ido waje,
Mommy itama tashi tayi tana cewa "ka ƙwantar da hankalinka my son nice momminka ban mutu ba..."
ta ƙarasa maganar tana yowa kansa da gudu ya juya yana ƙoƙarin fita daga cikin officer sai ga Marshal shima ya shugo cikin rashin sani sukayi gwarai, Junaid baya ya yo yana riƙe da goshinsa shima marshal riƙe goshinsa yayi yana kallon Junaid tareda cewa "wannan wani irin ganganci ne haka..." shi kuwa Junaid bai wani damu da gwaran da sukayi ba tsabar hankalinsa yana kan mommy, malam Lawan ne ya nufo kanshi yana faɗin "kaga Junaid ka kwantar da hankalinka mahaifiyarka ce ta dawo gareka ba mutuwa tayi ba, ta samu agajin gaggawa ne yanzu kuwa ta samu sauƙi ta dawo..."