Showing 12001 words to 15000 words out of 186041 words

Chapter 5 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53934

faɗin "ni sa'ar ki ce da zaki mun tsuka? na fahimci tinda kika zo kanki yake gigiwa..." duk wannan maganar Aditi ta juyar da shi zuwa yaren turanci saboda Lailah tafi ganewa,

Lailah kama bakinta tayi ta fara kwarara ihu a wajen jinin bakinta duk ya wanke mata hannu, Doctor Hasheem ne ya riƙo Lailah yana kallon Aditi yace "ya haka baiwar Allah metayi miki?.."
Aditi ta kalle shi sannan tace "baka ji menace bane?..." kafin Doctor Hasheem ya sake yin magana Lailah ta katse shi da cewa "wallahi tallahi Yaya bada ita nake ba, kawai dai zaluncin ta ne a kusa, ni ba abunda nayi mata ta fasa mun baki naaaa..." kuka take sosai tana riƙe da bakin, Doctor Hasheem yace "it's okay Auta muje na wanke miki kinji koh, don't worry.."
har sunyi kusan fita Lailah ta juyo tana kallon Aditi tace "munguwa, azzaluma, bad girl..." Aditi ranta yayi mungun ɓaci dajin kalaman Lailah da gudu ta taro su tareda fincikar Lailah tayi wurgi da ita ciki, ta ɗagata sama ta ƙwanɗarata a ƙasin tiles, Lailah kuka ɗaya tayi ta suma a wajen,
Doctor Hasheem a fusace yayo kan Aditi, da sauri Aditi ta fitar da bindigarta ta saita masa a goshi tareda kunna kunamar bindigar tana faɗin "idan ka sake matsowa saina fasa maka kayi da harsashi, kuma idan na kashe ka na kashe banza a bola, i am a girl army..." ta ciro katinta ta nuna masa still bakin bindigar yana saite akan sa,
Doctor Hasheem ganin ita soja ce yasa ya risina ya ɗaga hannunsa sama yana faɗin "kiyi haƙuri ban saniba, insha Allahu za'a kiyaye gaba.."
sauƙar da bindigarta tayi ƙasa tana hura hanci ta nemi guri ta zauna,
shi kuwa a tsorace ya ɗauki Lailah suka yi waje,
Angel tana hararar Aditi tace "meye haka kikayi Aditi? anya kuwa kinada hankali?..." kafin Angel ta rufe baki Aditi ta kwasheta da mari tana huci,
Angel zabura tayi zata miƙe tsaye domin ɗaukar fansa mommy tayi saurin dakatar da ita tareda cewa "a'ah Angel kiyi haƙuri ki barta dan Allah, kindai san halinta daman bata da haƙuri ko kaɗan, kar kema ki biye mata kinji ko?.."
komawa tayi ta zauna tace "Allah mom da kin barni na koya mata hankali wallahi..." mommy tace "ke dai ki shareta kawai..."
Aditi shuru tayi tana jinsu amma saidai da hausa suke maganar bata jin yaren..

Rumana kam tana zaune ko kallon yanda suke bata yiba, saima ɗaukar jakarta datayi ta miƙe tsaye tana faɗin "let me go home, i need to rest.."
Mommy ce kawai ta amsa mata tace "ok shikenam Allah ya kiyaye hanya sirikata.." ficewa Rumana tayi tana taku da takalminta mai shegen tsini...

Ayush kam tana kwance akan ƙirjin mommy tana kallonsu sai gani sukayi Aditi ta janyo ƙafar Ayush zuwa ƙasa tana cewa "kina kallon mom ba lafiya kin wani kwanta mata a jiki, ke jaririya ce? ki tashi ki zauna ko kuma nayi miki dukan tsiya a waran nan..." da sauri Ayush ta tashi zaune kamar zatayi kuka, ita tsoronta kar tayi mata dukan da tayiwa Lailah wanda har ta suma, Angel tana kallon Aditi daga bisani kuma ta girgiza kai tana mata kallon marar hankali ba tareda tace komai ba ta kawar da kanta gefe...
Itama mommy kallon Aditi kawai take tana murmushi aranta tana faɗin "oh haka ke kuma kike da masifa, Allah ya shirye ki..."

suna cikin wannan halin saiga Junaid ya shugo hannunsa riƙe da ledoji na siyayya daya yo, yana shugowa yace "lafiya kuwa yana ganku kunyi shuru..."
Angel ce ta buɗe baki zatayi magana ta sanar masa abunda Aditi tayi, mommy tayi saurin tarar yawunta gurin cewa "babu komai.." yace "ha'a yana ji kuna haɗa baki waran yin magana?.." saida ya ajiye ledojin hannunsa akan glass table tukun ya kalli yanda Angel take yace "my Angel meya farune?.." turo baki tayi tace "ina dai Aditi ce.." tayi maganar tareda nuna ta,
Aditi jin Angel ta ambaci sunata ta waiwayo tana mata kallon up and down tace "what's wrong..."
itama Angel hararar ta take tace "bansani ba munafuka.." Aditi da sauri takai hannu zata naushi Angel, Ogah Junaid yayi saurin riƙe mata hannu yana faɗin "ke ke ke kinga matsala ta dake kenam Aditi, saurin kaiwa hannu meye matsalarki ne kam?..."
fuzge hannunta tayi tana fushi ta miƙe tsaye sannan tace "ai daman kafi sonta, shiyasa kake nuna warayya a tsakanin mu..." tana kaiwa karshe tayi ficewarta a cikin ɗakin, Junaid yana ƙiranta amma ko ta waiwayo haka tayi tafiyarta,
Angel itama surutan ta take tana faɗin "ai wallahi da ka barta ta naushe ni saidai uwarta ta haifi wata amma babu abunda zai hana na harbeta.." Junaid yana jin abunda Angel take faɗa amma ya sharar da ita sai cewa yayi "ina Rumana?..." mommy tace "ta tafi gida.."
sauƙar da ajiyar zuciya yayi tareda kaiwa idonsa kan Ayush wacce tin shugowar Junaid kanta ke ƙasi ta kasa ɗagowa...

Mommy kallon yanda Angel take tayi tace "Angel da kin koma gida kema kinyi mana girki saboda masu zuwa ganin jikina, nima anjuma kaɗan zan koma gida, ai na samu lafiya...."
Angel ta amsa mata da "toh mommy sai kun dawo, bari na hanzarta na koma gidan.." miƙe wa Àngel tayi tareda yi musu sallama tayi tafiyarta..

Mommy ta kalli Ayush tana shafa kayinta tace "Dota waya taɓa mun ke naga kamar kinyi kuka?..." a hankali Ayush tace "babu komai mommy, kawai na damu da ganinki a asibitin nan a mazannin marar lafiya..." murmushi mommy tayi sannan tace "ba komai Ayush ai naji sauƙi yanzu kam sai komawa gida.."
Ayush tana hawaye ta kalli mommy tace "dan Allah mommy kiyi hakuri, na wargaza miki lissafi bansan ke kika haɗa baikon nan ba, da bazan bijire ba kuma a lokacin a tsorace nake da Yaya Janaid...." mommy ce ta katseta da cewa "kinga kiyi shuru maza kar kina tunowa da abunda ya wuce, idan har Junaid mijinki ne babu makawa sai anyi auren nan, idan kuma ba shi bane mijinki ba ko mai mukayi baza'a taɓa yin auren nan ba, don haka mahakurci mawadaci ke dai ki cigaba da addu'a, insha Allahu Allah zai zaɓa miki wanda yafi alkhairi my Dota..."

Junaid yana zaune akan kujerar d'akin yana jinsu amma baice musu komai ba, sai ma daddannan wayarsa da yake yi....

Bayan wuni guda Angel ta kammala girkinta ta gyara gidan tsab, yanke shawara tayi cewar zata je gurin swimming pool taje tayi wanka acan, zagayawa tayi ta baya, wani ɗanƙareren swimming pool ne ya tsaru sosai, ruwan mai colour green, tarar da Rumana tayi a wajen tana zaune a kujerar wajen da ɗan ƙaramin table a gabanta ga lemuka a jere, saidai babu kaya ajikinta daga ita sai ɗan pant da kuma rigar breziya, jiki fari sol da ita sai karatun wani ɗan littafi take a hannunta....

ta ɗayan ɓangaren kuma Àdhiti ce a cikin ruwa da breziya sai pant a jikinta sai wasan ruwa take, tana tafiyar kifaye...
Àngel ɗan tsuka taja ganin duk sun tare duk anan wajen ko aikin gidan basu tayata ba, da kamar zata juya kawai ta fasa itama ta cire kayan jikinta ta zauna daga ita sai short nicket,
tana zuwa tayi tsalle ta faɗa cikin ruwan saida Aditi ta nutse cikin ruwan sosai tsabar tsallen da tayi a cikin ruwan,
itama Rumana tana zaune agefe tana karatun littafin ta taga ruwa duk ya jiƙe littafin sakamakon tsallen da Angel tayi a cikin ruwan,
Rumana rarumar glass cup tayi akan table saida ta saita kan Angel tukun ta wurga mata a tsakiyar kanta, da sauri Angel ta juyo tana riƙe da kanta tace "kuturun uban cannn...." bata ƙarasa maganar ba taji Aditi ta shaƙo wuyanta ta baya,

daƙer Angel ta samu ta kuɓuce a hannun Aditi ta fito tana maida numfashi ta nufi gurin da Rumana take a zaune ta hankaɗata ƙasi ita da kujerar,
Aditi ce itama ta fito daga cikin ruwan da gudu ta nufo yanda Angel take ta kamata da kokuwa suka fara kirɓawa juna naushi, Rumana itama tasowa tayi ta shiga suka fara faɗa kowa wanda yake jin haushi yake daka,
a wannan lokacin Aditi tayi nasarar gurɗa ƙafar Angel sakamakon kwantar da ita datayi ƙasa ta kama ƙafarta ta murɗe mata shi, har saida Angel ta saka ƙara sosai tana kwance ta kasa motsa ƙafar,
Aditi ganin Rumana tana ƙoƙarin cakumo ta yasa ta zari ƙwalbar lemo ta rausawa Rumana a goshi, nan da nan jini ya fara kwararowa daga goshin Rumana, baturen mutum da baya son ganin ciwo a jikinsa hakan yasa Rumana faɗuwa ta sume a gurin...

Aditi tashi tayi tana huci tareda faɗin "ku taso mana inadai kun raina ni ko? toh zan nuna muku ni mahaukaciyar soja ce, ku taso..." tana haki da ƙarfi-ƙarfi tana fitar da maganar daƙer kamar wacce tayi aikin ƙarfi..

Junaid ne yazo gurin yana faɗin "ku kuma kunzo nan duk kun tare guri ɗaya kun bar falo babu kowa....." bai kai ƙarshen maganarsa ba yaci karo da Rumana kwance ko motsi babu ga kuma jini ya wanke mata fuska, yakai idonsa kan Angel sai juye-juye take tana riƙe da ƙafarta tana kuka,
kallon yanda Aditi take a tsaye tana huci yayi bakinsa na kakkarwa tsabar ɓacin rai yace "meya faru dasu?..."
juyowa tayi tana fuskantarsa hannu a dunƙule tace "nine nam nayi aiki akansu, idan kuma kaima kana son tabbatar da aikina kazo ka ga..." tana tsalle irin na ƴan dambe...

da sauri yayo kan Rumana ganin tafi jikkata, da gudu Aditi ta shige gabansa tana faɗin "babu wacce zaka taɓa" tureta yayi gefe sannan yasa hannu zai ɗauki Rumana sai ji yayi Aditi ta kirɓa masa naushi a baya, cikin ɓacin rai ya juyo tareda zabga mata mari, zata kawo masa naushi kuma du ya riƙe hannayenta biyu da hannu ɗaya ya zaro ƙafafunta da ɗayan hannun ya cillata cikin ruwan swimming pool,
ya juyo ya ɗauki Rumana a kafaɗarsa, sannan ya miƙawa Angel hannu ta tashi daƙer ya riƙe kunkuminta da ɗayan hannunsa, ɗayan kuma yana riƙe da Rumana yanda ya saɓata a kafaɗa haka suka nufi falon gidan, Ańgel tana ɗingishi daƙer take takawa..

suna shiga cikin falon mommy da Ayush duk suka miƙe tsaye daga zaune,
Mommy cike da mamaki tace "subhanallah ya haka kuma?..." ganin yanda suke ba kaya a jikinsu ko wacce daga pant sai breziya, Ayush kam rufe idanuwanta tayi da hannayenta biyu,

Junaid ne yace "mom please ki biyo mu can medicine room kiyi treat ɗinsu, sunji rauni sosai...."
Mommy ce ta taɓa Ayush tana faɗin "kije ɗakunansu ki dubo musu kayan sakawa yanzun nan.." tana kaiwa karshe tabi bayan Junaid da sauri...

Bayan Ayush ta jido musu kayan sakawa tana fitowa falo saiga Aditi ta shugo falon ita da kayanta a jikinta domin tin acan ta sanya su, tana zuwa ta wuce ɗakinta tana jan zuciya ga idonta yanda sukayi jaa.....

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 009 ➡️ 10


Junaid da sauri ya fito falo ya nufi yanda frig yake ya buɗe tareda ɗaukar ruwan faro mai sanyin gaske ya koma yanda ya fito,
ita kuma Ayush bayan ta kai musu kayan komowa tayi falon ta nemi guri ta zauna tayi tagumi kamar wata marainiya,
bayan wasu mintuna saiga mommy ta fito hannunta riƙe dana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login