Showing 153001 words to 156000 words out of 186041 words
mommy dake su ba'a gari suke ba, wasu suna Kaduna wasu Kano wasu Bauchi wasu kuma ba'a cikin Nigeria suke ba akwai waɗanda suke Camaroon da London da Sudan...
Mommy tanada ƴan uwa sosai, saboda Junaid ne basa zuwa don idan sukazo bakinsu baya mutuwa sun rinƙa tambayar ƴan uwan mahaifin Junaid shi kuwa yaita musu rashin mutunci har koransu yake daga gidansu, kuma yayi musu warning akan kar su sake zuwa yanda suke dalilin da yasa basa zuwa kenam, amma yanzu tinda komai yayi normal duk zasu zo amma sai ana gobe suna, kuma a ranar suna za'a ɗaura Auren mommy da sarki Raamud...
★★★★★
Ranar Suna, ranar daya kama ranar Jumma'at kenam, gidan mommy ya cika da mutane, ƴan uwan mommy su sukafi yawa dake gidan babban gida ne, akwai ɗakuna part to part, kuma an ƙara tsara gidan yayi kyau sosai, an chancanza furniture's ɗin ɗakunan, sunyi bala'in kyau sosai,
Ko wani ɗaki ƴan gari ɗaya ne aciki, ɗakin ƴan Bauchi daban, ɗakin ƴan Kano daban, ɗankin ƴan Kaduna daban, ɗakin ƴan Katsina daban, ɗakin ƴan Adamawa daban, ɗakin ƴan ƙasar London daban, ɗakin ƴan ƙasar Camaroon daban, ɗakin ƴan ƙasar Sudan daban, waɗannan duk ƴan uwan mommy ne sun samu wadatattun ɗakuna!!!!
Sai kuma iyayen su Hafzat suma sunzo hidimar tareda ƴan uwanta kusan su goma, daga Kano suma...
Ga Mutanen ƙasar Iran wato ƴan uwan mahaifiyar Uncle Artaff suma kusan su goma sun zo aciki harda mahaifiyarsa ta fara samun sauƙi Alhamdulillah ita kam ɗakinta daban aka tanadar ita kaɗai dake bata son hayaniya,
Duk ƴan uwan mommy an nuna musu cewa itace mahaifiyar Máahmud Baban Junaid kuma an nunnuna musu sarki Raamud da Uncle Artaff cewa sune ƴan uwansa kuma sun gamsu sosai har suna cewa "ai kuwa suna kama da Máahmud sakk especially sarki Raamud kamar an tsaga kara..."
Sai yanzu hankulansu suka kwanta ganin ƴan uwan mahaifin Junaid,
Gasu Lailah suma sunzo hidimar ita da Maimoon dasu Ammy,
Daga ƙasar China Aunty Adity itama tazo jin labarin ƙaruwar da Ogah Junaid ya samu,
A masallacin da aka ɗaura Auren mommy da Abbah anan aka raɗa sunan ƴan ukun Junaid da Ayushert,
An sanya musu sunaaa!!!
Namijin yaci sunan mahaifin Junaid wato
MÁAHMUD *(AREEPH)*
Ita kuma ɗaya daga cikin macen ta samu sunan Mommy wato.
FATEEMA *(AMREESH)*
ita kuma ɗayar Junaid yayi alƙawarin indai ya samu ɗiya mace zai yiwa jarumarsa mai suna, toh wannan alƙawarin yana nan tafe an sanya mata sunaaa..
MARYAM *(ANGEL)*.....
Masha Allah kowa yayi farin cikin zuwan
Areeph da Amrish da Angel, hidima kamar baza'a dena ba, acikin ƴan uwan mommy akwai waɗanda suka haɗa diner party sun kashe kuɗi sosai, An yanyanka dabbobi kamar na mai domin saniyoyi akai ta yanka wa kusan guda Ashirin ga kuma raƙuma suma sun kai Ashirin har rasa yanda zasuyi da nama sukayi,
Ayush tana ɗakinta dake batada wasu ƙawaye daga Lailah ne sai Maimoon sai kuma wasu ƴan mata daga cikin ƴan uwan mommy, sai ƴan uwan uncle Artaff waɗanda basuyi Aure ba da kuma masu Aure,
Sun sa Ayush a gaba wai sai anyi mata kitso, ita kuwa Ayush furr taƙi domin ita tinda aka haifeta ba'a taɓa mata kitso ba tsabar tsayin gashinta,
Filawar lalle ma bata yadda anyi mata ba sai jan ƙunshin ƙafa da hannu, kowa yaga lallen Ayush sai ya yi santi,
kitso kuma saida aka kai ƙarar ta gurin mommy tukun tazo ta sameta, daƙer ta yadda za'ayi mata,
mai mata kitson wata ƙwararriyar mai kitso ce daga ƙasar Camaroon, tana soma taɓa gashin Ayush taji wani irin laushi kamar Audiga ga tsayi kamar na masifa har kan tudun mazauninta, ta soma yi taji bazata iya ba haka tasau mata gashin tana cewa "wallahi bazan iya da wannan gashin ba, tsayinsa yayi yawa, Ni tinda nake ban taɓa ganin mai tsarin gashi kamar Aunty Ayusher ba..."
wata makitsiyar ce tazo zata mata itama haka ta haƙura tace "waii bansan ya zanyi da wannan gashin ba, saidai ayi miki rolling ɗinsa amma bazai kitsu ba..."
Saida mutane biyar suka kama gashin Ayush suna sakewa bazasu iya ba,
Maimoon ce ta miƙawa Lailah yaronta Rapeekh tace "bari na gwada tawa basiran..." Mutanen waran kuwa haka sukayi caaa akanta suna faɗin "muma ƙwararrun makitsa bamu iya ba sai ke wanda bayin kitso kike yiba, ku ƴan Nigeria babu abunda kuka iya..."
Maimoon ta kalli wacce tayi maganar tace "ke dube Ni dakyau nayi miki kama da ƴan Nigeria? Kije ki tambaya!! Larabawa babu wanda yakaisu iya abun duniya..."
Wata a ciki tace "yoo duk nan waye ɗan Nigeria ne, ko itama Aunty Ayusher ai ba ƴar nan bace, kuma itama mommy asalinta bar ƴan nan Nigeria bace, ƴar Sudan ce suka zo nan Nigeria da sauran ƴan uwa ..."
Lailah jin kowa yana tofa albarkacin bakinsa itama tace "Hmmm mukam ƴan asalin Nigeria ne, kuma banga dame aka fimu ba..."
tana ƙarasa maganar ta kawar da kanta gefe tana wasa da Rapeekh...
Ita kuwa Ayush kanta a sunkuye tinda suka fara ko motsi batayi ba balle ta musu magana, suna cikin maganganu har Maimoon tayi nisa da kitsonta, kuma kitson yana mungun tsaruwa gasu ƴan ƙananu take yinsu hakan yasa bata shan wahalar kitson,
Nan danan Ayush ta fara shessheƙar kuka tana dafe da kanta,
Duk suka zuba mata ido wasu suna cewa "haba Aunty Ayush kukan kitso kuma?..."
wasu kuma suna faɗin "dan Allah ku bar mata gashinta tana jin zafin kitson ne, kuma kinga ba'a taɓa mata kitso ba dole taji zafi ...."
wasu kuma suna cewa "kaiiii amma kitson nan yana mungun tsaruwa wallahi, ga gashin baƙi ƙirin sai yake fidda zanen kitso, kawai a ƙarasa mata tinda anyi rabi ..."
Bayan awa guda Maimoon ta kammala kitson kan Ayush, daƙer ta iya ƙarasawa tsabar ciwo da yatsunta suke mata, ba ƙaramin wahala tasha ba kafin ta gama kitson,
Ai kuwa haka aka rinƙa ɗauka kitson kan Ayush a photo, yayi kyau sosai gasu ƴan ƙananu, zirin kitson har kan tudun mazauninta, ga an fidda style, ba ƙaramin kyau Ayush tayi ba...
Triplets kuma suna can ɗakin tsofi...
★★★★★★ Ogah Junaid sam baya son mutane sosai hakan yasa yaje ya buɗe ɗaya daga cikin gidajensa ya shiga,
gidane ɗan ƙwaƙwass shi ba ƙarami ba sannan shi ba babba ba, bayan ya shiga da motarsa ciki yaje ya parker a waje guda sannan ya fito yazo ya rufe gate ɗin tareda saka key, zuwa yayi ya buɗe murfin motar ta ɗayan ɓangaren nan itama Adity ta zuro zankaɗeɗen sawayenta ta fito tana sanye da jeans da t-shirt mai dogon hannu, da ƴar jakarta, ga kuma takalmi mai tsini tayi gyaran gashi ba ƙaramin kyau tayi ba, kuma yanzu ta dena yawan faɗace-faɗace tinda taji Rumana da Angel sun mutu daga nan ta shiga taitayinta, daga baya aka koreta daga aikin soja amma Junaid yasa an mayarta yanzu tana kan Aikinta, kuma itama an saka ranar Aurenta da wani cousin ɗinta shima Soja ne..
Junaid ya kawota nan gidan ne saboda acan kowa kallonta yake ana tsegumin daga ina take kuma alhalin ba ƴar uwarsu ba, kuma basuda ƴan uwa Arniya hakan ma ƴar china, da haka Adity taje ta gano Jarirai sannan suka gaisa dasu Mommy da Ayush,
ƙarasa shiga cikin falon ɗakin sukayi, ta zauna akan sofa tana fuskantar plasman, shi kuma zuwa yayi ya ɗauko musu abincin da zasu ci domin basu samu damar cin abinci ba,
Shi Junaid bazai iya cin abincin gidan hidima ba, ita kuma idon mutane ne suka hanata cin abincin gidan hidimar, kuma bayan haka ma bazata iya ci acikin mutane over ba......
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 81 to 85
Bayan Ansha hidimar suna dana biki kowa ya watse, sai Ayush da yaranta uku da Oganta Masha Allah suna samun kulawa sosai, itama mommy tana can part ɗinsu ita da sarki Raamud anata cin Amarci...
A satin nan su Junaid zasu tafi ƙasar california tare zasu tafi da Sarki Raamud shida mommy domin cigaba da rayuwarsu a cikin masarauta, jin haka ba ƙaramin tashin hankali Ayush ta shiga ba ganin duk za'a watse a barta,
Ƙwance take akan gado sai faman rera kuka take ga jarirai a gefen gado sai sharar baccinsu suke gwanin burgewa, Junaid ne ya shugo da sallama a bakinsa jin ba'a amsa masa ba yasa ya ƙara maimaitawa, still ba'a amsa ba, ƙarasa shugowa yayi cike da mamakin ganin Ayush kanta a kife sai kuka take tayi, zama yayi a bakin gado ya ambaci sunanta a hankali cikin nuna damuwa yace "Yushert meya faru dake kike kuka?..."
shuru bata bashi amsa ba, yasa hannu ya ɗago da ita tareda kwantar da ita saman faffaɗan ƙirjinsa yace "Yushert gaya mun mana kar kisa nima nayi kukan, please my wife..."
Ɗagowa tayi da rinanan idanuwanta waɗanda tasha kuka dasu suna kallon juna lips ɗinta na kakkarwa daƙer ta iya cewa "Zaujul! zaku tafi ku barni, bana son ku tafi ku barniii..."
Nan ta ƙara fashewa da kuka daƙer ya rarrasheta kanta akan ƙirjinsa yana bubbugan bayanta a hankali yace "kiyi haƙuri My Yushert tafiya ai ba mutuwa bane, kuma nikam ai ba jumawa zanyi ba zan dawo..."
tace "duk da hakan ma Ni a tafi dani..." zaro dara-daran idanuwansa yayi dasauri ya katseta da cewa "Yushert ina zan kai ki da waɗannan jarirai ba ɗaya ba, ba biyu ba kedai kiyi haƙuri idan yaran sun fara girma in yaso sai in tafi dake koh..."
ƙara fashewa tayi da kuka tana faɗin "mommy da Abbah zasu tafi, kaima zaka tafi toh yazanyi.." murmushi yayi yace "gaki ga Hafiza mezai same ki, kuma kafin na tafi zan sa a nemo miki wasu matan da zasu miki renon yara da wasu ayyukan gida..."
saida ya tabbatar ta haƙura tukun ya daina rarrashinta ya tashi ya cigaba da shirye-shirye domin fitar asubanci zasu yi, saboda jirginsu a wannan lokacin zai tashi,
itama tashi tayi tana taya shi shirya kayayyakinsa haɗe da shan soyayya...
itama Hafzat tana kitchen gaba ɗaya ta rasa sukunin ta na tafiyar Judan, ta shaƙu dashi bana wasa ba, sai sharar hawaye take tayi ita kaɗai, yayin da shi kuma yana can ɗakinsa ya gama shirinsa tsab, yana kwance akan gado yayi shame-shame kansa na kallon ceilling yana tunanin tafiyar da zaiyi yabar Hafzat, baya tunanin zai iya tafiya ya barta amma saidai ya zama dole ya tafi, dan ma Ogah Junaid ne ya tsayar dashi da tin yaushe ya tafi, ga kuma soyayyar Hafzat tana shirin zamo masa matsala indai ya rasata a matsayin matar Aurensa, haka ya dinga waɗannan tunanika...
A part ɗin su Mommy kuwa suma sun gama shirinsu sauran tafiya ne ya rage musu, Abbah kamar bazai mutu ba tsabar murna da farin cikin mallakar mommy a matsayin matarsa ta sunna, kuma gashi yana ɗaukin komawa masarautarsa da matarsa,
Mommy kuma ba'a son ranta za'ayi wannan tafiyar da ita ba saboda tana tunanin wahalar da Ayush zata sha waran rainon triplets, twins ma ya ake ƙarewa dasu balle har triplets, saidai dake Junaid yace mata akwai waɗanda zasu na rainon yaran, anan hankalinta ya kwanta....
A ranar kuwa aka kawo wasu mata su huɗu, ɗaya zata na aikin girki da sauran Ayyukan gida, ɗaya kuma zatana gyaran ɗakuna da goge-goge da wanke-wanke da wanki kayan yara dana uwar....
sauran biyun kuma sune masu rainon yara da sauran Ayyukan gida suma,
Bayan sallar asuba su Mommy ne suka fiffito da kayayyakin su, duk suka saka su a booth ɗin motar kai tsaye suka shiga falon su Ayush, zasu musu sallama Ayush tana kuka haka suka sauƙo falo ita da Junaid tana riƙe da hannunsa, kowa ya hallara a falon mommy taje gaban Ayush tana goge mata hawaye tace "kiyi haƙuri Daughter kema ba jumawa zaki iso mu, Addu'a muke buƙata daga wajenki..."
Ayush tana kuka haka ta rungumi mommy tana faɗin "Allah ya kiyaye hanya mommy amma zanyi kewarku sosai..." itama mommy kuka take ji take kamar ta haƙura da tafiyar..
Daƙer suka raba jikinsu Ayush ta nufi gurin Abbah shima ta rungume shi tace "Abbbaaahhh..." anan ta ƙara fashewa da kuka, daƙer Abbah ya rarrasheta tayi shuru...
Itama Hafzat kuka take na rashin ganin Mommy da Judan ɗinta,
Judan sai faman rarrashinta yake amma taƙi yin shuru, saida mommy tazo itama ta rungumeta tana rarrashinta tukun ta haƙura, kafin su bar falon saida suka sanyawa triplets Addu'o'i tukun, suna fita suka tarar da Uncle Artaff shima yazo yin rakiya zuwa Airport domin shi tin jiya sukayi sallama, Junaid bai samu fitowa harabar gidan ba yana can falo shi da Ayush ya rungumeta sosai a jikinsa kamar zai mayarta cikin cikinsa shima har da ƙwallarsa domin ba ƙaramin kewar ta zaiyi ba,
Bayan sun gama rungume² suka fito kowa a cikinsu jiki ba ƙwari, duk sun shiga motar shi kawai ake jira, kafin ya shiga motar saida ya rabawa Ƴan Aikin da aka kawo kuɗi kowa saida ya bata dubu