Showing 93001 words to 96000 words out of 186041 words

Chapter 32 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53951

Bayan sallar asuba gari yaɗan fara wayewa Junaid yana ƙwance bai tashi ba har yanzu domin wani irin nannauyar bacci ne ya ɗauke shi,
yana cikin bacci yaji an turo ƙofa da ƙarfi Malam Lawan ne ya shugo da hanzarinsa yana ƙiran sunan Junaid,
"Junaid! Junaid!! Kai Junaid ka tashi mana"
Mutsil-mutsil Junaid yake yana shirin buɗe idonsa, malam Lawan ne yasa hannu ya finciko shi zaune yana faɗin "ko sallah bakayi ba, shin kasan maiyake faruwa ne yanzun?.."
Junaid waige-waige ya somayi yana faɗin "ina Yushert take?.."
malam yace "Ayshert kuma tazo ne?.."
cikin rashin fahimta malam yake kallon Junaid,
Junaid ganin kar malam yayi tunanin wani abu yasa ya kawai da maganar Ayush yace "lafiya kuwa malam?.."
Malam yace "mafarki kayi koh?.."
sunkuyar da kai ƙasi Junaid yayi yace "Hmmm!.."
Malam yace "yanzun tashi kayi sallah tukun kaji wani zance.."
sauƙa daga kan gadon Junaid yayi yana tunanin abubuwa da dama a ransa ya nufi toilet ya ɗauro Alwala, yana maganar zuci "shin ina Yushert taje? yaushe ta tafi? daman ba zuwa tayi ta zauna dani ba?..." haka yake wannan tunanin har ya komo ɗakin ya ɗauki jallabiyarsa yasa sannan ya daidaita nutsuwarsa ya fara sallah, bayan ya idar ya fuskanci malam Lawan yaga kamar yana cikin matsala yace "wai malam meyake faruwa ne kam?..."
Malam ne ya miƙe tsaye yaje ya ɗauki remote ya kunna plasman dake manne a jikin bangon ɗakin yace "Junaid kalli abunda yake faruwa..".
Tashar labarai ne ta ko ina ana maganar Ayush cewar ita tasa wuta a gidan Doctor Fateema, ita tayi sanadiyar mutuwar Doctor Fateema, ga photunan Ayush yanda yaketa yawo ana nunota ga kuma photon marigayiya Doctor Fateema, ga photon gidan yanda yayi ƙurmus, an bayyanar cewar Ayush tana nan a gidan Doctor Hasheem a ɓoye..
Sai kuma aka nuno video gidan Doctor Hasheem yanda mutane suka taru a ƙofar gidansa kowa yana riƙe da makamai ga ƴan jaridu ga sojoji da ƴan sanda dasu human rights duk a ƙofar gidan, a cikin television ganan maigadin gidan yanda aka cire masa kayan jikinsa a barshi daga shi sai gajeren wando ana tilasta masa akan ya faɗi yanda Doctor Hasheem ya ɓoye Ayush....
Kawar da wannan video akayi suka kunna recording maganar Ayush yanda ta amsa da cewa ita ta ƙona Doctor Fateema a lokacinda take magana da Doctor Hasheem duk a cikin television yanzu ta tabbata cewar ita ta kashe Doctor Fateema ta hanyar dasa gobara a gidanta....

Junaid yana zaune baisan lokacin da ya miƙe tsaye ba kamar zai haɗiyi ransa, a fusace yace "waye ya sanar da ƴan jarida wannan maganar? Waye yayi wannan aika-aika? bazan zauna ba dole zan nemo Yushert bazan bari a raunanata ba, tana da juna biyu a jikinta..."
a tsawace yake wannan maganar ya fice daga cikin ɗakin a ruɗe,
Shima Malam tashi yayi yabi bayansa da sauri, suna zuwa Malam ya buɗewa Junaid motar shima ya shiga suka tafi, kai tsaye gidan Doctor Hasheem suka nufa yanda ƴan jaridu da sojoji suke...

Shima Doctor Hasheem yana daga hospital yaga yanda mutane suke kallon labarai a babban television cikin hospital ko tsayawa sauraro baiyi ba ya fice da gudun gaske yana ambaton sunan "Ayush"
motarsa ya shiga a ɗari yabar asibitin ya nufin gidansa...



*TOPAH LABARI YANATA TAFIYA..*
*WAI ME AYUSH TAKE NUFI NE🤔? SHIN DA JARIRIN MU ZATA KOMA JEJI KENAM🙄 GASKIYA JARIRIN MU BAZAIYI IRIN RAYUWAR DA TAYI ACIKIN JEJI BA YACIINN😳😳*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 47 ➡️ 48

*FOREST*

tin da safe Ayush take faman haɗa ɗakin kara har zuwa yanzu bata ƙarisa ba, dajin babu motsin kowa sai zallan kukan tsuntsaye, ata kusa da ita kuma bishiyoyin mangoro ne da su kashu, idan kayi tafiya kaɗan kuma rafine daga nesa zakaji ƙarar tafiyan ruwa, ga zunzurutun sanyi da iska da akeyi amma da haka take wannan aikin...

Ta ɓangaren su Junaid kuma bayan isowarsu gidan Doctor Hasheem da sauri ya sauƙo daga cikin motar kai tsaye ya miƙi hanyar shiga cikin gidan, ƴan jaridu ne suka yo kansa da gudu suna masa magana akan ya faɗa musu abunda yake cikin ransa da kuma kalar hukuncin da zai ɗauka akan yarinyar, Junaid ganin sun tare masa hanya kuma ga jerin tambayoyin da suke masa yasa ransa ɓaci sosai a fusace yasa hannu ya hankaɗasu baya yana faɗin "stay away from me, stupid people's.."
Duk ƴan jaridun nan faɗuwa ƙasi sukayi a tsorace suka miƙe suna guduwa, shiga cikin gidan Junaid yayi yana ƙwallah ƙiran Ayush, "Yushert! Yushert!! Yushert!!! ki fito babu abunda zai sameki, ina tareda ke..."
wani Ma'aikaci ne ya biyo bayansa yana faɗin "yallaɓai bata gidan fa duk mun dudduba, ina tunanin Doctor Hasheem ya ɗauketa sun gudu..."
a firgice Junaid ya juyo yana kallon Ma'aikacin ido a zazzare yace "Whatttt?..."
juyawa yayi da gudunsa ya fita daga gidan yana fita ya tarar da Ogansu na Sojoji shima yazo wajen, nufa gurin Ogan yayi yaje gabansa yana faɗin "Please Oga kuyi haƙuri kubar mun aikin nan a hannuna, kace wa duk sojojin su tafi kar su saka kansu cikin wannan case, Please..."
Oga murmushi yayi yana kallon Junaid yace "Captain Junaid Wannan case ɗin bai shafeka ba, Ni General nace ka cire hannunka akan wannan case, ka bar mana komai a hannun mu tinda kai baka kishin mahaifiyarka, bawai zamuyi aikin nan saboda mahaifiyarka bane no zamuyi ne saboda mu kare hakkin ƙasar mu, bazamu lamunci wannan zaluncin da yarinyar nan tayi ba dole hukuma tayi aiki akanta, kuma ko waye yayi ƙoƙarin aikata wannan laifin sai mun hukunta shi, balle a aikata wannan ƙazamin hukunci akan mahaifiyar Captain kuma muna ji muna kallo mu ƙyale no impossible, kuma ko kaine ka aikata hakan dole mu ɗau hukunci akanka!
You Understand?"
Junaid gyara tsayuwarsa yayi yace "Yes Sir..." tareda sara masa...
General karɓan lasfika yayi yana sanarwa akan cewar "Sojojin mu inaso kafin zuwa gobe ku tabbatar kun kamo yarinyar nan duk yanda ta shiga, da zaran kun kamota ku tabbatar kun miƙata hannun hukuma daga nan a kaita Kotu a yanke mata hukunci daidai da ita, idan kuma taƙi kamuwa da zaran kun ganta ku harbeta wannan umarni nane..."
yana kaiwa nan ya shige motar suka bar wajen da sauran motacin sojojin da suka zo a tare...

Junaid yana tsaye zuciyarsa sai faman bugawa take, gaba ɗaya ya tsorita da jin kalaman General, yana kuma tunanin taya akayi maganar nan ta fito waje har kowa ya sani? "Shin waye ya tona wa Yushert asiri kuma harda ɗaukan video ba tareda saninta ba? ina zargin mutane biyu! Hasheem ko Lailah..."
yana ƙarasa maganar saiga Dr Hasheem yazo shima da motarsa, dasauri ya fito daga cikin motarsa yana mamakin ganin yanda aka taru a ƙofar gidansa, ga motar sojoji gana police ga kuma ƴan jaridu,
Da gudu Junaid yayo kansa yaci ƙwalar rigarsa yana faɗin "where is my Yushert? Ina ka kaimun ita?..."
Dr Hasheem ƙoƙarin zamewa yake yana cewa "Ni kuma? rabona da ganin Ayushert tin jiya ai.." kafin Dr Hasheem ya ƙarasa maganar Junaid ya haɗe musu goshi da ƙarfin gaske ya gwara kansa dana Dr Hasheem har saida ya kifu a jikin motarsa ɗagowa yayi yana kallon dishi-dishi tsabar buguwar da Junaid yayi masa,
Junaid ɗago shi yayi ya fara kai masa naushi yana tambayarsa "ina Yushert? where is her Ina ka kaita?..." yana tambayarsa amma bai daina dukansa ba, haka ya rinƙa kwaɗa shi da ƙasa yana ɗagoshi....
Ƴan jaridu duk sun saita camerar su kan Junaid duk yayi wa Dr Hasheem jinajina, sannan duk wanda yayo kansa zai ceci Hasheem haɗasu yake ya mazgesu tare, shiyasa duk aka rasa wanda zaije ya karɓi Dr Hasheem,
haka sojojin nan duk tsoron Junaid suke shiyasa suma suka make a guri ɗaya babu wanda yazo kansu,
Malam Lawan ganin Junaid yana shirin yin kisan kai ne yasa ya nufi gurin da yake da sauri yana faɗin "kai Junaid kanada hankali kuwa? ka barshi haka mana..."
Malam Lawan ne ya rirriƙe shi Junaid a fusace ya dunƙule hannunsa zai kaiwa malam naushi dake bayansa, ganin malam ne yasa ya fasa Lokaci guda kuma ya durƙusa a ƙasi yana kuka....
Maganganun General ne suke masa yawo a ƙwaƙwalwa,
Ga kuma Dr Hasheem a yashe a ƙasi yanata birgima, jini ta ko ina fita yake, duk Junaid ya faffasa masa hanci da baki ga idonsa yanda ya kumbura suntum tsabar naushin da aka kai masa a gurin,
wasu Police ne su uku suka zo gurin da Dr Hasheem yake a ƙwance suna ƙoƙarin ɗaga shi, Junaid yana durƙushe da gwiwowinsa ya ɗago da dara-daran idanuwansa waɗanda suka kaɗa sukayi jawur tsabar baƙin ciki a tsawace yace musu "ina zaku kaishi?..."
wani daga cikin ɗan sandan ne yace "am amm yallaɓai daman zamu kaishi ofishin mu ne zamuyi wasu bincike akansa ne sakamakon ya ɓoye mai laifi..."
Kafin yakai ƙarshen maganarsa Junaid ya darara masa uban tsawa yana faɗin "police station ɗin banza! Ina sojojin mu suke?..."
da gudu sojoji suka yo kan Junaid suna sara masa tareda faɗin "Yes Sir..."
cikin ɓacin rai yake magana yace "ku tafi dashi can headquarter kuyi ta dukansa har saiya gaya muku yanda yakai Yushert, idan kuwa bai gaya muku ba ku ƙwaƙule masa idanuwansa gaba ɗaya umarni nake baku ba shawara ba..."
gaba ɗayansu hannu suka kai saitin goshinsu suna faɗin "Yes Sir an gama..." haka suka ɗauki Dr Hasheem kamar babu rai a jikinsa suka sashi a motar suka nufi headquarter...
wani ɗan jarida ne ake masa video yanata surutai akan abubuwan da suke faruwa, a fusace Junaid ya juyo ya wurga masa wani ƙaton dutsi akan goshinsa, a razane ɗan jarida yayi ƙara game da sa hannu yana dafe da goshin kafin kace mai goshi ya fashe nan danan jini ya wanke masa fuska,
Ganin haka duk ƴan jaridun suka fara gudu suna shiga motocinsu, shima wanda aka fasawa goshin tinin ya shiga motar sun gudu, suma ƴan sandan gurin kama hanya sukayi suka tafi, kowa ya watse ya rage daga Malam Lawan sai shi Junaid ɗin, daƙer Malam Lawan ya rarrashi Junaid akan ya tashi su koma gida, zuciyarsa ne yake wani irin tafarfasa da haka yake jan ƙafa ya buɗe murfin motar zai shiga ƙwatsam sai yaji ana ƙiran sunansa ta baya "Ogah Junaid! Ogah Junaid!! ga wannan jakar mun sameshi ne a cikin asibiti..."
wani ma'aikacin asibiti ne ya kawo masa, Junaid hannu yasa ya karɓi akwatin cike da mamaki yace "wannan ai akwatin Yushert ne" yana cikin wannan tunanin yaji likitan yace "ga wannan takardar a jikin akwatin muka ganshi..." Junaid karɓa yayi idonsa akan likitan,
Likitan ganin irin kallon da Junaid yake masa ne yasa shi tsarguwa ya fara yin dariyan yaƙe yana faɗin "am saidai Ogah ban karanta saƙon ba wallahi, naga a bayan takardar an rubuta sunanka da manyan baƙi shiyasa nace wannan saƙon naka ne..."
yana kaiwa ƙarshen maganar ya juya da sauri ya tafi,
Junaid mota ya shiga malam Lawan ya jasu suka tafi...

Bayan isar su Junaid gida zama yayi a bakin gado yana karanta rubutun jikin takardar, abunda Ayush ta furta wa Junaid a yayin da yake bacci kafin ta tafi shi ta ƙara maimaita wa ajikin takardar!!
Junaid ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba har da ƙwallarsa a hankali ya furta "why Yushert meyasa zakiyi mun haka? ke da yarona bansan halin da zaku shiga ba, ya zama dole na nemoku a yanda kuke...."
tashi yayi ya fara tattara kayansa ya shirya duk wasu abubuwansa ya haɗesu a cikin jakarsa, sannan ya shiga wanka shaf-shaf ya fito yayi shirinsa a nutse, yana sanye da blue jeans da t-shirt mai zanen White and blue, da blue cover shoe a ƙafarsa, yana tsaye a gaban mirror yana taje suman kansa daya ƙwanta luf-luf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login