Showing 90001 words to 93000 words out of 186041 words

Chapter 31 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53960

fa mahaifiyarka ta ɗaura muku Aure ne a ɓoye indai ba waɗanda aka ɗaura a gabansu ba babu wanda zai bada shaidar Aurenku, amma Alhamdulillah akwai shaidu da yawa waɗanda a gabansu aka ɗaura acikinsu har da ni da kuma abokin mahaifinka Barrister Aminu, kuma sannan ga katin shaidar Aure an bugosu tin a ranar, idan na samu zama da Ayshert zan sanar mata cewa tayi tunanin lokacin da Angela ta musulunta, a lokacin a gabansu nayi waya da Hajia Fateema akan batun Auren, ita marigayiya Maryam ta fara mun tambayoyi akan maganar Auren da nake yi da mahaifiyarka, tabbas da Maryam tana raye ita zata fahimtar da Ayshert toh amma nima zanyi iya ƙoƙari na domin Ayshert ba ƙaramin tsanarka tayi ba..."

Junaid yana dafe da goshinsa yace "bani na kashe mata mahaifiyarta ba, wallahi bani bace! hasali ma in badan mahaifiyarta ba da yanzu bana raye a doron ƙasa, an kawo mun hali ta baya a daiden lokacin mahaifiyarta tazo ta shige tsakiya harin ya sauƙa akanta, ta ceci rayuwata,
taya zan kashe ta? bayan Mahaifinta har dashi ya taya mu yaƙan babban maƙiyi tabbas ya taka rawar gani sosai, daga ƙarshe aka kamashi a matsayin mai laifi, shin taya zan bari ya cigaba da zama a matsayin mai laifin? Bayan yanzu na tabbatar shi ɗin ɗan uwan mahaifi nane, kafin na dawo Nigeria saida nayi silar fitowarsa daga cikin maƙarƙama, yanzu haka yana can cikin masarautar sa cikin ƙoshin lafiya, amma Yushert ta gagara fahimta ta tasa wuta a gidan mu ta ƙona mun mahaifiyata, da wanne zanji a cikin zuciyata, nasan ciwon raɗaɗin mutuwar mahaifiyarta ne yasa nima ta rabani da tawa farin ciki, shiyasa na danne ƙonar dake cikin zuciyata a yanzu burina shine Yushert ta dawo gareni ta yadda dani sannan ta maye mun gurbin mahaifiyata data rabani da ita, nima kuwa na maye mata gurbin data rasa, to ya zanyi mata..."
ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka kamar wani yaro ƙarami...

Ayush dake bayan labule itama kuka take ba tareda ta bari kukan ya fito ba, duk ta gama jin tattaunawarsu a zuciyarta take faɗin "na yarda dakai Yaya Junaid, na yarda dakai, amma bazan iya cigaba da zama dakai ba, ni na kashe maka mahaifiya taya zanji daɗin cigaba da tarayya dakai,
nayi dana sanin aikata wannan zaluncin da nayi, nayi dana sani wayyo tirr dani! Mommy ta rufa mun asiri ta nuna mun kulawa kamar ƴar cikinta, Allah sarki matar arziƙi ki gafarce ni, na aikata babban kuskure a rayuwata, tabbas rayuwata bata da wani amfani..." ta toshe bakinta tana kuka ciki-ciki...

Malam Lawan daƙer ya samu ya rarrashi Junaid sannan ya buɗe ledar daya shugo da ita, ya fitar da gasassun kaji ya baza masa su a cikin ledar, sannan ya buɗe masa lemuka na fata dana ruwa..
daƙer yake lallaminsa yake ci cikin nutsuwa da kulawa..

Ayush ƙamshin kajin ne yake kawo mata hari, kwata-kwata bata ƙaunar jin wannan ƙamshin, zuciyarta ne yake ta faman tashi, da sauri ta toshe bakinta da hannayenta biyu sakamakon aman da ya tsaya mata a maƙogaro, sai faman zazzaro ido take waje, yunƙurawa tayi ta ɗanyi wani ƙara kaɗan..
wannan ƙaran aman ne ya sauƙa akan kunnen Junaid, ɗagowa yayi yana waige-waige,
Malam Lawan yace "lafiya kuwa?.."
cikin sassanyar murya yace "ƙara naji, kamar wani yana cikin ɗakin nan..."
murmushi malam yayi sannan yace "kai dai ba'a rabaka da mita, ni banji motsin kowa ba, kaide cigaba da cin abincin ka, so nake na samu na tafi gida idan ka kammala kaga yanzu ƙarfe 12 saura dare yayi sosai, amma ina tunanin barinka kai kaɗai.."
Junaid idonsa akan malam yace "dare yayi kam malam yakamata ka koma gida, asibitin akwai security sosai, ba damuwa..."
da murmushi a saman fuskar malam ya ɗan shafi gefen fuskar Junaid yana faɗin "shikenam zan tafi ka kula da kanka, Allah yayi maka Albarka.."
Junaid jinjina kai kawai yayi yana kallon Malam har ya fice daga ɗakin...
Bayan fitar malam ɗaukar ledar kajin yayi ya ajiye a gefe guda domin baya buƙatar cin komai, kawai malam ne ya takura masa akan yaci,
har zai kishingiɗa ya ƙwanta kuma du ya sake jin yunƙurin amai, fasa ƙwanciyar yayi yakai idonsa saitin yanda yaji ƙaran, fincike kalurar hannunsa yayi sannan ya sauƙo daga kan gadon ya nufi gurin, hannu yasa ya yaye labulen ƙwatsam idonsa ya sauƙa akan Ayush wacce take tsaye duk ta ɓata kayan jikinta da amai, hannayenta dake toshe da bakinta suma amai ne yake gangarowa, ganin yanda Junaid ya zuba mata ido ne yasa ta wuce ta gefensa ta shige toilet, kai tsaye wajen sink ta nufa taje ta cigaba da ƙwarara aman da bai gama fitowa ba, Junaid ne shima ya shugo cikin toilet gaba ɗaya hankalinsa ya tashi jin yanda take ta yunƙurin amai kamar zata amar da kayan cikinta ga bata ci komai ba..
ji tayi ya dafa kafaɗunta biyu cikin sexy voice ya furta sunanta "Yusherttt..."
itama ɗagowa tayi a hankali tana kallonsa ta cikin madubi idonta yayi lufu-lufu sun kumbura tsabar kuka, fuskar nan yayi jawur murya a sanyaye take magana "Ni ni bana son jin warin nama!, banason jin warin nama!..."
juyar da ita yayi suna fuskantar juna yana kallonta cikin so da ƙauna, hannunsa yakai ta bayan rigarta ya soma zuge mata zip har zuwa ƙasa, ta saman kafaɗarta ya zamar mata da doguwar rigar har ƙasa ta zauna daga ita sai breziya da pant, haka suke kallon juna kamar zasu haɗiyi junansu daga baya Junaid yasa hannu ya rungumota kan faffaɗar ƙirjinsa ya manneta sosai da jikinsa yana shafar sumar kanta har zuwa gadon bayanta, yana cikin shafar bayanta ya ɓalle mata brezy,
itama hannu tasa ta bayansa ta rungume shi tana kuka...

Ɗaukar ta yayi sannan ya zaunar da ita a cikin farin bahon wanka ya kunna mata fanfo mai ruwan ɗumi saida ruwan yazo mata saitin ƙirjinta tukun ya kashe ruwan tareda ɗaukar sabulu mai ƙamshin gaske yana murza mata a jikinta cikin salo, haka yake bi yana mulmulka mata sabulun a duk ilahirin jikinta, lumshe ido tayi sannan ta ƙwantar da kanta a bakin bahon tana kallon sama,
shima cire singet jikinsa yayi da gajeren wandonsa ya shiga cikin bahon dake baho ne mai girman gaske domin zai iya ɗaukan mutane uku zuwa huɗu, ƙara kunna musu ruwan fanfo yayi mai zafi har saida ruwan yazo saitin wuyansu tukun ya kashe, hannu yasa yana wanke mata jikinta ta ko ina daga sama har ƙasa daiden lokacin da ya rufu kanta a cikin ruwan ya manna mata kiss akan goshinta, still idonta a lumshe ko buɗe su batayi ba, sai daga baya ta buɗe idonta a hankali tana kallon cikin ƙwayar idonsa, hancin su yana manne dana juna haka numfashinsu yake hargutsuwa dana juna, a haka yake wanke mata jikinta a hankali yana shafar jikinta kamar wanda yake shafar jikin kifi tsabar tsantsi da laushi hannunsa yakai saitin pant ɗin ta ba tareda yasa hannunsa ta cikin pant ɗin ba haka ya soma shafar saman pant ɗin cikin salo,
daiden lokacin ta sauƙe ajiyar zuciya tareda lumshe ido kamar mai yin bacci, haɗe musu lips yayi yana socking a hankali har ya zura harshensa cikin bakin ya kamo harshenta yana tsotsa kamar wanda ya samu lollipop, haka yake tafiya da hannunsa yana shafar tumbin cikinta har zuwa saman breast ɗinta, nan ma shafawa yake yana murzawa a hankali,
gaba ɗaya ta gama fita hayyacinta haka itama take mayar da martani suna kissing junansu, ta zagayo da hannayenta biyu ta bayansa tana shafa shi itama a hankali,
gurin yayi shuru sai motsin ruwa ake ji yana bada sauti a hankali,
ƙara sauƙar da hannunsa yayi kan tumbin cikinta yana shafawa a hankali ji yayi kamar ba tumbin Ayush yake shafawa ba domin yasan kalar tumbinta ɗan ƙarami ne a shafe kamar babu komai a cikin cikinta, yanzu kuma yaji tumbinta ya sauya sosai cikin ya ɗan yi girma sannan yayi tauri, raba lips ɗinsu yayi sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin yanayi a hankali ya ambaci sunanta "Yushert.."
Itama buɗe eyes ɗinta tayi a hankali take binsa da kallo cikin sexy voice yace "you have a pregnant?..."
zaro Ido tayi sosai tana binsa da kallo, murya a sanyaye ya kuma cewa "Please ki gaya mun gaskiya my wife, cikin ki ya ɗago sosai..."
girgiza masa kai tayi babu bakin magana, zuciyarta ne yake wani irin bugawa, ta tsorita sosai jin abunda ya faɗa,
Junaid hannunsa yakai ƙasin marar ta yana shafawa a hankali yake motsi da lips ɗinsa yace "marar ki ya ɗago Yushert, kina ajiye da Baby na.."
ya ƙarasa maganar yana goga musu hancinsu guri ɗaya, ji yayi tace "tayaya hakan zata faru?..."
ɗagowa yayi yana kallonta da murmushi a fuskarsa yace "our first night, kafin na tafi California shin kin tuna? kinsan lokacin ma an ɗaura mana Aure..."
Ayush rufe idonta tayi sosai tana tariyo abunda ya faru a tsakaninsu, a cikin zuciyarta take maganar cewa "kenam daga yi sau ɗaya sai ciki? Impossible I can't believe..."
a daiden lokacin Junaid ya manna mata kiss a saman lips ɗinta...

tashi yayi Junaid daga kanta yana faɗin "rufe idonki kar ki sake suma mun irin na wancan lokacin farkon zuwanki gidan mu..."
Ayush ganin yana shirin miƙewa a tsirararsa yasa ta rufe idonta ta sauri, har saida ya fita daga cikin bahon ya ɗauki 3quater sa ya zura, jikinsa duk damshin ruwa yasa hannu yayi wa Ayush ɗaukar luɗa ya fita da ita cikin room ɗin da yake a asibiti, ƙwantar da ita yayi sannan yasa hannu ya cire mata jiƙaƙƙen pant ɗinta ya jawo mata mayafi ya rufe mata jikinta gaba ɗaya, har yayi wannan ɗawainiya idonta a rufe yake,
komawa cikin toilet yayi yaje ya wanke mata kayan sakawarta daya ɓaci da amai har pant ɗinta da breziya duk saida ya wanke su tas sannan ya shanyasu,
ɗaukar singlet ɗinsa yayi ya sanya shi a jikinsa sannan ya koma cikin ɗakin, saida yasa key a ɗakin tukun yazo shima ya ƙwanta tareda rungumo Ayush jikinsa ya rufa musu mayafi kafin a ƙirga mintuna har bacci yayi awun gaba dasu....

Asussuban farko Ayush ta tashi daga bacci tana mutsil-mutsil jin yanda Junaid ya ƙanƙameta ne yasa ta ɗanyi shuru saboda kar ta tashe shi, a hankali take zamar da hannunsa daga rungumar da yayi mata, da haka har tayi nasarar tashi ba tareda ya farka ba, duban kanta tayi taga ashe tsirara take ƙwance, da hanzarinta ta nufi toilet taje ta saka kayanta sannan ta fito tazo gaban Junaid ta durƙusa tana hawaye a hankali take faɗin "kayi haƙuri Yayana nima na sani ina ɗauke da cikinka na tsawon wata huɗu, amma sai dai a wannan lokacin bazaka kasance tareda mu ba, dani da jaririna zamuyi nesa dakai saboda bamuyi maka halacci ba, munci amanarka, jaririna a jikina yake dole zai kasance dani a koda yaushe, Yaya Junaid daga yau bazaka ƙara ganin mu ba, ina fatan Allah ya baka wata matar da ta fini komai, kuma Allah ya baka ƴaƴa masu albarka waɗanda suka fi jaririna, ina sonka mijina...."
tana kaiwa ƙarshe ta miƙe tareda kai masa sumbata akan goshinsa daga nan ta nufi bakin ƙofa a hankali ta murza key ta buɗe tayi ficewarta,
tana fita daga cikin asibitin ta fara gudu ko tsaya ɗaukar akwatinta batayi ba, haka ta wuce security tayi ficewarta,
Garin shuru ba kowa sai hasken nepa ta ko ina, wani wajen kuma duhu ne ba haske da haka take tafiya ƙafarta ko takalmi babu,
wani mai mashin ne ya tsaya a gefenta yana faɗin "Hajia lafiya kuwa na ganki a cikin daren nan ko asuba ba'a ƙira ba.."
juyowa tayi tace "lafiya ƙalau wani warai mai ɗan nisa nake son zuwa.."
yace "toh idan babu matsala hau na kai ki yanda zaki sauƙa, Allah yasa dai ba aljana zan ɗauka ba..."
Ayush kuka take jin abunda ya faɗa ne yasa ta yin dariya ta hau mashin suka tafi,
tafiya suke ba ƙaƙƙautawa har sun fara fita daga cikin gari babu wasu gidaje sai jeji,
Mai mashin ne ya tsayar da mashin yana faɗin "dan Allah baiwar Allah wallahi da niyar temako na ɗauko ki naga kina cikin matsala, nima asibiti zanje dubowa mahaifiyata dan Allah karki cutar dani, yanzu na gane cewa ke ba mutum bace amma ki rufa mun asiri ki barni na koma cikin garin mu lafiya, wallahi daga nan bazan ƙara yin gaba ba, wallahi ni ko fuskarki bana iya gani tsabar duhu sai iya hasken mashin ɗinane kawai..."

Girgiza kai Ayush tayi tace "shikenam ba damuwa hakan ma nagode sosai, ka juya kawai ni zan ƙarisa gurin da zanje..."
tana kaiwa nan tayi gaba abunta ko tsoro da fargaba babu niyarta shine ta koma jejin da suka zauna da mahaifiyarta...
Shi kuwa mai mashin da gudu ya juya ya koma baya..


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login