Showing 63001 words to 66000 words out of 186041 words

Chapter 22 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53910

ga ciki ɗurumma a gaba ya girma sosai!
Haka yayi waje dasu a haka yana riƙe dasu da hannu ɗaɗɗaya, ita kuwa Bara'at har numfashinta ya soma ɗagewa,
ya fito a fusace domin ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin duk an tarwatsa masa mayaƙan dabbobinsa, yana fitowa harabar masarautar yanda su Junaid suke a tsatstsaye, ganin Munafurr yasa duk suka razana,
haka ya wurga sarki Raamud da Bara'at gaban su Junaid, Bara'at ihu takeyi saboda cikinta ba ƙaramin buguwa yayi ba tana faɗin "wayyo cikinahhh, innalillahi wa inna ilaihi raju'un cikina zan mutu..."
Junaid kallon Bara'at yake yana tuna mahaifinsa da tayi sanadiyar mutuwarsa, sannan ya juyo yana kallon sarki Raamud wanda shine silar rashin lafiyarsa kuma shine wanda yake wahalar dashi, tsananin tsanarsu ne ya ƙara shiga masa zuciya,
Idonsa ya ɗaga yana kallon Munafurr ji yayi Angel ta ƙanƙame shi tana faɗin "wallahi Oga Junaid ba'a turomu mu yaƙi wannan basamuden dodon ba, mu rufawa kan mu asiri mu kama waɗanda ake nema...."
Junaid duk yana jin abunda Angel take faɗa amma bai bata amsa ba,
Sauran sojojin guda biyu kuma duk fitsari suka sau a jikinsu ganin halittar Munafurr a yayin da kuma ɗaya acikinsu ya makance tsabar irin kallon da yake yiwa Munafurr, sai ihunsa akaji yana murtsika idonsa tareda faɗin "wayyo ido na, wayyo idona bana gani wallahi, duhu nake gani..." yanata lalumen mutane, lokaci guda kuma yayi tsitt ya ƙafe a guri ɗaya sakamakon ƙarfen da Munafurrr ya wurgo masa ya soki maƙogaronsa ya faɗi ƙasi matacce,
Junaid zaro ido yayi waje yana kallon ɗaya daga cikin sojojinsa wanda aka masa wannan ɗanyen hukunci...
Ita kuwa Angel ƙara ƙanƙame Junaid tayi jikinta na kakkarwa tace "idan kuka haɗa ido dashi zaku makance, Munafurr ne mungun mutum ne wannan anban labarinsa....."
Munafurr wani ƙarfen kuma du ya wullowa Angel jin tana magana sauran kaɗan ƙarfen ya shige mata goshi Junaid yayi saurin cabkewa sannan ya wurgar gefe,
duk wanda yayi magana haka yake wannan hukuncin,
Bara'at kuwa tintinin sarki Raamud ya toshe mata baki....

Munafurr da ƙwayar idonsa ya rufe babban gate ya kulle yana wani irin dariya yana cewa "yau kun shugo masarautar sarki munafurr, nine mai wannan masarautar kuma anan zan bisine gawarwakinku...", yana mai ƙara tintsirewa da dariya,
ɗayan soja ne ya ɗago bindigarsa ya fara harbin Munafurr kafin bullet's su ƙarasa gurin Munafurr har ya juyar da bullet da ƙwayan idonsa sun koma kan sojan da yayi harbin, lokaci guda shima ya faɗi matacce,
Yanzu iya Junaid da Angel ne suka rage sojoji!
Ga Uma Bara'at kwance kan cinyar Sarki Raamud sai murƙususu take tayi cikinta ba ƙaramin ciwo yake mata ba, tana jin yanda twins ɗinta suke mata juyi a ciki......




*WAƊANDA AKAYI YAƘI DASU NACE BAAAA HOW MARKET🙌🙌*
*Naga iya Angel da Junaid ne suka tsira a yaƙin waje kodai kuma an sheshsheƙeku ne ko kuma kun bi Adity kun gudu🤔🤔*

Wai shin kunga laifin Aditi data gudu kuwa? Nidai banga laifinta ba yaciin🤣🤣🤣

Akwai waɗanda basa comments dalilin da yasa nake hutawa kenam wallahi,
Mutane kusan 50 amma bazaka samu mutum 10 waɗanda zasuyi maka sharhi ba haba dan Allah..
Duk temakon kai ne dai, zaku karanta abu amma ba liking bare comment
Kodan gadararku kun biya kuɗi ne🤔🤔
Amma ai nima idan akayi mun godiya zanji daɗin yin typing next
Dan Allah ku gyara wannan bayi bane, mu kyautatawa junan mu shine zaman tare....
🙏🙏🙏🙏🙏🙏

𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 33 ➡️ 34


Angel tana ƙanƙame da Junaid tana ta Addu'a idonta a rufe,
Junaid ya kawo kansa saitin kunnenta yace "ki zamo jaruma, kisa a ranki zaki iya yaƙar wannan ma..." bai ƙarisa maganar ba yaji Munafurr yana cewa "Junaiduu idan kana son fita daga cikin masarautar nan da ranka toh sai kayi mun abu ɗaya! da hannunka nake so ka kashe sarki Raamud a yanzu babu jira..."
Junaid abun mamaki ya bashi, kallon sarki Raamud yayi yana mai jin takaicinsa sannan ya kalli Munafurr yace "inda ace anban damar na kashe shi ai da yanzu babu labarinsa saboda kallonsa ma banaso nayi, yanzu a raye ake buƙatarsa..."
Munafurr yace "kaii yaro kar kamun tirjiya kayi abunda na saka ka.."
"Shaiɗani baya bani umarni nabi..." a cewar Junaid.
tintsirewa da dariya Munafurr yayi yana faɗin "idan baka kasheshi ba ni zan kashe ka..." ya ƙarasa maganar yana cillo wa Junaid takobinsa, cikin nuna jarumta Junaid ya kaicewa takobin tareda yowa kan Munafurr da gudu zai naushe shi daman yana jin takaicin kashe masa sojoji da yayi a gabansa, yana zuwa kuwa Munafurr yasa hannu ya cabke wuyan Junaid ya ɗaga shi sama da hannu ɗaya, Junaid ƙoƙarin ƙwace wa yake yi amma ba hali domin ba ƙaramin riƙo akayi masa ba,
Angel saita Munafurr tayi da bindigarta ta harba, Lokaci guda Munafurr ya cabke bullet da ɗayan hannunsa yana karya wuya idonsa akan Angel ya ƙara tintsirewa da dariya yana faɗin "kee zaki iya dani ko?.."
Angel fashewa tayi da kuka ta durƙusa da gwiwowinta, shi kuwa Junaid ƙafarsa ne yake ta lilo ya gagara ƙwacewa daga shaƙar da Munafurrr yayi masa ana cikin wannan halin har Junaid ya fara fita hayyacinsa lokaci guda Munafurr ya cillashi gefe sakamakon mashin da aka caka masa ta bayansa, kafin ya waiwaya an ƙara caka masa!
Munafurr waiwayawa yayi yana kallon sarki Raamud wanda ya zagaya ba tareda kowa ya saniba yaje ya ɗauko takobi da mashi ya wurga wa Junaid da Angel yana faɗin "ku tashi ku yaƙi wannan shaiɗanin mutumi marar tausayi idan baku kashe shi ba to shi zai kashe ku..." shima yana riƙe da nasa takobin zai ƙara caka masa yaji Munafurr yayi wurgi dashi gefe guda yasa hannu yana cire mashin da sarki Raamud ya caka masa a fusace ya miƙa hannunsa saiga takobinsa shima ya tafo gareshi ya cabke shi,
Junaid miƙe wa yayi yana maida numfashi hannunsa riƙe da takobin da sarki Raamud ya wurga masa, itama Angel miƙewa tayi saiga sarki Raamud shima ya taso duk suka jeru suna fuskantar Munafurr,
Uma Bara'at kam tana gefe guda tana zaune sai kallon Junaid take wanda goshinsa yake ɗaure da jan ƙyalle, ta gane ƙyallen Ayush ce itama Ayush daga wajen umanta ƙyallen ya fito wato ita kanta Bara'at, sai dai ba haka kawai Ayush ta ɗaurawa Junaid ƙyallen ba akwai saƙo a tattare da wannan ƙyallen...

Junaid da sarki Raamud ne suka rufa gurin Munafurr da gudu suka fara kai masa sara shima haka yake binsu da takobinsa har ya sari Junaid a ciki yayin da ita ma Angel ta rufa masa ta sari ƙafarsa saboda Munafurr ba ƙaramin tsayi ne dashi ba duk ɗinsu a kunkuminsa suka tsaya,
Munafurr jin zafin sarar da Angel tayi mishi ne yasa yakai mata canki itama tayi baya tana birgima, shima sarki Raamud saida ya saita wajen penus ɗin Munafurr ya caka masa wuƙar, wani irin ihuu Munafurr yayi har saida duwatsu suka fara girgiza a fusace Munafurr yakai sara wa sarki Raamud badan sarki ya kaice ba babu abunda zai hana Munafurr ya fille masa kai, Junaid ne shima ya tashi ga jini yanda yake zuba masa domin ba ƙaramin yankuwa yayi a ciki ba Allah yaso ba caka wa akayi ba, ya ƙwalla ƙiran Angel yana faɗin "ki miƙe mu gama da wannan matsiyacin.." wani irin tsalle Angel tayi ta miƙe tsaye da takobinta a hannu ta tafo gurin Junaid da gudu yayin da shi kuma ya sauƙe tafin hannunsa ɗaya ƙasi tana zuwa ta taka hannunsa ya ɗagata sama ya cillata wajen Munafurr ta ƙara yin sama tayi wani ihu ta dage ta sari hannunsa daga saman kafaɗa nan take saiga hannun Munafurr ɗaya ya faɗo ƙasi, kafin Angel ta sauƙo ƙasa kuwa Munafurr ya juyo a wahale ya kai mata sara a wuyanta da hannunsa ɗaya mai riƙe da takobi sannan ya canketa gefe saida tayi sama kamar ƙwallo zata faɗo ƙasi Junaid a ruɗe yayi wani irin ihu yana ƙiran sunanta "Anngeeelll...." ya yo kanta da gudun gaske kafin ta ƙarasa faɗowa ƙasa yakai hannu ya cabketa sukayi ƙasi a tare yana rungume da ita ga jini kuwa yanda yaketa tsiyayowa daga wuyanta ga shatar yankan da akayi mata a wuya ya yanke mata maƙogaro dan ma bakin takobin ne ya sareta da wuyanta zai sare mata gaba ɗaya,
Jikin Angel ne yake kakkarwa sosai murya na rawa daƙer take faɗin "mutuwa zanyi! mutuwa zanyi!! mutuwa zanyi!!! innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Ogah Junaid ka te te temake niiii...."
Shima Junaid hawaye yake yi yana faɗin "bazaki mutu ba Angel insha Allahu zaki tashi kinji..". Angel dishi-dishi ta fara gani idanuwanta suna shirin rufewa bakinta na kakkarwa a hankali take furta "Laa i la ha illa llaa mu ha mma du raaasulullaahh.....". ta cacumi Junaid sosai daga nan bata ƙara motsi ba ga baki a buɗe kamar wacce zatayi magana abunda ta gama furtawa last kenam rai yayi halinsa, ga ido a buɗe tana kallon sama!!!!

A hankali Junaid ya furta "Angel.." bakinsa na kakkarwa jikinsa ne gaba ɗaya yahau ɓari yana jijjigan Angel tareda faɗin "No! no!! noo!!! noooo!!!! kar ki tafi Maryam Please help me don't leave me aloneeee...."
wani irin ihuu Junaid yayi, kuka yake sosai kamar wanda ransa zai fita yana rungume da Angel sosai a jikinsa, Rumana ce ta fara masa gizo ga kuma Angel idonsa a ƙanƙame, haƙwarensa ne suka fara kakkarwa suna dukan juna tsabar raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarsa....

Sarki Raamud ne yake ta fafatawa da Munafurrr shima sararsa akayi a saitin ƙirjinsa sannan aka wurga shi gefe,
tintsirewa da wani irin mahaukacin dariya Munafurr yayi da hannunsa ɗaya, idonsa akan Junaid wanda yake rungume da Angel, Munafurr da takobinsa ya saita Junaid sannan ya wurga masa takobin kafin takobin ya iso ya soki Junaid Bara'at ta tafo da gudun gaske ta rufa kan Junaid tana juyowa kuwa wannan takobin ya shige cikinta, wani irin ƙara Bara'at tayi ta yo báyá ta kwanta a jikin Junaid ta bayansa yaji sauƙar mutum a kwance, juyowa yayi a tsorace yana gudun abunda zai gani domin ihunta ya girgiza masa kunne, ido ya zaro waje baki a buɗe ganin Mata ga tsohon ciki ta sadaukar da rayuwarta akansa, wuƙar gaba ɗaya ya lume a cikinta sai ƙotar wuƙar a waje!!
Da gudu sarki Raamud ya tafo gurin yana ambaton sunata ya ɗagota daga kan Junaid ya kwantar da ita a saman cinyarta ya rungumeta sosai da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana rungume da tsinin cikinta ya kasa furta komai sai ido da yaketa zarowa, hankalinsa ne ya fara barin jikinsa, ƙwaƙwalwarsa ce take juyawa, sarki Raamud gaba ɗaya ya fita hayyacinsa ko kuka ya kasa yi...

Junaid ne ya ƙwantar da Angel ya tashi yazo gaban Bara'at ya durƙusa sannan yasa hannu ya zaro takobin da yake nitse a cikin ta, lokaci guda shima ya ƙara fashewa da matsanancin kuka ga jan ƙyalle a ɗaure da goshinsa,

Wani irin ihuuuu Munafurr yayi na azaba Junaid yana durƙushe ya fara ji suna girgiza, tsabar ƙarfin ihun Munafurr a gigice Junaid ya waiwaya yana kallon gurin da Munafurrr yake a tsaye yaga wani halittar Mutum ne ya caka masa takobi na tsafi ta bayansa, ga yanda takobin yake fidda farfatsin haske, zaro takobin yayi sannan ya ƙara datsa masa a saitin zuciyarsa still wannan takobin yana bada haske,
wannan mutumin ba kowa bane face *NARASIMHA* ga kuma Damusa shima yana tsaye ta gefen Narasimha,.
Junaid sake baki yayi yana kallon Narasimha cike da mamaki yana maganar zuci "wannan wani irin halitta ne shima? mutum mai kama da biri..."
Narasimha yana zare takobin Munafurr ya faɗi ƙasi ya durƙusa da gwiwowinsa,.
Narasimha ya kalli Junaid yace "ka tashi kazo ka cire masa kayi da hannayenka yaa Sarkin wannan masarautar na gobe...". Junaid ɗaukar takobi yayi ya riƙe sosai tareda tahowa da gudun gaske a fusace ya taka kafaɗar Munafurr yayi tsalle ya fille masa kai sannan ya dirƙo ƙasi yana huci,
Kayin Munafurr ne ya faɗo ƙasi, gangan jikinsa shima ya faɗi,
Junaid zuwa yayi wajen da kayinsa yake a yashe ya saita idanuwan Munafurr masu hatsari ya caccaka musu wuƙa, shikenam an gama da rayuwar Munafurr!
Narasimha yana kallon Junaid yace "ba dan wannan Damusan ba da bazaku samu tsira ba gaba ɗayanku, domin shi yake ajiye da wannan takobin mai tasirin gaske a gurinsa, wannan mutumin bazai taɓa mutuwa ba indai ba'a yi aiki da wannan takobin ba, na zo ni ne domin na kawo muku agaji yanzu kuwa zan tafi, zan koma daga yanda na fito saboda ba'a duniya nake zaune ba, kwanana ya daɗe da ƙarewa daga zaman nan duniya sakamakon rashin wannan takobin..." ya ƙarasa maganar yana nuna takobin hannunsa, ya fiddo da wani ƙaton littafi ya miƙawa Junaid yace "ga wannan karɓi.." Junaid ya karɓa sannan Narasimha ya cigaba da cewa "kaine magajin wannan masarautar, duk abunda kake son sani akan wannan masarautar toh wannan littafin ya ƙunshi komai a ciki, idan kanason yin tambaya to duk amsoshinka yana cikin wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login