Showing 165001 words to 168000 words out of 352722 words

Chapter 56 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30787

da kiran wata Nurse ya gaya mata magungunan da zata amsa musu a Pharmacyn nasu, cewa Dr Jabeer ba lfy.
Ai lokacin ɗaya sai gata da manyan likitoci har uku.
Cikin tarin kulawa, suka fara dubashi ganin yana gab da fita haiyacinsa ne, yasa suka mishi allurar bacci.
Da sauri Dr Arabi kuma ya kira, Jalal ya sanar mishi.
Jalal kuwa dake falon Hajia Mama ba tare da ya gaya mata ba ya miƙe da sauri ya fita.
Tana tambayarshi lfy.
Yace lfy sabida baison tayar mata da hankali.
A bakin ƙofar fita ya haɗu da Ya Affan da sauri ya kamo hanunshi suka juya yana cewa.
"Ya Affan Hamma Jabeer ba lfy, yana Genaral Hospital Ɓadawaya, yanzu Yayan abokina Umar Dr Arabi abokinshi ya kirani ya gaya min yace baida lfy sosai fa".
Ai da sauri Affan ya fara lalubo car key dake cikin al'jihunsa cikin kiɗima da tashin hankali yace.
"Muje, muje da sauri mu tafi a maidashi Valli Hospital yafi kwararrun likitoci".
Kusan a tare suka shiga motar Affan suka tafi.

Kafin suje kuwa tuni bacci ya ɗauke shi, an ɗaura mishi ruwa da allurai.
Sauran Doctors ɗin sun fita.
Sai Dr Arabi da yake zaune gabanshi.
Da sauri Affan yasa hannun shi ya taɓa jikinshi tamkar wuta.
Jalal kuma yatsarshi daketa karkarwa yake kallo tare da rauni a fuskarshi yace.
"Yah Arabi meya sameshi ne?".
Cikin sanyi Dr Arabi yace.
"To wlh nima shigowa kawai nayi na sameshi yanata karkarwa, yace min zazzaɓi yakeji sanyi na damunshi.
Na kira Nurse ta kawo min injections and drip kafin muyi mishi allurar ma tuni ya kusa suma, abun yafa bani tsoro.
Amman Alhamdulillah kunga yanzu kuma da sauƙi".
Ajiyan zuciya sukayi kana suka zauna a nan, ba tare da sun gayawa kowa ba.


A can masarautar Joɗa kuwa.
Cikin tarin firgici da al'ajabi Jamil da Ummi ke kallon Shatu.
Data fizgo macijin da ƙarfi cikin tukunyar.
wurgar dashi tayi a ƙasa sai gashi yayi wutsul-wutsul sau biyu, shike nan ya mutu."
Mazargin mondo ta fitar da kuma hula wanda duk na Sheykh ne.
Cikin murya mai rauni tace.
"Yanzu Jamil zaka iya taɓasu.
Haɗasu kaje in akwai inda zaka wurgar dasu ka wurgar dasu, ka fasa tulun.
Kada ka binne macijin ya bushe akeso.
Ummi ɗauki Hular Yah Sheykh da zariyarshi a wonkesu.

Da sauri Jamil yace.
"Eh akwai inda zan wurgar dasu".
Nan ya tattare macijin da da layun ya saka cikin tulun ya fita.
Key ɗin ƙofar baya ya ɗauka ya buɗe ya tafi cikin Garden ɗin.
Tafiya yayi sosai saida yaje can cikin dajin ya fasa tulun macijin da layun suka watse kana ya juyo ya dawo ba tare da ko waiwaya ba sabida tsoro.


Ita kuwa Ummi bathroom ɗin shi ta shiga a take ta wonkesu kana ta fito dasu.
Cikin sanyi Shatu tace.
"Wai hannuna Ummi yi sauri ki wonko gero ki kawo min ruwan tsarin."

Da sauri Ummi ta fita.
Murmushi tayi ganin Ɗalha mai gyaran tayis yaci yayi haniƙan yana kallon tv.
Cikin sauri tace.
"Yi haƙuri dan Allah Ɗalha muna tattare ɗakin ne da yake tayis ɗin ƙasan gadone ya fashe".
Cikin shan iskar yace.
"Ba komai Ummi".
To tace kana taje ta wonke gero, sannan ta fito da ruwan tsarin tazo.
Tana zuwa ta bawa Shatu cikin ramin ta watsa ruwan.
Kana ta fara tura ƙasar da kuma fashesshe-fashesshen tayis da fulo ɗin tanayi tana yayyafa ruwan.

Dai-dai lokacin Jamil kuma ya shigo.

Ganin yadda hannunta yaketa karkarwane yasa ya tayata tura ƙasar saida suka gyara komai fes kamar ba fasawan ganganci akayiba.
Kana ta miƙe tare dasa hannun hagunta ta riƙo na damanta tana cewa.
"Shima Yah Sheykh dole zaiji wani abu a jikinshi duk inada yake".
Sai kuma tayi shiru tare da rumtse idanunta tace.
"Wash hannuna".
Cikin sauri Ummi tace.
"Sannu hannun ya gaji ko".
Kai kawai ta gyaɗa mata.

A haka suka fito falon. Kai tsaye bedroom ɗin ta ta nufa.

Shi kuwa Jamil yayiwa Ɗalha jagoro,
Suka shiga suka gyara wurin da aka fasa ɗin fes.
Kana Ummi ta share wurin ta goge, sannan suka tura gadon suka maidashi.

Nanma ta ƙara gyara ɗakin Jamil kuwa ya ɗauki Ɗalha ya maidashi wurin aikinshi.

Ummi na gamawa taja ƙofar ta rufe tana al'ajabin wannan abu da ta gani da idonta.
Kitchen ta wuce ta ɗaura musu Lunch tana kiran Umaymah ta gaya mata duk abinda ya faru.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kaɗan daga cikin mafarkan da nakeyi kan Sheykh ya auro ba fulatar daji sun fara tabbata.
Ya Allah kasa abinda zai faru a sanadin shigowar Shatu masarautar Joɗa ne kake nunamin a mafarkaina".
Umaymah ta faɗi lokacin da Ummi ta mata bayanin abinda ya faru.
"Amin Amin, Ummi tace kana ta katse kiran jin muryar Aunty Juwairiyya da Hibba."

Umaymah kuwa da sauri ta kira Lamiɗo ta gaya mishi abinda ya faru.
Murmushi yayi irin nasu na manyan sarakuna yace.
"Alhamdulillah warakafa nan shigowa masarautar Joɗa baki ɗayanmu zamu rabu da mugun iri a cikinmu, kada ki gayawa kowa Khadijatu kinji ko".
Cikin jin daɗi Umaymah tace.
"In sha Allah kuwa ko Jadda bazan gaya mishi ba".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Masha Allah, Allah ya miki al'barka Khadijatu da ace duk ƴan uwa haka suke riƙe ƴaƴan yar uwarsu da zumunci ya ƙara ƙarfi kin musu abinda mahaifiyarsu bazata iya musuba".
Amin Amin tace kana ya katse kiran.

A cikin ɗakin Shatu kuwa.
Wani irin...!


By
*GARKUWAR FULANI*


Wani irin zufane ke tsastsafo mata.
Tako wani hudan gashin jikinta.
Gaba ɗaya ji takeyi hannunta na dama wanda dashi ta buɗe tukunyar ƙasan yana wani irin suka kamar ana tsikarinta da allurai masu dafi.

Jiki na rawa ta konta bisa gadon.
Wani zazzafan zazzaɓi ne ya rufeta a take.
Cikin rawan jiki tasa hannun hagunta ta jawo tattausan blanket ɗin ta rufe jikinta.
Rumtse idanunta tayi da ƙarfi tanajin zafin na ratsa mata jiki a hankali take addu'o'in cikin ranta. Jikinta na ci gaba da ɓari.

Ita kuwa Ummi a kitchen ita da Hibba da Aunty Juwairiyya sukayi girki suka gama.
Saratu ta share ko ina.

Ganin azahar tayi ne, sukaje sukayi salla kana suka dawo falon.
Shiru-shiru Shatu bata fitoba, hakane yasa Ummi tace Hibba take ta kirata.
Hibba na tafiya Jamil ya shigo.
Nan suka zauna.
Juyowa Ummi tayi tana kallon Hibba dake cewa.
"Ummi! Ummi!! Aunty Shatun kamar bata da lfy, naga sai rawan sanyi takeyi."

Da sauri Ummi ta miƙe ta nufi cikin ɗakin bisa sallaya ta sameta alamun tayi sallan azahar kenan.
Da sauri ta nufi inda take tare da cewa.
"Shatu meyake damunki".
Cikin sanyi murya tace.
"Zazzaɓi ne Ummi".
Cikin tausayawa tace.
"Subahanallahi sannu ko! Barin in Sheykh ya dawo sai ya dubaki, yanzu muje ki samu kici wani abu".
Cikin rawan murya tace.
"Na ƙoshi Ummi".
Hannunta takai ta taɓa jikinta kamar wuta cikin kula tace.
"To me kikaci da zakice kin ƙoshi?".
Danne kukan dake son kubce mata tayi, wanda halittartace dama in ɓata da lfy dai to kuka kuma zata shashi.
Cikin rawan murya tace.
"Na ƙoshi bazan ciba".
Cikin jin ba daɗi Ummi tace.
"To tashi in taimaka miki ki koma kan gado.
Sai anjima kici abincin".
Ta ƙarishe mgnar dasa hannu ta kamo hannun daman Shatu.
Da sauri ta miƙe tare da saƙin ƙara a hankali tace.
"Wayyo Ummi hannun zafi, kamanin wannan in tashi".
Ta ƙarishe mgnar hawaye na zuba.
Cikin tsoro Ummi tace.
"Ayyah sannu. To amman kin bige hannune ko kin yankene?".
Cikin karkarwan zazzaɓin tace.
"A a".
Konciya tayi a kan gadon.
Borgo Ummi taja ta rufeta dashi.

Kana ta fita tana cewa.
"Allah ya sauwaƙa".

A falon ta samesu zaune, cikin sanyin jiki tace.
"Jamil ina Jalal naga kai kaɗai".
kanshi ya ɗago ya kalli Ummi tare da cewa.
"Yau tun da mukayi breakfast ban ganshi ba.
Bari in kirashi".
To tace kana ta zauna. Shi kuma wayarshi ya zaro ya kira layin Jalal.
Bugu biyu ana uku ya ɗaga sabida baya son sautin kiran wayarshi ya tashi Hamma Jabeer ɗin nasu daga baccin da yakeyi.
"Hello Jalal ina kake ne, yau tunda safe ban gankaba".
Cikin sanyi yace.
"Jamil Hamma Jabeer baida lfy, yanzu haka muna asibiti dashi nida Yah Affan".
Cikin ruɗani Jamil ya kalli Ummi kana ya kalli wayar tare da cewa.
"Meya sameshi? Wanne asibiti kuke?".
Affan ne ya amshi wayar Jalal tare da cewa.
"Jamil kadafa ka gayawa Mama hankalinta zai tashi.
Jikinshi da sauƙi sosai zazzaɓi ne kawai yanzu kam ma bacci yakeyi, yana farkawa dai zamu dawo gida".
Cikin ɗan samun nitsuwa yace.
"Ka tabbatar Ya Affan?".
"Zan maka ƙarya ne?".
Affan ya amsa mishi tambaya da tabaya.
Kana yace.
"Bawa Ummi wayar".
To yace kana ya miƙa mata wayar.
Nan yace mata. Sheykh ba lfy, amman jikinsa da sauƙi.
Su kontar da hankalinsu in ya farka zasu dawo.
To Ummi tace tare da mishi addu'a kana sukayi sallama.

Shiru sukayi a falon suna nazarin to meke faruwa.
Musamman shi Jamil da yaji Ummi na cewa Aunty Juwairiyya cewa Shatu ba lfy.

A haka dai sukaci abinci.

Sheykh Jabeer kuwa, sai ƙarfe Shida na yamma gab da magriba ya farka.
Da sauri Affan ya matso kusa dashi.
Tare da kama hannunshi yace.
"Sannu Hamma Jabeer, ya jikin naka? Da sauƙi ko? Me yake maka ciwo?".
Shiru yayi yana kallonsu yana tuna lokacin da yayi baccin.
Jalal ne ya ɗan kalleshi cike da rauni yace.
"Hamma Jabeer ya jikin naka.
Me zakaci in kawo maka?".

A hankali yace.
"Meyasa baku tadani ba nayi sallan azahar, la'asar, gashi har magriba ta kusa."
Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa zaune da alamun ɓacin ran rashin tada shi da basuyi ba.
A hankali Affan ya miƙe tare da kamo hannunshi alamun zai tallafa mishi ya tashi.
"Janye hannunshi yayi tare da kallonshi cikin alamun faɗa yace.
"Lokacin Sallah yayi kuna ganina ku barni ina baccin asara baccin yammaci sabida baku ɗauki salla da mahimmanci ba, ai ko bana gani bana mgn zaku tasheni kuyi min alamun lokacin salla yayi inyi niya kuyi min al'wala inyi salla.
Bare ina cikin hayyacina, ku jinyarku sai kace jinyar kafurai babu tada majinyaci batun salla".
Ya ƙareshe mgnar yana nufar hanyar bathroom.
Da ido suka bishi suna cewa.
"Kayi haƙuri".
A hankali yake taku sabida har yanzu yanajin kamar ana zare mishi jijiya a jikinshi dai-dai inda zanen tafiyar macijin nan yake.
Al'wala yayi kana ya fito, yayi salla.
Sannan yace.
"To mu tafi ko".
Cikin sauri sukace to sukabi bayanshi.
Suna sauƙa ana kiran sallan magriba a masallacin cikin asibitin.

Nan suka tsaya a masalacin asibitin sukayi sallan magriba.
Kana suka nufi gida.
Ana kiran salla. Isha'i suna shiga masarautar Joɗa shiyasa kai tsaye suka wuce masallacin.

A cikin masarautar kuwa, sosai jikin Aysha yayi zafi da zazzaɓin.
Da kyar Ummi ta taimaka mata tayi al'wala kana tayi salla.
ana ta zauna saida tayi sallan isha'i kana itama tayi.
Sannan ta kalli Hibba tare da cewa.
"Hibba haɗo min koda tea ne ki kawo in bata tasha".
Cikin rauni ta girgiza kai alamun bazata shaba, murya na rawa tace.
"Ummi zan kwanta".
Cike da mamaki tace.
"To Aysha jinya ba abinci kuma ai shike tsananta jinyar.
Ki ɗan sha koda tea ɗin ne in Sheykh ya dawo ya dubaki.
Shiyama ɗin baida lfy yau wuni yayi kwance a asibiti".
Cikin rumtse idanunta tace.
"Ba matsala zaiji sauƙi, dama dole zaiji a jikinshi alamun a kunce abubuwa da yawa a jikinshi".
Sai kuma ta miƙowa Ummi hannu tare da cewa.
"Ummi zan kwanta, kaina ciwo kamar zai rabe gida biyu hannu ciwo kamar zai tsinke".
Cikin tausayawa tace.
"Aysha ko dai taɓa abun nanne da kikayi ya jawo wannan abun".
A hankali tace.
"Wata ƙil".
Amsar kofin da Hibba ta miƙo mata tayi tare da cewa.
"Yauwa amshi kisha kinji ko Aysha".
Cikin sauri ta girgiza kai sabida bazata iya ci ko shan wani abun a yauba irin zafin da takeji".

Ganin haka ne yasa Ummi ta taimaka mata ta miƙe tsaye kana ta koma kan gado.
Sannan ta rufe mata jiki tace.
"Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu kafin Sheykh ya dawo".
Cikin sanyi tace.
"To amma Ummi kada kice mata na cire wani abu".
To tace kana ta juya ta fita.
Tuni dama Hibba ta fita.

A falon ta samesu harda Jalal Affan da kuma Sheykh yana zaune da alamun jinya a jikinshi.
Jamil kuwa tamkar likita haka ya tsareshi da tambayoyin meke damunshi meke mishi ciwo.
Ummi kuwa babbar yatsarshi da har yanzu take motsine ta kalla tare da cewa.
"Sheykh sannu ko! Ya jikin naka? Da sauƙi ko?
Me zan kawo maka kaci?".
Cikin lumshe ido yace.
"Alhamdulillah da sauƙi".
Aunty Juwairiyya da Ya Jafar da yanzu suka shigone,
Ya Jafar ne ya zauna a gabanshi.
Yana kallon yatsarshi. Murmushin yayi wanda ya bawa su Jalal Jamil Affan mamaki yayi kana ya kalli Sheykh sai ya kuma miƙa ya zauna gefenshi ya ruggumeshi.

Ummi ce ta kuma kallonshi tace.
"Sheykh me kakeso in dafa maka".
A hankali yace.
"Ummi bani nono mai sanyi da zuma, insha ya isa".
Da sauri ta juya ta nufi kitchen, Jim kaɗan kuwa ta fito da cup a cike da haɗin mai sanyi.
Amsa yayi tare da riƙewa.
Yana kallon Hibba da ke cewa.
"Hamma Jabeer Aunty Aysha ma bata da lfy, yau babu abinda taci tun safe".
Uhum yace tare da kai kofin burgeggen kinɗirmo da zuma a madadin sugar bakinshi.
Zuƙa ya ɗan yi, a hankali ya lumshe idonshi jin sanyin nonon ya ratsashi.
yaji zafin da yakeji cikin jikinsa yana raguwa.
Hakane yasa yaci gaba da sha, idonshi ya ɗan ɗago ya kalli Ummi jin tana cewa.
"Sheykh Aysha fa babu lfy sosai.
Dama kai nake jira, ka dawo ka dubata".
Maida idonshi yayi bisa kofin
Yayi kamar baijiba, saida ya shanye madarar ne, ya ɗan miƙe tsaye cikin sanyi yace.
"Affan je ka ɗauko Dr Kubra tazo ta dubata".
Da sauri Affan yace.
To kana ya miƙe ya fita.

Shi kuwa Sheykh a hankali jiki a mace ya wuce Side ɗinsa.
Cikin jan ƙafa ya ƙarasa bedroom ɗinsa.

Kai tsaye kan gado ya faɗa sabida har yanzu allurar baccin tana ɗan fizgarshi ko dan haka ya haɗu da rashin lafiyar ne.

Ko gariyarsa bai cireba ya kwanta.
Yana konciya kuma ya fara tasbihi kamar koda yaushe.
Lokaci ɗaya daddaɗan bacci ya kwasheshi.

A falon kuwa bayan ya shiga ne.
Aunty Juwairiyya ta miƙe ta tare da cewa.
"Ummi bari in koma na bar yara su kaɗai".
Ta miƙewa Ya Jafar yabi bayanta.
Jalal kuwa da Jamil Dinning area suka nufa dan cin abincin dare.

Ba jimawa Affan ya dawo.
Da wata Kekkyawar mata yar duma-duma mai sakin fuska.
Bayan sun gaisa da Ummi ne Hibba ta gaidata kana suka wuce ɗakin Aysha.
Bisa jagorancin Ummi.

Da sauri ta ɗan yaye borgon tare da kife tafin hannun ta kan goshin Aysha da yake kamar wuta.
Da sauri ta zauna kan Bedside.
Cikin kula ta kamo hannunnta mai ciwon.
Da sauri ta buɗe idonta tare da tashi zaune, murya na rawa tace.
"Wayyo Ummey na".
Cikin tausayawa tace.
"Afwan hannun yana ciwo ne?".
Kai ta gyaɗa mata alamar eh.
Ita kuwa ido ta zuba mata tana kallon kekyawar fuskarta tace.
"Dame kuma yake miki ciwon?".
A hankali tace.
"Kaina sai kuma zazzaɓi da hannun".
Ɗaya hannunta mai lafiyar ta kamo tare da cewa.
"Shi wannan baya ciwo ne".

"Eh baya yi".

"To faɗuwa kikayi ne hannun yaji ciwo".

A hankali tace.
"A a haka kawai yake ciwo".

Jakarta ta jawo tana kallonta.
Ta buɗe.
abubuwan buƙatar ta, ta ɗauka.
Jininta ta ɗiba, kana.
Ta gwada BP'n ta a take.
Bata da matsalar hawan jini.
Bugun zuciyarta ta gwada.
Shima Normal.
Ganin hakane ta kalli Ummi tace.
"Zan tafi zamuje Valli Pharmacy.
Zan bawa Affan magunguna ya kawo mata, tasha.
Gobe da zafe zan zo.
Ni yanzu asibiti zan wuce."
Cikin gamsuwa da hakan Ummi tace.
"To mun gode Dr Kubra a gaida yara".
Murmushi tayi jin Aysha na cewa.
"Banda allura ko?".
Kai ta gyaɗa kana ta fita.

Koda sukaje da kanta ta shiga ta sai magungunan ta bawa Affan.
Shi ya wuce gida ita kuma ta nufi asibitin.

Cikin ikon Allah kuwa datasha mgnin zazzaɓin da ciwon kai ɗin ya ɗan lafa.
Har ta samu tayi bacci.

A nan Ummi ta kwana a ƙasa.
Hibba na sama gefenta.
Kamar dai randa ta faɗi a ɗakin Sheykh.


Washe gari da safe, kuma tana tashi ta tashi da ciwon hannun.
Kuma bai kumbura ba bai kuma yi ja ba.

Zazzaɓi kuma da ciwon kai da sauƙi.

Bayan Ummi ta gama aikin kitchen ne tazo da kanta ta haɗa mata ruwan wonka.
Ta shiga.
Sannan ita kuma ta fito mata da zani rigar atamfa mai gajeren hannu da maya finshi, da siket da bra and pant.

A cikin bathroom ɗin kuwa,
gaba ɗaya ta kasa yin yadda takeso.
Sabida ko motsa hannun tayi sai taji kamar ta ɗaura hannun a kai tayi ta kurma ihu.

Gashi shine hannun dama, haggun bai iya abubuwa sosaiba.

Cikin tsoro da zubda hawaye take cewa.
"Wayyo Ummey na, shike nan zan zama mai hannu ɗaya,
Wa zai taimaka min bakya kusa Junainah bata nan.
Ya zanyi iyi wonka inci abinci".
Ta ƙarishe mgnar tana goga sabulu a jikinta da hannun gadun.

A haka dai tayi wonkan a karkace

Koda ta fito.
Dole siket kawai da pant ɗin tasa,
bra ɗin barinshi tayi sabida bazata iya juya hannun ta saƙalashi ba.
Rigarma da kyar ta sata nanma saida tai hawaye.

Yunwa takeji kamar zai kasheta,
Hakane yasa ta yafa gyalen.
Ta nufi falon.
A gefen Ummi ta zauna.
Da sauri Ummi ta kalli Hibba dake Dinning area tace.
"Hibba kawo min tray'n nan."
"To". tace kana ta ɗauko tray'n.
A gabanta ta ajiye.
Tea Ummi ta haɗa mata, ta miƙa mata cup ɗin.
Da sauri tasa hannun hagun ta amsa.
Kana ta kai bakinta dan har wani duhu-duhu take gani.
Bakinta ta nufa da kofin.
Amman sai taji abin a karkace hannun kuma sai rawa yakeyi.

Cikin rawan hannun ta manna kofin a bakinta.
Idonta ta ɗan rufe, sabida zafin shayin.
Daurewa tayi ta fara zuƙanshi tanayin abin a karkace.
Hannun daman kuwa shima rawa yakeyi.

Cikin sauri ta shanye tea ɗin.
Wani na ɗan bin gefen lips ɗinta, sabida a karkace kofin take.
Ajiye kofin tayi tare dasa hannun hagun ta goge baƙin ta.

Sam tea ɗin bai isheta ba,
dan jikinta sai rawa yakeyi alamun yunwa.

Fahimtar hakane yasa Ummi sake haɗa mata wani tea ɗin ta miƙa mata cup ɗin tare da cewa.
"Amshi ki ƙara sha kafin Dr tazo".
Cikin sanyi tace.
"Hannuna ya gaji Ummi ajiye min shi in ɗan huta."
Ajiyewan tayi kana ta jawo Foodflaks ɗin,
soyayyan Arish da kwai ta saka mata a plate kana tasa mata.
ferfesun kaɗan a ɗan side plate mai ɗan zurfi.
Kana tace.
"To kici wannan sai kina ɗan shan tea ɗin a kai".
Kallon plate ɗin tayi.
Cikin sanyi tasa hannu ta ɗauki fork sokawa tayi a cikin plate ɗin.
A karkace ta kaishi bakinta tare da dawo da cokalin ta ajiyeshi.
Kana ta fara taunawa. Tare da kora tea ɗin.
A haka dai ta ɗanci kana ta ture plate ɗin tace.
"Alhamdulillah".
A hankali Ummi tace.
"Ki ƙara mana kiga ko rabinshi baki ciba.
Gashi ferfesun ko taɓawa bakiyi ba".

Cikin maida numfashi, tace.
"Alhamdulillah Ummi na ƙoshi".
Kai ta jinjina mata.
Hibba ce ta kalleta tare da cewa.
"Sannu Aunty Aysha".

Kai ta gyaɗa, tana mai taune lip ɗin ta na ƙasa.

Jamil da Jalal ne suka iso tsakiyar falon,
Cikin kula Jamil yace.
"Aunty Aysha ya jikin naki?".
"Da sauƙi". tace a taƙaice
Jalal ne ya ɗan kalleta ganin yadda taketa tsastsafo zufa yace.
"Sannu Allah ya sauwaƙa".
Amin tace.
shi kuwa maida dubanshi yayi kan Hibba yace.
"Ƙara gudun AC mana".
Cikin sauri Hibba ta miƙe ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login