Showing 135001 words to 138000 words out of 186041 words

Chapter 46 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53949

tsabar yawan ƙiran da sarki yake yiwa mommy a waya Hafzat har ta riƙe numbersa daman dake number a saved yake an rubuta KING OF KINGS akan numbersa....

Hafzat kallonsu kawai take tana murmushi daga Junaid ɗin har Abbah, kawar da kai tayi ta maida hankalinta kan Judan wanda tin ɗazu yake ta zuba kamar kurna...
Bayan wasu mintuna suka ji an turo ƙofar falo da sallama a bakinsu suka shugo, mommy da Ayush a zabure sarki yayo kan mommy yana faɗin "Sarauniya ina kika shiga ne haka gaba ɗaya na shiga damuwa, sauran kaɗan na fita nemanki..."
Mommy tayi murmushi tana kallonsa cikin yanayin shagwaɓa tace "kayi haƙuri My king wallahi Ayyuka ne suka riƙeni..."
Yace "toh Sarauniya please ki dena kaiwa dare a waje kinji koh?..."
tace "Insha Allahu my king zan kiyaye..."
cikin farin ciki da annushuwa ya ƙibta mata ido ɗaya, tayi saurin kawar da kanta tana dariya ...."

Dasauri Ayush ta waiwayo tana kallonsu cikin mamaki ido kamar zasu faɗo ƙasi jin yanda mommy take ƙiran Abbanta! cikin rashin fahimta ta maimaita sunan da ƙarfi tace
"My King kuma?...."

a zabure mommy ta ɗago tana kallonta ita sam ta manta cewa akwai mutane a wajen, ganin sarki Raamud yakan sa ta manta da abunda take yi,
shima tsabar hankalinsa yana kan mommy kwata-kwata ya sha'afa da cewar akwai mutane a falon, cikin jin kunya yayi saurin barin falon ya koma part ɗinsa,
itama mommy bata tsaya bawa Ayush amsa ba ta ratsa ta gefenta ta wuce ɗakinta jiki duk a sanyaye...
Gaba ɗaya hankalin Ayush ba ƙaramin tashi yayi ba jin irin maganganun da sukayi irin na masoya, a hankali ta furta "Whatttt can't believe..."

Shi kuwa Junaid tin shugowar Ayush yake ta jifanta da wani irin kallo na takaici, sunyi akan idan taje hospital zuwa azahar ko la'asar zata dawo sai gashi har 10 na dare, kuma ba yau ta saba masa haka ba, sai gadarar idan tayi laifi ta soma kuka tana bada haƙuri da magiya amma hakan bashi zaisa gobe ma ta ƙara yin laifin ba,
yana cikin huci tazo ta wuce shi ko kallon yanda yake batayi ba haka ta wuce da ƙaton tumbin cikinta kamar zatayi ihu haka take ji tana mamakin yanda mommy da Abbah suka shaƙu har haka...

Haka take taka matakalar Benin kamar babu jini a jikinta da haka harta shige bedroom ɗinta,
shima Junaid a fusace ya haura yabi bayanta, sai iya Hafzat kawai aka bari ita da Judan har ta fara sakin jikinta dashi...


★★★★★★★ "Yushert! Yushert!! Yushertttt!!! tsabar iskanci kinaji ina ƙiranki amma ko ki kulani bayan laifin da kika yi?.."
Ayush tana zaune a bakin gado tana jinsa yanata surutansa amma ko kallonsa batayi ba, kawai maganganun su Mommy ne yake mata yawo aka, dogon tunani ta faɗa ga kuma hawaye shaɓe-shaɓe akan fuskarta,
ganin haka yasa Junaid zama a kusa da ita yana faɗin "ke kuma fah? me akayi miki kike kuka?..."
murya ciki-ciki tace "Babu komai"
Yace "a'a akwai banason ɓoye-ɓoye a lamarina ki fito ki faɗa mun gaskiyar abunda yake faruwa..."
cikin nuna rashin son hayaniya da damuwa kamar zata rausa ihu tace "haba Yaya Junaid mekake so nace maka, nace babu komai ba dole ne saika ji ba, please ka ƙyaleni da abunda ke damuna banson hayaniya da damuwa..."
cike da mamaki yake binta da wani irin bahagon kallo yace "whattt! Yushert Ni ne hayaniya da damuwa? okay thanks..."
cikin takaici ya miƙe tsaye tareda cire jallabiyan jikinsa ya faɗa cikin toilet yayi wanka shaf-shaf sannan ya fito yana ƙamshin sabulu mai daɗin gaske, ya shirya cikin ƙananun kaya three quarter da singlet sannan yazo gaban Ayush kamar bazaiyi magana ba cikin ƙarfin hali yace "tashi mun zan ƙwanta..."
tashi tayi tana haɗe rai ta koma kan wata doguwar sofa ta zauna tareda kifa kanta akan gwiwowinta tana rera kuka ciki²
Shi kuwa hannu ya miƙa ya kashe hasken ɗakin sannan ya kunna green lamp sai ɗakin ya bada green light mai kyan gaske, ya kwanta tareda jawa kansa mayafi ya lumshe idonsa kamar meyin bacci sai dai yana jinjina maganganun Ayush data yi masa cikin rashin ɗa'a da biyayya sannan yana tunanin shin meya sameta ta shiga damuwa har haka,
yana cikin wannan tunanin da haka har bacci ɓarawo yayi awun gaba dashi....


Ayush kasa rintsawa tayi! zuciyarta ba ƙaramin jagwalgwalewa tayi ba, tsananin kishi ne acikin zuciyarta bataso ace mommy da Abbah sun ƙulla soyayya ba domin tana taya mahaifiyarta kishi duk da bata raye, ta shiga kewar mahaifiyarta sosai,
kasa haƙuri tayi ta tashi da sauri ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice lokacin misalin ƙarfe 12 da rabi ne na dare, kai tsaye falo ta sauƙo cikin rashin sa'a kuwa taga mommy ta fito daga kitchen da flask a hannunta ta nufi part ɗin Abbah,
wani irin ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci cikin kogon zuciyarta, daƙer ta iya haɗiyar yawu jiki a sanyaye haka ta ƙarasa saukowa falo kai tsaye ɗakin Hafzat ta nufa, tana zuwa ta fara knocking a hankali tana ambatar sunanta,
a lokacin cikin sa'a kuwa Hafzat tana kan sallaya ta gama idar da sallar dare tana cikin jan carbi taji kamar Muryar Ayush, cikin mamaki ta taso a hankali tazo dab da bakin ƙofar tace "waye ne?.." tayi maganar domin ta tabbatar ko ita ɗince, cikin kakkarwar murya Ayush tace "nice kiyi sauri ki buɗe mun..."
Jin haka yasa Hafzat tayi saurin buɗe mata, Ayush tana shugowa tayi saurin mayar da ƙofar ta rufe saboda bata son mommy tazo ta ganta...

Cike da mamaki Hafzat tace "lafiya kuwa Aunty Ayusher? ya naga kamar kuka kike meya faru?.."
dasauri Ayush takai yatsanta ɗaya saitin bakinta tana faɗin "shuuuuuu kinayi a hankali kar a jiyo ki kinga dare ne..."
ta ƙarasa maganar tareda riƙo hannun Hafzat ta zaunar da ita a bakin gadonta itama ta zauna tana cewa "magana nake so nayi dake.."
Hafzat tace. "ina jinki Aunty..."
tace "akan mommy nakeso muyi magana naga kinfi kusanci da ita shin meye alaƙar dake tsakanin mommy da Abbah?..."
Hafzat bata ji komai aranta ba tace "soyayya mana.."
Ayush ta kuma cewa "shin meye hujjarki na cewa haka?.."
Anan Hafzat ta ƙwashe komai akan alaƙar dake tsakanin mommy da Abbah ta gayawa Ayush, har zuwansu hira can guess place dake cikin gidan ba tareda kowa ya saniba,
daga ƙarshe kuma ta ƙarasa maganar ta da cewa "idan kinason ƙarin bayani kije ki binciki wayar mommy ki shiga WhatsApp ɗinta ko wajen message zakiga an rubuta KING OF KINGS shine number Abba datayi saving dashi zakiga duk wani chatting da sukayi na soyayya abun saiya baki shauƙi...."

Ayush kamar wacce aka ɗauke mata wuta haka ƙwaƙwalwarta ya fara juyawa duk ta gama haɗa zufa, zuciyarta ne yake wani irin harbawa da ƙarfin gaske Fattt! Fattt!! Fattt!!! muryarta har harɗewa yake tace "kinsan bansan password ɗin wayarta ba saboda ban taɓa ɗauka ba ki gaya mun yanzu..."
Hafzat tace. "amma Aunty Ayusher meyake faruwa ne haka naga gaba ɗaya kin fita hayyacinki?..."
tace "kedai faɗamun password ɗinta kawai..."
Hafzat ta gaya mata cike da mamaki ganin yanda Ayush ta canza lokaci guda...

Dasauri Ayush ta tashi ta fice a ɗakin kamar taza fura sama, ita kuwa Hafzat girgiza kai kawai tayi tareda cewa. "Allah yasa muga Alkhairi toh..." ta tashi taje ta kulle ɗakinta sannan ta dawo ta rage kayan jikinta ta miƙe akan katafaren gadonta nan danan bacci ya ƙwasheta....

Ita kuwa Ayush tana fita daga ɗakin Hafzat kai tsaye ɗakin Mommy ta shige cikin sanɗa har zuwa yanzu mommy bata dawo ba cikin sa'a kuwa ta samu wayarta asaman gado dasauri taje ta ɗauki wayar ta buɗe cikinta daga nan ta shiga waran duba saƙonni, kamar yanda Hafzat ta gaya mata, saƙonnin ta fara karantawa tana kuka tsantsar soyayya kawai suke sha, kuma tana mamakin yanda Abbanta ya iya kalaman soyayya har haka, saida ta kammala karantawa tass har sun gama yanke shawarin yin Aure,
Girgiza kai Ayush ta soma yi tareda faɗin "impossible wallahi babu maganar Aure, bazan taɓa barin faruwar haka ba, saboda Ummana bata raye shine za'a ci amanarta? toh bazaiyu ba..."
tana maganar zuci tareda ƙoƙarin buɗe WhatsApp ɗinta, jin motsin mutum yana ƙoƙarin shugowa ɗakin ne yasa tayi saurin wurgi da wayar akan gado gudu² sauri² haka ta shige cikin toilet,
Mommy ce ta shugo ɗakin cikin farin ciki da annushuwa tana daga tsaye ta zamar da hijabin jikinta ta ajiye shi sannan ta zauna a bakin gado tana tunanin gobe zata sanar da Artaff maganar Aurenta da Sarki Raamud, har sun gama tsaida maganar sadakinta sannan suna tunanin kota ɓangaren yaransu ma basuda matsala, domin zasuyi farin ciki da wannan haɗin shiyasa sukeso suyi bazata,
ita kaɗai sai murmushi taketa zabgawa tana murza zoben zinaren yatsanta, juyawa tayi tareda ɗaukar wayanta tana son turawa Artaff saƙon domin bazata iya barin gari ya waye ba tsabar ɗauki, kuma dake hausawa sunce a bari ya huce shi ke zama rabon wani! hakan yasa bazata haƙura zuwa gobe ba,
tana buɗe wayar taga tana kan WhatsApp cike da mamaki mommy take kallon wayar,
murya a bayyanai tace "WhatsApp kuma? Ni yau kwata² ban hau WhatsApp ba amma taya zan ganni akan WhatsApp alhalin ban shiga ba..."
Juyar da wayar ta somayi cike da mamaki gira a haɗe, shiga cikin wayar tayi taga har waran saƙonninta aka duba dake wayar duk yanda mutum ya shiga a wayar za'a iya gani daga baya, itama Hafzat dake tasan kan wayar mommy da zaran tayi shige-shigenta take goge duk yanda ta shiga,
ita kuma Ayush ganin babu lokaci ne yasa bata tsaya yin waɗannan goge gogen ba kawai ta ajiye wayar bayan tahau kan WhatsApp...

Ayush tana cikin toilet gaba ɗaya harta gaji da tsayuwa ga cikinta yanda yayi mata nauyi sosai bata iya juran tsayuwa,
Mommy jikinta ne ya bata cewa akwai wanda ya shugo room ɗinta, ajiye wayar tayi akan drower sannan ta miƙe tsaye tareda nufan hanyar toilet har takai hannunta zata buɗe taji wayarta tana ringing juyawa tayi cikin zumuɗi ta nufi wajen wayar dasauri domin tasan King ɗinta ne, ɗaukar ƙiran tayi tareda karawa a kunne tareda faɗin. "Assalamu alaikum My King..."
amsa mata yayi tareda sanar mata cewar takai masa maganin ciwon kai da kuma zazzaɓi domin baya jin daɗin jikinsa jurewa kawai yake bayan mommy babu wanda yasan bashida lafiya..
itama amsa masa tayi cikin rashin jin daɗin rashin lafiyarsa tace "gani nan zuwa my king .."
jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin kai tsaye medicine room ta nufa zataje ta haɗo masa maganunnuwa...

Ayush tana toilet jin wayarda sukayi yasa ta fashewa da kuka ciki² kar a jiyota, jin alamun mommy ta fita yasa itama ta fito tana maida numfashi, haka kawai taji bata ƙaunar soyayyar mommy da Abbah tafison kowa ya Auri nasa a waje can ba lallai sai sun haɗa zumunci ba....
tana cikin wannan tunanin tayi firgit ganin lokaci yana ƙure mata dasauri taje ta buɗe ƙofa tayi ficewarta cikin sanɗa tayi hanyar upstairs dazai sadata da ɗakinsu,
kwatsam taji an ƙira sunanta tsayawa tayi da tafiyar domin tasan mommy ce kuma bata son kallonta saboda idan ta tuna irin soyayyar data ga suna sha har kunya take ji da kuma haushi...

Mommy tace "keɗin daga ina kike?..."
shuru tayi ba amsa har saida mommy ta sake maimaita mata amma still shuru tayi mata,
Mommy har zuwa dab da ita tayi tace "Ayushert bai kamata kimun shuru ba, shin ina kika je a wannan daren...?
Juyowa Ayush tayi tana kallon mommy fuska a haɗe tace "toh mommy banda abunki ai baza'a rasa wajen zuwa ba..."
Mommy tace "A wannan daren?.." cikin ɓacin rai tace "to kema mommy me kikeyi a wannan daren bakiyi bacci ba?..."
cike da mamaki mommy take kallon Ayush Lokaci guda kuwa jikinta yayi sanyi domin taga Ayush daga cikin ɗakinta ta fito kuma duk yanda akayi ita ta ɗauki wayar har ta karanta saƙonnin ta da aka tutturo mata na soyayya, jin irin amsuwar da take mata ne yasa ta cewa "Ayush kinada hankali kuwa? shin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login