Showing 177001 words to 180000 words out of 186041 words

Chapter 60 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53965

ring-ging, bai tsaya duba wayar ba sai ya cigaba da aikin gabansa domin ya saba irin haka sai a ƙirashi sau nawa amma bai ɗaga ba kuma yana kusa da wayar, bayan ƙiran ya katse sai kuma aka turo da message, anan ne yakai hannunsa kan wayar domin duba saƙon da aka turo masa, lokaci guda ya miƙe tsaye a razane yana faɗin "what .."
Ƙirjinsa ne ya hau bugun uku uku ido a zazzare, daƙer ya iya haɗiyar yawu wanda ya tokare masa maƙogaro, ganin text ɗin ba karamin razana shi yayi ba,
{Sorry your wife....}
abunda aka rubuta kenam, ya gagara gane mai hakan yake nufi, dasauri yabi number da akaita ƙira amma abun mamaki lokaci guda akayi switch up, jiki ba ƙwari ya fice daga office ɗin, yana fita a gaggauce ya shige motarsa kai tsaye gida ya miƙa domin tabbatar da abunda ke faruwa da matarsa, ko zasu iya sanin komai...

Mommy tana dinning tana shirya kayan abinci a sarki Raamud, wannan aikin ba na masu aiki bane aikinta ne, saida ta gama tsab zata haura upstairs ta nufi ɗakinsa kwatsam taji ana ƙwallah mata ƙira tin kafin a shugo falon, mommy ba ƙaramin tsorita tayi ba tace "innalillahi wa inna ilaihi raju'un, Allah yasa dai lafiya ..". dasauri ta sauƙo falo daiden lokacin da Junaid ya shugo hankali a tashe ya nufeta tareda faɗin "meya faru da Yushert?..."
saida gabanta ya yanke a tsorace tace "wani abu ya faru da ita ne?..." Nuna mata message da aka turo masa yayi mommy ta karɓa tana dubawa lokaci guda ta sauƙe ajiyar zuciya tana hararar sa tareda cewa. "wallahi saika kashe mai rai, haba wannan wani irin tayar da hankali ne haka, Ni nayi tunanin wani abu ya faru ne ashe abunda aka rubuta kenam..."
Junaid yana kallon mommy yace "sorry your wife?...! Abunda aka rubuta kenam toh amma me hakan yake nufi? shin meya faru da ita? kuma ba ita ta turo wannan message ba still nabi number but switch up...."
sai a yanzu itama mommy ta shiga yin nazari tace " wait bari na ƙira number Sameeha naji meke faruwa ne saboda Ayushert a wajenta ta sauƙa..."
tana shirin ƙira saiga ƙiran Uncle Artaff mommy tace "yawwa ga Uncle ɗinku ma ya ƙira.."
ta ɗauki ƙiran tareda sallama, mommy tace "yadai naji muryarka sanyi² meke faruwa?..."
Junaid eyes ɗinsa akan mommy kansa har wani juyawa yake, saiji yayi mommy tana faɗin "Alhamdulillah Masha Allah mai aka samu?.."
daga ɓangarensa ya bata amsa da cewa "Namiji...". Mommy tace "toh amma ita Ayush tana lafiya koh?.." Uncle Artaff bai bata amsa ba ya katse wayar..
cike da mamaki tace "ha'a lafiya kuwa"..

Junaid jin ance Namiji ne har yaji sanyi a ransa, ya ɗaga hannu sama yana godewa Allah cike da farin ciki, ya kalli mommy yace "amma wanda ya turo saƙonnan ba ƙaramin tsorata Ni yayi ba, me makon yasa congrats amma wai sorry, Sorry for what?..."
Mommy tace "toh yanzun ya za'ayi?..."
Junaid yace "me kuwa za'ayi illa a ɗauko mun matata da jariri a dawo mun dasu gida..." Mommy tace "haka ya kamata ayi, kawai zance wa Uncle Artaff su dawo gida kawai ko kuma Ni naje na dawo da ita..."
Junaid yace "gaskiya Mom gobe da sassafe jirgin Makka zai tashi yakamata kije da kanki, yaranki kuma tinda sun fara wayo kuma ga masu aikin ki kawai ki barsu...."
tace "ehh daman barinsu zanyi, yanzu dai bari naje na samu Abbanku na sanar masa..."
Junaid ya amsa tareda ficewa daga part ɗin gaba ɗaya, kai tsaye part ɗinsu ya nufa...

Bayan shigar Mommy room ɗin Sarki Raamud tarar dashi tayi akan sallaya bayan ya idar da Sallah ya kifa kansa akan gwiwowinsa, itama zama tayi akan sallayar dab dashi ta ambaci sunansa cool voice. "My King.."
Ɗagowa yayi da rinanan idanuwansa waɗanda suka kaɗa sukayi jaa tsabar kukan da yasha, mommy a tsorace taja baya cikin tashin hankali take faɗin "Subhanallahi Mai martaba mai zan gani haka, kuka fah kake yi? Na juma ban ganka acikin wannan halin ba dan ALLAH ka sanar mun..."
Jinjina kai yayi sannan yace "yanzu na gama yin waya da Artaff..."
Mommy cike da mamaki tace "nima nayi waya dashi yake sanar mun cewa Ayushert ta haifi ɗa Namiji..."
Girgiza kai sarki Raamud ya shiga yi yace "Ɓingel ta haifi Jaririnta kuma yana nan cikin ƙoshin lafiya amma sai dai ita ta rasa tata Rayuwar...". wani irin razana mommy tayi tareda ja da baya tana faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un⁴..." haka ta rinƙa nanatawa lokaci guda ta kifa kanta aƙasin carpet ta fashe da matsanancin kuka jiki na kakkarwa,
Sarki Raamud jiki ba ƙwari haka yake rarrashinta shima yana zubda ƙwallah, daƙer yake furta "kiyi haƙuri kulli nafsin za'ikatul maut, duk mai rai mamaci ne...". Mommy kuka take ba bakin magana, a wannan ranar haka ta wuni tana wannan kukan...

Washe gari mommy da Sarki Raamud sun shirya akan zasu je makkah, amma sun kasa sanar wa Junaid halin da ake ciki, shi a tunaninsa zasu je ne su taho da ita da Jaririnta...
Bayan kwana biyu da tafiyarsu, Ogah Junaid yana zaune a babban falonsa yana kallon tv ga Amrish kwance saman cinyarsa ta damu sosai da rashin ganin mommyn ta, kullum saita tambayi yaushe zata dawo, kullum tana cikin kuka wai ita akaita gurin mommynta daƙer Junaid yake rarrashinta domin Amrish tanada rarraunar zuciya kamar Ayush, abu kaɗan take saka abu aranta, ita kuwa little Angel tana can tanata wasanta bata damu ba, tayi kewar mahaifiyarta amma akoda yaushe tanasa ran zata dawo, shi kuma Areeph koda yaushe yana cikin dube duben littafinsa na school, ko kuma yaita danne² computer sam bai damu da tafiyar Mommynsa ba saboda yasan zata dawo...
Ogah Junaid yana zaune yasan yau ne su Mommy zasu dawo, saboda hakane yasa tinda suka tafi bai fita yaje gurin aiki ba saboda yaran,
Ji yayi an buɗe gate mota ta shugo, yana jin parking mota yasan su ne suka dawo da murmushi akan fuskarsa ya ɗago da Amrish yana faɗin "Mamana tashi maza ga mommynki ta dawo..". a ruɗe ta tashi tana cewa "Mommy ta dawo ina take? kafin su nufi bakin ƙofa saiga su Mommy sun shugo da sallama a bakinsu tana ɗauke da Jariri a hannunta, sai sarki Raamud yana biye da ita da kuma Uncle Artaff su uku, Junaid kallonsu yake ganin ba Annuri a fuskokinsu, idon mommy a kumbure yanda tasha kuka, haka suka shugo gaba ɗayansu suka zazzauna akan kujera shima Junaid zama yayi ya kasa cewa komai, ita kuwa Amrish da gudu taje ƙiran sauran ƴan uwanta cewa Mommynsu ta dawo,
Ogah Junaid murya na kakkarwa yace "ina take?..." Mommy sunkuyar da kai tayi ƙasi tana sharar hawaye, Uncle Artaff ne yayi ƙarfin halin cewa "Junaid kayi haƙuri akan abunda zamu ce maka, inaso ka kwantar da hankalinka kayi imani da ƙaddara mai kyau ko akasin haka, mu sani cewa duk rintsi duk wuya wata rana zamu bar duniya ko yau ko gobe kai ko yanzu ma idan Allah yaso zai karɓi rayukan mu..."
Cikin rashin fahimta Junaid yake bin Uncle Artaff da kallo yace "Please uncle duk nasan da wannan nidai buƙatata a sanar mun a inda Yushert ta tsaya, na ƙosa dana ganta kuma ƴaƴanta suma sun damu sosai..."
Mommy ce ta taso daga yanda take zaune ta zo gurinsa tareda miƙa masa Jariri tace "ganan yaronta nan ita bata samu damar zuwa ba..."
yatsina fuska yayi tareda faɗin "ban gane bazata samu damar zuwa ba, shin meya faru da Yushert ne kuke ƙoƙarin ɓoye mun?..."
Sarki Raamud kam babu bakin magana sai hawaye domin yayi babban rashi a rayuwarsa, Ɓingel Abar ƙaunarsa kuma farin cikinsa....
Uncle Artaff yayi ajiyar zuciya sannan yace "kayi haƙuri Ayshert Allah yayi mata rasuwa..."
Junaid jin kansa yake kamar a sama yake ga wani irin hajijiyan da yake ɗibansa Lokaci guda, a ruɗe yace "whattt...". yana riƙe da Jariri a hannu badan a zaune yake ba babu abunda zai hana hajijiya ya ɗebe shi, lips ɗinsa ne yake kokarin motsa shi amma ya kasa furta komai, lokaci guda idanuwansa suka rine sai hawayen dake gangaro masa, a hankali yakai idonsa kan yaron yana ƙareshi da kallo, girgiza kai ya soma yi tareda faɗin "i can't believe, Yushert bazata mutu ta barni ba, inaji ajikina Ni zan rigata mutuwa, zanje na ɗauko matata tinda kun kasa tafo mun da ita..."
a gigice ya miƙawa mommy yaron dake hannunsa yana sambatu ya tashi zai nufi waje, Sarki Raamud yayi saurin riƙo shi yana faɗin "kayi haƙuri mana Junaid, ka sani fah kowa ma zai mutu kuma lokacinta ne yayi, ka godewa Allah ta hanyar Haihuwa ta mutu, tana buƙatar addu'ar mu dan Allah ka kwantar da hankalinka...."
Junaid idonsa akan sarki Raamud daƙer yake motsi da bakinsa yace "Abbah da gaske Yushert ta mutu?..."
Jinjina masa kai kawai yayi yana zubda ƙwallah, cikin ƙanƙanin lokaci numfashinsa ya ɗage luuuu yayi baya zai faɗi sarki Raamud yayi saurin taro shi yana faɗin "innalillahi wa inna ilaihi raju'un Junaid! Junaid!! Junaid!!!..." haka ya kiɗime yana ƙiran sunansa amma ko motsi Junaid babu,
Mommy tana zaune kawai ta fashe da kuka, Uncle Artaff ne shima ya miƙe suka ɗago shi kai tsaye upstairs suka haura dashi yanda zai kai su room ɗinsa...

Mommy ɗagowar da zatayi idanuwanta suka sauƙa akan Triplets suna tsaye suna kallon duk abubuwan da ke faruwa, Amrish ganin yanda Daddynsu ya faɗi aka ɗauke shi yasa jikinta ya soma ɓari yana kakkarwa kamar mejin sanyi, ta tsaya cak ta kasa motsawa a yayinda Angel da Areeph suka nufo gurin Mommy suna faɗin "Mamy meya samu Daddyn mu?..." dake sunan da suke ƙiranta dashi kenam,
Mommy tace "babu komai ta ƙarisa maganar tareda goge hawayen fuskarta..."
Areeph yace "Mamy kina kuka kuma kina ce mana babu, shin meya samu Daddyn mu kuma ina Mommyn mu take?..."
Itama Angel tace "wannan Jaririn waye?..."
Mommy tace "Jaririn Mommynku ne ta haihu...". Angel ta kuma cewa "toh tana ina Mommyn namun?..."
Mommy ta kasa basu amsa kwatsam idonta ya sauƙa akan Amrish wacce take tsaye guri ɗaya sai fitar da numfashi take sama-sama, a tsorace mommy ta tashi ta nufi wajenta tareda faɗin "takwara meya faru ne? dan Allah ki temake mu kar ciwonki ya tashi please, ki kwantar da hankalinki kinji koh..."
Haka take rarrashin ta cikin kulawa domin ita daman Amrish batada cikakkiyar lafiya an haifeta da ciwon zuciya amma ba'a ankara ba sai bayan ta soma girma, zuwa yanzu dai sau biyu ciwon yake tashi, shiyasa akafi lallaɓata kuma tanada raunin zuciya bata juran damuwa, fargaban mommy a yanzu shine kar ciwon ya tashi a halinda take ciki yanzu...
Amrish ba abunda take faɗi illa "Mommy! Daddy!! Mommy!!! Daddy!!!!...". Ido yayi zuru-zuru. Mommy tasa hannu ta rungumeta tana rarrashinta ta ɗayan ɓangaren kuma tana riƙe da Jariri,
Can saiga su Uncle Artaff sun sauƙo yace "Suma yayi amma yanzu ya farfaɗo yana buƙatar hutu domin jikinsa yahau temporary...". Sarki Raamud yasa hannu ya ɗauki Amrish zasu tafi da su can part ɗinsu...

Bayan Kwana biyu Ogah Junaid yana nan a cikin Damuwa na rashin matarsa uwar ƴaƴansa kullum sai mommy taje parts ɗinsa tayi masa girki daƙer take rarrashinsa akan yaci amma duk da hakan baifi yaci 2 spoon ba shikenam, gaba ɗaya ya lalace duk ya rame cikin kwana biyu, ba bacci ba cin abinci sosai kullum acikin damuwa, mommy har ta rasa yanda zatayi dashi,
A ranar ciwon zuciyan Amrish ya tashi a part ɗin mommy acikin tana motsawa har ta daina motsi kwata-kwata, numfashi ya ɗage cakk ga jinin dake fita a bakinta gaba ɗaya Mommy ba ƙaramin razana tayi ba, duk sun saddaƙar da cewa Amrish itama ta mutu, domin babu alamar da zai nuna cewa tana a raye, haka sauran ƴan uwan natan suka fara kuka, itakam Angel ihu take tana ambatan sunan Amrish, shi kuwa Areeph shima faɗuwa yayi ganin ƴar uwarsa ta mutu, duk ana cikin wannan halin Amrish ta mutu shima Areeph ya faɗi amma an kasa sanar wa Ogah Junaid dake can part ɗinsa saboda ana gudun tayar masa da hankali, yanzu ma ba'a cikin hayyacinsa yake ba,
Mommy ta kasa aiwatar da komai duk jiki ya mace sai kukan da take tayi, Sarki Raamud ne ya ɗauki wayarsa ya ƙira Uncle Artaff akan yazo, kafin nan kuwa acikin ma'aikatan gidan an samu wacce tayi gudu taje har part ɗin Ogah Junaid tana zuwa ta haura saman Upstairs taje tana bubbuga room ɗinsa,
Junaid yana kan sallayarsa yanda ya idar da Sallah yana kan addu'o'i kunnuwansa suke jiyo masa bugun ƙofa kamar daga sama, kafin ya buɗe baki yayi magana kwatsam yaji an turo ƙofar da ƙarfi wata mata ƴar dattijuwa ta shugo ta durƙusa a gabansa tana haki numfashi sama-sama yanda tasha guda,
Junaid kallonta yake hankali a tashe domin yasan ba lafiya ba, fuskarsa har yayi fiyau, idanuwansa kuma suna nan a dishe basu koma normal ba,
Haka ya jira saida matar da daidaita numfashinta sannan ta soma magana tana faɗin "Yallaɓai Amrisha ciwon zuciyarta ya tashi ta rasu, shima yaron Areeph ya faɗi suna can..."
Ogah Junaid idanuwansa ya zazzaro waje kamar zasu faɗo ƙasi, lokaci guda hawaye suka bayyano masa akan eyes ko ƙibtawa bayayi idonsa akan matar,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login