Showing 60001 words to 63000 words out of 186041 words

Chapter 21 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53914

Munafurr ganin sojojin sun kusan isowa yasa Dabbobinsa suka fara kai musu farmaki,
Dragon's 🐉🐉🐉🐉 ne suka fara tashi sama sunkai ɗari biyu suka nufi wajen rundunan sojojin,
Sojoji kuwa suna ganin abubuwa sun nufosu anan suka fara fitar da bindigoginsu suna harbawa, suma Dragogin haka suke amayar musu da wuta,
ga kuma jegaru suma suna bata nasu wutan, suma sojojin wasu suna harbi wasu kuma suna guduwa, haka motocin sojojin nan suka fara tashi sama suna bom kasancewar akwai bomabomai acikin motocin,
tin daga nan aka fara asarar rayukan sojoji saboda motocin da suke ƙonewan akwai sojoji aciki, waɗanda suke sauran motocin da wuta bai taɓa su ba haka suka rinƙa fitowa daga cikin motocin suna harbi kamar ruwan sama,
suma jegarun an harharbesu domin dragon's da jegaru an harbi sun kai ɗari saboda yawan harbin da ake musu,
Acikin motor gudà kuwa wata soja ɗaya ce take ciki bata fito ba sakamakon ƙafarta daya maƙale a tsakanin ƙarfe da ƙarfe na cikin motar, sai ihu take tayi ganin ko wani mota ƙonewa yake, tana ta ƙoƙarin cire ƙafarta amma ta kasa, sauran sojojin kuwa kowa ƙoƙarin ceton ransa yake ko sauraronta ba'ayi ba, tana cikin wannan halin sai ga Junaid ya nufo gurinta akan doki da gudun gaske zai cetota, kafin ya isa gurin kuwa har wani jegarin ya huro wutan bakinsa kan motar wuta da bom sun haɗu lokaci guda motar ta tashi sama tana kamawa da wuta ga sojar nan tana ciki sai faman kurma ihu take,
A razane Junaid ya ƙwalla ƙiran sunanta da ƙarfin gaske ya furta
"Rumaaanaaaa...."
daiden lokacin motar ta faɗo ƙasi ta dagargaje!
hatta shima Junaid saida ya yi sama shida dokinsa suka doku a ƙasi tsabar ƙarfin boom ɗin daya tashi da motar,
cikin firgici ya ɗago yana ƙiran sunanta "Rumana! Rumanaa!! Rumanaaa!!!...". Rumana kuwa tintinin ta dagargaje ita da motar babu sauranta, motar kuwa sai ci da wuta yake...

wani Dragon ne yazo ta bayan Junaid ya buɗe bakinsa ya amayo masa da wuta lokaci guda Junaid yayi wani irin juyi ya saita bindigarsa ya fasa masa kai da harsashi, takaicin mutuwar Rumana ne yasa ya harzuƙo ya fara harbin jegarun nan kamar mai, gani kake sunata faɗowa daga sama zuwa ƙasa, jegaru sunkai hamsin suka rufo kan Junaid suna hura masa wuta, wani irin juyi Junaid yakeyi yana tashi sama tareda faffasa musu kai, waɗanda suke cikin jirgi kuma tinin an rufe babinsu duk an ƙoƙƙone musu jirgaye da mutanen dake ciki duk da suma sunyi iya ƙoƙarinsu sun kashe jegaru da yawan gaske,
rabin sojoji duk sun mutu daga yaƙin farko, wasu kumá duk sun koma dá báyá sun gudu kuma yawancin su sojoji mata ne waɗanda suka gudu aciki kuwa har da Adity itama ta gudu,
iya waɗanda suke yaƙin ƙalilan ne basuda yawa daga Junaid ne sai Angel itama tana ƙoƙari sosai domin ta kashe dragon's ba adadi..
da haka duk saida suka gama da jegaru da dragon's ya rage babu ko ɗaya, Angel juyowa tayi ganin mutanensu da yawa a kwance babu rai yasa Angel tsorita sannan ta dubi kansu iya waɗanda suke nan bazasu wuce su hamsin ba, kuka Angel ta fara yi tana faɗin "dan Allah kuzo mu juya, kunga bamuda yawan sojojin, kuma bamu san mai zamu tarar a gaba ba..."

Gaba ɗayansu ja da baya suka soma yi sun ɗauki maganar Angel,
Junaid ya dakatar dasu da cewar "lusarai ne idan sunje gurin yaƙi suke guduwa, sojoji babu tsoro a zukatansu saboda haka ku saki jikinku insha Allahu mune da nasara, kamar yanda aka umarce mu damu kawo sarki Raamud haka kuwa zamu kamo shi dumu dumi a hañnu, idan kuwa bai kamu ba sai mu dagargaza masa kai shikenam..."

Daganan suka saki jikinsu, a mata kuwa Angel ce kawai take nan amma sauran wasu sun mutu wasu kuma sun gudu..
Junaid ne ya kalli Angel sannan yace "ina camera?.." irin mai hango abu daga nesa,. tace "gashi nan ta miƙa masa.."
Saitawa yayi a idonsa ɗaya yana hango irin abubuwan da aka tanadar dasu, Junaid jinjina kansa yayi yace "kowa ya zauna akan shirinsa, kowa ya saka hular glass saboda akwai manya-manyan tsuntsaye masu cakan ido, sannan a tanadi boms domin akwai corocodiles da kuma macizai...."
wani ne a ciki yace "Oga ina dai ba Aljanu? inhar babu toh abun zai zo da sauƙi...."
Junaid yace "wasu su shiga Egwa da zaran mun isa saiku fara harbi ku tattaka su da motar, wasu kuma su hau doki tinda akwai sauran dokunan..."
haka kuwa akayi ita Angel motar ta shiga ta miƙe tsaye tayi ready da bindigarta...

Su Junaid sune tafiyar farko domin sune akan dokin, basu fi su ashirin ba masu dokunan,
waɗanda suke cikin motár Egwa kuma an barsu a baya saboda rashin gudun motar amma daga nesa zasu rinƙa harbi har su iso gurin,
Mikiyoyi kuwa haka suka rinƙa tashi sama suna kai musu yakushi da carkwala, sojojin nan haka suka rinƙa harbesu suna faɗowa ƙasi, shi Junaid bai tsaya harbi ba kai tsaye wucewa yayi da gudu yana rataye da bindigarsa ga kuma jakar bom yana riƙe dasu,
so yake ya tsallake gate ɗin domin a rufe yake, shi kuma wanda za'a yaƙa yana ciki, toh shi da Ogan yake so ya yi bada dabbobi ba,
dayazo gurin corocodiles haka ya rinƙa jefa musu bom yana samun hanyar da zai wuce, duk suna kawo masa hari sosai yana kauce musu da haka ya tsallake su, yazo kan macijai suma bom ya rinƙa jefa musu, yana gudu da dokinsa, macizai kuma tsabar na masifa ne haka suke tashi sama suna sarar dokinsa, shi basu samu isoshi ba saboda miƙewa tsaye yayi akan dokin yanda maciji bazai taɓashi ba domin sara ɗaya suke wa mutum,
Junaid daƙer dokinsa ya ƙarasa dashi waran ginin masarautar a yayin da dokin yake shirin faɗuwa tsabar saran da macijai sukayi mishi, a lokacin kuma Junaid yayi wani irin tashi sama kamar mai furawa haka ya yi sama sosai ya kamo wani ƙarfen jikin ginin masarautar wanda yake rabin tsayin ginin, ba ƙaramin dogon gini akayi wa masarautar nan ba, duk tashi saman da Junaid yayi amma a iya rabin ginin ya tsaya, haka ya rinƙa jawuwa yana ƙara yin sama, yanason tsallake ginin...

Sojojin da suke ƙasi kuwa wasu sake baki sukayi suna kallon Junaid, suna kuma mamakin yanda suka ganshi yayi tsalle ya tashi sama kamar ɗan China ko kuma super man ko bad man ko spider man, suna cikin wannan tunanin kusan su goma haka kadoji suka rinƙa kayar dasu suna fata-fata da naman su, yayin da wasu kuma suke fafatawa da mayaƙan dabbobin, Angel ce ta ƙwalla ƙiran Junaid tana faɗin "wannan wani irin garaje ne, ina zaka iya tsallaka katangar nan? zaka iya faɗowa fa kuma idan har ka faɗo sai dai ƙashshushuwanka...." ta ƙarasa maganar itama tana mamakin yanda yahau wannan katangar mai uban tsayi ga tsantsi duk jikinsa..."
wani kada ne yayo kanta tareda buɗe bakinsa zai rufa mata a fusace Angel ta wurga masa bom a cikin bakinsa nan danan corocodile ya dagargaje haka ta cigaba da faffasa musu kai da harsashi, wasu kuma suna jejjefa musu bomabomai,

Junaid gaba ɗaya ya gaji sauran masa kaɗan ya isa saman katangar, yana riƙe da ƙarfe wanda yake riƙe da katangar, yana sauƙe numfashi ya sunkuyar da kansa ƙasi yana kallon abunda ke faruwa ata ƙasa, zaro ido yayi waje cikin firgici ya furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, oh my God..."
Ganin duk anyi fata-fata da sojojinsu iya mutum uku ne kawai suka saura, daga Angel ne sai maza biyu sune suketa faman faɗa, dan ma dabbobin duk suma sun ƙare corocodile ɗaya ne ya saura sai macijai dake sunfi sauran yawa amma suma an ƙarar da fin rabin su, sojoji maza biyun ne suketa aikin jefa musu bom a macijen nan, ita kuma Angel crocodile wanda ya rage ne yayo kanta da zafinsa, ga babu bom a hannunta sannan bindigarta ya faɗi babu halin ɗauka yana tsakiyar macijai,
Junaid kallonta yake domin shikam har ya fidda rai akan rayuwarta,
Crocodile ɗin ne yayi sama tukun ya faɗo mata a kanta ya danneta bakinsa a saitin wuyanta zai datsa mata wuya da haƙwaransa masu kaifin bala'i,
Haka zuciyar Junaid yake bugawa da ƙarfin gaske, jikinsa na rawa kamar zai faɗo ƙasa,. zuba wa crocodile ido yayi wanda ya rufe Angel gaba ɗaya ba'a hangota, ganin corocodile baya motsi abun ya ɗaure masa kai, sai can bayan wasu mintuna idon Junaid still yana kansu yaga crocodile yana motsi lokaci guda kuma saiyaga an ture shi gefe ga jini yanda yaketa tsiyaya daga wuyansa, Angel ce ta tureshi gefe ta tashi zaune tana jan numfashi ga duk jinin crocodile ya ɓata mata jiki,
Junaid daga nesa yake kallonta cikin mamaki yace "how comes?..."
ba tareda ta jiyoshi ba domin yayi nisa da ginin sosai..
Tunani ya shiga yi yanda abun ya kasance wato a lokacin da crocodile ya rufo kanta ta rigada ta cire wuƙar jikin takalminta ta cakawa crocodile a wuya, bataji ciwo ba sai kurzuwan da tayi...
Junaid murmushi yayi ya furta "gud jaruma ta..." da ƙarfin gwiwarsa ya cigaba da yin sama,

suma sauran sojojin da suka rage su biyun murna sukayi ganin Angel bata mutu ba, domin tana temaka musu sosai, babu wanda zai iya yin faɗan da tayi...
Angel hango bindigarta tayi a cikin macijen kamar wanda ake ƙara yawansu, ɗaya daga cikinsu ne ya kalli Angel a tsorace yace "Madam bom fa ya kusan ƙarewa sauran guda goma kuma naga macizen da sauransu,
Angel ta miƙe tsaye tareda faɗin "zanyi maganinsu kuwa yanzu zasu ƙare..."
ta karɓi sauran bom ɗin tace dasu "ku fara aiki da bindiga, Ni kuma zanji dasu da wannan bom..."
duk faɗan nan da takeyi da jaka a bayanta ta sauƙe jakar ta ciro takalmin mai taya, sannan ta cire takalmin ƙafarta ta sanya maitayar ta miƙe tsaye da jakar bom a hannunta ta rufu kan macijen nan da gudun gaske tana mummurƙuse su da takalmin tayanta tareda jejjefa musu bom, da zaran maciji ya kawo mata sara saita zamar da ƙafarta tana wasan gudun takalmin taya akansu...
maza biyun nan haka suka tsaya suna kallonta ga yanda take bada action Kamar a film, shima Junaid kallon ƙasa yayi yaga irin abunda Angel takeyi smile kawai yayi a daiden lokacin har ya isa sama ya zauna yana hutawa,

cikin ƙanƙanin lokaci Angel ta gama da macijen nan tas sai gawarwakinsu dake wajen kaca-kaca,
tana gamawa tazo ta cire takalmin tayan ta mayar cikin jakarta sannan ta maida asalin takalminta na soja,
suna tsaye suna jiran Junaid ya haura ya buɗe musu gate su fantama cikin masarautar domin ta ciki aka kulle,
Junaid igiya ya ciro shima daga cikin jakarsa ya ɗaure a jikin ƙarfen saman gini sannan ya kama igiyar nan ya fara sulalowa ƙasi ta cikin masarautar haka har yaje ƙarshe, yaji babu alamun motsin mutum ko ɗaya, hannu yasa ya buɗe gate ɗin da ƙarfin gaske yake tura gate ɗin zai buɗe, suma su Angel ɗin tafowa sukayi da gudu suka sa hannu kowa yasa ƙarfinsa aka buɗe gate ɗin gaba ɗaya,
Bayan sun shige cikin masarautar tsayawa sukayi suna tunanin ta yadda zasu fara kutsawa ciki,
Junaid yace "kowa ya riƙe makaminsa da gaske saboda wannan yanada hatsari sosai..."

Ɗaya daga ciki yace "dan Allah kasa a turo mana wasu sojojin, mu kaɗai bazamu iya da wannan ba, mu huɗu ne fa kawai muka rage..."
Junaid yace "taya za'a turo su bayan babu waya a hannun mu duk sun faɗi..."

********

Sarki Raamud kuwa shida matarsa duk sun ruɗe jin tashin bomabomai da ƙarar bindiga,
Uma Bara'at kam sumar ta sau uku jin halinda ake ciki ga tsohon ciki,
tana kuka tareda faɗin "shikenam mun mutu an kawo mana farmaki, nasan bazamu bar nan a raye ba..."
Sarki Raamud yana rarrashinta yace "ki kwantar da hankalinki tabbas ni sukazo farmaka amma kuma akwai wanda zai tari faɗan, yanzu haka nasan yaƙin ya koma kan Munafurr..."
Daƙer ya rarrasheta tayi shuru, suna cikin wannan halin suka ji an buɗe ƙofa, ganin Munafurr ne yasa duk suka razana, kafin suce komai Munafurr ya riƙo wuyan sarki Raamud ya ɗagashi sama da hannu ɗaya sannan ya cabko wuyan Bara'at itama ya ɗagata sama tana lilo da sawayenta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login