Showing 117001 words to 120000 words out of 186041 words
ya ƙarasa maganar yana dafe da kafaɗarsa shi kuwa idonsa akan mommy baki na kakkarwa yace "are you sure? ka tabbatar mamana ne? bata mutu ba?..." Malam Lawan ya nuna sarki Raamud yace "kasan wancan mutumin?..." Junaid idonsa yakai kan sarki Raamud yana jinjina kai tareda faɗin "wannan shine Baban Yushert..." malam Lawan yace "tabbas shine kuma Baffanka, a lokacin da mahaifiyarka take neman agaji Narasimha ne yazo ya ɗauke ta sukayi mata magani..."
cikin rashin fahimta Junaid yace "wanene Narasimha?.." malam Lawan girgiza kai yayi sannan yace "haba Junaid kodai duk firgicin ne ya hanaka tuna komai? na gaya maka komai akan su ai, sannan shi Narasimha shine malaminsu kuma likitansu kuma mai basu kariya..."
sai a lokacin Junaid ya sauƙe nannauyar numfashi yace "wayyo Allah nah! na fahimta Allah na gode maka daka ceci mahaifiyata..." itama mommy kuka take tayo kansa tana faɗin "Junaid my son.." tasa hannu tana goge masa hawaye, cike da farin ciki Junaid yake kallon mommy yana dariya tareda zubar da hawaye yasa hannu ya rungumeta lokaci guda ya fashe da matsanancin kuka yana ƙiran sunan mommy, shi da mommy gaba ɗaya kuka suke yi babu mai rarrashin juna, Sarki Raamud ne ya zo yanda suke yasa hannu yana bubbugan bayan Junaid a hankali yana rarrashinsa, ɗagowa Junaid yayi yana faɗin "Mom meyasa zakiyi nisa dani, meyasa zakiyi tsawon watannin nan baki dawo gareni ba, na shiga damuwa sosai na rashin ganinki ga Yushert bansan a wani hali take ciki ba, shin sun kasheta ne ko tana raye, Mom Ina cikin damuwa..."
Itama mommy kuka take tace "a'a my son Ayush tana raye, na dawo kenam bazan ƙara tafiya na barka ba my son,
ka duba kaga yanda ka koma? duk ka fita hayyacinka akwai rashin kulawa a tattare dakai my son..."
Junaid kallon yanda Marshal yake yayi sannan yace "Mom sun zalunce ni, suka kulleni tsawon wata uku banji iskar duniya ba, nabar aikin nan bazan ƙara zuwa aikin nan ba, gwara naita zama a gida amma babu ni babu aikin soja na ajiye, kuma daman ai sun koreni...."
Mommy tana shafar fuskarsa tace "it's okay my Omomo duk yanda kace haka za'ayi tinda basu kula mun dakai yanda ya kamata ba...."
General dake zaune yana sauraronsu ya katse su da cewa "a'ah Junaid bafa koranka akayi ba, an ɗan dakatar dakai ne kuma yanzu an dawo dakai bakin aikinka..." kafin ya iddasa maganar Junaid ya katse shi da cewar "impossible! bana juran wulaƙanci, da a wulaƙantani gwara na ajiye komai nawa sabida haka na ajiye aikina...." yana ƙarasa wa yaja hannun Mom yana faɗin "please Mom mu tafi am not feeling well..". ya jata sukayi waje, malam Lawan da sarki Raamud kuwa haƙuri suka tsaya bawa General kafin suma suka fice, duk ba wanda ya gane sarki Raamud sakamakon yayi shiga irin na hausawa, danƙararriyar gizna ne a jikinsa da babban gariya sai kuma hular daya ɗora akansa bayan rage tsayin sumar kansa dayayi,
suna fita suka tarar da Junaid da Mommy a bayan seat suna zaune zaman jiransu, malam Lawan da sarki Raamud kuwa gaban motar suka shiga malam ne mai driving kai tsaye gida suka nufa, Junaid ganin gida ake shirin komawa yayi saurin dakatar dasu tareda faɗin "bazan koma gida ba saida Yushert ɗina..." murmushi malam yayi sannan yace "okay mu wuce prison kawai..."
Mommy abun ya bata mamaki sosai tace "my son wai yaushe ƙullaliyar soyayya ta shiga tsakaninku har haka ne?...".
kawar da kai Junaid yayi yace "Ni ina fushi dake mommy tinda har zaki ɗaura mun Aure ba tareda sanina ba..."
Murmushi mommy tayi sannan tace "Hmmm! a lokacin wahalar dani zakuyi shiyasa ban sanar muku ba amma tinda yanzu kun gane da kanku shikenam..." suna cikin hirar su har suka isa gidan prisoner, wani ne daga cikin security ya shugo dasu har cikin prison aka kaisu wajen da zasu zauna, shi kuwa ya tafi ƙira musu Ayush...
Ayushert tana ƙwance a ɗakinsu sakamakon ciwon cikin dake damunta, ga yanda cikinta yaketa motsi shi kaɗai ita kuma Hafizat taje tana musu wanki, wata mata ce christal ta shugo cikin ɗakin ganin Ayush a cikin wannan halin ne yasa tazo gabanta da sauri ta tsuguna tana faɗin "sorry kinji koh, cikinki na miki ciwo ko sorry, tashi maza kinji..." Ayush daƙer ta iya tashi saida christal ta temaka mata ta kuma cewa "cikin ki yanzu wata nawa ne?.."
Ayush tana kallonta cikin sanyayyar murya tace "jiya likita tazo dubani ta ce yanzu ya shiga wata takwas ne..." Joy tace "wow halalluya kin kusan haihuwa, yanzu aka sanar mun cewa kinyi baƙi suna can guess place...". Ayush zaro ido tayi tana dafe da ƙirjinta tace "daga kotu ko? sun zo dubani ne da zaran na haihu su ratayeni.." Joy tayi murmushi tace "ki ƙwantar da hankalinki babu abunda za'a miki, wannan baƙin bana kotu bane tashi muje ko.." ta riƙe hannun Ayush ta tallafa mata ta tashi daƙer take tafiya tsabar girman cikin,
Bayan isar su guess su Mommy suna zazzaune akan kujeru, Junaid ne ya fara ganin Ayush da sauri ya miƙe ya nufi wajenta yace "Yushert..." rungumarta yayi tare da faɗin "nayi kewar ki Yushert, i missed you my Yushert..". itama rungumarsa tayi sosai tare da fashewa da kuka ba tare da tace komai ba, su Mommy suma miƙewa tsaye sukayi ko wannensu da damuwa a fuskarsu ganin Ayush a cikin wannan halin,
shi kam sarki Raamud yafi kowa shiga damuwa domin har da ƙwallarsa yana maganar zuci "wai yau Ɓingel ce a prison? ban taɓa tunanin yarinyata zata shiga cikin wannan halin ba, innalillahi wa inna ilaihi raju'un..."
Junaid ne yasa hannu ya raba jikinsa dana Ayush yana nuna su Mommy tareda cewa "Yushert kin gane waɗannan?..."
Ayush kallonsu take ɗaya bayan ɗaya tadai gane malam Lawan amma sarki Raamud sam bata gane shi ba, still idonta ta sauƙar akan Mommy sai murmushi take tayi amma a cikin zuciyarta ta damu sosai ganin Ayush a prison...
Zaro manya-manyan idanuwanta tayi sosai kamar zasu faɗo ƙasi tasa hannu ta ƙanƙame Junaid da ƙarfi, leɓɓen bakinta har rawa suke haƙwaranta na dukan na juna sam ta kasa furta komai sai jikinta dake kakkarwa idonta kuwa akan mommy,
Itama mommy zaro ido tayi waje cike da mamaki take kallon tumbin cikin Ayush, tin zuwanta bata lura ba sai yanzu, cikin ɗaga murya mommy tace "Junaiddd!! yaushe ka bata ciki? har ta kusan haihuwa innalillahi..." haka ta baza idanu ta kalli Junaid sannan ta maida idonta kan cikin Ayush still ta kuma kallon Junaid haka ta rinƙa yawo da eyes ɗinta,
Junaid kuwa tsabar kunya kawai da kansa gefe yayi ga mutane a wajen waɗanda aka kawo musu visit, yana jin yanda Ayush take ta bubbugansa tana so tayi masa magana amma yaƙi juyowa,
Ita kuwa Mommy sai cewa take "Junaid! Ayush!! wai yaushe kukayi cikin nan ne kam ku mun bayani mana, amma bayan tafiyata kukayi wannan cikin koh? Alhamdulillah Allah yaga zuciyata gwara dana ɗaura muku Aure bansani ba ashe a matse kuke..."
haka mommy take ta wannan surutan gashi ba'a hankali take magana ba kowa sai jiyota yake,
waɗanda suke gefen can duk hankulansu ya dawo kan su Mommy,
Malam Lawan da sarki Raamud kam ficewa sukayi suka nufi waje saboda mutanen dake wajen,
Junaid kamar ya nitse ƙasi cikin takaici yace "Oh my god haba Mommy sai kace wata ƙaramar yarinya..."
sake baki mommy tayi tana kallonsa tace "ahhh ku kam ai kun girma, tabbas na yarda kun girma kun wuce ace muku yara gashi har zaku haifi yara ai kun zama manya tinda har kuka aikata abun manya..."
kamar zai rausa ihu yace "eh ai ba bad pregnant bane..." Mommy tace "eh ai nasani tinda ni da kaina nasa akayi muku Aure, ikon Allah kenam gashi har ka samu damar ɗura mata ciki...."
Junaid hararar Mommy kawai yake kamar zaiyi kuka ita kuma Ayush sai jijjiga shi take juyowa yayi yana faɗin "wai ke ɗin menene kam?.." cikin kakkarwar murya tace "Mommy ce ko Fatalwa?..."
yace "Da fatalwa ce zaki jita tana wannan surutai ne, ni sake ni! my headache ta dawo gaba ɗaya ta ɓata mun raii..." haka ya zamar da hannunsa daga jikin Ayush yabar wajen yana gunaguni...
Mommy ce tayo kan Ayush tana faɗin "Oyoyooo my Ayushertttt..." ta rungumeta sosai a jikinta,
Ita kuwa Ayush tinin ta ƙafe a wajen tsabar tsoro saida tasau fitsari a jikinta tana daga tsaye.....
*ASSALAMU ALAIKUM ƳAN UWANA BARKA DA WANNAN LOKACIN, INA MAI MIƘA GODIYATA A GAREKU NAJI DAƊIN ADDU'O'INKU AKAN ƊAN UWANA WANDA YA RIGAMU GIDAN GASKIYA🙏🙏🙏*
*BAZAN TAƁA MANTAWA DA WANNAN HALACCI DA KUKA MUN BA INA GODIYA SOSAI...*
*YAU DAI NA DAURE NAYI MUKU UPDATE, NACE BARI NA SAMU NA KAMMALA MUKU KAR NIMA NA MUTU DA HAKKIN KU AKAINA, INA ROƘON ALLAH DA YA ARA MUN RAYUWA HAR NA KAMMALA MUKU LITTAFIN NAN SAKAMAKON ƊARA RANKU DA KUKAYI AKANSA INA MAI JINJINA MUKU MASOYANA NA FILI DANA ƁOYE🙏🙏🙏*...
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 59 ➡️ 60
Mommy tana rungume da Ayush bata san lokacin data suma ba, sai nauyinta data ji yayi over ga tilin tumbi Mommy har tana shirin faɗuwa ta tattaro iya ƙarfinta a hankali ta kai Ayush ƙasa saboda bazata iya riƙeta a tsaye ba, zaro ido waje mommy tayi tareda faɗin "nashiga uku me kuma ya faru dake Ayushert?..." tattaɓa fuskarta ta soma yi amma shuru Ayush ko motsi, fashe wa da kuka mommy tayi tana neman agaji ƙiran mutanen wajen ta soma yi, duk aka rufu akanta amma an rasa wanda zai taɓata suna cikin wannan halin saiga su Junaid da malam Lawan sun shugo da sauri sakamakon sanar musu da akayi a waje, a ruɗe Junaid yasa hannu ya ɗagota yayi hanyar waje da ita, masu tsaron prison ne suka bi bayansa suna son dakatar dashi, har zai buɗe murfin motar suka dakatar da shi da faɗin "ba'a bada umarni a fitar da mai laifi a cikin wannan prison ba, wannan kuskure ne..."
Junaid ya juyo yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan yace "baku ga a halin da take ciki bane?..." suka ce duk da haka sai an bada umarni tukun, su Mommy ne suma suka ƙaraso wajen da sauri cikin damuwa take faɗin "dan Allah kuyi haƙuri mu kaita asibiti idan baku yadda damu ba saiku biyo mu muje tareda.."
wani ne daga cikinsu yace "okay amma kafin nan sai kun bada information nakun.." a lokacin suka bada sannan suka shiga motar kai tsaye hospital suka nufa da ita tareda security guda biyu...
Ranar a hospital suka kwana, iya malam Lawan ne kawai ya koma gida amma Junaid da Mommy da kuma sarki Raamud duk a asibiti suka wayi gari, a lokacin da Ayush ta farfaɗo su Mommy basa nan sunje shigar da report akan Ayush na anason fitar da ita daga prison, an karɓi ƙorafinsu amma sai an sake zama a kotu an nunawa duniya cewar Doctor Fateema ba mutuwa tayi ba sannan kuma a wanke Ayush a kotu....
Bayan farfaɗowarta Junaid kawai ta tarar a kusa da ita yana zaune ya zuba mata ido, itama kallonsa take a hankali take motsi da leɓɓenta tace " mafarki nayi ko? nasan mommy bazata taɓa dawowa ba, na tamka babban kuskure a rayuwata, da hannuna na kashe mommy nima rayuwata batada wani amfani..." kuka ne yaci ranta sosai dasauri Junaid yasa hannu yana rufe mata baki tareda girgiza mata kai yace "kar na sake jin wannan batun, mommy bata mutu ba ta samu tsira ne.."
hannu tasa ta zamar masa hannunsa dake kan bakinta tana ƙoƙarin ɗagowa zaune daƙer har saida ya tallafa mata tana kallonsa cike da mamaki take cewa "tayaya hakan zata faru? taya zakace mommy bata mutu ba shin ɓacewa tayi ne ko meye?..."
murmushi yayi sannan yace " Narasimha..."
da sauri Ayush ta ɗago tana kallonsa baki na kakkarwa ta maimaita sunan "Narasimha?..." shima idonsa akanta yace "yes ko kin sanshi ne?.." idonta akansa ko ƙibtawa batayi ta jinjina a cikin ranta take cewa "na sanshi shine yayi mun magani lokacin da na cire zobe a jikin cibiyata, kenam shine yazo ya ɗauketa..." tana cikin wannan tunanin taji Junaid yana faɗin "tunanin mai kike yi ko kin sanshi ne?..."
a ruɗe tace "kenam masarauta aka kaita ta ɗebi tsawon watannin nan?.." jinjina kai Junaid yayi yana kallonta, a lokacin jikinta yayi sanyi kamar wacce aka zuba masa ruwan sanyi kai a ƙasi, daiden lokacin da su Mommy suka dawo da wasu takardu a hannunta, Ayush tana ganinsu tayi saurin ƙwanciya ta kifa kanta acikin filo domin a halin yanzu bazata iya haɗa ido