Showing 159001 words to 162000 words out of 186041 words

Chapter 54 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53917

Areeph saida ya gama juye-juyensa da ɗagun kai saida yaɗau kusan mintuna tukun ya buɗe baki yace "Doctor.." ataƙaice...
Junaid yace "kenam a ƙarƙashin mata zaka ƙare?..." Areeph kallon Daddynsa yayi sannan yace. "ra'ayina na faɗa zan kuma iya canzawa idan naso..."
yana kaiwa nan bai tsaya sauraron abunda za'a ƙara cemasa ba ya tashi zai koma ɗakinsa, har zai haura stairs ya sake juyowa yace "nifa kar a sake shugo mun ɗaki, duk yarinyar data shugo kuma zan karyata ne...". ya maida kallonsa kan Ayush ya kuma cewa "mommy kizo ki mun wanka...". yana ƙarasa maganar ya fara ɗale stairs yankinsa daban ne, ba kowa ne yake zuwa wannan yankin ba sai Ayush kawai, ita zataje tayi masa wanka sannan takai masa abinci domin baya ci acikin mutane, idan lokacin tafiya makaranta ne haka Ayush zataje ta shirya shi ya fito su tafi makaranta, amma bayan makaranta baya fitowa daga cikin ɗakinsa,
Shikam Areeph har yaso yafi Babansa girman kai da jiji dakai da kuma ɗagun kai...

Junaid kamar wanda aka watsa mar ruwan sanyi haka ya ƙafe a wajen, a tsorace ya kalli Ayush yace "anya ba ƴaƴan Aljanu kika haifa mun ba? especially Areeph du Da du how many years ?? Bai fa shiga shekara huɗu ba?...". a ruɗe yake wannan maganar idonsa akan Ayush,
Itama Ayush jiki a sanyaye ta tashi ta nufi ɗakin Areeph ba tareda tace komai ba,
Girgiza kai yayi ya furta "impossible zan gyara shi, I'll make him a good parson..."
ya kalli su Little Angel da Amrish yace "Oyaah kuje ɗakinku kuje ku kwanta ko, gobe akwai school...". tashi suka yi suka nufi ɗakinsu suma ɗakinsu yana can saman stairs...

Shima miƙewa yayi zai tafi ya kalli gurin da Hafzat take yace "ke ma Yakamata kije ki kwanta koh dare yayi ƙarfe 10 yanzu?.."
ta amsa masa da "toh"
har ta miƙe zata tafi ɗakinta ya tsayar da ita yana cewa "Judan yamun magana yace next week zai turo iyayensa daga nan zamu wuce dasu can garinku muje mu samu iyayenki akan maganar Aurenku, tinda har kin kammala karatun ki...."
Hafzat bata san lokacin data sau murmushi ba tace "toh Uncle Allah ya kaimu..." ta juya da gudu ta nufi ɗakinta,
Shima Upstairs ya haura ya nufi ɗakinsu...


Itama Ayush saida ta wanki Areeph ta shirya shi cikin sleeping dress ya ƙwanta akan gadonsa ta tottofa masa Addu'o'i tukun ta rufe masa ƙofa, kai tsaye ɗakin ƴan mata ta nufa suma taje ta gyaggyara musu ƙwanciya ta rufesu da mayafi sannan ta yi musu addu'o'i suma ta kulle musu ƙofa, daga nan ta nufi ɗakinsu,
tana zuwa ta tara da Junaid har ya shiga wanka, itama shiryawa tayi cikin kayan bacci ta haura saman gado, ba jumawa shima ya fito ya shirya sannan ya haura shima, anan aka fara love an daɗe ba'a haɗu ba, kowa yana kewar kowa,
Kashe hasken ɗakin sukayi daga nan suka shige mayafi,

(Asmeetah kuma tayi ficewar ta, domin kar taga abunda zai hanata bacci🤪🤪)



★★★★★★

Alhamdulillah 🙏
An fitar da Doctor Hasheem daga prison, amma daƙer aka samu ya fito jiki duk ya jikkata,
Kai tsaye gidansa aka nufa dashi aka bashi Makullin gidan ya buɗe ya shige abunsa, gani yayi gidan yayi datti over dake bamai shugowa gidan tsawon shekara huɗu, haka ya shiga yaje ya watsa ruwa a jikinsa, saida yayi wanka sau biyar, yana gamawa zai ƙara yi kuma du saida yaga jikinsa yayi fes tukun, shi da kansa yaje kitchen ya girka abunda zai ci,
Gidan nan kuwa haka yasa aka turo masa masu gyara suka zo suka gyara gidan tass,
Gaba ɗaya furniture's ɗin ɗakin duk yasa an canza su, komai da komai an gyara gida ya koma normal, Doctor Hasheem saida yayi wata guda acikin gidansa bai leƙa waje ba, saida ya tabbatar jikinsa yayi normal, haskensa ya bayyano duk ya hashaske gemun fuskarsa yayi gyaran fuska yayi kyau sosai, komai nashi ya dawo normal tukun ya yanke hukuncin zaije gidan su Maimoon domin saka yaronsa a idonsa, yanzu baima san ya kamannun yaron yake ba, ga kuma ƙanwarsa Lailah a gidan dole zaije ya gansu, tinda Daddyn Maimoon shida kansa yasa aka fito dashi,
Ita Lailah tana yawan zuwa prison gano Yayanta...

Fitowa harabar gidan yayi yana sanye da jamfa a jikinsa da hularsa duk yasa an wanke masa motocinsa saida ya zaɓi ɗaya daga ciki tukun yaja saida yaje wajen gate kuma du ya fito ya buɗe gate da kansa ya koma cikin motar ya fita, yana fita ya ƙara fitowa ya rufe gate yasa key,
Kai tsaye gidansu Maimoon ya nufa...

Yana zuwa ƙofar gidan yaje yayi parking da motarsa a waje guda sannan ya fito yazo yana knocking, ƙirjinsa kuwa haka yake masa bugun tara-tara, domin gidan ƙwarjini yake masa, cikin sa'a saiga gate man ya buɗe suka gaisa,
daƙer maigadi ya iya gane Doctor Hasheem saboda shekaru har huɗu ba wasa bane,
Cikin ikon Allah yana shiga wantalelen gidan daga nesa ya hango wani ƙaramin yaro yanata buga ball shi kaɗai sai faman gudu yake,
Da haka har Doctor Hasheem ya ƙaraso wajen yaron fuska ɗauke da murmushi yace "fine boy how fi?.."
yaron tsayawa yayi yana kallonsa cikin rashin sani, buɗan bakin yaron yace "waye kai?.."
Doctor Hasheem rage tsayinsa yayi ya durƙusa a gaban yaron tareda dafa kafaɗarsa yace "what's your name?.." yaron yace "my name is Abubakar better known as Rapeekh...". Doctor Hasheem yace "wow Nice name, which class are you?..."
Rapeekh yace "Nursery 2..."
Ya kuma cewa "how old are you?..". Rapeekh yace. "I'm forth years old...". kafin Doctor Hasheem ya kuma sake masa wani tambayar Rapeekh ya katse shi da cewa "And than you, please should will tell me your own details?..."
murmushi Doctor Hasheem yayi yana jinjina kai, kafin ya buɗe baki yayi magana yaji daga nesa ana cewa "Kai Rapeekh kai da waye a wajen nan?.."
juyawar da zaiyi ƙwatsam yaga Maimoon ta nufo gurinsu da sauri, ganin Doctor Hasheem yasa gabanta faɗuwa da ƙarfin gaske ta furta "A"uzubillahi mina shaiɗanin rajinn, meya kawo ka gidan mu? shin waya fito dakai daga prison? Nayi tunanin acan zaka ƙare rayuwarka ai..."
Dasauri Doctor Hasheem ya miƙe tsaye sam baiji daɗin kalaman Maimoon ba,

Lailah da Doctor Mansur suna can wajen flowers ɗin gidan suna ta shan soyayyarsu, basu ma san Doctor Hasheem ya shugo gidan ba sai muryar Maimoon suka jiyo tanata maganganu a fusace,
tasowa sukayi suka nufo wajen dan tabbatar da abunda ke faruwa, Lailah ganin Yayanta yasa tayi ihu ta tafo da gudu ta rungume shi sosai tana tsallan farin ciki, shima rungumarta yayi yana faɗin "Autar Mama nayi kewarki..." tace "nima haka Yayanaaa nayi farin cikin ganinka..."
Bayan sun gama tace "Yayana yaushe ka fito daga prison?..."
Yace "Auta watana guda da fitowa.."
Ta ɗan turo lips ɗinta tace "Yaya shine baka nemeni ba tsawon wata guda da fitowarka..."
Tace "Amma Yaya Daddy bai sanar mana cewa an fitar dakai ba...". Murmushi kawai yayi bai bada amsa ba,
Doctor Mansur ne ya miƙa masa hannu yana faɗin "your welcome my friend...". suka gaisa sosai cike da kewar juna..
Suna cikin wannan halin saiga Daddy ya shugo da motarsa, parking yayi sannan ya fito yazo wajen yana gyaran murya tareda faɗin "meyake faruwa anan?..."
Jikin Doctor Hasheem ne yayi sanyi ganin Daddy,
Daddy ne ya kalli Doct Hasheem yace "Ohh kazo ne, naga shuru-shuru ban ganka kazo ba, shikenam tinda Allah yasa kazo ku shiga ciki inason magana daku gaba ɗayanku..." ya kalli Doctor Mansur yace "harda kai kaima..." daga nan yayi wucewarsa ciki,
Maimoon riƙo hannun Rapeekh tayi taja dogon tsuka sannan tayi wucewarta itama, daga baya suma suka nufi ciki....





*TOH PAH LITTAFI YAZO ƘARSHE, SAURAN ƘIRISSSSS...*


𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 86 to 90


Kowa ya hallaru a falo ana sauraron abunda Daddy zai ce,
Ga Ammy a kusa dashi, Doctor Hasheem kuma yana zaune akujera ɗaya da Doctor Mansur, Maimoon da Lailah kuma suna zaune aƙasin carpet,
Daddy yana ɗauke da Rapeekh akan cinyarsa ya fara magana kamar haka "Ba komai ne yasa duk na tara ku anan ba sai don na tabbatar muku da wani sirri, sannan na magance matsalar data daɗe da afkuwa, anyi mun abunda banji daɗinsa ba sam.."
ya kalli Doctor Hasheem sannan ya kalli yanda Maimoon take ya girgiza kai tareda faɗin. "haƙiƙannin gaskiya baku yiwa kanku adalci ba, amma ba laifinku bane, duk laifi nane dana barku kara zube bayan nasan akwai ƙulalliyar alaƙa a tsakaninku..."
Daddy ya ambaci sunan Dactor Hasheem murya a sanyaye yace "Hasheem kayi haƙuri abunda nayi maka, nayi hakane saboda ka gyara kuskurenka sannan ka gane cewa abunda kayi sam bai dace ba, bawai nayi maka hakane saboda na ƙuntata maka ba, alokacin da Maimoon ta sanar mun cewa kai kayi mata ciki wallahi naji sanyi acikin zuciyata, kuma hankali na ba ƙaramin ƙwanciya yayi ba saidai ban nuna hakan a fili ba, babban tashin hankalina shine fargaban kar ta sanar mun cewa bakai kayi mata ciki ba, wallahi tallahi na tabbata inda a lokacin Maimoon ta ambaci wani ba kai ba, Da alokacin zuciyata bugawa zata yi kuma babu abunda zai hana na yanke mata maƙogaro, amma jin kaine zuciyata tayi sanyi sosai ma ..."
Maimoon gaba ɗaya ta rasa gane kan Daddynta, kuma maganganunsa sunyi matuƙar ɗaure mata kai, ba ita ba hatta shima Doctor Hasheem yayi mamakin jin haka daga wajen Daddy, yana tunanin meye dalilin da yasa hankalin Daddy ya kwanta jin shine yayi mata cikin...
Daddy ƙiran sunan Maimoon yayi sannan yace "kiyi haƙuri Daughter tsawon shekaru huɗu kenam na ɗauke miki farin ciki nah dalilinda yasa haka shine kasancewar Hasheem yana can prison hankalinsa ba'a kwance yake ba, taya Ni kuma zan sanya ki farin ciki? idan nayi haka banyi masa adalci ba,
yanzu zan sanar muku sirrin da muka daɗe muna ɓoyeshi tsawon shekaru ashirin, babu wanda yasan wannan sirrin daga Ni sai Mahaifinka Hasheem sai kuma Mahaifiyarka da kuma Matata Mahaifiyar Maimoon gata nan a gefena, sai kuma Kakanunku waɗanda suka rasu tintini, sai kuma Yayan Mahaifinka dake ƙasar Niger...."
yana kaiwa nan yaja dogon numfashi,
Kowa ya baza kunnuwa domin jin wannan sirrin, Daddy ya cigaba da cewa "Hasheem tin kuna yara soyayya ta ƙullu atsakaninka da Maimoon, koda yaushe kuna tare hakan yasa muka yanke shawara Ni da Mahaifinka Alhaji Bukar na Aurar daku a lokacin, tin kana Ɗan shekara goma ita kuma Maimuna tana shekara biyar akayi muku Aure ba tareda kowa ya sani ba, sai iya mu, kuma abunda yasa bana fargaban komai akanku shine kun kasa rabuwa har Allah yasa kuka mallaki hankalin kanku, akwai waɗanda suka zo neman Auren Maimoon amma naƙi amincewa aciki harda ƴan uwanta, duk wanda yazo nakan koreshi saboda Auratayyar dake tsakanin ku, kuma itama Alhamdulillah bata tsayawa da kowa sai kai, bata ambatar ko wane suna sai sunanka, wannan shine sirrin da muke ɓoyewa yanzu kuma na bayyanar shi, saiku fara ɗaukan kanku a matsayin ma'aurata..."

Doctor Hasheem cike da mamaki yake bin Daddy da kallo gaba ɗaya kamar babu rai a jikin shi, murya na kakkarwa yace "Daman akwai igiyar Aure atsakani na da Maimoon? kuma tin muna yara..?"
Jinjina kai Daddy yayi yana kallonsa, kowa dake wajen yayi mamakin jin haka banda Ammy wacce itama tasan da maganar,
Hawaye ne suka wanke mata fuska cikin kuka tace "Daddy a gaskiya ni yanzu bazan cigaba da son Hasheem ba, bana sonsa yanzu, inda a baya ne zanyi farin cikin jin hakan amma yanzu kam sam baya raina..."
Ammy tace "banda abunki ai yanzu ne ya kamata ki soshi saboda yaron dake tsakaninku, kuma Ni a wannan lamarin nafi ganin laifinki shin meya kaiki ɗakinsa cikin dare?..."
Daddy yace "ya isa haka banason taune-taune, abinda ya wuce ya wuce kenam tinda Allah yaso ba aikin alfasha suka aikata ba, kuma yaronsu ɗan sunna ne ba shege bane..."
Ya kalli Maimoon yace "ke kuma duk abunda zaki faɗa bazaiyi tasiri anan ba, shin mekike nufi? kinaso kice mun a raba Auren? toh wannan labarin kuyange ne abunda aka ɗaura tin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login