Showing 162001 words to 165000 words out of 186041 words

Chapter 55 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53952

shekarun baya yanzu bazaki warware shi ba, nagaya miki ki cire wannan batun a bakinki, Hasheem mijinki ne har a lahira saboda haka ku sasanta kanku kafin nan da ƙwana biyar zaki koma gidansa ku cigaba da rayuwar ku acan da kuma yaronku..."

Ya maido da kallonsa kan Lailah wacce tin farko kanta yake ƙasi jin an ƙira sunanta ne yasa ta ɗago tana kallon Daddy yace "ke kuma Auta abunda yasa ban tsayar muku da maganar Aurenku ba shine inaso sai Yayanki ya fito daga prison tukun, tinda Allah yasa kin kammala karatun N.C.E kuma Yayanki ya fito abunda ya dace shine ayi maganar Aurenki kema ki tare agidan mijinki, sannan na sama miki aiki a gidan redio, tinda ɓangaren da kika karanta kenam Journalist Koh?..."
Dasauri ta ɗaga masa kai alamar ehh,
Sannan ya kalli Doctor Mansur ya sanar masa cewa "tinda lokaci yayi abunda nakeso dakai Mansur shine ka turo magabatanka nan gidan, in yaso daga nan zamu wuce dasu can ƙasar Niger domin nema maka Auren Lailah a gurin Baffanta wato Yayan Mahaifinta wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya shine kawai ya rage musu...."
Doctor Mansur ya amsa cikin farin ciki......


★★★★★★


Return to Ogah Junaid part★★
Washe garin safiyar Monday around 7:30 kowa ya hallaru akan dinning, Amreesh da Angel suna sanye da kayan uniform ajikinsu alamun school zasu tafi, ga kuma Hafzat itama, Junaid ne ya sauƙo daga stairs yana sanye da jallabiya ajikinsa sauƙowarsa kenam yaran suka fara gaishe shi suna faɗin "Good morning Daddy.." fuskarsa ɗauke da murmushi yace "morning my Child's, fatan kun tashi cikin ƙoshin lafiya..". suka amsa masa gwanin burgewa, ya kuma cewa "bana breakfast da sassafen nan amma saboda ku zan rinƙa breakfast da wuri..." Little Angel tace "meyasa Daddy?.." yace. "saboda kuna zuwa school Ni kuma nafison nayi breakfast da yarana masu albarka...". duk sukayi dariya, sai daga baya itama Hafzat ta gaishe shi duk suna zazzaune Oga ya kalli Amreesh yace "Momy where is your mother?..". tace "ai Daddy tana can tana shirya Yaya Areeph" yace "okay..."
suna cikin wannan zancen sai gata ta sauƙo falo tareda faɗin "kuyi haƙuri na zaunar daku ban zuba muku abinci ba koh...". Junaid kansa akan wayar hannunsa yanata pressing ɗinta har ta gama zuba musu sannan ta ɗauki kular abinci zata nufi upstairs daiden lokacin da Junaid ya ɗago ya kalleta tareda faɗin "ina zaki kai kular?.."
tace "Amm zan je nayi feeding ɗin Areeph ne shima ya kammala shirin school..." Abun ne yayi matuƙar ɗaure masa kai cike da mamaki yace "ban gane wannan wani irin bad behavior ne haka, shi bazai fito cikin ƴan uwansa yayi breakfast ba kenam? ke da shi your very stupidity, kizo ki ajiye kular ki ƙira mun shi..."
Ayush jiki a sanyaye ta dawo ta ajiye kular fuska ba Annuri tana baƙin cikin yanda yake mata tsawa agaban yaranta, haka ta haura taje har ɗakin Areeph, kafin ta fito dashi saida tayi masa warning sosai akan in sunzo ya durƙusa har ƙasi ya gaishe da Daddynsa gudun kar ya fusata yace zai daki yaron, bayan sun sauƙo falo Areeph ƙin zama yayi yanata bayan Daddynsa daƙer ya buɗe baki yace "Good morning Daddy..."
Juyowa yayi jin muryar Areeph ata bayansa alhalin bai san da zuwansa ba, yana kallon Areeph yace "haka ake gaisuwa a tsaye?..." bai bashi amsa ba saima ƙafe shi da yayi da ido, zaro ido Junaid yayi yace "ba magana nake maka ba?".. yayi maganar cikin tsawa domin har saida su Little Angel suka tsorita shima kansa Areeph saida ya tsorita sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya fara jin tsoron Daddynsa ganin baya masa da wasa,
ƙanƙame Ayush yayi dake a gefensa take, tasowa Junaid yayi a fusace ya fizgo hannunsa tareda dokashi a ƙasin carpet, sai buguwar kansa kawai aka ji yayi gabbbb, hakan ma yasa hannu ya zabge shi da mari, dasauri Ayush tasa hannu akan kuncinta kamar ita aka mara, kamar zatayi kuka haka take ji, jin yanda Junaid yaketa zabga masa mari,
Areeph ba abunda yake sai ihu yaji mazgar manya, shi tinda aka haife shi ba'a taɓa sa hannu an dake shi ba sai yau,
Ogah Junaid bai daina dukan yaron ba saida yaji Angel da Amrish sun fashe da kuka ganin anata dukan ɗan uwansu tukun ya daina dukan a fusace rai a ɓace yake cewa "bazan juri ganin yaro ƙarami yana abu irin na marasa tarbiyar yara sannan na zuba masa ido ba, i'm a not crazy man...". ya ƙarasa maganar yana kallon Ayush ya kuma cewa "zan iya karairaya shi in har baki canza masa tsarin rayuwa ba, daga yau inaso na rinƙa ganinsa acikin ƴan uwansa, sannan dole zai rinƙa cin abinci acikin mutane, wannan tsaurin idon nashin zan caccaka su...". ya juyo kan Areeph yace "Kneel down..."
Areeph a gigice ya tashi daga kwance zaiyi kneel, Ayush tana goge hawaye tace "bai ci abinci ba sannan kuma zasu makara a tafiya school..."
wani irin harara ya wurga mata sannan yace "banga amfanin zuwansa school ba tinda ba'a koyar da tarbiyya, ya zauna a gida I'll teach him a lesson..."
Bayan su Angel sun kammala breakfast ɗinsu wucewa sukayi suna kuka suka ɗaɗɗauki lunch bag ɗinsu, already akwai dreban su wanda yake kaisu makaranta sannan idan lokacin tashi yayi ya ɗauko su, a wannan ranar Areeph baije school ba, haka Junaid yake gana masa azaba kamar ba ɗansa ba, duk ya faffasa masa jiki da wayar nepah hakan ma ya cire masa kayan jikinsa gaba ɗaya daga shi sai pant yake zabga masa wayar,
Ayush ganin bazata iya juran ganin ana azabtar mata da yaro ba yasa ta nufi ɗakinta ta rufe, itama Hafzat ba ƙaramin tausayin Areeph tayi ba, har da hawayenta, da gudu tazo ta durƙusa agaban Ogah tana roƙonsa cewa "dan girman Allah Uncle kayi haƙuri ka ƙyale shi haka, yayi ƙanƙanta sosai a irin wannan dukan, zai iya shiɗewa wallahi...". ta ƙarasa maganar tana kuka,
kallon ta yayi yace "tashi ki bani guri..." jiki a sanyaye haka ta tashi itama ta nufi ɗakinta,
Ogah Junaid saida yayi kwana uku yana azabtar da Areeph kuma yaƙi barinsa yaje makaranta, a waɗannan kwanakin itama Ayush ta daina kula Junaid ko gaisuwa bata haɗasu tasha kuka kamar ranta zai fita ganin yaron duk ya fita hayyacinsa, hakan yasa ta fice a gidan kai tsaye gidan Uncle Artaff taje takai ƙaransa, shima Uncle Artaff jin hakan yasa yayi gaggawar zuwa gidan, a lokacin da su Uncle suka shugo falon daiden lokacin Areeph ya faɗi ƙasi ko motsi babu, a rikice Ayush ta nufo gurin da gudun gaske tana kuka tareda faɗin "wayyo Allah na shiga uku ya kashe mun yaro..." Shima Uncle Artaff nufan gurin yayi yana salati hatta shima Ogah Junaid ya tsorita ganin yanda yaron ya yanki jiki ya faɗi, cikin gaggawa aka ɗauke shi sai hospital....


★★★
Bayan ƙwana Biyar
An kai Maimoon gidan mijinta daƙer Doctor Hasheem ya samu nasarar shawo kan Maimoon har ta haƙura, yanzu soyayyarsa ta dawo mata cikin zuciyarta duk da daman tana sonsa kawai tana masa wulaƙanci ne saboda abunda yayi mata amma daman bata daina sonsa ba,
Doctor Hasheem yasa an gyara masa gidansa, an chancanza design ɗin gidan da penti gaba ɗaya komai ya dawo sabo, ga yaronsu yanzu yasan waye Babansa kullum yana manne a jikinsa, yanzu rayuwa ta canza musu ta dawo musu sabuwa, Doctor Hasheem kamar baiyi zaman prison ba, ya cika ya murmure haskensa ya dawo masa, yana ƙoƙarin bawa Maimoon kulawa sosai ita da yaronta,
sannan kafin mommyn Junaid tabar Nigeria ta bar saƙo cewa da zaran Doctor Hasheem ya fito a prison a bashi letter cewa "ta bashi shugabanci a hospital ɗinta, shine mai kula da hospital sannan duk ma'aikatan hospital a ƙarƙashin jagorancinsa suke...

Ita kuma Lailah an yanke ranar bikinta itama sauran sati Uku, ga ta samu aiki a gidan redio, rayuwa ta sauya mata,
fitowar ta daga cikin ma'aikatansu kenam zata tari napep ya kaita gida, tazo tsallakawa bata ankara ba saiga wani ƙaramin jeep yazo ya ƙwasheta saida tayi sama tukun ta faɗo ƙasin ƙwalta, kayinta ba ƙaramin buguwa yayi ba, tin daga lokacin bata ƙara motsi ba,
kafin kace mai mutane har sun taru, ba'a tsaya jiran kowa ba sai hospital...

Doctor Hasheem ba karamin razana yayi ba jin abunda ya faru da Lailah, daman yana hospital yana duba majinyata yazo zai fita da gudu yaga ashe itama Lailah har an iso da ita, a rikice ya karɓeta sai cikin emergency room,
Shima Doctor Mansur ba karamin ruɗewa yayi ba jin Lailah tana asibiti, ba shiri shima ya nufi hospital ɗin Doctor Hasheem ba abunda yake furtawa sai "innalillahi wa inna ilaihi raju'un ².."
da haka har ya isa.
kafin a ankara Daddy da Ammy da Maimoon har sunji labari suma ba shiri suka nufi asibitin,
Lailah saida tayi ƙwana biyu tana kwance tukun Allah yasa ta farfaɗo, kafin ta gama buɗe ido bakinta ya fara motsi tareda faɗin "Yaya ka dena dukan Ogah Junaid dan Allah, meya maka hakane, zaka kashe shi fah...". Jin haka yasa Doctor Hasheem nufan gurin dasauri yana ambatar sunanta, Lailah ƙoƙarin tashi zaune take, Doct Hasheem ne ya ɗagota zaune yana kallon ta tareda cewa "Lailah kin gane ni?..."
bugan ƙirjinsa tayi tana murmushi tace "haba Yaya idan ban tuna dakai ba shin wazan tuna, nifa ban manta komai ba..."
Doct Hasheem yace "amma naji kina ambatar sunan Ogah Junaid shin kin sanshi ne?..."
Lailah cike da mamaki take kallon Doct Hasheem tace "Haba Yaya taya zan manta Ogah Junaid, tsohon saurayina ne fah, shine mutum na farko dana so a rayuwata, amma Yaya nayi mamaki taya abubuwan baya suka dawo mun ƙwaƙwalwata? yanzu ina iya tuna komai abunda ya faru a baya, tayaya Yaya? shin ina Ogah Junaid fatan ya samu lafiya koh? amma Yaya inadai baka illata shi ba dukan da kayi masa, naji tausayinsa sosai, toh ina kuma Ayushert take kodai ta gudu kashe mommy datayi ta hanyar gobara, naje na bayar da dukkan rahotannin ta agidan rediyo, an kamata ne?..."
Doctor Hasheem tsayawa yayi yana kallonta cike da farin ciki memory sense ɗin Lailah ya dawo mata, amma abun fargaba shine kar Lailah ta dawo da soyayyar Junaid cikin zuciyarta,
Lailah murya na kakkarwa tace "Aunty Maimoon.." tana kallon wajen da Maimoon take zaune itama Maimoon tasowa tayi tazo har wajen gadon Lailah tace "Lailah your welcome..". Lailah tana kuka tace "Aunty Maimoon kiyi haƙuri da laifin da muka aikata miki..." kafin ta ƙarasa Maimoon tayi saurin toshe mata baki tareda cewa "abunda ya wuce ya wuce kenam, ki cigaba da tsara rayuwarki na yanzu, Ogah Junaid ki manta dashi kawai yanzu Aure zakiyi..."
Lailah dariya tayi tace "daman ai kawai na tuno ne amma rayuwata ta yanzu tafi mun, a baya abubuwa marasa kyau na rinƙa aikatawa yanzu kuma Insha Allahu zan zamo uwa ta gari wa ƴaƴanta...." Duk sunyi farin cikin jin abunda Lailah ta faɗa, shima Doctor Mansur yana daga gefe har jikinsa yayi sanyi amma jin har yanzu Lailah tana tare dashi yasa ya sauƙar da doguwar ajiyar numfashi, shima ya nufi wajenta yana murmushi itama ganinsa yasa tace "mijina na kaina, kayi haƙuri lokacin da mota ta bugeni ina sauri ne zan koma gida shiyasa ban jira kazo ka ɗauke ni ba...". shafar gefen fuskarta yayi ba tareda yace komai ba sai murmushin farin ciki...
Suma su Daddy da Ammy sunyi farin cikin dawowar sense ɗin Lailah....

suna cikin hirarsu sai sukaji an turo ƙofar ɗakin gaba ɗayansu kallon bakin ƙofar sukayi ganin yaro ya shugo,
Doctor Hasheem yace. "kaii zo mana..". yaron yazo har gabansa ya riƙe hannunsa yana cewa "daga ina kake, meye sunanka?..."
Rapeekh dake zaune saman cinyar Ammy yace "Laaaa Daddy shine Abokina wanda nake baka labarinsa class ɗin mu ɗaya dashi kuma kullum sai munyi faɗa...."
Doctor Hasheem ya kalli yaron yace "kaine Areeph?.." Areeph dasauri ya ɗaga masa kai alamar ehh,
ya tambaye shi meye full name ɗinsa, Areeph kamar bazaiyi magana ba daƙer ya iya cewa "Máahmud Junaid Khan..."
Jin sunan abunda ya ɗaure wa Doctor Hasheem kai, cike da mamaki yace "sunan Babanka Junaid Khan Máahmud?...". dasauri Areeph ya ɗaga masa kai,
Doctor Hasheem kallon Lailah yayi yace "wannan yaron Ogah Junaid ne..."
A zabure Lailah tace "yaron Ogah Junaid kuma? Innalillahi haka yaran suka girma, yaushe ne mukaje hidimar sunansu...."
suna cikin tattaunawarsu saiga Ayush ta shigo ɗakin kamar zata kife tayi sallama, duk suka juyo suna kallonta bayan sun gaisa tace "Areeph inata nemanka ban ganka ba...".
Doctor Hasheem ne yace "Malama Ayushert your welcome...". cike da mamaki Ayush take kallon Doctor tace "Doct Hasheem

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login