Showing 120001 words to 123000 words out of 186041 words

Chapter 41 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53926

da mommy ba, mommy zama tayi a bakin gadon ta ɗora hannunta akanta tana faɗin "ya hakane Ayushert ki ɗago mata na ganki nayi kewar ki, Alhamdulillah da Allah yasa kika farfaɗo lafiya duk da nasan saboda ni kika suma, kiyi haƙuri kinji ni ɗin ce mommy ba wata ba ...."
Ayush tana jinta amma ta kasa ɗagowa, har saida sarki Raamud ya matso kusa da ita ya kawo kansa saitin kunnenta yana mata raɗa da cewa "Ɓingel karki nuna rashin wayo ki tashi ki nemi yafiyar ta akan abinda kika aikata mata, zata ji daɗi domin in baki kasheta bama kin tafka mata babban asara...."
yana ɗagowa itama ta tashi tareda fashewa da matsanancin kuka ta sauƙa daga kan gadon ta ɗayan ɓangaren ta zagayo tareda durƙusawa ƙasi agaban mommy tana kuka tana faɗin "mommy dan Allah kiyi haƙuri akan abunda na aikata miki wallahi nima nasan banyi miki adalci ba, haƙiƙa nayi miki butulci a rayuwa domin ko mahaifiyata bata nuna mun kulawar da kika nuna mun ba, kin nuna mun soyayyar gaskiya tamkar uwar da take matuƙar son ɗiyarta, ..." kuka ne yaci ranta sosai har ta kasa ƙarisa maganar, itama mommy kuka take tana kallon Ayush cikin tausayawa tasa hannu ta ɗagota tareda rungumarta a jiki tace "kiyi shuru my daughter banson jin kukan ki, wallahi baki mun komai ba abunda kika aikata ko kaɗan banji tsanarki ba domin na ɗaukeki tamkar ƴar dana haifa a cikina, karfa ki manta ciki na fa kika ƙi sannan kika fito a cikin ƴar uwa Bara'at, saboda haka ki ƙwantar da hankalinki komai yazo ƙarshe, insha Allahu daga yau baza ki sake kwanan prison ba, my daughter na yafe miki duniya da lahira..."
Ayush itama rungumar Mommy tayi tana rera kuka mai ratsa zuciya, sun shafi mintuna a haka kafin mommy ta samu nasarar rarrashinta sannan tayi mata albishir da cewa daga nan ba komawa prison, ba ƙaramin farin ciki Ayush tayi ba tana cikin murna lokaci guda ta maida fuskarta kalar tausayi a shagwaɓe tace "Mommy.." kallonta mommy take cikin kulawa ta amsa mata da cewa "na'am ƴar mommy ya akayi ne?.."
tana zubda hawaye tace "missing someone very close to my heart..."
Junaid cikin rashin fahimta yake kallonta fuska a ɗaure, sarki Raamud shima yana zaune akan kujera baiyi tunanin komai ba ya ɗauka ta tuno da mahaifiyarta ne, shima ba ƙaramin tausayawa ɗiyarsa yake ba amma saidai ta wani ɓangare hankalinsa a ƙwance yake tinda har Allah ya haɗasu da mommy mai ƙyakykyawar zuciya.
Mommy kallon Ayush tayi sannan ta kalli yanda Junaid yake a zaune still ta maido da eyes ɗinta kanta tareda faɗin "amma waye wannan wanda kika yi missing ɗinsa haka?..."
girgiza kai Ayush tayi sannan tace "ba namiji ba, mace ce na haɗu da ita ne a prison, yarinya ce ƙarama tana buƙatar temako..."
Junaid ne ya sauƙe wata nannauyar numfashi a bayyane yace "thank God..."
Daga Ayush har mommy tsaya kallonsa suka yi daga bisani mommy tace "lafiya kuwa Junaid?...". ɗaga musu hannu yayi tareda faɗin "no ku cigaba da hirarku..." daiden lokacin da Malam Lawan ya shugo da sallama a bakinsa suka gaggaisa sannan ya nemi guri ya zauna, ya sanar musu cewa "ranar 10 ga watan January za'a koma kotu koh?..". Mommy tace "eh ganan takardar ma amma daga nan gida zamu wuce da Ayush..." Ayush dasauri ta katse mommy da cewa "dan girman Allah mommy ku temaki Hafiza tana cikin mawuyancin hali, gashi na baro cikin prison ba tareda ta saniba saidai ta nemeni ta rasa, yarinyar ta shiga raina du Da du mah shekarar ta 18 a duniya..."
Mommy zaro ido waje tayi tana maimaita kalmar "18 years old? amma ya akayi ta shiga prison a wannan ƙarancin shekarun natan?..." anan Ayush ta kwashe komai dangane da yarinyar ta gaya musu, ba ƙaramin tausaya mata sukayi ba, mommy tace "insha Allahu baza mu barta ta ƙare rayuwarta a cikin prisoner ba, zan tsaya mata tsayin daka Allah Sarki baiwar Allah, saboda iyayenta basu da kuɗi shine akayi amfani da dukiya domin aga ta tagayyara, insha Allahu hakan bazata faru ba, nima zan zubar da ruwan kuɗi domin naga ta fito ta cigaba da rayuwarta cikin aminci..."
kowa saida ya tofa albarkacin bakinsa, Ayush ba ƙaramin farin ciki tayi ba jin Hafiza zata fito daga maƙarƙama....
anan suka shiga hirar su na rayuwa, mommy kaf saida ta ƙwashe rayuwar da tayi a cikin masarauta ta sanar musu ta ƙare maganar da cewa "ai wallahi banso barin masarauta ba, kawai nazo ne saboda yarana amma banda haka babu abunda zai dawo dani Nigeria..."
Sarki Raamud yace "Ni ai bazan iya zaman wannan ƙasar takun ba, duk zafi yabi ya ishi mutum ga ƙura da rana bazan iyaba, yanzu idan na tashi komawa tare zamu koma ai..." ya ƙarisa maganar yana kallon mommy,
juyowa mommy tayi tana kallonsa cikin gatsine tace "waa? saidai gaba ɗayan mu zamu tafi tare da su Junaid, yauwa ga ƙafata ga ƙafarsu domin bazan iya rayuwa ba tareda su ba..."
Malam Lawan ba abunda yake musu inba dariya ba, Ayush itama dariya take tace "ai masarauta ba ƙaramin haɗuwa yayi ba, Ni tinda nake ban taɓa ganin tsararren masarauta haɗaɗɗe kamar masarautar mu ba ga girma, yanzu iya Yaya Junaid da malam Lawan ne kawai basu shiga masarauta baa..."
Zaro ido Junaid yayi yana kallonta yace "waya gaya miki?..."
Mommy tace "kin manta yaƙin da suka je neh?..." Ayush tace "wooo hakane fah ashe! Yaya Junaid ya kaga tsaruwar masarauta?..." juyar da kai gefe yayi domin shi Junaid har yanzu akwai wannan miskilancin nasan, shi baya son irin wannan doguwar hirar..
Sarki Raamud yana kallon Ayush yace "shima Malam Lawan ai ɗan cikin masarauta ne, a cikin masarauta aka haife shi kuma ya taso a cikinta..."
Ba Ayush ba hatta Junaid da Mommy abun ya ɗaure musu kai, gwara ita mommy sun sanar mata a baya amma har yanzu tana mamakin faruwar hakan,
Ayush cikin rashin fahimta tace "tayaya kenam? nifa malam Lawan a daji na sanshi ya zauna damu ni da mahaifiyata daga baya ya tafi domin shine ya koya mun karatun Alkur'ani da wasu abubuwa na addinin musulunci..."
Shima Junaid abun ya bashi mamaki domin malam Lawan bai taɓa sanar musu haka ba, kuma shine ya bashi labarin rayuwar Ayush a daji ita da mahaifiyarta amma bai sanar masa yayi rayuwa dasu ba...
Malam Lawan ne ya kalli Junaid da murmushi a fuskarsa yace "yadai Ogah Junaid kaji abu kamar daga sama koh?..." shima Junaid ɗin shi yake kallo cikin rashin fahimta.
Malam Lawan yace "kar ku damu yanzu zan warware muku komai, zaku san ko ni wanene a yanzu,
Da farko dai sunana Artaff Zaidullah Hussein Ni ɗa ne agurin Sarki Zaid mahaifin Raamud da Máahmud ni ƙaninsu ne amma mahaifiyar mu ba ɗaya bane, su alokacin da mahaifiyarsu ta haifesu ƴan biyu Allah ya karɓi rayuwarsu, kasancewar masarautar ba'ason sarki ya zauna babu mata yasa aka Aura masa ƴar Sarkin ƙasar Iran, wato mahaifiyata Gimbiya Maryama! tinda aka haifeni Máahmud yake jana a jikinsa har na fara wayo a yayinda shi kuma Raamud yake ƙina, ko inuwarsa naje yakan hantareni haɗi da duka, koda mahaifiyata baya son zuwa yanda take daga waran mahaifin mu babu waran da yake zuwa, hakan yasa ya fara jin haushi ɗan uwansa saboda ni, haka rayuwa take tafiya yanda ya kamata har muka mallaki hankalin kan mu a lokacin ne ƙiyayya ta ƙullu a tsakanina da Raamud baya ƙaunar ganina saboda wai kar a bani mulkin masarauta, Allah Sarki ga yayuna waɗanda suka rigani shan iskar duniya taya za'a ban mulki kuma, a lokacin da mahaifin mu yake shirin sauƙa ya tara mutane ya sanar cewa zai bawa Yayan mu wato Máahmud mulkin masarauta anan Raamud ya maida ƙiyayyata zuwa kan ɗan uwansa Máahmud,
har yayi sanadiyar da aka kai farmaki cikin masarautar,
a ranar ni kuma da mahaifiyata munje ƙasar Iran gano mahaifinta yana ƙwance ba lafiya ciwon ajali ya riskoshi, a ranar da mahaifin mahaifiyata ya rasu a ranar saƙo ya risko mu kan cewar an kai farmaki cikin masarautar mu har anyi nasarar kashe mahaifin mu sarki Zaid, Máahmud kuma an ɓatar dashi ƙwata-ƙwata, naji ba daɗi sam na kuma yi rashin mahaifina da kuma kakana na waran uwata,
Mahaifiyata kuwa tinda ta suma jin mahaifinta ya rasu ga kuma saƙon mijinta shima ya rasu ga kuma Máahmud wanda ta sashi a ranta shima baya nan daga nan bata ƙara farfaɗowa ba sai bayan watanni uku nan ma saida aka dage da addu'o'i da maganganuwan Musulunci tukun Allah ya bamu nasarar ceton ta amma har zuwa wannan lokacin tana nan a ƙasar Iran ko magana bata iya yi saboda damuwar dake ranta, tana dai cin abinci tana komai amma bata cewa komai sannan ba sosai take iya gane mutum ba sakamakon hawan jinin da take fama dashi amma tana raye har yanzu, wasu lokuta nakan je na dubota,
tare muka cigaba da zama da mahaifiyata a ƙasar Iran bamu sake komawa ƙasar california ba cikin masarauta, a Iran na cigaba da karatuna har nayi boko da Arabic, amma nafi zurfafa karatuna akan musulunci har Allah yasa na zamo babban malami a ƙasar Iran, amma duk hankalina yana kan binciken yanda zanyi na samo ɗan uwana Máahmud, har Allah ya bani sa'a na samo shi, ya kuma ɓoyeni a gurin matarsa wato Doctor Fateema ya nuna mata cewa ni Abokinsa ne, muka zauna a haka amma bansan dalilinsa nayin haka ba, har Allah ya kawo Bara'atu cikin rayuwarsa ina ganinta nasan akwai ƙullaliyar al'amari domin Ni Allah ya bani wani irin baiwa na saurin gano mutum, ni ba matsafi bane amma ina iya gano komai akan mutum kuma duk wasu bayanai na Raamud ina sanin su domin shima bazan iya fita daga cikin rayuwarsa ba, duk wasu ƙalubalen da yake faruwa da Raamud na sani, domin shi ya shiga jikin Bara'at ta hanyar tsafi ya Aureta ya kuma shiga jikin Máahmud har yayi sanadiyar mutuwarsa ta dalilin cikin Raamud dake cikin Bara'at, wanda a lokacin mun shirya ni da Mahmud akan cewar zamu sanar da matarsa gaskiyar lamari akan Máahmud da kuma ni kaina sai dai Allah bai yadda ba...
A lokacin da Bara'at ta koma jeji da zama nabita naje na zauna dasu saboda nasan ba laifinta bane na koyar dasu abubuwanda basu saniba, nayi hakane saboda bazan taɓa barin Ahalina su tagayyara ba, koba komai Bara'at da ɗiyarta sun zamo jinin mu bazan gujesu ba, kuma shi kansa Raamud bazan taɓa ƙinsa ba duk da ƙiyayyar da yake nuna mun a baya, naji daɗi yanzu da aka sanar mun cewa Masarautar mu ta gyaru, insha Allahu masarautar mu bazai taɓa barin hannun mu ba saidai idan mun ƙare gaba ɗayan mu....."
Daga nan yaja ajiyar zuciya a yayin da hawaye suka wanke masa fuska...

Cikin macewar jiki sarki Raamud yakai hannu ya dafa kafaɗar malam Lawan sannan yace "Artaf kayi haƙuri nasan na aikata babban kuskure a rayuwata, nima kawai ina rayuwa ne amma bana jin daɗinta, na tsani kaina! idan na tuna cewa nine nayi sanadiyar mutuwar mahaifin mu sai naji kamar na rataye kaina, idan na tuna cewa ni nayi sanadiyar mutuwar ɗan uwana sai naji kamar nasha guba na kashe kaina, idan na tuna cewar ni nayi sanadiyar tarwatsewar rayuwar matata da kuma ɗiyata sai naji kamar nake gaban trailer ta murƙusheni, idan na tuna cewa ni nayi sanadiyar wargaza rayuwar Junaid da kuma sanya mahaifiyarsa cikin damuwa sai naji kamar na nasa wuta ajikina, idan na tuna cewar ni nayi sanadiyar jefa matar mahaifina cikin jinya sai naji kamar na datsawa kaina wuƙa amma idan na tuna cewa Allahu gafurur Raheem sai naji nutsuwa a raina, amma kuma idan na tuna cewa Allah baya shiga tsakanin bawa da bawa saidai idan wanda ka zalunta ya yafe maka sai naji kamar naita ihu, idan har haka ne aina zan samo Babana ya yafe mun? Aina zan samo Ɗan uwana ya yafe mun?..."
kuka ne ya ƙwato masa mai cin rai, da ƙarfi yake wannan kukan, shima Artaff rungumar ɗan uwansa yayi yana tayashi kukan,
Gaba ɗaya jikin mommy ne yayi sanyi babu ƙarfi ko kaɗan, Junaid kansa a sunkuye ko ɗagowa ya kasayi sakamakon hawayen da suka wanke masa fuska,
Ayush itama jin yanda Mahaifinta yake kuka yasa itama ta fashe da matsanancin kuka duk idanuwanta sunyi jawur kana ganinta kasan ba tin yanzu ta fara kukan ba,
Artaf yana kuka ya ƙarasa musu labarin da cewa "Matata ba ƴar nan ƙasar bace, ƴar ƙasar Iran ce ƴar ƙanwar mahaifiyata aka Aura mun, muna zaman mu acan na ɗaukota muka dawo nan Nigeria saboda iyalan Ƴan uwana wato Máahmud da Ɗansa da kuma Matar Raamud da Ɗiyarsa, saboda ku na dawo Nigeria da zama sakamakon nayi Alƙawari wa kaina cewa zan kula daku, zan riƙe ku Amana, bazan bari ku tozarta ba, duk rintsi duk wuya ina tareda ku, shi Raamud ban damuba saboda nasan Amanar Mahaifinmu yana tareda dashi wato Narasimha...."
anan ya ƙara fashewa da kuka....

Sarki Raamud shima ƙara volume kukan yayi saboda abunda ya wuce a baya ba ƙaramin tayar masa da hankali yake ba,
Ga muryar Ayush itama yanda take ta kuka bugu da ƙari ma ta tuno da mahaifiyarta,
Mommy jin yanda suke ta kuka ne yasa itama ta fashe da kuka ta tuno da mijinta,
Junaid jin yanda suka hargutsa cikin ɗakin da kuka babu mai rarrashin kowa yasa ya tashi yabar ɗakin domin a halin yanzu bashida sukunin da zai iya rarrashinsu, kuma acikinsu baisan wazai fara rarrashi ba,
shin Uncle Artaff zai rarrasa ne ko kuma Sarki Raamud ko kuma Ayush ko kuma mommy wacce ta fara yanzu?.."
haka yana ji yana gani ya barsu ya fice abunsa....



*TAPAH ASHE ƳAƳAN SARKI ZAID SU UKU NE MUKA MANTA DA ƊAYA ACIKINSU, WATO ARTAFF MALAM LAWAN KENAM*
*JINI BAYA ƁUYA SAI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login