Showing 81001 words to 84000 words out of 186041 words

Chapter 28 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53942

Junaid ba ƙaramin jijjiga yayi ba a wannan labarin gaba ɗaya ya shiga taitayinsa, fuskar nan ta koɗe har wani yellow+² yayi tsabar firgicin da ya shiga da tashin hankali, idonsa kamar wanda yayi shaye-shaye daƙer yake lumshe su ga fatar lips ɗinsa duk ya bushe, kana ganin Junaid kasan ba ƙaramin jiki yake sha ba, duk ya fice a kamannunsa ya rarrame lokaci guda,
wani irin ƙaunar Ayush ne yaji ta shige masa zuciya domin ba ko wace mace bace zata ita sadaukar da rayuwarta akan wani ba, kuma ta dajirce sosai akan Junaid, ta ɗauki duk wani wahalarsa, ta kuma jure duk wulaƙancin da yayi mata...
Jinjina kai yayi a hankali ya furta "tabbas soyayyar gaskiya bazata taɓa gushewa ba, bazan taɓa rabuwa da Yushert ba domin bazan samu mace kamarta ba, Mommy tamkar mahaifiya take a gurin Yushert don haka nabarwa komai a hannun Allah, shine mai yanda yaso nidai burina Yushert ta dawo gareni, inaso na biyata da nawa dubun alkhairin data aikata mun a baya, zan sa a raina cewar mu marayu ne daga ni har ita wanda ya rage mana mutum ɗaya ne shine mahaifinta kuma mahaifina wato sarki Raamud..."
Junaid ya ƙarasa maganganunsa tareda miƙewa tsaye...
Malam Lawan yace "toh daka miƙe tsaye ina zakaje?.."
Junaid kallon Malam Lawan yayi sannan yace "zan koma gurin Yushert, zanje na tafo da ita domin ita ɗin rayuwata ce kuma jinin jikina..."
Malam Lawan yace "idan kaje Ayshert bazata taɓa sauraronka ba a halin yanzu, zata walaƙantaka ne.."
Junaid yace "zan iya juran duk wani wulaƙancin ta Malam, nidai burina ta kasance dani..."
Malam Lawan ne ya riƙo hannunsa yace "shikenam! Shikenam!! yanzu dai zauna inaso na baka wani albishir ɗin labari wanda yau zakayi ƙwanan farin ciki"
Junaid jin wannan batun yasa ya zauna cikin gaggawa yana facing ɗin Malam, gaba ɗaya yana ɗaukin malam ya sanar masa, gani yayi malam yasa hannu ya ɗauki wani ɗan ƙaramin akwati wanda yayi baƙi ƙirin daka ganshi kasan acikin wuta aka ciro shi,
Junaid yana kallon akwatin yace "wannan kamar boxes ɗin mommy.."
Malam Lawan yana jinjina kai yace "shin kasan meye a cikinsa?.."
Junaid ya jijjiga kai alamar a'ah, malam Lawan yana murmushi yace "wannan ɗan ƙaramin akwatin a cikin shirgin mommy na ganshi, komai ya ƙone amma banda shi sakamakon jikinsa na ƙarfe ne..."
yasa hannu ya buɗe cikinsa ya ɗauki card guda ɗaya ya miƙawa Junaid, da sauri ya karɓa yana dubawa, ƙirjin Junaid ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin a jikin katin an manna photonsa dana Ayush kuma ga sunansu a jiki..
Junaid miƙewa yayi da sauri yana faɗin "Malam wannan kamar katin Aure koh?.."
Malam yana murmushi yace "ba alamar tambaya Junaid! hakane ka duba date ɗin da aka ɗaura muku Aure kai da Ayushert, a washe garin zaka tafi yaƙi aka ɗaura Auren, kuma a ranar da Angela ta musulunta a ranar aka ɗaura Auren ba tareda kun saniba, ban san dalilin da yasa mahaifiyarka ta ɓoye muku ba, amma mune shaidun Aurenku domin nine maɗaurin Auren Ayshert kai kuma Barrister Aminu ne abokin mahaifinka..."

Junaid kamar zai sume a gurin tsabar farin ciki haka ya ɗora katin a saitin zuciyarsa yana fitar da numfashi a hankali ga wani irin murmushi a saman fuskarsa har saida dimple ɗinsa suka lotse yace "Allah na gode maka, Allah Ubangiji ya sakawa mahaifiyata da gidan Aljanna, ina Alfahari dake mahaifiyata, taga zuciyata ina ƙaunar Yushert sosai..."
Malam Lawan yace "Ma sha Allah, yanzu dai taho muje muyi sallah saika ci abinci cikin nutsuwa tinda farin ciki ya wanzu maka..."
Junaid yace "Malam idan nayi sallah zanje na ɗauko matata.."
Malam yace "a'ah ka bari sai gobe da safe sai kaje ka fahimtar da ita, idan ta yadda kun tafo shikenam, idan kuma bata yadda ba saika barta dani ni zanje na ɗauko maka ita cikin fahimtar juna..."
Junaid jinjina kai yayi da smile a kan fuskarsa yace "shikenam malam Allah ya kaimu goben.."
Amma ba haka yaso ba, lokaci guda kuma sai yake jin wani irin ƙololuwar baƙin ciki sakamakon zamanta a gidan Doctor Hasheem kuma tana mazannin matar Aure, sai kuma ya fara jin kishi a ransa...


******

Lailah tana tare da Sumaiya ƴar jarida duk ta gama basu wasu bayanai da hujjojin da zasu bayyana Ayush a matsayin mai laifi, Sumaiya ce ta kalli Lailah tace "gaskiya kinyi ƙoƙari mutumiyata, kin bamu duk wasu bayanai da ake buƙata insha Allahu zuwa nan da kwana uku zaki fara ganin photunan Ayushert da video maganganun ta a gidan television, toh amma saidai Yayanki Hasheem shima zai fito a cikin jaridar mu saboda shine ya ɓoyeta kuma zamuje har ƙofar gidanku tareda tarin ƴan jaridu da masu ɗaukan rahotanni, kuma nasan tabbas dole ƴan sanda da sojoji zasu je domin kamota because mahaifiyar Captain Junaid ta kashe..."
Lailah murmushi tayi tace "saina jiyo ku ƴar uwa..." tana kaiwa nan tayi tafiyarta...

Lailah bata koma gida ba sai waran ƙarfe 10 na dare saboda ta wuce gidansu Maimoon domin jin wasu matsalolinta, ta shiga damuwa sosai ganin halin da Maimoon take ciki ga kuma cikinta ya fito sosai, tana kuma tausayawa Yayanta idan maganar nan ta fito...
shugowa cikin falo tayi ta tarar da Ayush zaune a one seater tana kallon tv sai kuma Doctor Hasheem a 3 seater, zuwa tayi zata wuce ɗakinta da sauri Doctor Hasheem ya katse mata hanzari tareda faɗin "baki iya sallama ba koh?.."
tsayawa Lailah tayi ba tareda ta juyo ba tace "nayi mana sai dai baku jini ba.." tana wani kumbura domin ta tsani ta tashi taga Ayush a cikin gidan nan, gaba ɗaya bata da wargi..

Doctor Hasheem ya kuma cewa "ina kika je?.."
Lailah tana turo baki tace "gidansu Maimoon" ƙirjin Doctor Hasheem ne ya buga an fame masa ciwon dake zuciyarsa, cije leɓɓen bakinsa yayi yana jinjina kai tareda kallon Ayush wacce idonta akan tv, yace "Okay kije kitchen ki haɗowa Ayushert tea mai kauri ki kawo mata tana jin yunwa..."
Juyowa Lailah tayi tana faɗin "Yaya kafin nabar gidan nan fah nayi girki, ai bai kamata ace abincin har ya ƙare ba saboda nasan ba baƙi akayi ba.."
Doctor Hasheem yace "ehh ta cinye yanzu kuma tana buƙatar ruwan tea kafin ta kwanta idan kuma bazaki yi ba, Ni zan shiga kitchen na haɗo mata.."
Lailah kamar zata rausa ihu tana jumping da ƙafafuwanta tana gunaguni tace "wannan matar akwai shegen ci kamar mayya, tinda tazo gidan nan girki sau biyu zuwa uku nakeyi tsabar cinta yayi yawa, munafuka kawai..."
haka ta nufi kitchen tana wannan maganganun ba tareda Doctor Hasheem ya jiyota ba, amma saidai Ayush duk taji abunda ta ce,
Doctor Hasheem jin gunagunin da takeyi ne yasa shi faɗin "Lailah kina magana ne?.."
tace "a'ahh..."
Bayan minti talatin saiga Lailah ta fito hannunta ɗauke da cup na ruwan shayi da haɗin madara, tana zuwa gaban Ayush ta miƙa mata,
a cikin zuciyarta kuwa cewa tayi "ƴar buro uba na watsa miki dai akan fuska, acici mala'ikun tauna.."

Ayush tana murmushi tasa hannu ta karɓa tareda cewa "yauwa ƴar ƙanwata godiya nake.."
Lailah wani irin harara ta watsa mata ba tareda ta ganta ba sannan tayi wucewar ta ɗakinta tana kumbura kamar filfila,..

******

Around 11:00pm Junaid yana ƙwance a saman gadonsa yana kallon ceilling sai murmushin yake shi kaɗai ga kuma katin Auren su a saman ƙirjinsa, fuskan Ayush ce take masa gizo, sai kuma yake tunowa da abunda ya faru a tsakanin su kafin ya tafi yaƙi,
lokaci guda kuma ya tuno da Mommynsa saiga wani irin zazzafan hawaye yana faman gangaro masa, yana cikin wannan tunani-tunanin har bacci yayi awon gaba da shi...


_________________Lailah ce ta tashi cikin dare ta fito falo sanye da sleeping dress riga da wando ta nufi frig ta ɗauki lemon juice kai tsaye ɗakin Doctor Hasheem ta nufa tana zuwa ta fara knocking a hankali har sai da tayi sau uku tukun yayi magana tareda faɗin "waye?.."
Lailah tace "Ni ce dai Yaya.."
bai sake yin wata magana ba sai ji tayi ya buɗe mata ƙofa ya juya ciki, itama bin bayansa tayi ta samu ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ta zauna tana shan lemonta,
Doctor Hasheem kallon agogon ɗakin yayi yaga kusan ƙarfe 12 na dare yace "meyasa kika tashi a cikin wannan daren?.."
Lailah tace "daman ai ina tashi shan lemo ko cin Apple saboda yunwan dare ke damuna.."
kallonta Doctor Hasheem yake cikin takaici yace "kuma sai akace kizo ki takura mun a wannan daren?..." turo baki Lailah tayi sannan tace "haba Yaya amma dai kasan bana zuwa maka a cikin dare ko? yanzun ma matsala ce ta kawo ni..."
yace "matsalar bazaki bari saida safe ba?.."
tace "yoo Yaya da safe ka tafi gurin aiki kodan yanzu an bada hutun asibitin koh? sakamakon mutuwar mai asibitin da aka kasheta, yanzu kullum kana tareda da wancan yarinyar taya zan samu lokacin zama dakai har mu tattauna akan matsalar...". ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki tareda zuƙan lemonta,
Doctor Hasheem kallonta kawai yake yana mamakin iyeyi da kinibibi irin na Lailah ga kuma bakin mayar da magana tana yarinya ƙarama, wanda yanzu take shirin shiga 19years old,
girgiza kai kawai yayi yace "Allah ya shiryeki Lailah, yanzu dai meye matsalar daya kawo ki bacci nake ji..."

tana kora ƴar lemonta hankali kwance tace "Daman maganar shine akan Maimoon tana da tumbi.."
Doctor Hasheem cikin rashin fahimta yace "bangane Maimoon tanada tumbi ba, kowa ma ai yanada tumbi..."
Lailah tana lumshe ido tace "ehh amma ai ba kamar namu ba, ita nata na musamman ne..."
Doctor Hasheem yace "kinga bana son shirme fah idan bazaki gaya mun magana ba ki tashi ki tafi.."
miƙewa tayi tana faɗin "a'ah Yaya ba saika koreni ba, zan gaya maka yauwa, daman Maimoon tanada tsohon cikinka..."
zaro ido waje Doctor yayi yace "ban fahimta ba.." Lailah juyawa tayi zata fita tareda cewa "toh shikenam Yaya karka fahimta randa ta haihu kam ai zaka fahimta koh, idan nan ma baka fahimta ba saika jira isowar motar police a cikin gidan nan zakafi fahimta da kyau..."
kafin Doctor Hasheem ya ce wani abu har ta fice da sauri ta nufi ɗakinta, Doctor Hasheem yana tsaye idonsa a bakin ƙofa tin lokacin fitar Lailah yanata maimaita maganar Lailah akan Maimoon tanada tsohon ciki, nan danan kuma gumi ya fara tsirto masa yana furta "ciki! ciki kuma? Maimoon daman akwai ciki? Innalillahi wa inna ilaihi raju'un..."
A wannan lokacin kwana yayi bai rintsa ba, yanata tunanin Maimoon....

Itama Ayush tana can ɗakinta tana zaune ta kasa yin bacci, daga ta ƙwanta sai taji murɗa, gaba ɗaya ta fita hayyacinta tsabar yawan Amai, kuma komai taci saita amar tana cin abinci zata amar dashi hatta ruwa idan tasha baya zama mata a ciki, shiyasa take yawan jin yunwa har Lailah tana mata gorin yawan cin abinci,
Yunwa ne ya gama isarta haka ta tashi ta fito falo kai tsaye kitchen ta nufa taje ta haɗo kakkauran shayi da biredi ta fito ta koma ɗakinta, zama tayi a bakin gado tana cin bread ɗinta da shayi ko rabin ci batayi ba wani irin murɗa ya hautsino mata, da gudun gaske ta nufi toilet bayan ta ajiye kayan bread akan mirror, amai takeyi bana wasa ba, kamar zata amar da kayan cikinta haka take ƙwaƙulo amai,
Idanuwanta ne sukayi zuru-zuru ga wani irin hajijiyan da yake ɗibanta, fashewa tayi da wani irin matsanancin kuka tana faɗin "wannan wani irin masifa ne da bala'i, wai kam meyake damuna haka ne, duk abunda naci saina amar dashi, toh kenam haka zanyi rayuwata ba tareda naci komai ba, wayyo Allah nashiga uku..."
haka take magana cikin kuka duk ta rarrame ta kokkoɗe ta gama tuttujewa, haka ta wanke bakinta tana tafiya tana laluman jikin bango tsabar hajijiyan da take ji, daƙer ta shiga bedroom ta faɗa akan gado rubda ciki tana kuka, ai kuwa saiga wani aman ya tunkaro maƙogaronta, wani irin hautsinawa tayi daga saman gadon ta faɗo ƙasi tana rarrafe ta shige toilet, a wannan lokacin kam a ƙasin tiles tayi aman domin bazata iya miƙewa tsaye ba, cikin natan nan kamar wanda aka yashe komai, tsabar yunwar da take ji, ga tumbin cikinta har ya ɗan soma fitowa amma duk bata gane cewar ciki bane gashi har na tsawon 4months,
zama tayi a cikin toilet daga taji amai saita kwara shi a wajen, da haka har bacci ya ɗauketa a zaunen ta jingina bayanta a jikin bango, kayinta a sama da haka take baccin,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login