Showing 72001 words to 75000 words out of 186041 words

Chapter 25 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53924

Doctor Hasheem yace "amma ki sani idan Junaid yaji labarin ke kika ƙone gidansu bazai barki ba, kizo ki zauna damu anan gidan insha Allahu zan rufa miki asiri, shima Junaid zan san abunda zan gaya masa wanda bazai tuhumeki ba, amma muddin aka san cewa kece kika kashe Doctor Fateema ta hanyar wutar petur toh bakin mutane ma kaɗai ya isheki, za'ayi miki abunda akayi wa mahaifiyarki kema ki koma jeji da zama, idan kin zaɓi haka shikenam..."

Ayush juyowa tayi tazo gaban Doctor tana cewa "zan zauna dakai saboda gudun abunda zan tarar, amma bawai don ina tsoron Junaid ba, so nake na tinkare shi gaba da gaba, zan nuna masa cewa nima jar wuya ce..."
Doctor Hasheem yana tsaye baice mata komai ba, ta kuma cewa "inaso ka ƙira Junaid a yanzun nan ka sanar masa mutuwar mahaifiyarsa ya fara jin raɗaɗi a zuciyarsa kafin a wayi gari..."
Girgiza kai Doctor yayi yace "bazan iya sanar masa mutuwar mahaifiyarsa a halin yanzu ba, amma zan sanar masa cewa anayi masa ƙiran gaggawa! wannan ma zanyi ne saboda tsananin soyayyar ki..."
Ayush jinjina kai tayi sannan tace "Nagode.."
A lokacin kuwa Doctor Hasheem ya ƙira wayan Junaid bugu ɗaya kuwa ya ɗaga domin so yake yaga ƙiran wani daga Nigeria, domin yayita ƙiran wayan mommy a kashe bayan yaga missed call ɗinta,
Junaid ne ya fara yin magana yana faɗin "hello Doctor Hasheem lafiya kuwa? meyake faruwa ne naga ƙiran mommy misalin ƙarfe 1 har three missed call, nabi ƙiran kuma switch up kaima kuma ga ƙiranka yanzu ƙarfe 3, Allah yasa dai lafiya..."

Duk maganar da Junaid yake yi Ayush tana jinsa domin a handspring yake,
Doctor Hasheem kamar bazaiyi magana ba, tsabar fargaba da kuma baisan mezai gaya masa ba, maganar da Ayush tasa ya gaya masa yanada nauyi bazai iya gaya ba,
Junaid ne ya ƙara yin magana yace "lafiya kuwa Doctor Hasheem, yanaji kayi shuru..."
Ayush ganin Doctor Hasheem bashida niyar yin magana yasa ta karɓi wayar cikin yanayin fushi saida ta daidaita kanta tukun tayi magana tana faɗin "Yaya Junaidddd..." cikin kuka ta ƙira sunansa da nuna damuwa.
Gaban Junaid ne yayi mungun bugawa jin muryar Ayush, sai kuma ya tuno da mafarkin da yayi akanta..
tana kuka tace "Gobara ya tashi a gidan mu kuma mommy tana ciki mun kasa ceton rayuwarta, nima daƙer na kuɓuce, na kasa ceton mommy dake ɗakinta a kulle yake ta ciki, gida ya cinye ƙurmus, yanzu haka ina gidan Doctor Hasheem na rasa ina zanje, amma mun ƙira masu temakon gaggawa..." ta ƙarasa maganar tana haɗe fuska da gira...

Junaid ƙamewa yayi guri ɗaya ya kasa motsawa daga baya jikinsa yahau yin ɓari, wayarsa ta kuɓuce daga hannunsa ta faɗo ƙasi, numfashinsa ne yake shirin ɗagewa..


Ayush murmushi tayi bayan ta katse wayar tace "a yanzu kalamai na tamkar mashi yake, kuma nayi nasarar cakar cikin zuciyarsa, a lokacin da ya kashe mun mahaifiyata babu imani a tattare dashi, toh nima a yanzu babu wannan imanin, kuma saiya girbi abunda ya shuka..."
ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye tana riƙe da akwatinta tace "aina zan zauna?..."
Doctor Hasheem kwata-kwata lamarin Ayush ya fara bashi tsoro, gaba yayi yace "biyoni.." haka ta bi bayansa har yakai ta ɗakin da zata zauna, ɗakin kusa da ɗakinsa...

Duk tattaunawar da sukayi Lailah tana laɓe tana jinsu, gaba ɗaya ta girgiza dajin wannan batun, a hankali ta furta "whattt, Ayush kin ƙona mommy ta hanyar dasa gobara? Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, duk rashin imani na bazan iya wannan babban kuskure ba, tabbas biri yayi kama da mutum daman bada zuciya ɗaya take zaune dasu ba, daman ance ka kiyayi mai shuru-shuru domin wata rana zaiyi abunda ƙwaƙwalwa bazai iya ɗauka ba, hmm wai mace mai haƙuri gashi yanzu mommy kin mutu ata sanadiyar mace mai haƙuri, kuma Insha Allahu Ayush saina tona miki asiri bazan bari ayi wannan aika-aika a gabana na ƙyale ba..."
Lailah ta ƙarasa maganar tana zubda hawaye ta shige ɗakinta, mutuwar mommy ba ƙaramin girgiza ta yayi ba...



Ata ɓangaren Junaid kuwa da gudun gaske yayo bakin gate yana ihu tareda faɗin "My mom! My mom!! zata mutu ku temaka mun Please, banaso na rasata ita kaɗai nake da a duniyan nan, ita kaɗai ce gata na Please open the gate...."
Security ne suka riƙe shi sosai, shi kuwa ƙoƙarinsa shine ya fice yaje airport, ihun da yake yi ne yajawo hankulan sojojin hotel ɗin duk suka fiffito,
Sai rarrashinsa suke amma baya sauraronsu, shi dai abunda yake ambato shine mommy! Mommy!! Mommy!!! kunnuwansa gaba ɗaya sun toshe balle yaji rarrashi, gaba ɗaya ya rikice har saida aka masa allurar samun nutsuwa na sojoji tukun ya shiga hankalinsa..

Da sassafe bayan sallar asuba aka bar Junaid ya taho airport da jakarsa, cikin sa'a kuwa a lokacin jirgin zai tashi zuwa Nigeria...


******

Da safe mutane ne a cike tam a ƙofar gidan mommy, ga yanda wuta yayi ta'adi komai yayi ƙurmus a gidan, gidan yayi baƙi ƙirin, masu video sunayi masu ɗaukan photon gidan sunayi, kafin daga baya saiga ƴan jarida da masu rahotanni kowa yana son jin yanda akayi gidan ya ƙone da Doctor Fateema da kuma yarinyar gidan...
Malam Lawan shima yana cikin mutanen hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, wannan al'amarin duk ya zagaya garin Abuja part to part...
Kafin kace mai har an buga jaridu da kuma masu magana a television, magana duk ya zagaya social media...

____________Ayush tana zaune a bakin gadonta a gidan Doctor Hasheem tayi tagumi sai zubda hawaye take,
a haka Doctor ya shugo ya tarar da ita, a cikin damuwa ya shugo yana faɗin "Ayush yanzu maganar mutuwar mommy ya bazu ta ko ina, kuma ana tunanin kema kina cikin gidan wutar tayi gobara, idan har aka san kina raye to zargin zai koma kanki ne, kuma hukuma bazata ƙyaleki ba,
shin kinsan wacece Doctor Fateema kuwa? kinyi kuskure Ayushert, gashi kin sanarwa Junaid cewa kina raye a yayin da kuma mutane suke maganar har da ke wutar ta kama..."

Doctor Hasheem kasa ƙarasa maganar yayi ya dafe goshinsa yana mai jin takaicin abunda ya faru ga kuma indai aka san Ayush tana nan shikenam dole za'a tuhumeta....
Ayush ƙanƙame jikinta tayi tsabar sanyin da take ji, bakinta har wani kakkarwa yake tana kuka tace "ai daman nasan dole za'a tuhumeni, kuma dole zan amsa laifi na duk da nasan nima kasheni za'ayi, babu wata mafita a gareni..."

Doctor Hasheem yana kallonta cike da tausayawa yace "Ayush kuskure na biyu da kika aikata shine sanar da Junaid da kikayi, kinga shi yasan kina raye, amma in badan haka ba ni zansan yanda za'ayi baza asan kina raye ba, niyata shine na yanka miki visa kibar ƙasar nan gaba ɗaya, ni zan ɗauki ɗawainiyar ki har ƙarshen rayuwarki, amma yanzu idan kika tafi dole Junaid zaiyi zargin wani abu..."

Ayush gaba ɗaya ta rasa yanda zatayi, ga wani irin zazzaɓin da take ji...
Doctor Hasheem ne ya miƙa mata hannu yace "taso muje kiyi breakfast nasan kina jin yunwa..."
Ayush kallon tafin hannunsa tayi ta kawar da kanta gefe ba tareda ta miƙa masa hannu ba tace "inaso a kawo mun nan..."
shima kawar da hannunsa yayi yace "Okay don't worry, wait for me..."
juyawa yayi ya fice daga ɗakin...

yana fita ya nufi kitchen anan ya tarar da Lailah tana shirin fitowa da plate ɗin abinci a hannunta, tana kuka, yana ganinta yace "ke kuma fa keda waye kike kuka?.."

Da damuwa a fuskar Lailah tace "mommy Junaid ta mutu, gashi anata nuna wa a tv, gidanta duk ya ƙone..." ta ƙarasa maganar tana kuka shaɓe-shaɓe.
Doctor Hasheem yace "kiyi haƙuri ƙanwata gobara ne ya tashi a gidan basu saniba, dake bacci suke yi..."
taɓe fuska Lailah tayi gira a haɗe tana jinjina kai tace "toh amma meya kawo Ayush gidan nan?.."
har saida zuciyar Doctor ya buga jin wannan tambayar na Lailah, yana sosa ƙeya yace "Ayush daƙer ta kuɓuce ta gudo nan gidan sakamakon rasa inda zata je..."
ta sake cewa "toh Amma Yaya ai naji mutane suna ta faɗin har da ita ta ƙone.."
Yace "eh mutane sunyi tunanin harda ita.." harararsa tayi ba tareda ya saniba tace "toh ai saita fito ta bayyana kanta inba rashin gaskiya ba"
Doctor Hasheem ya kalle ta yace "ke bakida hankali ne, idan ta bayyana kanta ai zargin mutane zai koma kanta ne..."

turo baki Lailah tayi tace "Ohh hooo na gane..." a cikin zuciyarta kuwa cewa tayi "wallahi Yaya ka koyi munafurci yanzu, kuma ba ƙaramin raina mun wayo kayi ba, kuma saina tonawa Ayush asiri ehen ai nayi recorded duk maganganun da tayi...."

Shi kuwa Doctor Hasheem tinin ya shige cikin kitchen saboda kar Lailah ta sake jifansa da wata tambayar again...
Itama ɗakinta ta wuce da abincinta tana ta danne-dannen waya..


*Bayan Awa Biyar5*

Junaid ne ya iso ƙofar gidansu da motar haya da ta ɗauko shi daga airport,
Da gudun gaske ya fito daga cikin motar ya shige gidan, ganin ko ina ya ƙone yasa shi ganin dishi-dishi saida yasa hannu yana murtsike idonsa ko mafarki yake ganin a zahiri yake ganin al'amarin ne yasa ya rufa da gudu yayi cikin ɗakin da gudu duk ginin ya rurrushe yayi baƙi ƙirin,
tsayawa yayi kamar wani zararre ga hajijiyan da yake shirin ɗaukarsa, bai ma lura da mutanen dake wajen ba, baya yayi zai faɗi malam lawan yayi saurin riƙo shi yana faɗin "kai Junaid ka dawo hayyacinka mana, ka nutsu kaji abunda zan gaya maka..."
Shi kuwa Junaid a lokacin ma har ya sume a gurin...

mutanen wajen sun ragu sosai, a yanzun mutanen ba yawa daga malam lawan ne sai Baba maigadi sai kuma maƙobta, duk an gama ɗaukan rahotanni sun tafi...

Malam lawan yana tafe da Junaid a hankali har sukazo wajen motarsa ya kwantarshi a kujerar baya, yace da Baba maigadi shima yazo ya shiga su tafi gidansa, haka malam lawan shima ya shiga yana jan motar a nutse suka nufi gidansa...

Duk wannan hidimar da akeyi kar ku manta Damusa yana tafe a bayan Junaid, kasancewar Malam Lawan yasan da zaman Damusan bai wani tsorita ba, haka shima ya saka shi a cikin motar, amma sauran mutanen gurin duk sun gudu ganin Damusan...


*After 3 months*

Mommy tana ƙwance akan wani katafaren gado, tana ta shan baccin ta bayan farfaɗowa daga doguwar suma,
farkawar ta daga bacci yake da wuya ta soma buɗe eyes ɗinta a hankali, wani irin haske take gani da sauri tasa hannu ta rufe idonta tana ƙoƙarin tashi zaune, ji tayi ance "kodai na tayaki tasar dake?..."
da sauri mommy ta ƙarasa tashi zaune ta waiwayo tana kallon wanda yayi mata maganar,
Ganin mutumin yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfin gaske, leɓɓen bakinta ne suka ɗau rawa murya na kakkarwa tace "shin mafarki nake yi ne ko kuma na mutu da gasken? nidai nasan gidana ya kama da wuta kuma na ƙone a cikin wutan, mijina na iso yanda kake, daman ance duniya ba matabbata bane, yau gani ga mijina wanda na rasa shi tin shekara da shekaru, mijina shin yanzun a aljanna muke ne?..."
ta ƙarasa maganar tana kuka, ta zubawa wanda take kallo ido...

Sarki Raamud dake zaune a bakin gadon da take ne ya kalli Narasimha yace "Baba Narasimha har yanzu ƙwaƙwalwarta bai gama yin saiti ba, a ƙara duba ta mana...."

Mommy tana murmushi idonta akan sarki Raamud ita bata ma lura da Narasimha ba saida ta ɗan waiwaya tukun suka haɗa ido huɗu, ja da baya mommy tayi da sauri ta zaro ido waje kamar zatayi kuka tace "mijina wannan shine mala'ikan da yake gadinka? amma inadai kana samun rahama koh, wannan wani mala'ikan ne?..."

Sarki Raamud ne ya dubeta yace "Amm ki kwantar da hankalinki ba mutuwa kikayi ba, har yanzu kina nan a duniya, wannan ba mala'ika bane ba shima a doron duniya yake..."

Mommy tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login