Showing 84001 words to 87000 words out of 186041 words

Chapter 29 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53948


cikin ya hanata cin abinci sannan ya hanata ƙwanciya, daga tayi ne sai Amai koda bazata amar da komai ba haka zata rinƙa kakakin Amai,
tana zaune a toilet tana bacci jikinta har wani kakkarwa yake ga wani zazzaɓin da yake damunta, jikinta duk ya ɗau zafi, har wani canza colour tayi tsabar azaba launinta ya koma yellow......





*TOH PAH 🤣🤣🤣 ALLAH SARKI AYUSH HAR KIN BAN TAUSAYI WOLLAH...*

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 43 ➡️ 44



Bayan sallar Asuba da sassafe sai ga motar Junaid a ƙofar gidan Doctor Hasheem, buɗe murfin motar yayi ya fito da hanzarinsa hannunsa riƙe da katunan Aurensu, buga gate yake da ƙarfin gaske,. daga ciki ne maigadi yace "waye ne fisabilillahi da sassafen Allah" ya ƙarasa maganar yana buɗe gate ɗin! ganin Junaid ne yasa shi washe baki yana faɗin "ahoo ashe yallaɓai ne, sannu da zuwa" bai ƙarasa maganar ba Junaid ya bangaje shi tareda shige wa ciki, da gudun gaske ya ƙarasa zuwa cikin gidan yana zuwa nan ma ya fara buga musu ƙofar falo, har saida ya buga kusan sau biyar kafin yaji motsin mutum,
Doctor Hasheem ne ya buɗe yana yamutsa fuska yace "lafiya kuwa Junaid da sassafe kazo gidan mutane?.."
Junaid ne yake masa kallon up and down sannan yace "ina matata?.."
Doctor Hasheem cike da mamaki ya maimaita cewa "matarka kuma? aina kenam?.."
Junaid ne ya zuciyo ya cabki ƙwalar rigar baccin Dr Hasheem yana faɗin "nace ina matata Yushert? kayi kuskuren zama mun da mata a cikin gida ɗaya Doctor Hasheem, Yushert she's my wife don haka ka bani waje naje na ɗauko matata.."

Doctor Hasheem jin abunda Junaid yake faɗi ne yasa shi kwashewa da dariya yana nuna shi da yatsa, dariya kuwa yaƙi tsayuwa har wani kama ciki yake, daƙer ya tsagaita dariyar yana faɗin "shin ka haukace ne Junaid? taya Ayushert ta zamo matarka? kodai a daren jiya kayi mafarki ne toh kuwa idan mafarki kake gwara ka farka domin a halin yanzu Ayush tafi ƙarfinka, yanda ta tsaneka a rayuwa ai kana sanar mata cewa ita matarka ce zuciyarta bugawa zatayi..." ya ƙarasa maganar yana dariya yatsarsa akan Junaid yana nuna shi..

A fusace Junaid ya kama yatsar yayi baya da ita sai ƙarasss ya karya ta,
wani irin ihu Dr Hasheem yayi saida ya tayar da su Lailah da Ayush, maigadi kuwa da gudu ya nufo gurin yana zazzaro ido waje,
Doctor Hasheem wani irin mahaukacin naushi yakai wa Junaid
da sauri Junaid ya damƙe hannun da hannunsa ɗaya sannan yayi wurgi dashi gefe,
Miƙewa Doctor Hasheem ya kuma yi yana ihu yayo kan Junaid kafin ya ƙariso Junaid ya girbe masa ƙafa har saida yayi sama tukun ya doku a ƙasi daiden lokacin Lailah ta fito, itama ihu ta soma yi tana faɗin "dan Allah jama'a a kawo agaji za'a kashe mun Yayana wayyo Allah nahhhh.."
Junaid zuwa yayi a gigice ya zabga mata wani irin mari har saida ta kife ƙasi yace "idan na sake jin ihunki saina cire miki haƙwarai.."
Ɗagowa Lailah tayi tana toshe bakinta da hannu bibbiyu tana girgiza masa kai,
Doctor Hasheem ne yazo ta bayan Junaid ya ƙwaɗa masa wani ƙaton katako a gadon bayansa, kifewa yayi kamar zai faɗi ƙasi yayi saurin dafe ƙasa da hannunsa, ɗaga katakon Doctor Hasheem ya kuma yi zai ƙwaɗa masa a zabure Junaid ya juyo ya riƙe katako tareda girbe masa ƙafa ya kifu da bakinsa, shaƙe masa wuya Junaid yayi yana huci tareda faɗin "shin Yushert matarka ce ko matata?.."
ta bayansa yaji Ayush ta amsa da cewar "Ni ɗin matarsa ce ba matarka ba.."
Da sauri Junaid ya miƙe tsaye tareda waiwaya bayansa yana binta da kallo, bakinsa na motsi a hankali yace "Yushert..." kafin ya furta komai tayi saurin ɗaga masa hannu a tsawace tace "babu abunda zaka cemun Junaid, ka kyauta daka zo gidan mutane kayi musu duka, shin meya kawo ka?..."
Junaid ne ya nufi gurinta tayi saurin dakatar dashi tana faɗin "dakata mun malam kada ka sake kazo yanda nake domin bana ƙaunar jin ƙamshin jikinka ma.."
kawar da kanta gefe tayi tana kallon Doctor Hasheem wanda har zuwa yanzu yana ƙwance a ƙasi sai faman birgima yake tsabar ciwon da jikinsa yake masa,
da sauri tayo kan Doctor Hasheem tana faɗin "sannu koh Doctor, kayi haƙuri Allah zai saka maka, indai mutum zalunci ya iya toh wallahi Allah bazai barshi ba, mutum ba imani a zuciyarsa ko kaɗan..."
hannu tasa zata ɗago shi Junaid a fusace ya daka mata uban tsawa yace "kar ki taɓa shi Yushert..."
ko ɗagowa ta kalleshi batayi ba haka tasa hannu tana ƙoƙarin ɗago shi Junaid yasa hannu ya finciko ta tareda zabga mata mari sauran kaɗan ta faɗi ƙasi yayi saurin tarota ya haɗeta da ƙirjinsa,. hannu tasa ta tureshi da ƙarfin gaske tana ja da baya tareda fashewa da kuka,
Dr Hasheem tasowa yayi yana faɗin "meye dalilinka nasa hannu ka mareta? yanzu ni nake riƙe da ita ba kai ba..."
Junaid a fusace yakai hannu zai naushe masa hanci Ayush tayi saurin shige wa tsakaninsu sauran kaɗan ya nausheta, tana kuka tace "wallahi wallahi wallahi Junaid ka sake dukan Dr Hasheem zaka daina gani na har abada domin ba abunda zai hana na kashe kaina kowa ma ya rasa, daman ai rayuwata kake bibiya ko? so kake kaga bayana to kuwa zaka gani..."

Junaid cike da mamaki yake kallon Ayush yace "Yushert me kike faɗa ne haka?.."
Ayush ce ta kalli Doctor Hasheem sannan tace "Doctor.."
ya amsa cikin kulawa a yayin da idonsa yake kanta, tace "shin kana sona?.."
ya amsa mata da cewar "sosai ma gimbiyar mata..". sauƙe numfashi tayi sannan tace "indai kana sona da gaske toh inaso a cikin wannan satin a ɗaura mana Aure.."
Doctor Hasheem da ƙwarin gwiwarsa yace "an gama gimbiyata..."
Junaid kamar ya rausa ihu yana nuna Ayush da disashshiyar murya yace "Yu Yu Yushertttt kefa matar Aure ce, Mommy ta rigada ta ɗaura mana Aure..."
murmushi Ayush tayi sannan tace "My Doctor wannan ya haukace inaga saika koya masa hankali, ka ɗauki katakon nan kaita dukansa har saiya fita hayyacinsa, wannan umarni nane idan har kana sona da gaske..."
tana kaiwa nan tayi juyawarta zata koma cikin ɗaki,
Junaid kallonta yake ga hawaye yanda yake bin saman fuskarsa ya ware hannayensa biyu sannan ya durƙusa ƙasi da gwiwowinsa yana faɗin "Yushert tinda ke kika bada umarni ayi mun duka toh na amince, indai a kanki ne zan iya sadaukar da rayuwata, amma ki sani ina matuƙar ƙaunarki kuma keɗin matata ce jigon rayuwata, uwar ƴaƴana..."
tsayawa tayi tana sauraronsa daga baya kuma ta shige cikin falo da gudu tana kuka...
Duk abubuwan da akeyi Lailah tana zaune a ƙasi tana sauraronsu,

Doctor Hasheem ne ya ɗauki katakon yana juyashi yace "dukan da kayi mun a wancan lokacin a asibiti ciwon yana nan bai warke ba, still yanzu ma ka maimaita, ai kuwa zan ɗau fansaaa..." ya ƙarasa maganar tareda jibga masa katakon nan ata bayansa,
Junaid yana durƙushe a ƙasi yace "tinda Yushert ce ta baka umarni toh cigaba da dukana Doctor Hasheem...". haka Doctor Hasheem ya rinƙa kwaɗa masa katako ata ko ina a sassan jikinsa, har ya fasa masa kayi nan danan jini ya soma zuba, amma Junaid yana durƙushe ko motsawa baiyi ba,
Lailah ganin Yayanta zaiyi wa Junaid illa a kayi yasa ta taso da gudu tana faɗin "Yaya dan Allah ka bari haka zaka kashe shi fa, Yayaaa..."
ta riƙe Yayanta tana ƙoƙarin hanashi dukan Junaid, Doctor Hasheem cikin zafin rai ya hankaɗa Lailah gefe guda ta faɗi ƙasi goshinta ya bugu da floor da ƙarfin gaske, still ɗagowa tayi tana riƙe da goshinta tana faɗin "Yayaaa! Yayaaa!! ka ƙyale shi Yayaaa!!!..." cikin sassanyar murya take maganar ta gagara motsawa ko ina, kanta ne yake wani irin juyawa haka take kallon dishi-dishi tana lumshe ido tareda ƙara buɗe su a hankali, suffar wata mata take gani tana yowa kanta, tsugunawa tsohuwar matar tayi a gaban Lailah tana murmushi,
zaro ido waje Lailah tayi tana kallon matar domin tana yawan zuwa mata a mafarki ta ƙarashi iskancinta da Lailah ta cikin mafarki, domin matar nan ne wacce ta haɗa Lailah da Maimoon lesbian, a yanzu Maimoon ta kuɓuce daga hannunta sakamakon cikin dake jikinta, ita kuma tsohuwar daga lokacin ta cire Maimoon a zuciyar Lailah, hakan yasa yanzu Lailah bata sha'awar Maimoon ko kaɗan sannan haka Maimoon yanzu ta samu lafiya,
Sai kuma tsohuwar ta dawo da sha'awarta kan Lailah ita kaɗai, cikin dare take zuwa gurin Lailah ta gama maɗigonta ta ita, hakan yana matuƙar ɗaurewa Lailah kai saboda ita sai da safe tajita a jiƙe kuma jikinta a mace, tana kallon tsohuwar amma saidai babu halin dakatar da ita..
saboda haka Lailah bata lesbian da kowa saidai idan wannan tsohuwar ce tazo mata...

Lailah tana zaune haka duniyar taketa juya mata a lokacin bata iya ganin kowa sai fuskar wannan tsohuwar, haka tsohuwar take ƙiran sunanta a sanyaye tana faɗin "Lailahhhh! Lailahhhh!! Lailahhhh!!! Ina sonki Lailahhhh, banaso ki shiga tashin hankali Lailahhhh, gashi yau kin saka kanki cikin firgici Lailahhh, zuciyarki bugawa take Lailahhh! Ƙwaƙwalwarki juyawa take Lailahhh!! Lailah kin rasa tunaninki, kin cutar dani, meyasa zaki rasa tunaninki alhalin inajin daɗin kasancewa tare dakeee, a yanzu kin zamo marar tunani, Yayanki yayi sanadiyar juyewar ƙwaƙwalwarki, ni kuma bazan iya kasance dake a haka baáaa, na barki Lailahhh, zan cire miki sha'awar maɗigo acikin ranki, daga yau bazaki ƙara yin maɗigo baa, daman maɗigon nawa ne kuma yanzu na karɓi kayataaa, kin rasa tunaninki kwata-kwata bazaki iya tuna abunda ya faru a baya baa sakamakon buguwar da kikayi, ƙwaƙwalwarki ƴar ƙarama ceee...."
Haka tsohuwar nan ta ƙarasa maganganunta tana ambaton sunan Lailah,
"Lailahhhh! Lailahhhh!! Lailahhhh!!! Lailahhhh!!!! na barki lafiyaaa...." daga nan tsohuwar ta ɓace ɓattttt...
wani irin gigitaccen ihu Lailah tayi ta ƙanƙame kayinta sosai sakamakon juyawar da yake da sauri.
itama faɗuwa tayi ta ƙwanta a ƙasi sumammiya...

Ayush jin ihun Lailah ne yasa ta fito da gudu, ganin yanda Doctor Hasheem yake ta dukan Junaid ba ƙaƙƙautawa ga yanda jini yake ta zuba masa kuma yana durƙushe akan sawayensa,
Da gudu Ayush ta rufo kan Junaid tana zuwa itama ta durƙusa ƙasi tareda rungumarsa tana kuka tana faɗin "dan Allah Doctor Hasheem ka barshi haka kar ka kashe mun shiiii..." ta fashe da matsanancin kuka, ta kuma rungumar Junaid sosai a jikinta, duk ta ɓata kayan jikinta da jinin Junaid...
tana faɗin "hospital Dan Allah, kar ya mutu, ina buƙatarsa a raye Please a kaishi asibitiii.."
Shima Junaid rungumar Ayush yayi yana kuka tareda faɗin "Yushert i love you! I love you my Yushert!! I love you my wife!!!..."
Itama Ayush tana ƙanƙame dashi tana rera kuka mai taɓa zuciya...
saitin kunnensa ta kawo bakinta tana rera masa waƙa...
"you are my Sunshine🌞,
my only sunshine 🥀🌞,
you make me happy when skies are grey you'll never know 💫
dear how much I love you please don't take my sunshine🌞 away🥀🥀🥀🥀....."


haka ta rinƙa raira masa waƙannan a cikin kunnensa tana rungume dashi, shi kuwa shuru yayi yana sauraronta ya ƙanƙameta sosai kamar wanda za'a raba su...


Doctor Hasheem kai tsaye gurin da Lailah take a ƙwance ya nufa yana zuwa ya taɓa wuyanta yaji bata fitar da numfashi, yayi matuƙar tsorita sosai haka yasa hannu ya ɗauketa da sauri yaje ya buɗe murfin motarsa ya ƙwantar da ita a bayan motar shima ya zagaya ya shige, a ɗari ya finciki motar suka bar gidan daman maigadi ya buɗe masa gate ɗin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login