Showing 174001 words to 177000 words out of 186041 words

Chapter 59 - MATAR DAMISA book two complete novel

ASMEETI   

08 Oct 2024

53936

yanzu idan naje gurin Aiki mezance wa Abokai na da sauran yarana sojoji ina matsayin General nace Mamana ta haihu kenam? Impossible ku cigaba da ɓoye kuliyoyinku har su girma don nima babu a wanda zan gayawa, ai dole ku ƙi sanar mana kunya ce ta isheku, tayaya zaku ƙira kuce kun haihu daman ga jikokin ku...."
yana kaiwa nan ya juya zai fita kawai kunnuwansa suka soma jin kukan ɗayan jaririya dake kwance akan gado alamar ta tashi daga bacci ne,
Ayush tace "Mommy kawo wannan na hannunki na riƙe shi saiki shayar da wancan .." haka kuwa akayi mommy ta ɗauki ta kan gadon itama tasa mata Nono a baki,
Junaid juyowa yayi yana kallonta da jariran jinjina kai yayi yace "Hmmm!!!..."
ba tareda ya kuma cewa komai ba haka ya buɗe ɗakin ya fice,
Sarki Raamud girgiza kai yayi yana murmushi domin sai yanzu ya tabbatar da cewa har yanzu akwai sauran ƙuruciya ajikin Junaid...
Ayush ta kalli sarki Raamud tace "Abba Gaskiya banji daɗin rashin sanar mana da kuka yi..."
Yace "sorry Ɓingel bazata mukaso muku daman, sai kunzo ku tarar da ƙannenku..."
Mommy tasa baki da cewa "ƙannenku kuma kuliyoyinku...". Ayush kwashewa tayi da dariya sai yanzu ma abun yake bata dariya da maganganun Junaid,
Shima sarki Raamud dariya yayi yana faɗin "Allah ya shiryi Junaid..."
ya ƙarasa maganar tareda ficewa shima,
Ayush ta kalli mommy tace "mommy kiyi haƙuri da maganganun Yaya Junaid..."
Mommy tace "cabb haba Daughter kema dai kinsan nafi kowa sanin halin Junaid, wallahi ko kaɗan banji ciwon abunda ya faɗa ba, daman ai ya saba irin haka akan mai zan damu kuma, banda iya shege irinsa inda ace nayi Aure da wuri ai da yanzu ƙannensa sun girma, amma yana nan shi kaɗai kamar shaiɗan ba ƙanne ba yayu, ki rabu dashi kawai..."
Ayush tace "gaskiya kam, ai Mommy naga baki tsufa ba, babu wanda zai ce ke kika haifi Yaya Junaid saidai wanda ya sani...."
Mommy tace "daman ai shi ya tsufar dani, haba shekarunsa ma duka-duka 35 ne dai, ke kuma 25 yanzu daman ya baki shekara goma, tinda lokacin da Mamanki tabar gidan mu kina jaririya lokacin shekaransa goma, Babansa kuma yabar duniya..."
Ayush tace "Ahhh mommy 35 ai ya girma shima ya kusan tsufa..."
Mommy tace. "haba Ayusher lokacin danasa aka ɗaura Aurenku shekaransa 30 dai, yanzu kuma shekaranku biyar dayin Aure..."
. jinjina kai Ayush tayi da murmushi a fuskarta, ta kalli jaririn hannunta tace "Mommy ya sunansu?.."
Mommy tana riƙe da macen tace "wannan macece anyiwa Mamanki mai suna amma inkiya sunanta Ummul khair,
Shi kuma na hannunki mai sunan Uncle Artaff ne yaci inkiya Abul-Ameen...."
Ayush tinda mommy ta ambaci cewa anyiwa Umanta mai suna bakinta yake washe tsabar farin ciki, tace "wow Mommy naji daɗi sosai, Amma ni Ummy zan rinƙa cewa saboda Ummulkhair sunan yamun tsayi bazan iya faɗi ba..."
Mommy dariya tayi tana cewa "kaii Daughter saikace ba ƴar gari ba har ki gagara faɗin sunan Ummulkhairy?..."
gaba ɗaya dariya suke suna hirarsu abun burgewa kowa yana riƙe da jariri ɗaya.....

Su kuma Amriish da Angel suna part ɗin sarki Raamud sai wasa yake tayi dasu, Areeph kuma yabi Daddynsa sunyi can part ɗinsu...

Har dare Ayush tana tareda mommy anan suka ci abinci sukayi komai, daga baya Driver ya ɗaukesu a mota ita da yaranta biyu motar ta miƙe hanyar cikin masarautar, Ayush kalle kalle take tana mamakin irin girman masarautar nan, ga ya tsaru sosai saida suka isa bakin wani ƙaton gate tukun motar ta tsaya aka buɗe motar ta shige, nan ma Bodyguards ne suke gadin part ɗin, nan ne part ɗin su Ogah Junaid..
Part ɗin Uncle Artaff kuma sai an karya ƙwana tukun ɓangare ta dama kafin aje part ɗinsa shima akwai gate...
Ayush tana shiga babban falonsu ta tarar komai tsab tsab ko tsinke babu an gyara ko ina, sai ƙamshin turare gaba ɗaya part ɗin yake, bata tarar da kowa ba haka ta soma taka dogon Beni ta nufi wani part wanda bata ma san inane ba kawai dai ta miƙa ne amma tana tunanin bedroom ne, amma kuma Benin ya kasu kashi biyu ne akwai ta ɓangaren dama da kuma hagun saita rasa ina ɗaya zata nufa, ga Amrish da Angel suma suna bin bayanta, Angel tace "Mommy wai ina zamuje karfa mu ɓata, mu jira Daddy acan ƙasan kujerun nan.." ta nuna ƙasan falo, Amrish tace "mommy mu fara shiga nan" ta nuna ɓangaren Dama, haka kuwa akayi suna buɗe ɗakin sukaga wani fankacecen gado dasu wardrobe da mirror da drowowi ga ƙofar toilet ta ciki har da ƙaramin table a tsakiyar ɗakin a yayin da kujeru suke kewaye dashi, ɗakin ba ƙaramin kyau yayi ba, Angel tace "wow Mommy ɗakin kwanciyar waye?..."
Amrish tace "ke ɗakin kwanan mommy da Daddy ne kinsan tare suke kwana a gado ɗaya..."
Angel tace "eh kuwa amma to mu ina ɗakin mu?..."
Murmushi Ayush tayi tana jinsu tace "ɗakina daban na Daddynku daban wannan ɗaki nane muje na kaiku ɗakin Daddynku ..."
Anan suka fita sai suka nufi Beni ta ɓangaren hagun anan ne suka tarar da wani ɗaki suna shiga suka tarar da wani ƙaramin falo ɗan ƙwaƙwass ga kujeru a jere da ƙaramin glass table a tsakiyar ɗakin, har da plasman a manne ajikin bango, kana taka ɗakin carpet yake nutsewa da ƙafarka sai kaji wani irin naushi kamar Audiga, ga wani irin sanyin A.C mai daɗin gaske, gurin yayi shuru sai ƙarar agogon ɗakin kake ji ƙitt! ƙitt!! ƙittt!!! ga wasu arnakun labulaye kalar carpet duk an zagaye jikin bango dasu, ta gefe guda kuma a jikin bango makeken photon Ogah Junaid ne yana sanye da Kayan Sojoji na nan ƙasar california yana manne da tambarin ƙarin girma na zamowa General,
Angel ce ta zaro ido tareda cewa "Laaa Mommy ɗakin Daddy nane ga can ƙatoton photonsa..."
Amriish tace "toh ai banga Gadon kwanciya ba kuma banga toilet ba dasu wardrobe da mirror..."
Ayush ce tayi saurin rufe musu baki tareda faɗin "kuyi shuru naji motsi..." Duk sukayi tsittt, a hankali Ayush take taka carpet saboda ji take kamar zata nutse ciki tana bin hanyar da take jin motsi, buɗe labule tayi taga wani ƙofa kuma du tasa hannu ta murɗa take ƙofar ta buɗu tana shiga ta tarar da Ogah Junaid shi da Areeph suna kwance kan wani katafaren gado, tsayawa tayi ta kama kunkumi tana kallonsu, shi kuwa Junaid ya kara waya a kunne sai murmushi yaketa zabgawa alamun waya yake yi,
Areeph kuma yanata gefensa tinin bacci ya ɗauke shi...
Angel tace "wallahi room ɗin Daddy yafi na mommy kyau sosai..."
Amriish tace "ehh mana ai na Daddy falo da bedroom ne, Allah yasa muma ɗakin mu irin wannan ne..."
Angel ta kalli Ayush tace "mommy Daddy ya miki wayo ya baki ɗaki ɗaya na ƙwanciya shi kuma ɗaki biyu ya ɗauka falo da bedroom....."
Ogah Junaid ne yayi musu alamar suyi shuru da yatsansa saboda karsu tashi Areeph yana bacci..."
Ayush ganin bashida niyar gama waya kuma alama da mace yake waya yasa ta harareshi rai a ɓace taja hannun yaran suka fita, kai tsaye falo suka nufa, daga nan ne suka nufi wani part dake ƙasin beni anan ɗakin yaran yake, Angel da Amrish ɗakinsu ɗaya amma kowa gadon kwanciyarsa daban an ware musu, ga komai da komai acikin ɗakin har da computers na yara akan wani table dake gefe da kujeru biyu da mirror websites da wardrobe ɗinsu, ga toilet a gefen room, suma ɗakin nasun ba ƙaramin tsaruwa yayi ba,
daga nan suka nufin ɗakin dake can gefe dasu ɗakin Areeph kenam suna shiga sukaga ɗakinsa yafi nasu tsaruwa komai nashi ɗan ƙwakwass,
Akwai kuma ɗakin wasan yara daban an tanadar da kayan wasu irin su dokin roba manya-manyan wanda zasu iya hawa, da kekuna na yara har dasu motoci na roba wanda daga ɗan shekara ɗaya zuwa goma zasu iya shiga su tuƙa, komai da komai akwai su....
Ga kitchen ga store ga abubuwa daban daban babu abunda zaka nema ka rasa...

★★★★★

A kwana a tashi rayuwa tana tafiya yanda ya kamata, Ogah Junaid yanzu ya fara sauƙowa da fushinsa akan su Mommy haihuwar da sukayi, kullum indai zaije gurin aiki saiya bi ta part ɗin su yayi gaisuwa tareda kwasar Albarkarsu kafin ya wuce tin safe idan ya fita baya dawowa Sai Dare misalin ƙarfe 10, ga sojojinsa har gida suke rako shi da motoci,
Yara kuma har an sakasu a wani private school na manya-manyan ƴaƴan masu kuɗi, a makarantar nan kuwa babu Yaren da yaro bazai koya ba, ko wani term ana biya musu kuɗin school fees duk yaro ɗaya dubu ɗari biyu su uku gaba ɗaya dubu ɗari shida (600,000) duk wata uku👌

Yaran Mommy kuwa Masha Allah, tufarkallah yanzu watansu takwas a duniya sun girma sun zama ɓuka-ɓuka kamar kajin agric, kyawawa dasu..
Ayush kuma tin daga lokacin da cikinta ya soma girma anan ta fara shiga tashin hankali da damuwa, abunda ta shirya ba haka taso gani ba, tayi mamakin ganin ciki a jikinta bayan tayi planning kuma,
Babu yanda ta iya haka ta barshi amma ba haka taso ba,
Shi kuwa Ogah Junaid yayi farin cikin ganin haka sosai saboda shi daman ba'a son ransa taje tayi Allura ba, yayi mata dariya sosai,
sun tsara yawan yaranda zasu haifa guda biyar yanzu ga uku sauran biyu...
Mommy kuma daman ta rufe haihuwa daga waɗannan twins...

Ayush ciki ya girma sosai idan yara suka tafi school shima Ogah Junaid ya tafi gurin aiki wucewa take part ɗin mommy taje ta zauna wata rana kuma taje part ɗin Uncle Artaff,
Ƙarfe 3 yara suke dawowa daga school kullum Driver zai kaisu ya kuma ɗauko su, ta ɓangaren Arabic kuma wani babban malami ne yake zuwa koya musu a gida duk wata ana biyansa albashi mai tsokar gaske,
Karatun Alkur'ani sunyi nisa sosai kuma duk ajere suke tafiya dake yaran akwai ƙwaƙwalwa...

★★★★


Return to Nigeria

Maimoon An samu ƙaruwa ƴa mace, su Rapeekh anyi ƙanwa
Suma ta ɓangaren su komai Alhamdulillah 🙏,
Itama Lailah tana nan da ciki ya fito sosai...



Return to Jidda

Hafzat dai ana nan anata cin Amarci har yanzu, babu wani motsin ciki sun tsara cewa sai sunyi shekara uku suna cin Amarci kafin su haihu,
Babu yanda basu zagaya ba cin Amarci ƙasashen waje, sunje Saudiyya, sunje ƙasar India da Egypt da London da China dasu Canada da Cameroon sunje aikin Hajji, Umrah, Sunjejje california ma kaiwa su Mommy ziyara da Ayushert,
Hafzat tayi kyau sosai dake tana samun kulawa yanda ya kamata ga duk ƴan uwan mijinta suna ƙaunarta basa son ganin laifinta,
Akwana a tashi iyayenta ma sun zama shahararrun masu kuɗi a garin Kano dake Nigeria ata sanadiyar Hafzat,
Itama Hafzat tana godewa Allah kuma akoda yaushe tana yiwa Ayushert addu'a fatan Alkhairi saboda ata sanadiyar ta take wannan matsayin, badan ita ba da har yanzu wata ƙila tana prison.....


Ayush tana waya da mutanen Nigeria sosai taji labarin Doctor Hasheem da matarsa Maimoon sun jejje Hajji tana dawowa ta haifi ɗiya mace,
Itama Lailah a amarcin ta mijinta ya kaita Makkah,
Itama mommy anan sarki Raamud ya biya mata Makkah dake mommy duk shekara sai taje Hajj,

A kwana biyun nan Ayush ko kula Ogah Junaid batayi tana fushi dashi saboda kowa yana kai matarsa Umrah da Makkah amma bai taɓa kaita ba ko sau ɗaya, banda nan california da suka dawo bai taɓa fita ƙasar waje da ita ba,
Har kwatance take masa da Hafzat yanda mijinta Judan yake fita da ita ƙasashen waje amma ita yaƙi kaita kuma Junaid yafi su kuɗi sosai nesa ba kusa ba,
Saboda ƙorafinta yasa shi cewa yayi mata Alƙawari idan ta haihu zai kaita Makkah da sauran ƙasashen waje,
Amma taƙi yadda tace "ita nan duniya kafin ta haihu take son zuwa Makkah inyaso idan ta haihu saita je sauran kasashen Turai, haka ta dage akan saita je makkah saboda karta mutu kafin ta haihu ko a wajen haihuwa...
Ogah Junaid babu yanda ya iya haka yaje ya biya mata kujerar Makkah, har baza'a karɓeta ba saboda cikinta amma dake akwaj kuɗaɗen haka aka yadda akan zataje kuma yanada magoyan baya sosai....

Bayan Sati biyu Ayush angama shirya komai akan zata tafi Makkah, farin ciki kamar bazata mutu ba, taso taje da Ogah Junaid amma sam yaƙi zuwa sai haɗata yayi da Uncle Artaff akan zasu tafi tare saboda ana buƙatar muharraminta,
Shikenam su Ayush an tafi Makkah....




*LITTAFI YAZO ƘARSHE BAZAMU TSAYA BADA LONG STORY BA, AGURGUJE ZASU SAMU MU KAMMALA, YANZU DAI DAGA NEXT PAGE SHIKENAM MUN GAMA...*



𝑡𝑦𝑝𝑖𝑛𝑔✍️


𝗠𝗔𝗧𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗠𝗨𝗦𝗔

the wife of a tiger🐅🐅🐅🐅


𝙼𝚊𝚕𝚕𝚊𝚔𝚒𝚗 𝙰𝚜𝚖𝚎𝚎𝚝𝚊𝚑 ✍️✍️

𝙿𝚊𝚒𝚍 𝚋𝚘𝚘𝚔
𝚌𝚊𝚕𝚕 𝚘𝚛 𝚠𝚑𝚊𝚝𝚜𝙰𝚙𝚙 09065443871


*💫💫{{N W A}}💫💫*


Book two

C̶h̶a̶p̶t̶e̶r̶ 96 to 100


The End~End~End
★★ Of★★
The wife of a tiger


Bayan wata guda da tafiyar Ayushert aikin Hajj, Ogah Junaid yana zaune a Babban office ɗin shi sai faman danne danne yake a cikin computer sai ji yayi wayarsa tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login