Showing 168001 words to 171000 words out of 186041 words
su haddace amma kowa da nashi salon yanda zai gudanar, ba iri ɗaya bane rubutun, kamar debate kenam....
Kowa acikinsu sai ya ɗau yin murmushi alamun bazai gagaresu ba...
A cikin kwana uku nan kowa yayi bita sosai, sun haddace wannan rubutun paper gaba ɗaya da temakon iyayensu, domin kusan kwana suke suna karatu,
Areeph Daddynsa ne yake taya shi karatun, har kusan kwana suke suna karatun, ita kuwa Ayush bata ma arai ba domin bazata iya kwana tana taya yaro karatu ba, tinin bacci yake ɗaukanta...
Shima ata ɓangaren Rapeekh Abbansa ne yake tayashi karatun,
Yau ake ranar Debate kowa ya hallaru, ga part ɗin malaman makarantar daban, part ɗin ɗalibai daban, haka kuma part ɗin iyayen ɗaliban suma daban, ga kuma gurin da masu gasar zasu tsaya, Rapeekh ne first ɗin ƙira ya fito, yaron ya fito da zafinsa saida ya fara gabatar da kansa tukun ya fara sabarbaɗo turanci masu ma'ana, kuma yabi kan ƙa'idojin rubutun idan akazo wajen comma saiya dakata haka yaɗau tsawon awa guda tukun ya tsaya a gurin p-stop tukun nan ne kuma ƙarshe, yaron yasha tapi agun al'ummar wajen, kowa yabon Rapeekh yake, kuma ya burge mutane da yawa, ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba, karatun turanci kamar a bakinsa aka ƙera shi,
Abbansa da Mamansa murna kamar bazasu mutu ba, da sauran ƴan gidan Daddy da Ammy da kuma Lailah duk sun halarci gurin...
Anzo kan Areeph kuma jikinsa ne yayi sanyi ganin yanda aketa tapawa Rapeekh, gani yake kamar bazai samu masoyan da zasu tapa masa har haka, wasu har da hura wusir wasu kuma ihun farin ciki suke acikin ɗaliban, abunda yasa jikinsa ma ya ƙara yin sanyi saboda Rapeekh daman ya fishi masoya domin yaro ne mai faran-faran acikin mutane, kowa nashi ne, shi kuma Areeph sam baya shiga cikin mutane balle su shaƙu, amma bai damu da wannan ba saboda kowa ƙoƙarinsa ne zai fidda shi bawai yawan mutane ba,
ƙiran sunan Areeph aka dinga yi amma yaƙi fitowa, Ogah Junaid kamar ya nitse ƙasi haka yake ji gashi gurin zamansu ba ɗaya ba balle yasa shi dole ya fita, Ayush Addu'a ta shiga yi masa ido a rufe, wasu daga cikin ɗaliban har sun fara cewa "Rapeekh ne ta cinye shine yayo na ɗaya, gashi Areeph kam saboda bai iyaba ya kasa fitowa...". haka wasu suka shiga yimasa dariya, Areeph kansa a sunkuye ko ɗagowa beyi ba balle yayi niyar fitowa, saida shugaban makarantar ya tashi yaje har gabansa yace "Areeph meya farune ka kasa fitowa kodai bakayi karatu ba?...". shuru baiyi magana ba, akayi dashi ya fito yaron nan yaƙi, Ogah Junaid zuciyowa yayi ya miƙe tsaye zai bar makarantar Ayush tayi saurin riƙo hannunsa kanta a sama tana kallonsa tace "dan Allah kar ka tafi ka barshi a wannan halin, kaje ka same shi kaji meye matsalarsa na roƙe ƙa..."
zamar da hannunsa yayi ba tareda ya furta komai ba ya nufi yanda Areeph yake a zaune still kansa a ƙasi ya kasa ɗagowa, Junaid durƙusawa yayi a gabansa ya riƙo hannun Areeph sai a lokacin yaji tsananin tausayinsa ya kama shi, a hankali ya furta sunansa "Areeph...."
Jin muryar Daddynsa yasa ya ɗago kansa a hankali suka haɗa ido gaba ɗaya fuskarsa ya jagwalgwalewa da hawaye, har idonsa ya canza launi, Junaid ya cigaba da cewa "kada ka karaya yaron kirki, kaima ka fita da zafinka insha Allahu zakayi nasara, ragon namiji ne yake karaya dayin abu, ka tashi ka fita kamar Damisa kaje duk ka hargutsa taron da zazzafan turancin ka, jarumi na tashi mana, kar rashin yin baccin mu ya tashi a asara please my Son...."
Lokaci guda Areeph yasau ƙayataccen murmushi tareda goge hawayen fuskarsa ya tashi shima ya fita gaban taron, fitowarsa shima aka fara masa tapi tin kafin ya fara magana, hakan ya bashi ƙwarin gwiwar soma gabatar da kansa sannan yayi gaisuwa ta yaren turanci daga nan ya miƙi maganar sa har yanda ya dosa, shima ba ƙaramin turanci yayi ba, kamar ba ɗan Nursery school ba, hakan ma ba a Nigeria ba, domin shima Areeph yayi masoya sosai jin yanda yake suburbuɗo turanci shima har yakai ƙarshe, ihu da tapi kamar baza'a daina ba,
Wannan result ɗin da za'a basu tin daga yanzu kowa zai karɓi sakamakonsa,
Areeph da Rapeekh kowa acikinsu yana ɗaukin a bashi sakamakonsa domin ya duba marking nawa ya samu,
Cikin rashin sa'a sai sukaga D same marking again, yanzun ma Bracket ne...
Haushi kamar zai illata Areeph har da kukansa, shima Rapeekh kuka yake saboda baiso haka ba....
(ikon Allah yanzu acikinsu babu wanda zaije ƙasa yabarwa wani kenam?....)
Areeph suna komawa gida da ƙatuwar jakarsa yayi gudu ya shige ɗakinsa yasa sakata,
A ranar wuni yayi a cikin ɗakin bai fito ba har dare, Ayush ta bubbuga ɗakin tana ƙiran sunansa amma yaƙi buɗewa, shi wai yayi fushi ne hakan,
Shima Junaid yayi ya buɗe amma yaƙi har Junaid ɗin ya haƙura yace "yunwa ma zata fito dakai ai..."
har duk suka kwanta, cikin dare Ayush tazo bakin ƙofar tana bubbugawa a hankali tareda ƙiran sunansa amma yaƙi buɗe wa har zuwa yanzu,
A haka har akayi tsawon kwana uku amma Areeph bai buɗe ba,
Gaba ɗaya hankalin Ayush ba ƙaramin tashi yayi ba, tayi kukan har ta gaji, abun da tsoro ace yaro ya rufe kansa har tsawon kwana uku ɓaci ba sha, har ta saddaƙar da ya mutu a ciki, tsawon wannan kwanakin itama batasa komai a cikinta ba,
Ogah Junaid yayi da ita akan taci abinci amma taƙi sai cewa take "taya yarona baici komai ba kuma Ni na ci impossible wallahi..."
tayi tayi da Junaid akan yasa a ɓalla ƙofar ɗakin a dubo mata yaro amma shima yaƙi sai cewa yake. "ki barshi yunwa zata fito dashi..."
tana kuka taje ta samu ɗaya daga cikin Bodyguards ta ƙirashi akan yazo ya ɓalla mata ɗakin Areeph, amma Ogah Junaid yaƙi barinsa ya shugo masa ɗaki, ganin babu abunda zata iya yi yasa ta faɗi ƙasi tana ihu na gaske,
Hafzat itama kuka take saboda ba'a San halinda Areeph yake ciki ba, Angel da Amrish ganin yanda Mommynsu take ihu yasa suma suka fashe da kuka,
★★★★★ *DAY 4*
Ogah Junaid ya shirya yau zaije ziyartar abokansa can headquarters, kwatsam saiga Ayush ta dirƙo a gabansa kamar wata mai Aljanu duk tabi ta rarrame tayi duhu yana shirin fita tasa hannu taci ƙwalar rigarsa, zaro ido yayi yace "what? Yushert kinsan abunda kika aikata kuwa?..."
tana harararsa tace "abunda yafi haka ma zanyi maka indai bakaje ka buɗe mun yaro ba..."
Girgiza kai yayi sannan yace. "Ni na kulle shi ne?...". Tace "idan bakai ka kulle shi ba ai key ɗin ɗakunan gidan nan a hannunka suke meyasa baza kaje ka buɗe ba, nasan yanzu haka ya fita hayyacinsa in ma bai mutu ba...". ta ƙarasa maganar tana kuka..
ganin yanda taci kwalarsa yace "ok muje to na buɗe ɗakin .." yayi hakan ne saboda bayaso raini ya shiga tsakaninsu kuma daman yau yanada niyar buɗe ɗakin....
Binciko key ɗin ɗakin yayi suka nufi ɗaikin Areeph, Ayush kamar zata kife tsabar gaggawa, suna isa gurin yasa key ya murza ƙofar saiga ɗakin ya buɗu,
Ganin Areeph yasa Ayush razana ta zaro manya-manyan idanuwanta baki a sake tana kallon wajen da Areeph yake,
Shi kuwa Areeph yana nan zaune saman gadonsa duk ya ɓata ɗakin da ledar Cake dasu Biskit da lemon juice dasu Bobo, har da Nutric Milk, duk yanda ya cicci su da shaye-shayen lemuka kala-kala,
Yanzu ma haka yana kan tsakiyar gadonsa yana kan cin Cake ga lemon juice a gefensa yanda yaketa korawa, da zarar yaji bacci saiya kwanta yayi baccinsa, ga toilet ɗinsa a cikin bedroom bashida wata matsala ....
Ayush dasauri ta kalli Ogah Junaid wanda shi kuma ya jingine kansa da jikin ƙofa sai dariya yake tayi domin tin farko yasan lokacin da Areeph ya jijjido waɗannan abubuwan ciye-ciyen kawai dai yayi shuru ne, kuma dalilin da yasa bai damu ba kenam....
Kallon Ayush yayi yace "meye kike kallona, ke kin hana cikinki abinci shi kuma yana cikin ɗakinsa wuni yake yana ci da sha idan ya gaji ya kwanta yayi bacci, duk a cikin fushin ne ..." ya ƙarasa maganar tareda barin wajen yana faɗin "nidai na fita saina dawo....."
Gobe za'a sake yiwa Areeph da Rapeekh jarabawa again amma saidai wannan exam ɗin akan Mathematics ne masu zafin gaske duk wanda yaci acikinsu shine gwarzo kuma akwai kyaututtuka na musamman,
Wannan karan kam dole ɗaya zai faɗi ƙasi, bazasu iya cinyewa gaba ɗaya ba, koda basu cinye gaba ɗaya ba amma da zarar ɗaya ya wuce ɗaya da marking ɗaya toh shikenam shine wanda ya cinye....
(Toh pah Su Areeph masu fushi😂😂😂))))......
(Toh kuma yanzu dai ware zaici wannan exam ɗin. Sai Allah,)
Ina masoyan Areeph
Ina kuma masoyan Rapeekh??
Su fito suyi magana.....
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 91 to 95
Da gudu Ayushert ta ƙarasa shugowa cikin ɗakin tana ambatar sunan Areeph tareda faɗin. "Areeph yarona kana lafiya, ka tsoratar dani sosai, meyasa zaka azabtar da Mommynka haka, nayi kewar ka..." ta rungumo shi tana kuka, shi kuwa Areeph sai ƙara tura biscuit yake a bakinsa, yace "Mommy ni inason na cinye Rapeekh a jarabawa...". Ayush tace "ka kwantar da hankalinka gobe za'ayi muku jarabawar Mathematics, kuma inaji araina kaine zaka cinye, amma kar ka sake rufe kanka a ɗaki kaji ko?..." Areeph ya jinjina kai yana kallon Ayush, ita kuma ganin biscuit da lemon baja² yasa ta ɗauka ta ɓare tana turawa a bakinta kamar kuncen yunwa, domin ba ƙaramin yunwa take ji ba..
Ogah Junaid wuce wa yayi headquarter zai kai musu ziyara, an daɗe ba'a haɗu ba, kuma zuwa wani satin zai bar Nigeria, sunyi farin cikin ganinsa sosai...
A washe gari Areeph da Rapeekh sun zana exam ɗinsu na Mathematics kuma shine na ƙarshe, Mathematics yayi wahala sosai domin duk cikinsu babu wanda kansa bai ɗau zafi ba, don ko ɗan jami'a iya kacin exam ɗin da za'a masa kenam, duk da babu wanda ya cinye jarabawar gaba ɗaya amma an samu wanda ya fi ɗaya da marking ɗaya, saida akayi tsananin bincike akai tukun aka samu cewar Areeph yafi Rapeekh da marking ɗaya da rabi, ai kuwa a ranar Areeph farin ciki kamar kamar dai, Rapeekh shima duk da baici exam ɗin ba amma yayi farin ciki sosai ganin yanda Areeph yaketa tsalle yana murna shima saiya tsinci kansa cikin murnar abokin takararsa ya samu abunda yake so, sam Rapeekh baiyi baƙin ciki ba, saima taya shi murna da yayi, da haka har aka bawa Areeph kyaututtuka manya², shima Rapeekh an bashi wani abu amma bai kai wanda aka bawa Areeph ba,
Shima Areeph acikin kyaututtukan daya samu ya raba biyu ya bayarwa Rapeekh rabi shima ya riƙe rabi dake yaran ba masu son abun duniya bane, sunada dukiya sosai shiyasa basu wani damu akan kyautar ba, burinsu shine ɗaya acikinsu yafi ɗaya marking shine gwabzawar da suke tayi....
★★★★★★
Part of the kingdom..
Babban masarautar sarki Raamud ba ƙaramin tsaruwa yayi ba, domin an ƙara tsara shi, an mayar da masarautar part biyar, part ɗin farko shine yake ɗauke da Babban fadar sarki, daga nan za'a wuce cikin falon sarki Raamud da manya-manyan kujeru masu kyan gaske, ga babban plasman a manne da bango da wani glass table a tsakiyar kujeru, ta gefe guda kuma ƙaton dinning table ne da kujerunsa guda 12 a jere, daganan sai upstairs mai part biyu hagun da dama, upstairs na dama shine zai kai ka har bedroom ɗin sarki Raamud, upstairs na hagun kuma zai kai ka ne har ɗakin mommy....
Part na biyun gidan kuma saika wuce fadar sarki tukun a ƙara buɗe gate na biyu shine zai kaika part ɗin Ogah Junaid da iyalansa, kamar yanda na sarki Raamud yake haka shima nasu yake, daga nan sai anyi tafiya mai nisa an sake buɗe wani gate na uku sai kuma part ɗin Uncle Artaff wanda aka tanadar masa tinda shima yanada gado acikin masarautar shima kamar yanda aka tsara nasu part ɗin haka akayi wa nashi, daga nan sai babban hospital dake cikin masarautar wanda a wannan part ɗin Narasimha yake, shine mai musu magani da zaran basuda lafiya, sai kuma wani part na wasan yara, da kuma wajen buga ball, acikin masarautar akwai wani gate na ɓangare guda wanda ana buɗe shi sai lambun kayan fruits da vegetables da bishiyoyi mango da casho da banana da sauran abubuwa,
A wani part kuma akwai gate ɗin da idan aka buɗe wajen ma'ajiyin Dokunan sarakuna ne da wasu kayayyakin yaƙi, ga ta ɓangare guda kuma jerukan motoci ne na alhurma kala-kala...
Ga wasu karnukan turawa da aka zuba a kowani part na cikin masarautar, masu gadin masarautar kuma wasu manya-manyan sojojin Amurkawa ne da turawa, ga wasu munanan Bodyguards masu ƙarfin gaske da manya-manyan bindigunsu, mata masu ayyukan gidan, an nemosu ne ba ragwaye ba. Waɗanda kullum suna cikin Aiki,
Mommy ko ɗaga tsinke batayi acikin masarautar nan, komai yi mata akeyi da umarnin Sarkin amma ba'a son ranta ba, saboda ita ta saba da motsa jiki da wasu ayyukan gida, mommy tayi ƙiba sosai ta ƙara