Showing 69001 words to 72000 words out of 186041 words
maƙiyana ne, kiyi haƙuri mommy bazan iya zama daku ba, domin nasan wata rana zan iya sawa araina zan kashe ku to ke banason ki mutu amma dole zan kasheki saboda Junaid ya ɗanɗani kalar baƙin cikin dana shaƙa kafin shima mutuwar tazo kansa,
Junaid wallahi wallahi sai naga bayanka, bazan ƙyaleshi ba, sai na ɗau fansar mutuwar mahaifiyata da cikin dake jikinta...."
miƙewa tayi a fusace ta nufi wardrobe ɗinta ta ɗauko akwatinta ta tuttusa duk kayanta a ciki sannan ta zuge akwatin ta rufa mayafinta ta fice a ɗakin tana riƙe da jakar ta, har zata sauƙa down stairs ta fasa saida ta shiga ɗakin junaid ta fara yimasa bincike ko zataga wani abu mai muhimmanci, zuwa tayi ta tura wannan secret room cikin sa'a ta sameshi a buɗe, ta hanzarta ta shige ciki tareda kunna light ɗin ɗakin tsayawa tayi tana kallon photon mahaifiyarta da kuma mahaifinta tana zubda hawaye, nan danan ta fara bincika ɗakin tana kuka amma saidai abunda take bincikawa bata gani ba,
domin tin bayan ɗauke takobin da akayi Junaid ya gano hakan yasa ya ɗauki littafin yaje ya bayar wa malam lawan domin ya adana masa,
Ayush buga jikin gini ta fara yi tana kuka a fusace ta juyo tana wargaza shirgin ɗakin, su computer duk ta faffasa su, wasu abubuwansa masu amfani duk ta lalata masa su, fita tayi da gudu ta sauƙa falo kai tsaye kitchen ta nufa taje ta ɗauko galan petur ta dawo ɗakin Junaid ta wawwatsa petur sannan ta dawo falo nan ma ta watsa petur har su kitchen daga nan ta kunna gas saida ta kaishi ƙarshen number wutar yayi over da gudu ta ɗauki akwatinta ta buɗe falo tayi ficewarta, gudu take sosai har ta isa bakin gate cikin sanɗa ta buɗe gate ɗin ba tareda an jiyota ba, tayi ficewarta da gudu...
Kitchen ɗin ne ya fara yin bonding daga nan wutan ya fita falo saiya haɗu da wayar nepa lokaci guda falon ya kama da wuta duk kujerun falo sunata ci da wuta, gobara gidan ya fara yi ta ko ina wuta yake badawa har zuwa room ɗin Junaid da Ayush gobara ne
Mommy tana bacci ta fara jin warin petur ga wani baƙin hayaƙi da yake shugo mata,
Kafin ta Ankare ƙofar ɗakinta ya fara ci da wuta, ganin abun yayi yawa kamar a mafarki ta buɗe idonta da sauri, ganin da gaske ne ƙaurin wuta takeji hakan yasa ta tashi a firgice ganin yanda ƙofar ɗakin yake ci da wuta yasa ta zaro ido waje tace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, wuta kuma? Ayushert Allah yasa dai tana lafiya, mun shiga uku..." tana rufe bakin saiga ƙofar ɗakin ya faɗo ta ciki nan danan gadon da take ya fara ci da wuta, ko ina ya kama da wuta, Mommy ɗaukar wayarta tayi ta nufi cikin toilet da gudu ta kulle sakamakon babu hanyar fita hatta falon ma ta ko ina wuta ya cinye, kuka take sosai tana ta jero addu'o'i tareda danna wayarta tana ƙiran number Junaid waran sau uku bai ɗauka ba,
Dabara ne ya faɗo mata nan take tayi ƙiran gaggawa daga asibiti tana faɗin "dan Allah ku temaka gobara a gidana, ga can yarinya itama nasan ɗakinta ya kama da wuta emergency please...." ta katse ƙiran tana maida numfashi sama-sama sakamakon wani irin hayaƙi ne ya dabaibayeta ko numfashi bata iya fitarwa sai tari take tayi, ko gabanta bata iya gani tsabar hayaƙi lokaci guda hasken nepa ya ɗauke sai duhu daya biyo baya,
Mommy daga wannan lokacin ta nemi hankalinta ta rasa, ga ƙofar toilet shima ya kama da wuta,
tari take sosai kamar zata haɗiyi ranta har ta fara tarin aman jini, jini ne yake fita daga bakinta tsabar tari, sulalewa tayi ta faɗi ƙasi, ga wani irin ƙunan wuta da yake ratsa jikinta, ba abunda take furtawa sai sunan "Ayush! Ayush!! ku temake ta, Ayush kar ta mutu..." daga nan numfashi ya tsaya,
Daiden lokacin da motar kawo agajin gaggawa ta iso tana bada jiniya, da gudun gaske suka shige da wayar feshin ruwa,
Baba maigadi shima fitowa yayi ganin yanda gidan yake ci da wuta ne yasa ya fara ihu yana riƙe da kansa, domin ba'a tunanin za'a samu mutum mai rai a ciki saboda ta ko ina wuta ne yake ci.....
*******
Junaid mafarkin da yake yi ne yasa baiji ƙiran da akeyi a wayarsa ba,
yana cikin bacci bakinsa yana motsi a hankali yake furta "Yushert! Yushert!! Yushert!!! Please kar ki tsaneni, har yanzu ina kan sonki kuma bazan daina sonki ba har abada...."
Ayush tana tsaye a gaban Junaid wanda bayansa wani ƙaton rami ne mai zurfin gaske, tana ta kwashewa da dariya haɗe da tafa hannayenta biyu tana shewa ga bindiga a hannunta, lokaci guda ta tsayar da dariyan tana wani irin kallo na ƙasƙanci tace "kayi kaɗan Junaid kai babban maƙiyi nane kuma bazan taɓa yafe maka akan laifin da ka aikata mun ba, rayuwarka a tafin hannuna yake, idan kaga na yafe maka toh kasheka nayi, kar kayi tunanin zan ƙyaleka, saina ɗau fansar jinin mahaifiyata da kuma abunda ke cikinta...."
Junaid durƙusa wa yayi a gabanta yace "indai haka shine daidai agareki to Bismillah zaki iya kasheni yanzu, amma inaso ki sani soyayyarki bazata taɓa zamowa ƙiyayya ba acikin zuciyata inasonki Yaushert..."
Kafin ya rufe baki ta harbeshi a kafaɗarsa ta kuma saita kayinsa ta harba cikin rashin sa'a iya bullet ɗaya ne a cikin bindigar, cikin takaici ta wurgar da bindigar gefe tana faɗin "kash naso ace na dagargaza maka ƙwaƙwalwa wallahi, idan ka furta mun kalmar so ji nake kamar ana ƙara rura mun wuta a cikin zuciyata, ganin kalmar nake tamkar mutuwata, na tsani kalmar soyayya sannan na tsani mai yin soyayya, Junaid mutuwarka hutu ne a gareni kuma samun nutsuwa ne a gareni..."
Junaid yana riƙe da gurin da ta harbeshi yana kukan zuci idonsa akan Ayush wacce take tsaye akansa ko Annuri babu a fuskarta, idonta tsantsar ƙiyayya ne acikinsu buɗe baki tayi tace "kayi haƙuri ka gaida mun mahaifiyata da kuma ɗan uwana dake cikinta...." tana kaiwa nan tasa ƙafarta ta cankeshi yayi baya ya faɗa cikin wannan ƙaton rami mai zurfin gaske....
A ruɗe Junaid ya farka yana ihu tareda ambatar sunan "Yushertttt..." yana maida numfashi sama-sama ga gumin da ya wanke masa fuska, wani irin haɗiyar yawu yayi ga zazzaɓin da ya rufeshi ya ƙanƙame sai rawar sanyi yake tayi....
******
A wannan daren misalin ƙarfe 2 da rabi Ayush tana tsaye a bakin gate ɗin gidan Doctor Hasheem tana ta faman bubbugawa tana kuka, jin motsin mutum yasa tayi shuru da yin kukan, ji tayi an tambaya cewa "waye ne?.."
cikin sassanyar murya tace "Ni ce..."
maigadi yace "ke wa?.." tace "Ayushert.."
yace "ok ki jira toh mai gidan ya fito ya buɗe miki domin bazan mutu ni kaɗai ba wollah.."
maigadi ne ya fara hura wusir da ƙarfi, cikin lokaci ƙalilan sai ga Doctor Hasheem ya fito cikin rigar bacci yace "wai meyake faruwa ne?.." cikin muryar jin bacci yake magana,
Maigadi yace "daman Ogah wata mata ce take jiranka a waje..." cikin mamaki yace "wata mata kuma? a wannan daren? shin daga ina take?..."
maigadi yace "a'ahhhh ban saniba aradu..."
tafowa Doctor Hasheem yayi yazo ya buɗe gate baisha wahala waran ganeta ba saboda akwai hasken nepa ta wajen, gabansa ne yayi matuƙar faɗuwa cike da mamaki yake binta da kallo, baki na kakkarwa yace "Ayushert! ke daga ina?.."
Fashewa tayi da matsanancin kuka..."
girgiza kai yayi sannan yace "Junaid ko?.."
yasa hannu ya jawota ciki sannan ya karɓi akwatin hannunta yajata suka nufi cikin gidan...
A falo suka zauna tana kuka duk ta kwashe labarin ta gayawa Doctor Hasheem,
jinjina kai Doctor Hasheem yayi sannan yace "kiyi haƙuri Ayushert haƙiƙa Junaid bai kyauta miki ba, bai kamata ya kashe miki iyaye ba, amma kema inaso ki sani komai ana binsa ne akan tsari duba da yanda kema iyayenki sukayi masa, shi wannan fansa ya ɗauka kema kinsan Junaid baya yafiya, amma duk da hakan yayi rashin imani gaskiya yasa hannu ya kashe mata mai ciki haihuwa yau ko gobe innalillahi wa inna ilaihi raju'un, dole kema bazaki yafe masa ba, banga laifinki ba Ayushert, ki ɗauki duk hukuncin daya dace ki ɗauka ina goyon bayanki, sannan zaki cigaba da zama damu acikin gidan nan..."
Ayush tana kuka tace "a yanzu na ɗauki fansata akan mahaifiyarsa shima ya ɗanɗani raɗaɗin dana ɗanɗana..." ta ƙarasa maganar fuska a haɗe...
Doctor Hasheem yana kallonta cikin rashin fahimta yace "ban gane mai kike nufi ba? kar kiyi kuskuren ɗaukan fansarki akan Mahaifiyarsa domin tayi miki halacci sosai a rayuwa kuma ita batada wata matsala..."
Ayush juyowa tayi tana kallon Doctor Hasheem a fusace tace "kenam niɗin mahaifiyata matsala take dashi yasa ya ɗauki rayuwarta? mahaifiyata batada wani masoyi daya wuce Junaid, kullum maganar ta akan Junaid ne, mahaifiyata bata taɓa sa hannu ta mareni ba sai akan Junaid, shin sakayyar da zai mata kenam? uwa bata fi uwa ba, haka uba baifi uba ba, kamar yadda ya sheƙe mun mahaifiyata haka shima mahaifiyarsa yau za'a wayi gari itama ta sheƙa, sai mu zama marayu da gaske..."
Doctor Hasheem haka yake bin Ayush da kallo gaba ɗaya ta sauya masa, ba Ayush ɗin daya sani a baya bane, yana tunanin a ransa cewa "Anya kuwa wannan Ayush ce? ina tunanin Aljana ce tazo mun a suffar Ayush...." daga nan ya fara tsorita da ita domin kalamanta sun girgiza shi,
yana cikin wannan halin yaji ta ce "shin kana mamaki ko? kar ka damu ni ɗin ce Ayush, abunda akayi mun ne yasa zuciyata ƙaiƙashewa nima, kuma muje zuwa gaba shima Junaid saiya bar Duniyan nan, da hannuna zan kashe tsinanne la'ananne, ban taɓa yadda cewa soyayya takan zamo ƙiyayya ba sai yau kuma akaina..."
jikin Doctor Hasheem ne yahau rawa daƙer ya buɗe baki yace "shin mai kika aikatawa mommy?..."
kafin ya rufe bakinsa yaji wayarsa tana ring-ging a saman table ɗin tsakiyar falon,
Hannunsa na kakkarwa ya ɗauki wayar ganin number hospital ne yasa ƙirjinsa bugawa da ƙarfin gaske yayi picking tareda karawa a kunne, ba tareda yayi magana ba yaji ance "Doctor Hasheem kayi saurin zuwa gidan Doctor Fateema gidanta duk ya cinye da wuta kuma mun rasata a cikin gidan, ko ina ya ƙone yayi ƙurmus, ga Oga Junaid baya ƙasan, kuma an hanamu ƙiransa mu sanar masa, dan Allah kai ɗin kazo ance mutum biyu ne a cikin gidan kuma bamu ga ko ɗaya ba acikinsu...."
yana kaiwa nan ya katse ƙiran,
Doctor Hasheem yar da wayar yayi ƙasi, idanuwansa sun ƙafe akan Ayush ji yake kansa yana juyawa, girgiza kai yayi a ruɗe ya tashi da gudu ya fice a falon,. a wannan daren yaje ya shige motarsa ya finciketa a ɗari ya nufi bakin gate,
Maigadi ne ya fito da gudu jin ƙarar motar yazo ya buɗe masa gate, ya tafi da kayan baccin a jikinsa....
Bayan fitarsa Ayush fashewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai tana faɗin "ki gafarce ni Mommy Dan Allah, kiyi haƙuriiiii...."
kuka ne yaci ranta sosai, tana cikin rera kuka saiga Lailah ta fito tana sanye da rigar bacci zuwa gwiwarta, ganin Ayush yasa ta murtsuka idonta ko mafarki take ganin da gaske ne Ayush take gani ta sake baki tana kallonta....
*NACE BAAA YAU MA ZAN TAMBAYEKU HOW MARKET👋👋👋*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 37 ➡️ 38
Doctor Hasheem a ɗari ya iso da motarsa yana zuwa ya buɗe ya fito ganin gidan yanata ci da wuta ne yasa zuciyarsa bugawa baki na kakkarwa ya furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un..." da gudu ya shige gidan ya ɗauki robar feshin ruwa ya ƙarasa shigewa ciki, ruwa ake badawa sosai har Allah yasa wutar ta mutu, Doctor Hasheem a hanzarce ya shiga ɗakin mommy yana dubata amma bai ganta ba, ga yanda tiririn wuta yake tashi, haka suke duba wa amma ba alamun mommy ga toilet duk ya cinye da wuta, girgiza kai Doctor Hasheem yayi sannan ya furta "mu rasata, wuta ta cinye ta shikenam Mommy..." wani zazzafan hawaye ne yake zuba masa, sai ji yayi ta bayansa ance "Doctor akwai yarinyar gidan a ɗakinta fah.." Doctor Hasheem kawar da kansa gefe yayi ba tareda ya kulashi ba ya juya yayi ficewarsa...
*****
Lailah ce ta ƙaraso gurin da Ayush take tana tsaye tace "Ayushert meya kawo ki gidan nan a wannan daren?..". Ayush bata kulata ba ta cigaba da kukanta, ganin Lailah ta dameta da tambayoyi yasa Ayush miƙewa tana faɗin "idan kinaso na bar muku gida saina tafi ai koh.."
Lailah ta zaro Ido waje tace "me yayi zafi haka, cigaba da zamanki bani na kawoki ba, idan tayi tsami ma ji.." Lailah juyawa tayi ta nufi waran frig ta buɗe ta ɗauki Apple da farro ta koma ɗakinta daman yunwa ne ya fito da ita...
Ayush tayi waran awa biyu tana zaune bata rintsa ba, can saiga Doctor Hasheem ya shugo cikin damuwa yana tafiya kamar babu laka a jikinsa, zuwa gaban Ayush yayi ya tsaya yana faɗin "shin kin kyautawa kanki? yanzu kinji daɗi ko mommy ta ƙone tayi ƙurmus babu alamun gawarta, yanzu kin ji daɗi?..."
Ayush bata bashi amsa ba itama miƙewa tayi ta ɗauki akwatinta tayi hanyar fita, Doctor yace "ina zaki je kuma?.."
tace "zanje gurin da ba takurawa, na zaɓi nayi rayuwata ni kaɗai..."