Showing 96001 words to 99000 words out of 186041 words

Chapter 33 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53964

zuwa kafaɗarsa, ga ya gyara sajen fuskarsa shima ya ƙwanta har gemunsa kamar wanda ya wanke da shampoo gashin yayi baƙi ƙirin ga laushi, farinsa kuma saiya ƙara fitowa sosai ba karamin kyau yayi ba, ɗaukan turare yayi mai shegen ƙamshi yana feshe duk ilahirin jikinsa dashi,
Daiden lokacin malam Lawan ya shugo da tray ɗin abinci a hannunsa ganin Junaid yanata shiri kamar wanda zai bar ƙasar yace "ha'a mutumin ina zuwa ne haka naga ka fitar da akwatuna lafiya dai koh?..."
Junaid ƙarasowa gaban malam yayi ya karɓi tray ɗin hannunsa ya ajiye a saman table ya ɗago yana kallonsa da damuwa a fuskarsa,
Malam Lawan kansa a ɗage shima yana kallon Junaid, domin Junaid ba ƙaramin tsayi ne dashi ba, duk da malam Lawan nada tsayi amma bai kai kafaɗar Junaid ba, asalin sangami ne ga ƙiran jikin ƙarfi, duk jikinsa a mummurɗe babu alamar tamowa ajikinsa😜
Yace "malam kayi haƙuri bazan iya zama anan gidan ba, inaso zan koma ɗaya daga cikin gidaje na, tin shekaran jiya nasa aka gyara mun gidan da zan zauna, saboda haka yanzu inaso zan koma ne, kuma acan ni kaɗai zan fi jin daɗin gudanar da aikina! Nagode sosai malam, ka bani kulawa yanda ya kamata..."
Malam yace "toh shikenam Junaid ba laifi amma kafin ka tafi ka zauna kaci abinci ko..."
taɓe fuska Junaid yayi sannan yace "gaskiya bana jin zan iya cin komai a halin yanzu, idan akwai milk shi nake buƙata..."
Malam Lawan da hanzarinsa ya nufi gurin tray ɗin abinci yana faɗin "eh akwai mana bari na haɗa maka..."

*****

*AFTER 30 DAYS*

Ayush ce take tsaye a jikin bishiyan mangoro da wani dogon ice a hannunta sai faman tsalle take tana son ciran mango🥭, tayi nasarar ciran guda biyar ana shida ne ta soma jin gurnani ta bayanta, tsayawa tayi tana ƙoƙarin juyawa a hankali, idonta ne ya sauƙa akan wani ƙaton kura yana fuskantar ta,
a tsorace ta soma ja da baya juyawa tayi da gudun gaske shima kuran bin bayanta yayi yana binta da gudu itama gudu take har ta iso saitin ɗakin da take zaune tana zuwa ta ciri wani ƙaton mashi mai tsayin gaske kafin ta ankara kuran yayi sufa yakai mata yakushi, buɗe baki yayi zai kai mata cizo a gigice tayi ihuu tare da kai mashin nan cikin bakinsa ta caka masa har saida mashin ya fito ta bayansa, faɗuwa kuran yayi ta gefen ta yana shure-shure ga jini yanda yake fitowa ta bakinsa, itama Ayush ƙwanciya tayi ta gefen kuran tana maida numfashi hannunta kuma akan tumbin cikinta wanda ya fara girma tana jin yanda cikinta yake ta motsawa da ƙarfi tana jin raɗaɗin hakan jurewa kawai take idonta a lumshe,
Bayan ta ɗan huta kaɗan ta tashi ta maida mashinta yanda yake a ajiye sannan ta fara jan kuran nan har saida ta kaishi can nesa da ɗakinta ta jefashi cikin wani ƙaton rami ta juyo tana jan ƙafa daƙer domin ba ƙaramin gajiya tayi ba, zuwa tayi ta ɗauko mangwarayenta ta dawo ɗakinta,
Ayush haka take rayuwa a cikin dajin nan ita kaɗai, duk ta cire tsoro da fargaba a ranta gani take zata iya tinkarar kowa duk wanda yace zai kawo mata farmaki mutum ko dabba,
Abincinta daga mangoro sai kashu sai kuma ayaba da wasu kayayyakin itacuwa wanda baza'a rasasu acikin jejin ba,
Ruwa kuwa tana kusa da rafi takan je ta ɗebo ruwa a cikin jarkan ta kawo ɗakinta na kara,
cikin ɗakinta kuwa babu komai in banda bunannaki data haɗa gado dasu ta shimfiɗa mayafinta take ƙwana akai,
Ga cikinta kuwa yanzu yana 5months....


******

A ɓangaren Ogah Junaid kuwa ba yanda bai shiga neman Ayush ba amma ko labarin ta babu, cikin dare bai hanashi fita nemanta ba, haka ya ƙauracewa bacci saboda Ayush, ya shiga cikin damuwa sosai,
Haka sauran sojojin da akasa su nemo ta suma babu wani labari akanta,
Shi kaɗai yake zaune a gidansa babu kowa sai iya wani ƙarfaffan maigadi daya nemo sai kuma karnuka daya zuba a cikin gidan waran su uku irin buzajen nan na ƙasar waje,
gidane haɗaɗɗe wanda aka tsara shi, falon gidan ma abun kallo ne balle idan ka haura can upstairs mai hawa na biyar nan ne ɗakin Junaid tsararren ɗaki na alhurma,
(gaskiya idan nace zan tsaya tsara kyan gidan zamu ɓata lokaci ne...)
yana zaune a bakin gadonsa ya dafe kansa da hannu biyu yana kallon ƙasi duk abun duniya yabi ya isheshi, tunanin Dr Hasheem ne ya faɗo masa a rai wanda yake can a hannun sojoji a zabure Junaid ya miƙe tsaye yana faɗin "na manta da wancan mutumin tsawon wata guda yana headquarter ya kamata naje na sallame shi..."
yana kaiwa nan ya yi ficewarsa...

Doctor Hasheem yana zaune shi kaɗai acikin gadurum na sojoji ya zama abun tausayi, duk wanda ya ganshi saiya zubar masa da hawaye,
Gaba ɗaya an canza masa kamannunsa,
fuskan nan ya kumbura sosai! leɓɓerin bakinsa yayi dogo kamar bakin kare tsabar naushin hannun gardawa daya sha, idanuwansa sunyi fusu-fusu sun kumbura sosai don daƙer yake iya buɗe eyes ɗinsa, sun ƙaramce sunyi ciki sosai tsabar kumburi, gefen fuskarsa ɗaya yafi ɗaya kumbura ɗayan ɓangaren fuskarsa ta dama yanda kasan an hura filfila tsabar kumburi, hancinsa ya baje ya zama ƙatoto tsabar naushi,
wani irin rashin mutunci ma da suka tashi yimasa sai suka haske masa kayinsa gaba ɗaya sukayi masa malu tanɗal yanda kasan madubi haka kayin yake sheƙi ga sun faffasa masa kayi duk ya kumbura,
(Allah Sarki Dr Hasheem Allah zai saka maka wallahi😭😭)...

Bayan Ogah Junaid ya iso zuwa yayi ya zauna akan kujerunsu ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan table dake gabansa yana jingine da jikin sofa,
wasu sojojin suna zaune a wajen wasu kuma sunata kai kawo a wajen, Junaid idonsa a lumshe ya ƙira sunan ɗaya daga cikin yaransa sojoji yace "kaje ka tafo mun da wancan mutumin dake kulle ka kawo mun shi yanzu..."
wanda aka aika ne ya gyara tsayuwarsa sannan ya sara masa tareda faɗin "Yes Sir..."
daga nan ya tafi da saurinsa,
ɗaya daga cikin manyan sojojin wajen ne wato canal Ahmad yana fuskantar Junaid yace "wato Oga Junaid Wannan gayen ba karamin buguwa yasha ba, har na tausaya masa wallahi kuma shegen yaƙi faɗan gurin da yarinyar take..."
Sergeant Adams ne ya ari bakin Canal yana faɗin "toh daman akwai wanda zai shugo cikin headquarter ya fita lafiya ne?..."
Captain Junaid gyara zamansa yayi yana fuskantar su sannan yace "wannan mutumin gaskiya yake faɗa bai san yanda yarinyar nan take ba, na daɗe da sanin hakan just na rabu dashi ne saboda dalili ɗaya..."
Canal yace "toh amma kasan da hakan kuma ka barshi aka raunana shi haka?..."
Captain Junaid murmushi yayi yana motsi da lips ɗinsa a hankali cikin sassanyar murya yace "na tsani raini a rayuwata, hannu yasa ya daki Captain ɗin sojoji, shine dalilin dayasa na ƙwanta akan gadon hospital, but a lokacin na kyale shi ne because of my partner of mind...." ya ƙarasa maganar yana cije lips ɗinsa,
Sergeant ne ya zabura ya miƙe yana faɗin "whatt? Ogah shine tin a lokacin baka sanar mana mun dagargaza masa ƙwaƙwalwa da bullet ba, kutt gaskiya ya gama rainaka Ogah..."
Captain Junaid ya sake yin smile yace "no na ƙyale shi ne saboda girman Abokantaka tin yarinta amma in badan haka ba da tinin na yanke masa hannayensa duk biyun..."
Canal yace "gaskiya sai an ƙara hukunta shi domin abu ne mai wuya ace mutum yasa hannu yayi kokuwa da solder, solder ma babba acikin sojoji impossible..."
Commander Nazif dake zaune sai faman chatting yake duk yana jin tattaunawar da suke yi sai a wannan lokacin ya ɗago yana faɗin "toh shi Captain ina yake gani har ayi masa dukan da za'a ƙwantar shi a gadon asibiti? kodai daman hurarin banza ne babu ƙarfi...."
ya ƙarasa maganar yana tintsirewa da dariya, haka sauran sojojin wajen suma suka fara dariya...
Oga Junaid a fusace ya wurga masa key ɗin motar hannunsa ya miƙe tsaye yayo kan Commander yana shirin kai masa naushi!
a ruɗe Commander ya riƙe hannun Junaid yana faɗin "Please and please forgive me our Ogah, nayi kuskure..." fasa naushinsa yayi ya hankaɗa shi ƙasi ya faɗi daga shi har kujerar,
Junaid kallon sauran yayi yana nuna su da yatsa yace "ku kiyaye ni wallahi, idan na rikice muku bazaku gane kaina ba..."
haƙuri suka soma bashi suna faɗin "sorry Oga tiger we'll not try to hurt you again, please colm down! colm down!! colm down!!!..."
Junaid ransa a ɓace ya zauna yana huci daiden lokacin aka kawo Dr Hasheem, Junaid juyawa yayi yana binsa da kallo da farko baiyi tunanin Dr Hasheem bane saida ya ƙareshi da kallo tukun ya iya gane shi, Junaid miƙewa yayi tsaye yana faɗin "meye wannan nake gani?..."
Sojan daya kawo Dr Hasheem ne yace "Oga mutumin da kace ayita dukansa nan ne..."
Junaid taɓe baki yayi yace "kuma sai nace ayi masa rauni har haka?.."
Junaid ƙare wa Dr Hasheem kallo yake tin daga sama har ƙasa gaba ɗaya sun faffasa masa jiki tsabar duka da sanda, ga gefen kunnensa tabo guda ya fashe wannan fashewar gurin wani ne daga cikin sojojin ya maka masa waren ƙarshen bindiga a wajen kunnen, yana tafiya yana ɗingishi sun gurɗe masa ƙafa baya iya tafiya sosai,
Girgiza kai Junaid yayi sannan yace "ina Lailah?..."
Dr Hasheem daƙer yake motsa bakinsa tsabar ciwon da yake masa, baki yayi tsayi sai jinin dake burtsowa a hankali yace "tana asibitin Doctor Mansur..."
"meya faru da ita?..." Junaid ne yayi tambaya cike da mamaki domin yanaso ya kamota yayi mata hukunci daidai da abunda ta aikata domin ya rigada ya binciko itace ta watsar da duk bayanan Ayush wa ƴan jaridu....
Dr Hasheem fashewa yayi da kuka mai cin rai..
Junaid ne yazo kusa dashi yana faɗin "it's okay no anything can happen to you okay..." yana rarrashinsa yasa hannu ya ɗauke shi a saman kafaɗarsa suka nufi hanyar waje,
Junaid yana jin ɗaya daga cikin sojojinsu yana faɗin "ai wannan hukuncin mai sauƙi mukayi masa da sauran kaɗan mu yanke masa sawayensa ai..."
Junaid ko kula shi baiyi ba,
fita waje yayi ya buɗe murfin motarsa ta baya ya saka Dr Hasheem sannan shima ya shige ciki lokacin wani sojan ya fito yana cewa "Oga! Ogah ka manta key ɗin motar..." karɓa yayi sannan yaja motar suka tafi,
Kai tsaye Asibitin da aka ƙwantar da Lailah suka nufa daga nan shima Doctor Hasheem za'a duba lafiyarsa......




*ALLAH SARKI DOCTOR HASHEEM ƊINAAA😭😭😭*
*JUNAID KAI DA SOJOJINKA ALLAH YA ISAN MU...*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 49 ➡️ 50



Bayan isar su Junaid asibitin da aka ƙwantar Lailah, kai tsaye room 8 suka shiga da wani Doctor wanda ya rakosu har ɗakin da Lailah take, ganin ta sukayi akan gadon tana zaune ta naɗe sawayenta kamar mai cin tuwo, ido a rufe tana ta jujjuya hannayenta biyu tana wasu surutai marasa kan gado,
Doctor Hasheem ne ya nufo gurinta da gudu yana ambatar sunanta haɗe da kuka yake faɗin "Lailah! Lailah ki dawo hayyacinki dan Allah, haba Autar mama da Abba..." kuka ne yaci ransa sosai yana rungume da ita,
Shi kuwa Junaid yana tsaye ya zuba musu ido, ganin Lailah a cikin wannan halin ba ƙaramin tausaya mata yayi ba, suna cikin wannan halin saiga babban likita ya shugo wato Doctor Mansur, zuwa gefen Lailah yayi ya zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login