Showing 9001 words to 12000 words out of 186041 words
"babu amfanin biyo ni domin nima ba daɗewa zanyi ba.." tace "eh dan Allah Ogah Junaid badon halina ba"
ajiyar zuciya ya sauƙar sannan yace "ok.." tana murna da farin ciki ta buɗe gaban motar ta shiga, ita dalilin binsa tana son ganin shin har yanzu akwai sauran ƙaunar ce da Ayush ko kuma an bantse, kafin ta turo da wannan video, tana kallon gefe tayi murmushin gefen baki, tareda tarin mugunta a ranta..
bayan isowarsu gidan a falo suka tsaya Junaid ne ya soma taka matakala zai haura yaje ɗakin Ayush, itama Lailah bin bayansa tayi!
ya ɗan dakata tareda juyo wa yace mata "ki dakata mun a nan falon..."
turo baki tayi tareda juyawa ta sauƙa falon, tana maganar zuci "Hmmm! Ogah Junaid kenam daina zaƙewa akan Ayush domin watan dasa maka tsanar ta ya kama, wanda ko yanda take bazaka ji ɗaukin zuwa ba..."
shi kuwa shigarsa ɗakin Ayush ya tarar da ita tana kwance saman gadonta sai faman sharar bacci take sakamakon maganin ciwon kai data sha,
zuwa yayi waran gadon ba magana haka ya kama ƙafarta ya jawota gabansa sannan ya miƙar da ita tsaye yakai hannunsa ya ɗago ƙafarta yayi mata ɗaukan luɗa ya nufi bakin ƙofa da ita..
ita kuwa Ayush a gigice ta farka sauran kaɗan tayi ihu takai idonta kan Junaid ganin shine yasa tayi shuru tana kallonsa cike da mamaki, tana lumshe ido tareda buɗesu a hankali baccin bai gama isar ta ba,
har suka sauƙa downstairs Ayush tana manne a faffaɗar ƙirjin Junaid yanda yake ɗauke da ita, saida ya sauƙo falo tukun ya sauƙar da ita,
Lailah ganin su a haka yasa ta miƙe tsaye da sauri tana daga zaune tana kallonsu cike da takaici da kuma tsananin mamaki a ranta tace "kutt amma Ogah Junaid sam bashida zuciya wallahi, sauna ne shi! duk bonsa shi datayi a cikin mutane amma ya kasa yin zuciya dubi yanda ya cacumota kamar wata jaririya..."
Junaid ne ya jawo Ayush jikinsa bayan ya sauƙe ta, yasa hannu ya tallafo haɓarta suna kallon juna yace "meya hanaki zuwa hospital?.."
shuru tayi bata bashi amsa ba sai binsa da kallo take,
"tambayarki nake meyasa baki koma asibiti ba?.."
nan ma shuru tayi ta kasa cewa komai sai ido,
ransa ne ya sosu ganin bata bashi amsa ba, yana kallon cikin eyes ɗinta yace "Yushert ina sauraronki, meye dalilinki na ƙin zuwa hospital?.."
still tayi masa shuru,
cike da takaici ya dafe goshinsa tareda rufe eyes ɗinsa ya saketa, saida ya juya bayansa kafin ya sake juyowa tareda darara mata wani irin gigitaccen tsawa..
ba Ayush ba hatta Lailah wacce take tsaye tana sauraronsu saida ta tsorita sosai tasa hannu ta toshe kunnuwanta tsabar ƙarfin tsawar jikinta har ɓari yake,
Ayush kuma tafiya tayi luuuu tayi baya zata faɗi yayi saurin taro ta ya kwantar da ita saman ƙirjinsa,
ba ƙaramin tsorita tayi ba, ƙirjinta yayi wani irin bugawa lokaci guda kuma ta nemi numfashinta ta rasa, ƙara ɗaukarta yayi ya kalli gurin da Lailah take yace "zaki iya tafiya?.."
jin irin tambayar da yayi mata yasa ta sake jikinta tareda narkewa ta dafe goshin ta tace "Ogah Junaid bazan iya tafiya ba, hajijiya nake jiiii.." tayi maganar a shagwaɓe tareda faɗuwa ƙasin carpet ta lumshe idonta,
ganin makirci take son masa yaja dogon tsuka sannan ya fice da Ayush a hannunsa yaje ya buɗe murfin mota ya kwantar da ita a seat back sannan ya koma falo,
Lailah harta buɗe idonta tana jin motsinsa ta rufe idonta da sauri, yana zuwa kuwa ya riƙo ƙafarta ɗaya ya ringa janta a ƙasi har suka fita daga falon yana janta, ganin zai ƙoƙe mata gadon bayanta yasa ta buɗe ido tana faɗin "wayyo Allah na Ogah Junaid bayana, dan Allah ka sake mun ƙafa zan taka da sawaye naaaa"
tana maganar kamar zatayi kuka,
shi kuwa bai daina janta a ƙasa ba har saida suka zo daf da motarsu tukun ya sake mata ƙafarta, ta tashi tana dafe bayanta data kurzu da floor ɗin gidan, jikinta ne ya soma mata ciwo daƙer da shige gaban mota ta zauna tana matsar hawaye..
Junaid figar motarsa yayi ya fice daga gidan da gudun gaske ko kallon yanda Lailah take baiyi ba, fuska a haɗe ba annuri...
☆☆☆☆☆
A masarautar sarki Raamud!
Uma Bara'at ce take kwance saman ƙirjin sarki Raamud tana kuka tareda faɗin "Ayush ta bani kunya wallahi, ban taɓa tunanin zata yi haka ba, yanda ta nuna tana son Junaid nayi mamaki sosai.."
Sarki Raamud bubbugar bayanta yake a hankali yana rarrashinta yace "kiyi haƙuri mana BB, idan kinga haka akwai laifin da yayi mata, amma yanda Ɓingel take da haƙuri zaiyi wuya ta aikata hakan ba tareda dalili ba, ya kaita maƙura shiyasa..."
Uma Bara'at ɗagowa tayi tana kallonsa tace "haba shugaba a cikin dubban mutane fa tayi masa haka, aiko meyayi mata bai kamata ta yanke wannan hukunci ba, kaide kawai kana goyon bayan Ɓingel ɗinka ce shiyasa.."
ta maida kanta ta kwantar saman ƙirjinsa, yace "to ke meyasa zaki damu haka bayan kinsan zasu dawo su ƙara haɗewa, ai bazasu rabu ba saidai kuyi ta jin kunya.."
Uma Bara'at tace "hmmm! tayi wa kanta ai, ni badan NARASIMHA ya bani zoben da zan ɓace naje gurin taron ba ai da bazanje naga wannan takaicin ba, kasan Narasimha yana kallonsu duk abunda suke yi..."
Sarki yace "eh mana ba shi bane yazo ya sanar mana baikon su ɓingel ba..."
bai ƙarasa maganar ba yaji Bara'at tana yunƙurin amai, kafin ya buɗe baki yayi magana har ta tashi da gudun gaske ta nufi toilet tana kwarara amai,
biyo bayanta yayi yana faɗin "BB meyake faruwa ne? meya sameki?.."
ɗagowa tayi tana haki ya riƙo hannunta ya kuma cewa "BB bakida lafiya ne? muje mu gun Narasimha ya duba ki yaga meyake damun ki, kinji ko.."
wuce wa tayi ta gefensa tace "ba wani abu bane kawai ɗan zazzaɓi nake ji ne..."
shugo wa bedroom sukayi yanata binta akan suje gurin Narasimha ya bata magani amma furr taƙi yadda,
ganin bazata je ba yasa hannu ya ɗauketa ya fice da ita,
wurwurga ƙafafuwa take tana faɗin "ni ka sauƙe ni wallahi bazan je gurin Narasimha ba, ya cika bala'i, ni ka sauƙe niiii..."
a falo suka tarar da Narasimha tsaye, a lokacin ya sauƙeta ganin Narasimha a falon masarauta,
gaishe shi Sarki yayi ya kuma amsawa,
Baba Narasihma juyowa yayi yana kallon Bara'at da ƙananun idanuwansa da fuskar biri jiki duk gashi yace "keee wato nine mai bala'i ko? dan uwar uwarki ko mijinki bai isa ya ce ni inada bala'i ba, daman wancan munafukar ɗiyar takin taurin kanki ta ɗauko har ta bijirewa baikon Junaidu saboda ita ƴar banza ce, saboda ita munafuka ce tana son Junaidu amma ta rufe ido ta wulaƙanta shi, toh daga ke har ɗiyar takin da mijin nakin duk kunci uwar uwarku ƴan gwafar uba,
da bakya so na duba ki to cikin ƴan biyu gare ki ƴar banza kawai...." yana kaiwa nan yayi wuce warsa yana tafiya da ƴar jelar bindinsa, gashi a tsaye kamar mutum amma suffar biri ne dashi, kamar su ɗaya sak da biri, yana tafiya yana tokara sandarsa....
*MASHA ALLAH BACCI NAKE JIII SAI GOBE INSHA ALLAHU ZAN CIGABA MUKU DA TYPING...*
𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️
𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔
the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅
𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️
𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871
*💫💫{{N W A}}💫💫*
Book two
C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 007 ➡️ 008
Bayan shigar su Junaid cikin hospital kafin su fito daga cikin motar ya kalli Lailah yace "get out"
juyowa tayi tana kallonsa kamar wacce zatayi kuka ta ƙara juya bayanta tana kallon Ayush dake kwance a bayan seat, buɗe baki tayi zatayi magana ya darara mata tsawa "i said get out..." a tsorace tayi saurin buɗe murfin motar ta fice, kai tsaye compound na asibitin ta nufa tareda juyo wa tana kallon motarsa ko fitowa baiyi ba,
yana daga cikin motar ya ɗauki robar faro mai ɗauke da ruwa a ciki ya since murfin tareda tsiyayar ruwan a tafin hannunsa yana watsa wa Ayush a fuska, a gigice ta tashi zaune tana maida numfashi sama-sama tana juyar da eyes ɗinta tana kallace-kallace acikin motar, muryarsa taji ya daki dodon kunnenta da sauri ta kalli yanda Junaid yake a zaune a front car, shima kuwa kallonta yake ta cikin madubin motar ba tareda ya juyo ba yace "ki dawo gaba ki zauna.." a tsorace take binsa da kallo ta kai hannu zata buɗe murfin motar ya katseta da cewa "ba sai kin buɗe ba, ki hauro ta sama ki zo.." tashi tayi ta zuro ƙafarta ta gaba tana shirin dirƙowa har sai da ta dafa ƙafaɗarsa tukun ta samu ta zauna suna jere da juna,
"meyasa baki biyo su Angel kunzo duba mamana ba? ko saboda ba mahaifiyarki bace shiyasa baki damu da jinyarta ba, yanda ta damu dake ke baki damu da ita ba why...."
hawaye ne suka fara zarya a saman kuncin ta tasa hannu tana gogewa baki na rawa tace "sanin abunda ke zuciyata sai Allah, amma duk abunda kace dai daine, amma Allah na gani yanda nasa mommy a raina ko mahaifiyata bansata a raina kamar haka ba..."
katseta yayi da cewa "ƙarya kike, da kin damu da ita da bazaki so ganin ɓacin ranta ba, hasali ma saboda ke ta kwanta jinyan nan.." dogon numfashi yaja sannan ya juyo yana kallon ta ya kuma cewa "Yushert ki sani abaya kin shiga raina har na fara sonki amma a yanzu babu wannan so, domin ni bana son maso wani! muna tare a gida ɗaya amma banaso ki ƙara kusantar yanda nake domin na rigada na yanke alaƙarmu, Allah ya zaɓa miki wanda ya fini kuma wanda zai nuna miki ƙauna fiye da wanda na nuna miki a baya...." yana kaiwa ƙarshe ya buɗe murfin motarsa yayi ficewarsa, ita kuma rufe fuskarta tayi da hannayenta biyu ta fashe da wani irin matsanancin kuka mai ƙona zuciya,
sai da tayi kukanta mai isarta tukun ta share hawayen fuskarta idonta yayi lufu-lufu ta buɗe murfin motar itama ta nufi cikin asibiti tana kakkare fuskarta saboda kar asan kuka tayi,
a hanyar shigarta ciki ta haɗu da Doctor Hasheem yana tafowa suka yi kucuɓus, ƙiran sunanta yayi cool "Ayushert! kinzo ki ne.."
ɗaga masa kai kawai tayi tana sunkuye da kanta, hannu yasa ya tallafo fuskarta ya ɗago da fuskar sama suna fuskantar juna yace "meya faru dake kike kuka?.." girgiza masa kai tayi tace "babu komai"
murya ciki-ciki yace "ke da Junaid koh?.."
kallonsa kawai take ba tareda ta bashi amsa ba,
adaiden lokacin da shi kuma Junaid ya tafo, ya tarar dasu a haka Doctor Hasheem yana riƙe da haɓarta, wuce wa yayi ta gefensu ba tareda ya ce musu komai ba,
Ayush da sauri ta waiwaya tana bin bayan Junaid da kallo sabon kuka ne ya sake kuɓuce mata, Doctor Hasheem ya riga da ya gano matsalar riƙe hannunta yayi yana faɗin "muje na kaiki ɗakin da Mommy take, amma ki daina kuka bason ganin hawayenki nake ba kuma still zaki tayarwa mommy da hankali kinsan tana fama da heart pain..."
Ayush dakatar da kukan tayi ta goggoge hawayen fuskarta sannan suka nufi room ɗin da mommy take...
bayan jigarsu cikin room ɗin da gudu Ayush ta nufi yanda mommy take a kwance, itama mommin rungumar Ayush tayi a jikinta sosai tana ɗan bubbugar bayanta ganin yanda Ayush ta fashe da matsanancin kuka,
Lailah tsuka taja ta miƙe tsaye daiden lokacin suka haɗa ido da Aditi wacce jin tsukar yasa ta juyowa tana kallon Lailah,
a fusace Aditi ta miƙe taje gaban Lailah ta kirɓa mata naushi a baki, kafin kace mai jini ya fara ambaliya a bakin Lailah,
hakan ma Aditi ta ƙara zabga mata mari har sau biyu a fuskarta tana