Showing 126001 words to 129000 words out of 186041 words
ta manta dashi, cikin kasalalliyar murya tace "sunansa Junaid Khan yana da matarsa har ta kusan haihuwa..."
Lailah tayi saurin katse mommy da cewa "a'a mommy daman ba cewa zanyi inasonsa ba, ni yanzu burina shine komai nawa ya dawo mun ƙwaƙwalwata..."
Murmushi mommy tayi tana girgiza kai tace "Lailah kenam ni ɗin ma kawai nasar miki nayi saboda ki fara sanin kowa.."
itama Lailah murmushi tayi tace "Allah Sarki mommy nima wasa nake miki kiyi haƙuri..."
kaiwa hannu mommy tayi tana shafar suman gashinta ba tareda tace komai ba..
suna cikin wannan halin sai suka ji sallama an turo ƙofar ɗakin, Mommy da Doctor suka amsa sallamar cikin kulawa,
Maimoon ce ta shugo da yaro a hannunta ta rufa masa farin towel a kansa, sai kuma Ammy da Daddy! Doctor ne ya nuna musu waran zama tareda musu barka da zuwa suka gaigaisa, itama mommy tana murmushi suka gaisa cikin aminci da kyautatawa juna,
Daddy ne yazo har bakin gadon Lailah ya zauna yana faɗin "Autar Mama da Abba yadai?..." Lailah zuba masa ido tayi tana murmushi tace "babu komai..."
Mommy tace "waɗannan ɗin kin ganesu ne?.."
Lailah tana kallonsu tace "na ganesu mana ai suna yawan zuwa mun, kuma Doctor ya ce mun suna taka rawar ganin na samu lafiyata..."
Daddy yace "ni naso ace ma asibitin ƙasar waje aka fita da ita wata ƙila za'ayi dacen dawo mata da memory sense ɗinta..."
Lailah tayi saurin katse shi da cewa "a'a Daddy nafi jin daɗin zamana a wannan asibitin domin Doctor yana bani kulawa sosai da sosai.." ta ƙarasa maganar tana kallon Doctor Mansur wanda shima kallonta yake yana murmushi ...
Daddy yace "toh shikenam ai naga yanzu kin samu lafiya koh?.." jinjina kai Lailah tayi tareda cewa "sosai ma Daddy yanzu bana jin komai a jikina"
Daddy yace "Masha Allah haka nake son ji Autar Abba,
Daman yau nazo ne ma akan a sallameta zamu wuce gida da ita, akwai ƴan uwan mahaifiyarta cikin wannan satin zasu zo duba jikinta, ƙwanaki ƴan uwan mahaifinta ne suka zo, insha Allahu zan cigaba da riƙeta a gidana..."
Mommy tana zaune a gefe guda tace "Allah Sarki gaskiya rankayadaɗe kana kokari kam ka riƙe zumunci sosai, kace daman kuna ziyartar ta shiyasa ta saba daku..."
Murmushi kawai Daddy yayi domin kafin mahaifinsu ya rasu ya rigada ya bashi amanar yaran, kuma yaso su Doctor Hasheem su dawo gidansa da zama amma fur yaƙi yadda yafi son zama agidan iyayensa ganin haka yasa su Lailah suma suka ƙi tafiya subar gidan, kuma sunƙi zuwa gurin ƴan uwan iyayensa domin su ɗin haɗamammu ne suna harin dukiyar da aka bar musu ne...
Lailah tana zaune taji Ammy tana faɗin "nidai na ƙosa naji Lailah tamun magana amma taƙi kulani.."
Dariya Lailah tayi tace "wallahi Ammy mantawa nayi, amma amun Afuwa .."
Ammy tace "toh na miki Afuwan, gashi yau nazo miki da ƴar uwarki Maimoon da jaririnku..."
Lailah tana dariya tareda leƙen fuskar Maimoon tace "laaa daman itace Aunty Maimoon ɗin da kikace ita kaɗai ce ɗiyarki kuma ta haihu? Ayyah gashi kuwa kyakkyawa tanada kyau, shin zan iya ganin jaririn namun?..."
Maimoon murmushi tayi sannan tace "ba komai gashi nan.." ta tashi ta miƙa mata yaron tana mamakin yanda rayuwa ta sauyawa Lailah, gashi har itama ta mantata...
tana cikin wannan tunanin Lailah ta katseta da cewa "ya sunansa?"
Maimoon tace "Abubakar amma inkiya kuma Rapeekh.."
"Kaii kai kaii suna mai daɗi gashi shima Balarabe ne fari tas, ya ɗauko farinki amma ban saniba ko Babanshi ma fari ne ko kuwa baƙi, amma ina Abban shi yake?.."
a cewar Lailah wacce idonta ke kan yaron,
Maimoon sunkuyar da kanta tayi ƙasi domin batada bakin magana, sai Ammy ce tace "Abbansa baya gari yayi tafiya ne.."
tace "Ayyoh..."
Bayan wasu seconni Lailah ta fara shessheƙar kuka ga yanda hawaye ke zubo mata, hannunta kuwa yana riƙe da yaron,
gaba ɗayansu kallonta suke cike da mamaki, "daga wasa da dariya sai kuma kuka?"..
a cewar Daddy yana kallonta, kanta a sunkuye take cewa "ina son ganin halin da Yayana yake a prison, inason ganinsa ko hankalina zai ƙwanta, bansan ya kamannunsa yake ba, Yayana bai kamata ace yana zaune a prison ba yanda muke da dukiya kamar kamar...." lokaci guda ta sake fashewa da kuka na gaske,
Doctor gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake domin ba'a son tana yawaita kuka saboda ana buƙatar hutawar ƙwaƙwalwarta,
dasauri ya miƙe tsaye yana faɗin "kinga Baby ki ƙwantar da hankalinki yanzu za'a kaiki bana son yawan kukan ki, shin kinaso na shiga damuwa?..."
dasauri ta girgiza masa kai alamar a'ah
yace "toh banason kukan ki, idan kuma kinason na shiga damuwa shikenam cigaba da kukan..."
share hawayenta tayi tareda cewa "na daina JAAN bazan ƙara ba, amma ku kaini gurin Yayana dan Allah..."
Daddy yace "to zamu kai ki yanzu kuwa, daga nan sai mu wuce gida ko?.."
Lailah kamar zatayi kuka jin za'a wuce da ita gida tace "kenam na daina ganin JAAN?.."
Doctor yace "a'a zaki rinƙa ganina akai akai kinji, babu yanda za'ayi nayi nisa dake Baby..."
murmushi tayi sannan tace "Nagode JAAN..." mayar mata yayi da martanin murmushi duk da shima ransa ya sosu sosai jin Lailah zata koma gida, yanzu ba kullum zai rinƙa ganinta ba...
duk waɗanda suke wajen babu wanda bai fahimci alaƙar dake tsakanin Doctor Mansur da Lailah ba saidai su nasu soyayyar a bayyane take amma sirrinta tana cikin jijiyoyinsu wanda har yanzu basu fito fili sun sanar cewa suna son junansu ba,
Bayan an shirya Lailah fita akayi da ita waje saboda motar tana harabar hospital, tana fita waje taji kamar ba'a duniya take ba, ga rana wanda ta daɗe bata saka shi a ido ba, wani irin haske garin yayi mata saida ta nemi a bata glass dasauri Doctor ya ciro glass ɗin idonsa ya sanya mata, daga nan ta fara ganin daidai,
cikin yanayin damuwa Doctor ya kamo hannun Lailah tareda miƙa mata ledar hannunsa yace "Baby ga chaculaty nakin..."
tana sharar hawaye ta karɓa tana godiya...
shiga motar sukayi Lailah da Maimoon a bayan seat sai kuma Ammy da Daddy a gaban motar, Daddy ne mai driving ɗinsu,
A yayin da ita kuma Mommy ta shiga motarta tabi bayansu kai tsaye Prison suka nufa...
Doctor Mansur ya juma a tsaye a harabar hospital yana jimamin tafiyar Lailah....
★★★★★★
Hafzat tana zaune a falo tin ɗazu ko motsawa batayi ba, tana kallon tv taji anata knocking ƙofar falo, a tunaninta mommy ce ta dawo dasauri ta tashi taje ta buɗe, ganin wanda yake knocking ne yasa ta tsaya tana masa kallon rashin sani,
wani farin mutumi ne gabjejen soja yake tsaye shima binta yake da kallo daga sama har ƙasa, shigarta ba ƙaramin burgeshi yayi ba tana sanye da blue jeans dogo da kuma riga t-shirt mai dogon hannu, gata gajeriya ƴar ɓulɓul da ita, hips ɗin nan ya zauna ga breast a ɗage, ƴar kyakkyawar bafulatana!
ganin yanda yaketa kallonta ne yasa ta motsawa tace "ina wuni..."
ƙayataccen murmushi yasau mata tareda faɗin "your welcome Baby girl..."
sunkuyar da kanta ƙasi tayi tana wasa da yatsunta, ta kuma ji yace "Oga yana ciki ne?.." ɗagowa tayi tana kallonsa cikin rashin fahimta ba tareda tace masa komai ba
girgiza kai yayi sannan yace "hala bakya jin Hausa koh?..."
murya ciki² tace "waye Oga?.."
murmushi ya kuma yi dake sojan yana da sauƙin kai yace "maigidan nan toh.."
Dasauri ta ɗaga masa kai tareda faɗin"eee yana nan"
yace "ok bani guri na wuce mana kodai kina mun rowar shiga falonku ne..."
matsa masa tayi tana girgiza kai, yace "jeki ƙira mun shi toh"
jiki a sanyaye ta wuce kai tsaye upstairs ta haura, shi kuma zama yayi akan sofa yana bin bayanta da kallo,
yana ƙwance akan gado sai faman sharar bacci yake, a cikin baccin ne yake jin knocking a hankali yake buɗe eyes ɗinsa daƙer ya iya motsa lips ɗinsa yace "waye?.."
cikin kakkarwar murya tace "Uncle ni ce.."
"Ok come in"
turo ƙofar tayi a hankali ta shugo kanta a ƙasi saboda gudun yanda zata ganshi,
ganinta yasa ya tashi tareda sauƙe ƙafarsa ƙasan carpet daga shi sai 3quater zuwa cinyarsa ko riga babu a jikinsa, tasowa yayi yana takawa a hankali kamar mai tambayar ƙasi yazo har gabanta yana yamutsa fuska irin baccin nan bai gama isar sa ba
yace "keee..."
a ɗan ruɗe ta ɗago ta kalle shi, gabanta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin jikinsa fari sol duk gargasa ga ƙirar ƙarfi tinin ta ruɗe murya na kakkarwa take faɗin
"Daman! Daman! Damann wani ne ya zo nemanka...."
hannu yasa ya ɗago da haɓarta yana kallon fuskarta yace
"meyasa kike jin tsoro na? nayi miki kama da dodo?..."
dasauri take girgiza kanta kamar ta rausa ihu haka take ji tsabar tsoro da fargaba, kuma tana tsoron kar Aunty Ayushert tazo ta tarar da ita a cikin ɗakinta ga kuma mijinta a ɗakin.
tana cikin wannan tunanin taji yace
"waye yazo nema na?..."
da sauri tace
"wallahi ban sani baa amma soja ne..."
Allah! Allah take tabar ɗakin nan domin kwarjini ɗakin yake mata domin bata taɓa shugowa cikin ɗakin nan ba sai yau...
ƙura mata ido yayi yaɗan sau mata murmushi ba tareda ta sani ba sakamakon kanta dake kallon ƙasan carpet
yace "ki daina jin tsoro na kinji ko? ki ɗauke ni a mazannin uncle ɗinki..."
Kaɗa masa kayi kawai tayi ba tareda ta ce komai ba,
ya kuma cewa "kije ina zuwa..."
sai a lokacin taji wani sanyi a ranta kamar zata dungura ƙasi haka ta tafi a gaggauce ko waiwayowa bata yi ba,
jiki a sanyaye ta sauƙo falo tace "yana zuwa.." ta ƙarasa maganar tareda wuce zata koma ɗakinta taji mutumin ya dakatar da ita "please wait..."
juyowa tayi tana kallonsa fuska kamar zatayi kuka tace "Na'amm.."
fuska a sake yace "zo ki zauna mana"
ta girgiza masa kai tareda cewa "inaso zan shiga ciki ne"
"ban yarda ba to, kizo ki zauna anan" ya ƙarasa maganar yana nuna mata wurin da zata zauna a kusa dashi,
zaro ido tayi tace "kayi haƙuri zan zauna anam" ta ƙarasa maganar tareda ɗosana ɗuwawunta akan sofa mai ɗaya wanda yake ɗan nesa dashi,
Murmushi yayi tareda cewa "wooo this girl..."
ita kuwa kai a sunkuye fuska ba Annuri domin ba ƙaramin takurata yayi ba,
bata ankara ba taji shi a kusa da ita ya zauna akan hannun kujerar da take, yasa hannu ya tallafo kanta suna kallon juna
yace "fatan dai ban takuraki ba ko?.."
dasauri ta girgiza masa kai tareda kawar da kanta gefe,
a hankali ya furta "meye sunanki?.." a saitin kunnenta,
ɗagowa tayi ta kalle shi sannan tace
"Hafzat..."
yace "wow Nice name, Ni kuma *Judan*..."
ya kuma cewa "ajinki nawa a school?.."
tace "aji 3.."
yace "wow congrats kina level 3 but which university?..."
ɗan turo lips ɗinta tayi sannan tace "a Sacondary fa nake.."
juyar da eyes ɗinsa yayi yana faɗin "sacondary duk girmanki? how old are you?.."
kamar baza tayi magana daga ƙarshe tace "18 years old..."
hannu yasa rufe bakinsa yana ƙunshe dariyar ciki yace "wooo kice girman bread kika yi.."
Hafzat takaici kamar zai mata mai cikin ranta take cewa "wannan akwai ɗan rainin wayo wallahi, amma shikenam yanzu komai ya tambayeni bazan kulashi ba wallahi, gaba ɗaya ya takurani..."
tana cikin wannan zancen zuci taga Uncle Junaid ɗinta yana sauƙowa daga saman stairs iya farar jallabiyarsa kawai ya ɗora,
shi kuwa Judan bai ma san Oga Junaid ya sauƙo ba, idonsa akan Hafzat ko ƙibtawa baya yi, yarinyar tana matuƙar