Showing 141001 words to 144000 words out of 186041 words
Hafzat take yace "Ni ba'a kammala bane?..."
tace "an gama Uncle.."
miƙewa yayi ya nufi wajen domin ba ƙaramin yunwa yake ji ba, tin jiya da rana bai ci komai ba, mommy tace "yauwa duk kije kowa kice yazo an kammala breakfast su fito, kije ɗakin Judan shima kice yazo ...". Hafzat ta amsa da "toh mommy"
dake indai za'ayi breakfast ko lunch na rana dana dare duk a tare suke zama a dinning suci domin ƙarfafa zumunci, daman ance cin abinci a tare da mutane yakan ƙara ƙarfi zumunci a tsakani,
Hafzat part ɗin Abbah ta fara zuwa ta sanar masa cewa an kammala breakfast bayan ta gaishe shi, ta fito ta haura upstairs taje ta ɗakin Ayush tana knocking daga ciki tace "yesss..". Hafzat ta sanar mata cewa tazo suyi breakfast,
Ayush shuru tayi kamar baza tayi magana ba daga ƙarshe tace "bazan fita ba yanzu kije ki kawo mun yau Ni kaɗai zanci..."
cike da mamaki Hafzat tabi ƙofar da kallo a cikin ranta tace "lallai Aunty Ayusher baki so a zauna lafiya ba, tin jiya kina abu kamar wata mai Aljanu, shikenam..."
ta juya tayi tafiyarta tana sauƙa falo ta wuce part ɗin da aka ajiye Judan taje tana knocking ƙofar ɗakinsa ba jumawa sai gashi ya buɗe yana sanye da jallabiya a jikinsa da murmushi akan fuskarsa yace "shugo mana.."
tace "a'a daman cewa akayi nazo nace an kammala breakfast kazo aci dakai..."
idonsa akan kyakykyawar fuskarta yace. "okay am coming.."
juyawa tayi zata tafi yayi saurin riƙo hannunta dasauri ta juyo tana kallonsa, a hankali yake motsi da lips ɗinsa yace "you are a beautiful girl, please do you love me?...". kallonsa kawai take tama rasa mezata ce masa sai ƙoƙarin zamar da hannunta take..
shi kuwa ya riƙe hannun sosai yanda bazata iya ƙwata ba, ya kuma cewa "Afzee ki soni dan Allah zan riƙe ki da gaskiya ..."
Hafzat tsayawa tayi ta zuba masa ido cikin ƙanƙanin lokaci kuma ta tintsire da dariya jin sunan da ya ƙirata wai Afzee, ɗagowa tayi tace "Ni ka sake ni..."
Dariyarta ba ƙaramin burgeshi tayi ba yace "meya baki dariya?..." ya ƙarasa maganar tareda sakin hannunta kafin ya kuma cewa wani abu har ta ruga da gudu tabar wajen...
tana zuwa gurin dinning ta tarar da Abbah har ya fito yana zaune akusa da mommy shi kuwa Junaid yana ta ɗayan ɓangaren yana fuskantar su Mommy shima kujeru biyu ne a wajen nashi dana Ayush, sai kuma kujera ɗaya ta gefe itace wanda Hafzat ta zauna a gurin tana fuskantar kujerar da Judan zai zo ya zauna, Hafzat tana zama saiga Judan ya iso wajen shima duk ya gaishesu tareda zama,
Mommy ce ta kalli Hafzat tace "ina kuma Ayush?..." sai a lokacin ta tuno da abunda Ayush tace mata tace "Ohhhh na manta ta ce bazata samu damar fitowa ba wai nakai mata can ɗakinta..." ta ƙarasa maganar tareda miƙewa tsaye tana ƙoƙarin ɗaukar flask zata kai mata,
Junaid a fusace ya miƙe tsaye tareda faɗin "dakata ke ajiye kular ku fara cin abincin ina zuwa..." yabar wajen dasauri ya haura upstairs yana zuwa ya tura ɗakin yaji a ƙarƙame nan ya fara buga ƙofar,
tana daga ciki tace "wai waye ne kam?..." "Kizo ki buɗe mun..."
jin muryar Junaid yasa ta taso tazo ta buɗe masa fuska ba yabo ba fallasa har zata juya ta koma ciki yayi saurin damƙar hannunta tareda juyar da ita suna fuskantar juna cikin ɓacin rai yace "meyasa bazaki zo ayi breakfast ba?..."
kawar da kai tayi gefe tace "haka kawai" in short answer
binta yake da kallo yace "haka kawai? shin kin taɓa yin haka?..." ta finciki hannunta daga riƙon da yayi mata tace "ha'a yau banyi niyar ci da mutane ba ko ana dole ne, nace a kawo mun nan idan kuma baza'a kawo ba shikenam zan zauna da yunwa duk ba abun damuwa bane..."
ta juya kafin ta ankara ya cabki wuyanta ya mannata da jikin gini a ruɗe taɗan saki ƙara tana faɗin "wayyo Allah cikinaaa..."
Idonsa yakai saitin nata sai faman zazzaro mata su yake yana huci yace "ki kalli cikin eyes ɗina kin rigada kinsan halina, na fahimci akwai tsutsotsi acikin ƙwaƙwalwarki to kuwa zan cire miki su ɗaya bayan ɗaya,
Idan kina ganin wannan ƙaton cikin nakin ne zaisa na ƙyale ki toh kuwa tunaninki baizo daidai ba domin Junaid yakan makance ne a yayin da zuciyarsa ke tafarfasa, idan kika ce zaki ƙona mun rai wallahi zan iya wurgi dake ta window inyaso naga abunda zai faru, useless girl wanda baki san wanda yake miki amfani ba, kuma daga yau idan na sake ganin mahaifiyata ta zubar da hawaye ata sanadiyarki to kiyi kuka da kanki domin a ranar zan warware igiyar Auren mu kuma na hukunta ki...."
ya tsayar da maganar yana huci idanuwansa acikin nata yanda ya ɗago da haɓarta sama suna kallon juna,
Jikinta ne yahau ɓari tana son sauƙar da kanta ƙasi domin bazata iya juran ganin cikin eyes ɗinsa ba, tsananin tsoro da firgici ne zalla aciki idanuwansa, ta kasa sunkuyar da kanta sakamakon haɓarta daya riƙe ga hawaye duk ya wanke mata fuska, gwala-gwalan idanuwanta sunyi ja hatta fuskarta ma ya koma jaa abunka da farar mace, cikin zuciyarta kuwa kamar wanda ake lugujen hatsi tsabar bugawar da yake yi, leɓɓen bakinta kamar wanda ake jona musu shocking sai kakkarwa suke, yana jin yanda haƙwaranta suke dukan juna,
Gani take kamar zai koma mata tiger ne, firgicin da take gani a lokacin da yake komawa Damisa shine yake shirin bayyana a halin yanzu, batayi tunanin haka ba, tayi zaton zai komo mai sauƙin kai ne kuma zai iya juran duk abubuwan da take masa sai gashi ya kasa sauyawa daga tiger zuwa Junaid, bata san lokacin da ya saki haɓarta ba ya riƙo hannayenta ya ɗagesu sama yana manne dasu a jikin bango, still fuskar nan kamar zai rikiɗe zuwa tiger, idonta acikin nashi ta kasa ɗagesu kamar wacce tayi sumar tsaye tana cikin tunane tunane taji ya katseta da cewa "ki dena mun kakkarwa da lips ɗinki..."
tana so ta dakatar da faruwar hakan amma ta kasa saima ƙara kakkarwa suke, ido ta zaro tana kallonsa ganin ta kasa tsayar da kakkarwar,
"Nace ki daina mun kakkarwa da lips ɗinki..." ya ƙara maimaita mata tareda ƙara fusata, still lips ɗinta kamar wanda ake ƙara musu gudu gaba ɗaya jikinta kamar ana jona mata shocking,
Ganin taƙi denawa ne yasa ya daka mata wani irin gigitaccen tsawa har saida ta saki fitsari a jiki tareda sumewa ta faɗa jikinsa, ga tumbin cikinta yanda ya tokare shi babu halin da zasu haɗe gaba ɗaya, ɗago kanta yayi daga jikinsa ya jinginar da ita a jikin gini ido a lumshe, yanda ya jinginar da ita haka yabar wajen yaje ya ɗauki bottle na ruwa a cikin wani ɗan ƙaramin frig a ɗakin ya nufo warenta tareda buɗe murfin gorar ya tsiyayi ruwan sanyi ya watsa mata akan fuska, a firgice numfashi ta ya dawo mata tayi gefe zata faɗi yayi saurin riƙota ya maido da ita yanda take a tsayen,
a ruɗe ta haɗe hannayenta biyu tana roƙonsa cikin kuka take cewa "dan Allah kayi haƙuri wallahi wallahi bazan ƙara ba, kayi mun afuwa..." tana kuka tana masa magiya, still lips ɗinta bai daina kakkarwa ba,
Idonsa akan lips ɗinta wanda yaketa kakkarwa tana fizgar numfashi sama-sama, tana yin maganar cikin ƙiƙƙina!
Yace "kin kasa daina sheckin da lips ɗinki koh?..."
"Wallahi wallahi na kasa kayi mun rai, idan kana gabana a haka bazan iya denawa baaa..." ta ƙarasa maganar tana kuka,
Hannu yasa ya cabko sumar kanta ta baya ya ƙara matso da ita jikinsa cikin ɓacin rai yana zazzaro mata dara-daran idanuwansa yace "kika ce bazaki iya baaaa..." buɗe baki tayi zatayi magana cikin kuka yayi saurin haɗe musu baki guri ɗaya,
shuru tayi sakamakon haɗe musu baki da yayi cikin salonsa ya kamo harshenta ya soma socking a hankali yana shafar sumar kanta, yaga ba ƙaramin tsorita tayi ba kuma ba'a son mai ciki ta kasance cikin fargaba da tsoro hakan yana haifar da matsala a jariri tin kafin yazo duniya, bazai iya barin ta a cikin wannan firgicin ba shiyasa yayi mata haka saboda hankalinta ya kwanta,
saida ya ɗau mintina yana mata wasa da baki kafin itama ta soma mayar masa da martani, tayi niyar bazata biye mishi ba amma hakan ya gagara bazata iya jura ba, sun daɗe a haka kafin ya kawar da kansa idonsa akanta, ita kuma ƙwantar da kanta tayi saman faffaɗar ƙirjinsa ido a lumshe,
hannu yasa ya ɗagata suka nufi toilet zai wanke mata jiki saboda fitsarin datayi a jikinta, bayan ya kammala ya fito da ita ya sauya mata kaya, sannan ya zuba ruwa akan fitsarin ya juya yana kallon ta yace "kin ɓata mun carpet dole yau za'a fitar dashi a saka wani...."
yana rufe baki sai sukayi ana knocking ƙofar ɗakinsu,
fuska a haɗe yace "waye?..."
Tace "nice uncle dama mommy ce tace a kawo muku abincin..."
yace "ki koma da abincin kan dinning zata zo ta ci, banason shirme .." ya kalli yanda Ayush take zaune a bakin gado yace "ki taso muje..."
jiki a sanyaye ta tashi kallo ɗaya tayi mishi ta sunkuyar da kanta ƙasi da haka suka fice suka nufi falon...
Suna sauƙa falo suka tarar da kowa a zaune a kujerar falo ga Uncle Artaff shima yazo da matarsa Aunty Zainab da yaransa su uku, Junaid yana ganinsu ya fara sakin murmushi domin shi yanzu kamar bazai mutu ba tsabar farin cikin cikar ahalin mahaifinsa, gaba ɗaya gaggaisawa suka shiga yi ga mommy ga sarki Raamud suna zaune a kujera 3 seater saita ɗayan kujera kuma Judan ne sai kuma Hafzat dake zaune a ƙasan carpet, shima Junaid kujera ya samu ya zauna tareda faɗin "yanzu nake shirin zuwa muku ai..."
Uncle Artaff yace "wallahi kuwa ɗazu maimartaba ya ƙirani ai yake cewa akwai matsala agidan nan duk ya sanar mun abunda ke faruwa na Aurensa da Hajia...."
Mommy kallon sarki Raamud tayi ita sam bata san har ya sanar musu bama,
Junaid yayi murmushi kansa a sunkuye,
Ita kuwa Ayush dinning ta wuce ta zauna tareda tsiyayan ruwan tea duk tana jin abubuwan da suke faɗi, ji tayi Junaid yace "Ni wallahi so nake ace zuwa gobe an ɗaura Auren mommy da Abbah..."
dasauri ta burtsar da shayin data kurɓa tareda zaro manya-manyan idanuwanta tana kallon yanda Junaid yake,
Mommy tace "a'ah yayi sauri ai My son"
Junaid yace "ohh soyayyar wajen bata ƙare ba kenam?..."
Duk suka tintsire da dariya suna wasa da dariya a tsakaninsu, Sarki Raamud yace "daman matsalar akan Ɓingel ɗina ne bansan meye matsalar ta ba, kwata² bata son Auren nan, shine nake so a bincika mun ita ko akwai wani abu aranta ne..."
Junaid yayi saurin cewa "meye abunda yake ran natan wanda zai hana Aurenku? kawai ku rabu da ita daman zaman da tayi a daji Aljanu sun shafeta shiyasa kuka ga tana wasu abubuwa kamar mahaukaciya..."
Mommy tace. "Aljanu kuma?..."
yace "sosai ma Aljanu ne na masifa acikin wannan dajin, nima na gansu da idona balle ita da tayi watannu a wajensu, kuma akwai wani malamin daya tabbatar mun da cewa Yushert tana da Aljanu na rashin ji da fahimta, sun ɗanso su taɓa mata ƙwaƙwalwa, kawai kar ku biye mata..."
ya ƙarasa maganar tareda kallon wajen da take, itama ido ta zazzaro tana masa wani irin kallo, acikin ranta kuwa cewa take "tabb ɗin amma Yaya Junaid ba ƙaramin raina mun wayo yayi ba wallahi, kenam zaisa su rinƙa mun kallon mahaukaciya alhalin babu komai a jikina, toh wallahi Auren nan bazan bari ayi ba, zan hura wa Abbana wuta ne har saiya haƙura da maganar Auren aikin banza kawai, yaushe aka taɓa yin haka surkuwarka ta zamo matar ubanka mttssw..."
Uncle Artaff yace "toh amma meyasa baka sanar mana haka ba tin abaya? ai da mun tashi tsaye akanta..."
girgiza kai Junaid yayi sannan yace "yanzu ne abubuwan suka fara bayyana..."
Mommy tace "Allah sarki my daughter insha Allahu za'a nema mata magani, ga zaman da tayi a prison Sam banji daɗin haka ba, shiyasa gaba ɗaya nake ganinta a fizge..."
Sarki Raamud kawai yana jinsu ne amma yasan Ɓingel ɗinsa bata da wasu Aljanu, domin tin lokacin da aka haifeta yayi mata wani sihirin da ba wani Aljani ko Aljanar da zata raɓeta ko ta cutar da ita ko kuma