Showing 150001 words to 153000 words out of 186041 words
Kuka take tana shure-shure, bata san lokacin data ƙwanta tana birgima ba, haka ta sake tashi daƙer ta kamo hannunsa tana jansa amma saidai ya tureta sannan ya juya ya cigaba da baccinsa, ga duk ta ɓaci da jini!
Ganin bashi da niyar tashi yasa ta kama gadon daƙer ta tashi taje saitin kayinsa ta kafa bakinta akan kunnensa da ƙarfi ta garzaya masa cizo,
A firgice ya juyo a rashin sani ya zabga mata mari har saida ta faɗi ƙasi yana kame da kunnensa ya juya ya cigaba da baccinsa, shi a tunaninsa duk mafarki yake yi, a cikin mafarkin yake jin shessheƙar kuka amma ya kasa farkawa, saima jan pillow da yayi ya runguma a madadin Ayush, ya ɗauka ita ya runguma,
Ayush tana kuka ta soma rarrafe ta nufi hanyar fita daga ɗakin, ta kasa miƙe wa tsaye sakamakon cikinta da mararta sun riƙe babu halin tashi ita kaɗai, haka ta rarrafa daƙer ta buɗe ƙofar ta fice,
A zaune take jan mazauninta tana sauƙa daga kan beni duk yanda taja sai wajen ya ɓaci da jini, da haka tayi nasarar sauƙa daga beni na uku, saida ta huta tukun ta cigaba daja tana ƙoƙarin sauƙa a beni na biyu, in cikinta ya juya saita ɗanyi ƙara ta jinkirta kafin ta cigaba da ja da gindi, tana kaiwa ƙarshen beni na biyun ta ƙwata a wajen saida ta gama juye-juyenta bayan ya ɗan lufa kuma du ta soma ƙoƙarin sauƙa daga beni na ɗaya shine na ƙarshe wanda zai sadata da babban falo, daƙer tana kuka da muzurai ta ƙarasa sauƙa falon tana ja a zaune,
saida tazo tsakiyar falo zata nufi ɗakin mommy cikinta yayi wani irin juyi da ƙarfin gaske, taji wani abu kamar dutsi ya sauƙa mata ƙasin marar ta kamar zai fito ta farjinta a gigice ta saki wani irin ihuu sai a dodon kunnen mommy tayi sujjada kenam, ƙirjin mommy ne yayi wani irin bugawa a rikice take karanto addu'o'i acikin sujjadar amma ta kasa ɗagowa,
Hafzat itama idar da sallar ta kenam don ko addu'a bata fara yi ba taji wannan ihun, a ruɗe ta miƙe tsaye tareda addu'a,
kafin ta motsa ta ƙara jin wani ihun ana ƙwalla ƙiran sunan mommy,
a tsorace Hafzat tace "Innalillahi kamar Aunty Ayusher..." tayi hanyar fita da gudu, kai tsaye cikin falo ta nufa tana zuwa ta tarar da Ayush ƙwance ta naɗe sawayenta jin abu yana shirin faɗowa,
kuka take tana faɗin "wayyo Allah nah kayan cikina zasu zubo, kuzo ku temake niiii, mommy kayan cikina zasu zubooo..."
Hafzat itama ta tsorita sosai haka ta rinƙa zarya acikin falon ta kasa aiwatar da komai sai yarfe hannayenta take tareda faɗin "wayyo Allah mun shiga uku Aunty Ayusher ɗinmu zata mutu, wayyo Allah jini ta ko ina Aunty Ayusher zuba yake, dan Allah kar ki mutu..."
sai kuka itama take tayi kuma ta kasa taɓa Ayushert, suna cikin wannan halin saiga Mommy ta tafo da gudu kamar zata kife haka ta nufi gurin Ayush ta ɗagota tareda faɗin "Kiyi haƙuri haihuwa ne, ki ware sawayenki..."
Cikin kuka Ayush tace "wallahi bazan ware sawayena ba kayan cikin zubowa zasu yi, kuma mutuwa zanyiii..."
Mommy tace "ki ƙwantar da hankalinki yanzu hospital zamu kai ki, Ayush taya zan ɗagoki bayan kin tuƙwiƙwiye kamar maijin sanyi ki sake jikinki mu samu damar ɗagoki..."
"wallahi mommy kayan ciki nane zasu zubo idan na sake jikinaa..."
Mommy ganin Ayush zata iya kashe jaririn indai ba'ayi saurin kaita hospital ba yasa ta cewa Hafzat "riƙe mun hannayenta Ni kuma saina kama ƙafafuwanta mu ɗagata.."
Hafzat jiki na kakkarwa tace "wallahi mommy bazan iya ba tsoro nake ji..."
A fusace mommy ta daka mata tsawa tareda cewa "ki kama mun hannayenta mu fita da ita waran motar shine aiki?..."
fashewa Hafzat tayi da kuka ta kasa motsawa, itama Ayush kuka take sosai tana faɗin "wayyo Allah kayan cikina zasu zazzaɓoo ku temake niiii..."
Gaba ɗaya mommy ta rasa yanda zatayi ga Ayush taƙi sake jikinta balle ta ɗagota su fita, ga kuma jini yaƙi tsayuwa..
suna cikin wannan halin saiga Judan ya fito dasauri jin kururuwa yayi yawa yana sanye da baƙar jallabiya ya ƙaraso gurinsu yana faɗin "lafiya kuwa meyake faruwa ne..."
Mommy a gigice ta riƙo hannunsa tana daɗin "haihuwa ne munaso mu kaita hospital ne, temaka ka ɗauketa mu tafi dan Allah..."
Hannu Judan yasa ya ɗauketa tana ƙara tuƙwiƙwiye kanta saboda kar kayan cikinta su zubo..
da haka aka fita da ita har wajen parking, nan danan Judan ya tada motar suka miƙi hanyar gate,
Ayush tana bayan motar kanta yana kan cinyar mommy, ita kuma Hafzat tana gaban motar suna isa wajen gate security ya yi saurin buɗe musu suka fita da gudun gaske sai hospital....
Shi kuwa Junaid yana nan rungume da pillow bai san wainar da ake tuyawa ba, sai ana ƙiran Asuba nan ma saida ya kusan makara ana shirin shiga sallah ya yi saurin tashi yana miƙa tareda jero addu'o'i, idonsa a lumshe ya zuro zara-zaran sawayensa ƙasi yana shirin tashi, kai tsaye toilet ya miƙa ya ɗauro Alwala sannan ya fito tsabar bacci yana cin idonsa bai lura da Ayush bata nan ba haka ya ɗauki jallabiyarsa ya zura yayi hanyar fita tareda faɗin "My Yushert shine yau ɗin kikayi sallarki baki tasheni ba koh?..."
Daiden lokacin da ya buɗe ƙofa ya fice bai saurari ko za'a bashi amsa ba, yana sauri kar a shiga sallah ya rasa jam'i, dake kullum Ayush ce take tashin shi sallar Asuba, ana ƙiran farko zata tashe shi,
Duk bai lura da jinin dake ɗakin ba amma ba lallai ya gane cewa akwai jini ba saboda carpet ne irin mai dark ɗin nan da kuma gashi-gashi a jiki,
Amma Benin kam duk tiles ne indai ya kalli ƙasi dole zai gani...
Shima Abban duk kururuwan da akaita yi acikin daren baiji ba dake part ɗinsa da ɗan rata kuma a lokacin ba wai bacci yake yi ba shima yana sallar daren,
A harabar gidan Abban ya haɗu da Junaid sai faman sauri yake zai fita a tare suka tafi masallaci...
★★★★★★★★
A lokacin da aka kai Ayush labour room ihu take tana ƙiran sunan Yaya Junaid, a lokacin yaron ya jikkata sakamakon maƙurashi da tayi har ya daina motsi, saida aka mata wani Allura wanda zaisa yaron motsawa,
Itama mommy rigar likitancinta ta sanya ta shige ɗakin,
Judan da Hafzat kuwa a waje aka barsu suna zazzaune,
Ana ƙiran Asuba daƙer Ayush ta haifo santalelen yaronta, ƙato dashi fari tasss kamar balarabe,
tana haifansa kuwa ta suma, mommy farin ciki kamar bazata mutu ba, ganin Ayush bata motsi yasa suka ɗauko Allurar kashe jiki zasu yi mata Operation sakamakon akwai wani yaron a ciki, kuma a halin yanzu bazata iya amfana ba,
hakan akayi saida aka ciro mata jarirai biyu bayan wanda ta haifa kafin,
An samu ƴan uku
Namiji ɗaya shine wanda ta haifa da kanta,
sai kuma mata biyu bayan an mata Operation,
Amma ba ƙaramin wahala Ayush tasha ba, bata cikin hayyacinta kwata-kwata,
haka aka shiga gyara yaran gwanin sha'awa gasu triplets rass...
★★★★★
Bayan su Junaid sun koma gani yayi babu Ayush, saida ya ƙarashi dubata bai ganta ba tukun ya lura da jinin data ɓata, gabansa ne yayi wani irin bugawa a tsorace ya ƙwalla ƙiran ta "Yushertttt!!!!
da gudu ya sauƙa down stairs ya nufi ɗakin mommy, itama ya tarar bata nan, ya fito falo nan ma yaga jini duk ya ɓata carpet ɗin, a ruɗe ya wuce part ɗin Abba, nan ya sanar masa halinda ake ciki, nan danan Abba ya shiga ƙiran wayan mommy amma saidai wayar ta barshi a gida,
Abba yace "ina tunanin fah suna hospital ko haihuwa Ayush zatayi .."
Junaid kamar ya nitse ƙasi haka yake jin kansa na rashin ganin Ayush kuma ga jini ta ko ina, a gigice yace "Abba muje hospital ɗin banaso na rasa Yushert..."
Suma haka suka nufi hospital,
Kafin ka ƙirga mintuna har sun isa hospital dake Junaid shi yake driving gudu yake bana wasa ba..
suna sauƙa ya rufa cikin facility ɗin hospital da gudu, yana zuwa ya tarar da Judan da Hafzat zaune babu wanda yayi magana acikin su, Hafzat sai faman kuka take ta gagara yin shuru, ganin halinda ya tarar dasu yasa gabansa ya ƙara yankewa gaba ɗaya ya gama tsorita, a gigice ya dafa kafaɗar Judan yana faɗin "Ina Yushert? Meya faru da ita?..."
Judan yace "tana cikin can ɗakin..."
Da gudu Junaid zai nufi ɗakin Judan yayi saurin riƙo shi yana faɗin "Ah ahhh ka kwantar da hankalinka Ogah, can ɗin labour room ne haihuwa ne ya tashi mata..."
wani irin haɗiyar yawu yayi tareda faɗin "Allah yasa dai karta mutu..."
Judan yace "insha Allah zata haihu cikin ƙoshi lafiya .."
Shima Abban ƙarasowa wajen yayi dasauri yana addu'a Allah ya sauƙeta lafiya,
Suna cikin wannan halin saiga wata Nurse ta fito daga cikin ɗakin tana sauri zata ɗauko abu, Junaid yayi saurin tareda yana faɗin "Ina Yushert ɗina?..."
Nurse murmushi tayi tace "ta haihu..."
Junaid yace "toh Amma ita fah??..". bata samu damar bashi amsa ba ta wuce saboda saurin da take yi,
Can bayan wasu mintuna saiga Mommy ta fito tana kuka,
Ganin tana kuka yasa duk suka tsorata, gaba ɗayansu nufo gurinta sukayi suna tambayanta Ayush,
Mommy taƙi yin magana sai hawaye,
Junaid cikin firgici da tashin hankali ya mannu da jikin gini, jikinsa gaba ɗaya ya mutu idanuwansa sun kaɗa sunyi jawur yana shirin zubda ƙwallah yaji mommy ta tintsire da dariya, lokaci guda ta fara tsalle tana faɗin "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Alhamdulillah Masha Allah!!!! Allah mun gode makaaa..."
taje gaban Junaid tana murna tace "wannan kukan farin ciki nake yi Ayush ɗita ta Haifi triplets ƴan uku kuma tana cikin ƙoshin lafiya...."
Zaro ido Junaid yayi cike da mamaki yace "Mommmm are sure? Triplets fahh?..."
Mommy tace "yesss my son..."
Tsabar farin ciki Junaid baisan lokacin da ya rungumi mommy ba ya ɗagata sama yana juyi da ita..."
Momy buɗe baki tayi tana faɗin "kai kai kaiiii sauƙe ni dallah ni ɗin dai ba ƴar tsana bace, kaji mun wawan yaro..." ta ƙarasa maganar tana dariya, sauƙeta yayi ya nufi cikin ɗakin da gudu, daman an rigada an shirya ɗakin da yaran gaba ɗaya anyi musu wanka an sanya musu kayan sanyi na jarirai daman an tanadar dasu, ita kuma Ayush tana kwance an gyara ta itama tana rufe da mayafi zuwa ƙirjinta har yanzu bata farfaɗo ba,
ganan ledar jinin da aka ɗaura mata yana ɗiga a hankali saboda ta zubda jini sosai kafin azo asibitin ma....
Junaid yana shiga gurin Ayush ya fara nufa ya zauna a bakin gado yana shafar kyakykyawar fuskarta, ido a lumshe sai yaga ta ƙara masa kyau sosai ta ƙara fari daman gatanan kamar tsohuwar Aljana tsabar farin fata da kyau, yanzu kuma saita ƙara farin akan na baya,
Daga baya suma su Abba da mommy da Hafzat da Judan suma suka shugo fuskarsu a washe kowa bakinsa a buɗe an kasa rufe shi,
zama sukayi akan kujerun ɗakin kowa yana ɗaukin a bashi jariri,
Mommy ta ɗauki jaririn namiji ta miƙawa Abba, ta ɗauƙi ɗayan mace ta miƙawa Judan ɗayar kuma ta bawa Hafzat,
Shi kuma Junaid yana ta Yushert ɗinsa bai tsaya duba Jariran ba,
Kowa a cikinsu saida ya tottofawa jariran Addu'o'in neman tsari, kafin shima Junaid ya karɓesu ɗaya bayan ɗaya yana musu ƙiran sallah a cikin kunnensu tareda Addu'o'i....
A wannan ranar farin ciki saida mommy ta ƙira ƴan uwa da abokan arziƙi duk ta sassanar musu, Uncle Artaff kam shine first ɗin ƙira,
Kafin azozzo duba Ayush saida aka canza mata ɗaki zuwa wani katafaren ɗaki na alhurma ya gama haɗuwa kamar ɗakin ba'a cikin hospital yake ba,
harda plasman da frig ga A.C amma saide an kashe A.C an kunna abunda yake bada ɗumi a ɗakin saboda jarirai basu son sanyi,
(Nidai na manta sunan abun dake babu a house 🤣🤣)...
Ga labulaye masu tsada, carpet kuma kana takawa yana nutsewa dakai, ga wasu kujeru masu kyan tsada guda bakwai,
Cikin toilet kuma akwai shawer na ruwan sanyi da zafi, akwai kuma bahon wanka, anyi sa'a zuwa wannan lokacin Ayush ta farfaɗo saidai bata jin daɗin jikinta, ba jumawa saiga su Uncle Artaff da iyalansa shima sunzo hospital, a ranar anyi baƙi kam duk abokan arziƙi ne da masoya, banda ƴan uwansu