Showing 30001 words to 33000 words out of 186041 words
Da sallama Laylah ta shiga, Ammy ta amsa mata cikin nuna damuwa,
Samun guri Laylah tayi ta zauna suka gaisa da Ammy ta juyo tana kallon Maimoon tace "ashe Besty nah ta dawo.."
Ammy tace "wallahi kuwa Laylah wai ashe gidan kawunta taje ta toh sai matarsa ta riƙeta! sunyi ta ƙiran wayata basu samu ba, kuma yanzu basu da number Daddyn ta, dake ba'a Nigeria suke ba suna ƙasar Iran..."
Laylah tace "too har ƙasar Iran taje ta kuma bata sanar ba?.."
Ammy tace "cewa tayi baƙin cikin yayanki Hasheem ne yasa ta yanke hukuncin barin Nigeria, yanzun nan Daddynta ya gama yimata faɗa ai, ta tsoritar damu sosai wallahi..."
Laylah ta jinjina kai suna kallon kallo itada Maimoon tace "gaskiya Besty baki kyauta mana ba, kin hana mu bacci kullum acikin tunaninki muke..."
Wani irin harara Maimoon ta wurga mata ta juyar da kansa gefe guda..
Ammy tace "Maimoon baki ga Aminiyarki tazo bane?..."
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 17 ➡️ 18
Mommy ta shugo ɗakin Junaid da gudu kamar wacce zata kifu, Angel na biye da ita a baya haka suka shugo har secret room a yanda Angel ta barsu ahaka ta dawo ta tarar dasu,
Mommy jawo Ayush tayi daga saman Junaid zata faɗi ƙasi sukayi saurin tareta su biyu suka haɗu suka ɗauki Ayush sukayi ɗakinta da ita suna shiga suka kwantar da ita akan gadonta
tace "kInsan wani abu Angel ke zaki zauna da Ayusher ki yayyafa mata ruwa, ni kuma zanje naji da Junaid,
Angel tace "toh shikenam Mom..."
dasauri ta nufi toilet zata ɗebo ruwa,
ita kuwa mommy har ta fice,
da sauri ta shiga ɗakin Junaid ta samoshi a ɗayan room ɗin da bottle a hannunta na ruwan sanyi, tana zuwa ta fara watsa masa ruwan akan face ɗinsa, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa ba tareda ya firgita ba! dishi-dishi yake kallon ceilling, ya ƙara lumshe idonsa tareda sauƙe numfashi,
Mommy ce ta ɗaga kansa tukun ta zauna tareda kwantar da kansa kan cinyarta tana faɗin "Babana kana lafiya?..."
buɗe eyes ɗinsa yayi yana motsa bakinsa a hankali ya furta "Mom my heart zai fashe.."
ya riƙo hannun mommy ya ajiye asaitin zuciyarsa..
Mommy tace "My son ka kwantar da hankalinka ba abunda zai samu zuciyarka, ka daina saka abu a ranka kaji ko Babana..."
ya ɗago ƙwayar idonsa yana kallon Mommy yace "mom kin daina fushi dani?.."
Momy tace "daman ba fushi nake dakai ba, kaine idan ranka ya ɓaci baka iya control kanka, yanzu meye amfanin dukan Ayush? banaso ka mayar mun da yarinya jaka, yanzu ma naga naji rauni akan goshinta kuma nasan kaine! shiyasa take tsoron Aurenka ai...".
ta sauƙe numfashi tareda kallon gefe tana shafar sumar kayinsa,
yana kallon ceilling yace "tayi mun laifi babba Mom, meyasa zata kwanta da wani namiji daban wanda bani ba? bazan iya juran haka ba..."
Shuru Mommy tayi bata ce masa komai ba...
Ayush ce take zaune asaman gadonta sai faman rera kuka take bayan Angel ta farfaɗo da ita,
hakuri Angel take bata tana rarrashinta tareda cewa "Ayush kema bakya jin magana wallahi, bayan kinsan a halin da ake ciki yanzu Junaid ba'a cikin nutsuwarsa yake ba, mai zai kaiki ɗakinsa har ma ki shiga yanda ba'a lamunce miki ba haba dan Allah, gashi yanzu kin jawo ya fasa miki goshi bayan baki gama warkewa da dukan da yayi miki ba..."
Share hawayenta Ayush tayi sannan tace "kenam ni an mayarni dabba kullum acikin dukana ake, nifa ba yarinya bace! na mallaki hankalin kaina, saboda Yaya Junaid gaba ɗaya zaman gidan ya isheni, ni tafiya zanyi bazan iya rayuwa acikin wannan ƙuncin ba kullum ina cikin zubda hawaye, ina zaune a cikin gidan masu kuɗi amma ba kwanciyar hankali a cikin gidan kamar wacce nake cikin prison..." ta ƙarisa maganar tana kuka.
Angel tace. "a'ah ki kwantar da hankalinki gobe ma Junaid zai bar Nigeria kuma kafin ya dawo komai zai daidaita, idan kikace zaki tafi Mommy bazataji daɗi ba..."
Ayush jin gobe zasu tafi yaƙar iyayenta saita sake fashewa da wani sabon kukan,
daƙer Angel take rarrashinta har Ayush ta ɗan kwanta bacci...
daga nan Angel ta miƙe ta fice a ɗakin, da sauri ta sauƙa downstairs ta fice daga falon ma,
tana zuwa gurin parking motocin gidan ta zaɓi ɗaya ta shiga tareda tayar da motar ta miƙi hanyar get,
maigadi ne yayi saurin buɗe mata get ganin yanda ta tafo da gudun gaske, tana fita daga gidan ta miƙi hanyar gidansu Laylah..
Shi kuwa Junaid yana tsaye a bakin window ɗakinsa yana ganin lokacin da Angel ta fita masa da ƙaramin motarsa jeep,
Mommy ta daɗe da barin room ɗinsa domin yanzu haka tana kitchen...
Junaid komawa ɗayan room ɗinsa yayi yanason duba cameran tsaro na gidan shima,
yana zaune ya kafa eyes ɗinsa akan computer, a cikin camera video daya gani ya fuskanci abubuwa da dama,
jinjina kai ya shiga yi yana murmushi, tashi yayi ya koma bedroom ya ɗauko phone ɗinsa yazo ya jona a jikin computer zai kamo location na contact ɗin da aka turo da video ta WhatsApp bayan yayi tracking number,
computer ta nuna number a nan garin Abuja take, yana bibiyar number har ta kaishi yanda layin take a ajiye wanda tazararsu da ɗan rata kaɗan,.
daya bi location kuma sai computer ta nuna masa gidan Doctor Hasheem,
ƙara jinjina kansa yayi yana zargin mutum biyu acikin gidan nan!
Doctor Hasheem ko kuma Lailah, duk da baiga Doctor Hasheem ya shiga ɗakin Ayush ba amma yana konkonto akansa,
kodai Doctor Hasheem ne yasa Lailah ta haɗa Ayush da gardin nan ko kuma Lailah ce tayi hakan saboda ta ɓata sunan Yushert,
Amma kuma yana tunanin shin wacece matar nan mai liƙab....
yana cikin wannan tunanin wani abu ya faɗo masa arai dasauri ya shiga wani ɓoyayyen camera shutting na cikin ɗakin Ayush domin acikin ɗakinta ma yasa camera amma sai dai baya dubawa sakamakon ita kaɗai ce a ɗakin,
kafin ya shiga camerar ɗakin Ayush saida yasa security wanda ba wanda zai iya ganewa sai iya shi kaɗai, yana duba video abunda ya faru a cikin ɗakin bayan Ayush ta shiga da gudu tana kuka saiga wannan matar mai liƙab yana son ganin fuskar matar saidai kash camerar bayanta ya ɗauka banda fuskarta,
ga kuma lokacin da Ayush ta tafo zata rungumeta Umantata ta hankaɗata tareda marinta,
sai abun ya ƙara ɗaurewa Junaid ƙwaƙwalwa,
dasauri ya ɗauki abun jin magana ya kara a kunnuwansa yana jin duk tattaunawar da sukeyi, yaji Ayush tana ƙiran Uma kuma duk maganar da sukayi akan Junaid ne yaji Uma tana cewa "idan baki Auri Junaid ba, Babu ni ba ke kuma bazaki sake ganina ba har abada.."
Junaid ƙwaƙwalwarsa ce ta fara juyawa yana faɗin "me hakan yake nufi? shin wacece wannan matar? daman Yushert tanada iyayenta a raye? kenam munafurtar mu take yi? shin meyasa ta ɓoye mana abubuwa da dama?..."
abunda yake masa yawo kenam a ƙwaƙwalwarsa,.
gani yayi matar ta shige toilet da gudu a yayinda Angel ta shugo,
bayan ta fita kuma matar ta fito, a lokacin ne yake da damar kallon fuskar matar saboda ta fuskanci camera saidai kash tin a cikin toilet tasau liƙab ɗinta ta fice a ɗakin,
amma saidai abunda ya ƙara ɗaure masa kai a camera waje baiga fitarta ba,
yana zaune can saiga Lailah ta shugo ɗakin, duk yana kallonsu yana kuma sauraron abunda suke faɗa, gani yayi Lailah ta curo magani ta bawa Ayush daga nan kuma hankalinta ya ɓace mata, daga baya kuma saiga mutumin nan ya shugo, yana kallon yanda Lailah take musu video,
Ran Junaid ne yayi matuƙar ɓaci sosai, ya dafe goshinsa tareda tusa tafin hannunsa cikin sumar kansa ido a rufe, shi kaɗai yasa irin raɗaɗin da yake ji aransa,
Kawar da video waransu Lailah yayi yana son bibiyar matar data fita daga ɗakin Ayush kafin su Lailah su shugo domin matar tafi tsaya masa arai,
camerar wajen ɗakin Ayush ya buɗe gani yayi matar ta tsaya a bakin ƙofar Ayush bayan wasu ɗan seconni yaga ta ɓace ɓatt
A razane Junaid ya miƙe tsaye yana zaro ido waje yana ja da baya...
********
Angel ce ta shige cikin gidan su Lailah bayan maigadin gidan ya buɗe mata, saida yaje ya tambayo aka bashi umarnin ya buɗe mata,
dasauri Angel ta fito daga cikin motar ta nufi hanyar mashigar shiga falon,
Shiga tayi ta samesu sunata hira a falo ga plasman ana showing India film,
Iya su kaɗai ne a falon daga Doctor Hasheem sai kuma Lailah,
Lailah tana bashi labarin abunda ya faru a gidansu Maimoon data je suna dariya,
Ganin Angel yasa duk suka miƙe tsaye suna kallonta
saida Angel taje gabansu kafin tayi musu sallama tana murmushi!
Lailah har da kuka ta tana faɗin "innalillahi Yayana sune suka mun duka a hospital Koh, yanzun ma sunzo su ƙara sumar dani wayyo Allah nasara.".
tana ɓoye a bayan Doctor Hasheem.
Dariya Angel tayi sannan tace "awww daman kinada tsoro Lailah? gaskiya ban taɓa tunanin kinada tsoro har haka ba, bani na dakeki ba kuma banzo gidanku don na dake ki ba amma kuma idan kika nuna mun rashin gaskiya akan abubuwan da zan tambayeki toh kuwa nima zan dakeki, duka ma irin wanda bakiyi zato ba...."
ta ƙarisa maganar tana zaro mata ido.
Doctor Hasheem ne yace "lafiya kuwa Malama ya za'ayi kinzo gidansu kuma kice zaki dake ta, ina ruwanta daku meyasa kuke son shiga rayuwarta ne, marainiyar Allah kodan kuna ganin ku sojoji ne shine kuke iya zalincin ku..."
Angel ce ta ɗaga masa hannu tareda cewa "dakata Mallam Hasheem ba gurinka nazoni ba amma kuma za'ayi komai a gabanka! ku zauna domin ba wani ɓata lokaci zanyi ba..."
Gaba ɗayansu zama sukayi,
Angel tace "Lailah nazo gurinki ne saboda muna zargin wani abu daya faru, ki sani duk tambayoyin da zan miki karki sako mun ƙarya a ciki domin faɗar gaskiyarki shi zai sa ki kuɓuta daga zargin da ake miki..."
Gaban Doctor Hasheem ne ya buga da ƙarfin gaske a zabure yace "Please meya faru?.."
Angel ɗaga masa hannu tayi ta dakatar dashi tareda cewa "koma meye ne ai zaka ji.."
Doctor Hasheem shi tunaninsa kar maganar akan Maimoon ce,
Ita kuma Lailah tintinin tasha ruwan jikinta domin ta saddaƙar akan video Ayush ne,
zuciyar ta kuwa sai bugawa yake da ƙarfi-ƙarfi...
gyara zama Angel tayi sannan tace "Lailah a ranar shagalin Ogah Junaid da misalin ƙarfe 5 meya kaiki ɗakin Ayush?.."
Duk da fankan da yake kaɗawa a ɗakin amma haka Lailah take ta sharar gumi tana muzurai bakinta na motsi mutsil-mutsil,
Angel ce ta katseta da cewa "magana nake miki Lailah, ko ba amsa?.."
Dasauri Lailah ta ɗago tana ƙiƙƙina tace "wallahi tallahi ba abunda ya kaini ɗakin Ayusher, kawai dai mun samu matsala ne shine aranar naje neman yafiyarta kuma ta yafe mun..."
Angel tace "toh meye kike ta faman wallewa shin kinsan abunda ke faruwa ne? abunda na tambaye ki kenam fah amma dubi yanda kika rikice mun,
kina ɗakin Ayush akwai wanda ya shiga ɗakin shin wayene?.."
Lailah tana zazzarowa ido waje tace "ehhh to ina zaune da Ayush akwai wanda ya shugo shine nake tambayarta ko wayene wannan tace mun baƙonta ne, daga nan na tashi na barsu a ɗakin..."
Jinjina kai Angel tayi sannan tace "Lailah bana son ƙarya! nagaya miki idan kika mun ƙarya babu ke babu fita daga cikin wannan case har a gano gaskiyar, idan kuma Junaid yasan kina cikin wannan Case toh kiyi kuka da kanki, zaki raina mun wayo naga kusan awanku guda a cikin ɗakin Ayush, mutumin yana ciki kuma kusan a jere kuka fito daga ɗakin shine farkon fitowa before ke.."
Lailah fashewa tayi da kuka tana faɗin "wallahi tallahi fitowa nayi na shiga ɗakin Ogah Junaid nayi bacci..."
Angel hannu tasa a aljihun wandonta mai kakin soja ta ciro bindiga tace "ƙarya kike Lailah ɗakin Ogah Junaid da hannuna na kulle da key kuma lokacin key ɗin ɗakinsa na hannuna, shin zaki gaya mun gaskiya ko saina ragargaza miki ƙafa ki zama gurguwa..."
A ruɗe Lailah take faɗin "a'ah dan Allah ki rufamun asiri karki harbeni ƴar uwa zan gaya miki,
Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! ki temakeni fitowa nayi na tsaya a bakin ƙofa ina jiran su, amma ni bana cikin ɗakin.."
Angel tace "kenam iya su biyu kika bari a ɗakin?.."
A gigice Lailah tace "eh eh ehh wallahi..."
Jinjina kai Angel tayi tana murmushi tace "toh amma waye ya musu video?.."
Lailah tace "nima ban saniba.."
Kunna kunamar bindigarta Angel tayi ta saita ƙafar Lailah tace "ina dai baki saniba?.."
Ihu Lailah ta fara kurmawa a gidan tana magiya,
Shima Doctor Hasheem ɗin tasowa yayi da sauri yana roƙon Angel yace "kiyi haƙuri mana Angel kibi komai a hankali kar tsautsayi yasa ki harbeta.."
Angel juyowa tayi tana kallon Doctor Hasheem cike da takaici tace "whattt! tsautsayi fah kace Hasheem, ni ai bansan tsautsayi ba, abunda yake raina kawai nake aikatawa, domin mu harbi ba komai bane a gurin mu! bazan harbeta a wajen da zata mutu