Showing 180001 words to 183000 words out of 186041 words
tana gama iddasa saƙonta ta tashi ta fice abunta, haka jikinsa yake kakkarwa ya miƙe a razane hajijiya yana ɗibarsa haka ya nufi hanyar fita,
Da gudu yake taka matakalar beni yana saƙƙowa ƙafarsa ta zame haka ya faɗo yana gangarowa daga kan Benin har zuwa ƙasi, nan danan goshinsa ya fashe sai jini, ƙafarsa ta gurɗe Allah ya temaka bai karya wuyansa ba, tsabar yasa yaran acikin ransa haka yayi ƙarfin halin tashi yana jan ƙafa daƙer ya fice daga falon, yana jin jiri amma haka yake daurewa, cikin sa'a ya samu driver part ɗinsa cikin hanzari ya shige mota Driver ya miƙe dashi part ɗin su mommy, yana zuwa ya tarar da mommy zaune ƙasan carpet tana rungume da Amrish sai kuka take tayi shi kuma Sarki Raamud ya ɗauki Areeph a saman kafaɗarsa, ganin Junaid a wani irin yanayi yasa gaban Sarki ya yanke tareda faɗin "subhanallahi Junaid meya sameka haka, dubi fuskarka duk ya wanke da Jini..."
Mommy najin haka ta ɗago dasauri tana kallonsa still yana tafe yana ɗingishi! a ruɗe Junaid yayo gurin mommy tareda durƙusawa yakai hannu ya ɗago da Amrish yana bubbugan fuskarta tareda ambatar sunanta "Mamana! Mamana!! Please wakeup Mamana don't leave your Dad please....". ya rungumeta tareda fashewa da matsanancin kuka, ya miƙe tsaye da ita ya ɗorata saman kafaɗarsa ya nufi gurin Sarki Raamud yaje ya karɓo Areeph wanda shima yana nan a sume ba motsi duk ya ɗaukesu su biyun ya fice waje, yana zuwa ya sakasu a mota shima ya shiga kai tsaye cikin masarautar suka ƙara shigewa suka nufi hospital ɗin Narasimha, daga baya su Mommy suma suka biyo bayansu da nasu motar gaba ɗaya sun mance da hospital ɗin Narasimha tsabar tashin hankali da suka tsinci kansu shiyasa tin da basu kai yaran nan ba...
Suna zuwa Narasimha ya farfaɗo da Areeph daman suma yayi, Amrish kuwa saida akayi aiki sosai akanta, domin saida akayiwa heart ɗinta aiki sannan akayi nasarar ceton rayuwarta, shima Ogah Junaid anyi masa treat na ciwon da yaji sannan an haɗa masa da maganin rage damuwa dana saka bacci domin rabonsa dayin bacci yau kwana uku kenam bai rintsa ba,
Ogah Junaid da yaransa sai da sukayi sati guda a wajen Narasimha domin yaƙi barinsu su tafi har saida Amriish ta fara samun sauƙi, Idan suna tare da Daddynsu hankalinsu yafi kwanciya especially Amrish yanzu da take ganin Daddynta ta daina damuwa sosai, kullum sai mommy ta aiko musu da abinci, yanzu kuwa Ogah Junaid ya daina fita Aiki kwata-kwata tin lokacin da aka sanar masa rasuwar Ayushert ɗinsa,
Bayan an sallame su da wata guda Ogah Junaid yana kwance a saman gadonsa ga yaran suma suna kusa dashi a jere duk suna bacci, yanzu duk tare yake kwana dasu, su huɗu akan gado dashi kansa Junaid sai Areeph da Angel da Amrish,
Amriish ko kaɗan bata son motsawa ajikin Daddynta hakan yasa ta fara kwana a room ɗinsa itama Angel ganin haka yasa tace bazata iya kwana ita kaɗai a ɗakinsu ba itama ta fara kwana da Daddynta, shima Areeph ganin duk a ɗakin Daddynsu suke yasa shima ya dawo ɗakin, kullum kuwa sai mommy ta kawo musu ƙaninsu Jariri har ya fara wayo, dake madara mai kyau da tsada ake bashi, yaron ya samu sunan sarki Raamud inkiya kuma (KHUBAYR) wannan inkiyar Ayushert ce tin kafin ta haihu tabar wasiyya akan a sanya masa sunan...
Daga Nigeria sun samu labarin mutuwar Ayush kowa ba ƙaramin girgiza yayi ba dajin labarin, especially Doctor Hasheem yafi kowa shiga damuwa sosai, duk sun shirya akan zasu zo ƙasar california yin ta'aziyya,
Doctor Hasheem da matarsa Maimoon da yaransu biyu sai Lailah da mijinta Doctor Mansur da yarinyar ta mace, da Daddyn Maimoon da mamanta duk sun zo,
Mommy ba ƙaramin farin ciki tayi ba ganin yanda duk suka haɗa kayuwansu suka zo musu ta'aziyya,
Sunyiwa Ogah Junaid shima duk ya canza ya zamo kamar Maraya babu kuzari ajikinsa, saida suka ƙwana kafin suka dawo Nigeria...
Daga baya Hafzat itama da mijinta suka je, tinda hafzat take bata taɓa yin kukan da tasha a lokacinda aka sanar mata rasuwar Ayushert ba, har sukazo kuka takeyi gaba ɗaya ta fita hayyacinta, bata bar masarauta ba sai da tayi wata guda kafin saboda bataso tabar Triplets, ba ƙaramin tausayinsu tayi ba na rashin uwa tin suna yara....
★★★★★★
*AFTER 2 YEARS....*
Har zuwa wannan shekarar Ogah Junaid bai koma Aikin soja ba, a matsayinsa na General duk aikin da zaiyi saidai yayi daga gida, idan ana bukatar yasa hannu a takarda saidai a kawo masa gida yasa hannu duk wasu ayyukansa a gida yake yinsu, yanzu shine yake kula da yaransa, suma yaran sun ƙi school a duk lokacin da aka kaisu makaranta sai sun dawo da jinya a jikinsu tsabar ɗankwara har yanzu basu fitar da wannan damuwar na rashin mahaifiyarsu ba, akoda yaushe suna tsammanin dawowarta, ga khubayr ya girma ba tareda mahaifiyarsa ba yanzu yanada shekara biyu a duniya, yana samun kulawa sosai agurin ƴan uwansa, tsabar shaƙuwar da sukayi baya son yin nisa dasu don ko gurin mommy yanzu baya zuwa..
Ogah Junaid yana kwance ya ɗora Khubayr a saman ƙirjinsa sai bacci yaketa sha, ta gefen hannunsa kuma Amriish ce take kwance akan Damtsensa itama sai bacci taketa sha, ta ɓangaren ɗayan hannunsa ta dama kuma Angel ce itama tana kwance akan hannunsa tana shan bacci, Areeph kuma yana can gefen gado shima baccin yake yi,
Banda shi Ogan wanda idonsa biyu yana kallon ceilling fuskar Ayush kawai yake gani, har yanzu yana cikin wannan damuwar na kewar Matarsa,
yana cikin wannan tunanin yaji an turo ƙofar ɗakin Mommy ce ta shugo da sallama a bakinta tana murmushi saboda kusan kullum a haka take samun su, da kular abinci a hannunta,
ta ajiye akan table tana faɗin "toh Sarkin thinking kai baka bacci koh?..."
Murmushi yayi sannan yace "Hmmm! Mommy kenam .."
ta zauna a bakin gadon itama tana bin yaran da kallo tace "ka sabar wa yaran nan zama guri ɗaya, basa wasa sannan basa zuwa makaranta why?..."
Yace "Mom it's not my fault, har yanzu akwai damuwar rashin mahaifiyarsu acikin zukatansu, na rasa yanda zanyi na cire musu, idan na matsa a kusa dasu gani sukeyi kamar nima zan tafi na barsu ne kamar yanda suke tunanin Mommynsu ta tafi ta barsu..."
Mommy tace "a hankali zakana cire musu abun a ransu, yanzu tsawon shekara biyu amma har yanzu basu daina kewar nan ba? waɗannan wasu irin yara ne haka, yanzu suke da shekara shida fah, gashi har sun koyawa ƙaramin ƙaninsu zaman kewar, yakamata suje su haɗu dasu Ummulkhairy da Abul suna yin wasa tare kuma su rinƙa zuwa school, kar ka sakalta su da haka .."
Ajiyar zuciya Junaid yayi yace "toh yazanyi especially Mamana duk ta fisu ɗankwara ganinta koda yaushe ajikina ne yasa suma suka biye mata, ina tsoron tashin ciwonta, inda ace Yushert tana nan da duk hakan bata faru ba, amma zanyi iya ƙoƙari na naga sunje school sannan duk zasu koma ɗakunan su da kwana...."
Mommy tace "toh kai kuma fah? Kaima ai kamar yaran haka kake kaƙi komawa gurin aikinka..."
Yace "saboda yaran ne yasa bana zuwa..."
Mommy ta ɗanyi shuru kaɗan daga baya tace "Amm daman inaso zanyi magana dakai..."
Ogah Junaid cike da mamaki yace "ina jinki Mommy...'
Tace "daman maganar akan Aurenka ne, bai kamata ace kana zaune haka ba mata ba, idan kayi Auren suma yaran zasu fi jin daɗin kasancewa cikin nishaɗi..."
Junaid haka yake jin kalaman mommy a baibai cikin rashin fahimta yace "Aure kuma? da wa?..."
Mommy tace "mun zauna mun tattauna da Baffanunka akwai wacce zamu haɗaka da ita, Balarabiya ce ƴar ƙasar Makkah, tanada kyakykyawar zuciya, kuma zata riƙe maka yara tamkar mahaifiyarsu, idan har kaji halayenta da tarbiyarta zakaso kasancewa tareda ita a matsayin matarka, yaranka zasu ji daɗin kasancewa da ita domin ita ɗin uwar ƴaƴa ce tanada son yara sosai da sosai, ka yadda dani my son kasan bazan zaɓa maka abunda zai cutar dakai ba..."
Ogah Junaid jinjina kai yayi shi ya rigada ya tsara cewa bazaiyi Aure ba, zai tsaya ne ya kula da yaransa....
Yana cikin wannan tunanin yaji mommy ta katse shi da cewa "na roƙe ka my son ka amince dan Allah, ina neman alfarmanka..."
Kallon mommy yayi tareda haɗiyar yawu yace "shikenam Mom, babu abunda zaki roƙeni akan nayi shi banyi ba, domin kin wuce haka acikin zuciyata! duk abunda kika tsara dai dai ne saboda haka na Amince, indai kin yadda da tarbiyarta nima na yadda..."
Murmushi mommy tayi tana hamdala cike da farin ciki tace "Nagode sosai Yarona, Allah Ubangiji ya maka Albarka, Allah ya ƙara maka haƙuri da juriya, Allah ya ƙara buɗa maka ƙofofin Alkhairi..."
Junaid ba ƙaramin jin daɗi yayi da waɗannan addu'o'in mommy ba, shima yayj murmushi yace "Nagode Mom, Allah yabar mun ke..."
ta Amsa da Ameen sannan ta sanar masa cewa "Gobe insha Allahu su Baffanunka zasu je su ɗauro maka Aure acan ƙasar Makkah..."
Zaro ido Junaid yayi sannan yace. "Mom da sauri haka?..."
Tace "kai baka saniba har an gama komai yanzu Aure ne ya rage, inada yaƙini zaka amince shiyasa tinda ban sanar maka ba..."
Murmushi kawai yayi ba tareda yace komai ba,
Mommy ta fice a ɗakin cike da murna...
Bayan fitar ta kwantar da kansa yayi akan pillow kansa na kallon ceilling shi yasan irin damuwar da yake ciki na rashin Ayush......
Washe Gari su Uncle Artaff da Sarki Raamud sun shirya tsab zasu tafi Makkah,
Ga jirgi na jiransu haka suka tafi,
Junaid yana tareda yaransa bai ma san sun tafi ba saboda bai saka abun aransa ba, mommy haka tasa ƴan aiki suka gyaggyara ko ina na gidan, part ɗin Ogah Junaid an gyara wuri yayi kyau sosai,
A wannan lokacin a falo suke zaune suna kallo Angel tace "Daddy ya naga duk an gyara gidan, waye zai zo?.."
Junaid yayi murmushi sannan yace "Aunty za'a kawo muku gidan..."
Angel tace "Aunty kuma aina?..."
Yace "Aunty za'a kawo muku wacce zatana kula da ku.."
Angel kamar zatayi kuka tace "kenam Mommyn mu bazata dawo ba har abada?...". Junaid jiki ba ƙwari haka yake kaɗa mata kai.
Amriish tace "mommy ta gudu ta bar mu, ta guje mu, bata son mu, nima yanzu na daina damuwa da ita inaso a kawo mana wata Aunty wacce zatana kula damu, kuma zata zauna a matsayin Mommyn mu..."
Ogah Junaid yana kallon Amriish cikin tausayawa yace "Mommyn ku bata guje ku ba..."
Kafin ya ƙarasa maganar Areeph ya katse shi da cewa "mommy fah mutuwa tayi.."
Junaid cike da mamaki yake bin Areeph da kallo daƙer yake motsi da lips ɗinsa waran cewa "waya gaya maka cewa Mommynku ta mutu?..."
Areeph yace "na daɗe dajin labarin nan a wajen su Mamy....." kafin ya rufe bakinsa Amrish ta cabki wuyansa tana kuka tana faɗin "wallahi mommy bata mutu ba, ƙarya kake yi mommyna bata mutu baa.." nan suka fara kokuwa tsakanin Areeph da Amrish Ogah Junaid ganin Areeph ya ware hannunsa zai zabga mata mari yasa yayi saurin riƙe masa hannu tareda rabasu kowa yaja shi gefe, gaba ɗaya ya rasa mai zaice mAh,
Ita kuwa Angel fashewa tayi da kuka jin ance Mommynsu ta mutu,...
Daƙer ya rarrashe su sannan yaja su suka nufi bedroom.....
Su Sarki Raamud basu tashi dawowa ba sai washe gari suka tafo da Amarya tareda wasu matan waɗanda suka yo rakiya, ana kawo Amarya aka wuce da ita part ɗin Angonta wanda yasha tsaruwa sai ƙamshin turare ne yake faman tashi,
Shima Ogah Junaid yasha Gizner abunsa ba ƙaramin kyau yayi ba, sannan Angel da Amrish suma an haɗesu da dogwayen riguna na kanti masu kyan gaske da tsada kayansu iri ɗaya, shima Areeph da Khubayr sunsha Gizner irin na Daddynsu, sun sha kyau sosai kamar ƴan indiyawa kodama asalin ƴan India ne...
Misalin ƙarfe 10 na dare Ogah Junaid yana zaune a falo shida Yara suna kallon Film saiga Mommy ta shugo da flask a hannunta tana ganin Junaid ta tsaya tana kallonsa gira a haɗe,
Junaid yana ganin mommy a haka yayi murmushi yace "Mom what's wrong?..."
Tace "haba My Son yanzu fisabilillah hakan ya dace kenam!?.."
Yace "me kuma nayi?..."
Tace "meyasa kabar Amarya ita kaɗai acan room ɗinka baka je ka ganota ba?..."
Murmushi yayi sannan yace "Mom zanje so nake sai yaran sunyi bacci ."
Tace "a'ah basu ga Auntyn nasun ba zasuyi bacci?..."
Angel tace "Daddy nikam zanje naga Auntyn namun..." Itama Amrish tace "nima zanje naga Auntyn mu wacce zata zamo Mommyn mu.."
Mommy tana tsaye sai Dariya take tayi tace "toh shikenam kuje room ɗin Daddynku tana can, kuje kuce mata ta fito kuci Abinci...". Suka amsa da toh suna tsalle suka haura upstairs...