Showing 18001 words to 21000 words out of 352722 words

Chapter 7 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30708

magar da zurma sakalin ihu".
Bugawa da zuciyarshi keyi yana bada sautin dib dab dib dab dib dan shine ya kusan hallakashi lokacin data riko hannunshi, da sauri ya tura mata ruwan kana ya zare Allurar da ƙarfi.
Sannan ya miƙe tsaye, sabida muddin yana kusa da ita babu makawa wata ƙil zuciyarshi zata faso ƙirjinshi ta fito woje.
Wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya bi gefen Nos ɗin ya fice.

Itama da sauri tabi bayanshi bayan tasa hannu ta amshi ledan magungunan.

Shi kuwa da sauri yake tafiya sabid iya yedda yake nesanta da ita iya yadda kirjinshi ke dai-dai ta bugawa, sai kuma tsinƙewa da zuciyarshi keyi babu ƙaƙƙautawa.

Ita kuwa AYSHA da sauri ta nufi sashin makwancin ɗaliban Hostel dake cikin makarantar sabida ta fara jiyo alamun bakonta ya iso.

Baba Ado kuwa drevernshi yana hangoshi ya tashi ya buɗe mishi marfin motar, yana zuwa, ya shiga, maida kofar Baba Ado yayi ya rufe sannan ya shiga yaja motar suka fice daga harabar asibitin.


Ita kuwa Aysha tana shiga Side ɗinsu ita da Rafi'a, ta samu Rafi'a bata falo da alamun tana kitchen nasu, dan tajiyo ƙamshi alamun tana ɗan dafa musu abinda zasuci ne.
Kai tsaye bathroom ta wuce, tabbas kuwa baƙon ya iso, dan haka ta nitsu ta gyara jikinta, bayan ta gama ne ta miƙe a hankali ta kwance niƙabin tare da fara zare dukkan kayan jikinta dan yin wonka,
Aysha farar ba fullatanace irin farare ƙal-ƙal ɗin nance, gashin kanta kuwa mai tarin yawa da tsawone baƙine sit mai sheƙi, yanada cika,
jikinta ɗan fiyau, sai dai tanada welcome and bey bey masu girma da cika, cikinta kamar babu hanji a ciki ɗan fiyau dashi, breast ɗinta tirtsa-tirtsane masu cika tab-tab kuma irin mai gindin tasa ɗinnan wanda da alamun ba masu zubewa bane, domin suna nan cas dasu, kamar zasu tsone idon mai gani, tanada tsukekken ƙugu da kyawawan mazaunai, sawonta dai-dai musali baza'ace mata doguwa ba sam, kuma baza'a ce mata gajera sosaiba in tana kusa da dogo dai za'a iya kiranta da gajera.

Fuskarta kekyawa ce irin kyan da babu namijin da zai gani ya cire ido, hancinta dogo har kan ɗan ƙaramin bakinta mai jajayen tausasan laɓɓa idonta manyane sai dai ba ƙattiba, zirin idonta wurinda akesa kolli jane mai kyau, shiyasa yake ƙara baiyana farin idonta bakin ciki kuwa bakine sitik sai dai ɗan ƙaramin ɗigon cikin bakin shi kuma ruwan ƙasane wanda yakeda sirri namu samman.
Gashin idonta zara-zarane, gashin girarta kuwa irin mai W ɗin nanne kamar na Kajol, bi ma'ana yana haɗe bisa karan hancinta,
Tanada fararen haƙora masu kyau suna jere reras dasu tanada dimple ɗinta mai ɗan karen kyau. Idanunta kuma ko yaushe kamar maijin bacci suke.

Wonka tayi kana tayi al'wala dan ko bata salla bata zama babu al'wala.

Tana fitowa ta kimtsa jikinta kana ta zura tattausan doguwar riga.

Tana kokarin fitowa falo Rafi'a na ƙoƙarin shigowa da sauri Rafi'a ta zaro ido tare da cewa.
"Yaushe kika dawo?".
Hararanta ta ɗanyi tare da cewa.
"Ba dai kin gudo kin dawo kin barni ni ɗaya ba".
Cikin tausayawa Rafi'a tace.
"La wlh yanzu nake ƙoƙarin komawa, na dawone in ɗan dafa mana abinda zamuci in mun dawo, sabida naga rabonki da abinci tun jiya, shiyasa kina shiga Office ɗin Dr na dawo".
Kai ta gyaɗa alamun gamsuwa kana tace.
"Na dawo a guje fa, wannan Sheykh ɗin hannunsa zafi kamar allurar mashi yakewa mutun".
Zaro ido na mamaki Rafi'a tayi tare da cewa.
"Shida kanshi ya miki?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh".
Cikin taɓe baki tace.
"Lallai yau kin tashi da ƙafar dama, gashi kuwa naga har kin worke".
Wucewa sukayi zuwa tsakiyar falon, cikin sauƙe numfashin Aysha tace.
"Ba doleba yadda yake tura ruwan alluranshi nan kamar mai tura mai a mota, kuma ina dawowa nasha mgni, sannan abin ya iso, kinsan dama wuyar kafin ya isone".
Dariya Rafi'a tayi tare da cewa.
"Kinji allurar manyan likitocin da duniya keji dasu dai".
Uhum kawai tace sannan suka fara cin abinci, sunaci suna hira.

Cikin hirar tasu ne Rafi'a tace.
"Anjima da yammafa jirginmu zai tashi".
Da sauri Aysha tace.
"Haba dai Rafi'a dan Allah ki bar zuwa hutunnan mana ki bari mu zauna, wallahi in kin tafi nima dole in tafi kuma ke kin san matsalar da nake da ita a gida ko Mamey ma da mukayi waya dazu cemin tayi kar in koma hutu Rugarmu, in zauna a makaranta".
Cikin sanyi Rafi'a tace,
"Wallahi nayi kewar gidane Aysha, shekara guda kenan banje gidaba fa".
Cikin sanyi Aysha tace.
"Haka ne kam ba, matsala, ai hutun sati ukune, kina tafiya yau nima gobe zan shirya zan koma Rugarmu".
a haka sukaci gaba da hira suna cin abinci.

Ƙarfe huɗu dai-dai na yamma jirginsu Rafi'a ya tashi daga Ɓadamaya international airport, zuwa Farazan state.

Ita kuwa Aysha taci gaba da shirinta ba tare da ta gaya mutanen gida cewa zata dawo ba.
Kaya kaɗan ta ɗiba dan tanada kaya a gida, system ɗinta da wayarta da kuma kaya kala biyu kawai ta ɗauka, sai yan ƙananun abubuwan, ta da tayi nufin sai gobe zata koma.
Amman ina tafiyar Rafi'a yasa taji bazata iya zaman kaɗaicinba, dan haka huɗu da rabi, ɗaya daga cikin motocin dake maida ɗalibanda in gidajensu na kusane ya ɗauke ta.

Kai tsaye garin Shikan suka nufa.
Tafiyar ba wata mai nisa bace daga cikin birnin Joɗa zuwa Shikan, cikin mitina kaɗan suka isa,
Ƙarfe biyara da miti biyar suka isa.
Cikin Shikan a nan tasa drever ya tsaya ta sayi Junainah sweet.

Biyar da mintuna goma dai-dai suka isa kwanar mashigar Rukarsu Rugar Bani.

Cikin tsoron kada Ba'ana yaga wani yazo ya sauketa ya masa rashin mutunci, tace.
Ya sauketa a nan ba musu ya sauketa dan ai inda sabo ya saba.

Tana fita taja jakarta, ta rataya kana ta gyara tarhan da tayiwa kanta.
Shi kuma ya juya ya tafi.

A hankali ta zubawa yankin garin nasu ido, ko ina yayi kore shar, yabanya da ni'imar damina ta wadaci ko ina, wata iriyar sassanyar iska mai daɗin ke ratsa mata jiki da zuciya.

Ajiyan zuciya ta sauƙe a hankali tare da lumshe idanunta kana ta buɗe hannayenta cikin begen gida tace.
"Rayuwar ƙauye mu akwai daɗeeee".
Ido ta buɗe tana kallon tako ina makiyayen rugarsune suketa dawowa daga kiwo,
Dabbobi saffan-saffan sunata dawowa,
garin yayi lum ga wani hadari mai ƙarfi daya keto, daga ƙasan dutsen da yayiwa Kyauyen ko ince Rugar Bani ƙawanya, a hankali take taku tana bin kan faffaɗan hanyan da makiyayan sukayishi bi ma'ana burtali kenan.

Taku take yayinda gefen hagunta wutsiyar kogin Shikan ne konce iya ganinta,
gefen dama kuwa Garden ɗinsune mai girma wanda yasa sanyin wurin yake yawaita, sauri ta ɗan farayi sabida akwai ƴar tazara kana kuma gashi magriba ta karato.

Tana cikin tafiya tana rataye da jakarta, kamar daga sama taga wulgawar inuwan mutun, cikin sauri ta zaro idonta ta kalli gefen hagu da damanta,
Ba kowa ganin hakane yasa taci gaba da tafiyarta cikin dakiya, taku uku tayi ana huɗu taji ansa hannu an amshi jakarta, da sauri ta juyo ta kalli gefen da aka amshi jakar.
Babu kowa a wurin kuma ga jakarta a rataye ita ɗaya tana binta suna tafiya a jere.
Cikin wani irin fargaba tsaro kaɗuwa da tsananin firgita ta....!

By
*GARKUWAR FULANI*


📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 6

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*FREE PAGE*

*Kada dai ku manta har yanzu Free page kuke samu, wanda zamu datseshi cikin ko wanne lokacin, hamzarta ku biya darinki uku kacal ko 1k ga mai dama da niya, domin samun cikekken labarin daki-daki cikin salama. Turo kuɗin ta asusuna na Jaiz. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidan biyanki ta layina 09097853276. In ya zama larura ba halin turawa ta ac turo katin mtn na ɗari uku, ko na 1k ɗin domin ci gaban lbrin GARKUWA. Sayan na gari maida kuɗi gida. Ina mai yi muku fatan al'khairi masoyana makaranta, ina sonku domin Allah ina fatan kyautata alaƙa ta da kowa sabida nasan ko ina raye watarana zan zama tarihi a duniyar marubuta, sabida yauda gobe ta wuce watsa, in ba mutuwa akwai tsufa. Kana dole watan wata rana gwanayen zasu zama tsoffin hannu kana yan koyo na yanzu su zama gwanayen, domin da babu yan koyo tabbas da gwanayen sun ƙare, inada fata da burin ganin al'ƙaluman Adabi sun inƙanta baki ɗayansu ba nawa kaɗaiba, tsarkake rubutu ki/ka domin kece madubin wata marubuciya da zata iya tasowa nan gaba.Ina mai muku fatan al'khairi🙏🏻🤝🏻🥰😘makaranta da marubuta*



Cikin firgita da tsoron tace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun, Hasbunallahiwani'imanwakil, lailaha'illalahu Muhammadurasulillahi sallahu'alaihi wasallam Auzubikalimatillahi ta'ammati min sharrin ma khalaƙa Allahum...".
Da sauri ta koma da baya ba tare da karisa addu'ar ƙarshen data faro ɗinba. Ganin Ba'ana ne tsaye a gabanta cikin wata iriyar dariya yace.
"Ke ki nitsu masoyinki ne ke gadinki, gsky *Mata* dole in rage miki wannan tsoron, domin matar Ba'ana bazata kasance matsoraciya ba, dole in ƙara tsumaki in dafaki da kyau, ta yadda idanunki zasu buɗe da kyau".
Cikin karkarwar da bai bar jikintaba tace.
"Bana so. Ni ka barnin da tsorona, nifa macece ba namiji irinka ba, kaine ke shiga daji da tsaunuka kake buƙatar wani abu ya kare ka".
Da sauri Ba'ana farin kekyawan babarbare ya matso gareta cikin shigar fulanin da ya zame mushi sutura yace.
"Mata ke bakya buƙatar kariyar ne?."
Da sauri ta gyaɗa mishi kai tare da cewa.
"Ni na yarda cewa addu'a'u saiful muminin ne, kuma shi na riƙe, so bana buƙatar waɗannan asirce asircen".
Murmushi yayi tare da murza ƙafarshi ta hagu sai gashi ya zama kamar inuwa ba mutun ya ɓacewa ganinta ɓat.
Da sauri ta rufe idanunta tare da cewa.
"Bana so ina tsoro ka dena caccanza kamanni a gabana".
Da sauri tayi baya ganinshi gab da ita,
Dariyar ƙeta yayi tare da cewa.
"Baga irinta nanba, idonki baya iya ganin komai, dole zan ƙara haɗaki irin haɗin da zaki ke banbance mai layar ɓata data zana da jingina bongo da dama duk mutun mai juyewa i zuwa wata halittar".
Ya karishe mgnar yana nuna mata hanya alamun su tafi.
A hankali suka jera suna tafiya a tare.

Allah ya sani Ba'ana yana masifar son Shatu tun tana ƴar ƙaramar yarinya, yana sonto irin sonda ko ƙudane in ya sauƙa kanta in dai namiji ne to zai kasheshi, ganinta kusa dashi kawai yana sashi jin daɗi, duk muguntarsa baya yi mata, duk duniya babu wanda Ba'ana ya yarda da shi bare yasan sirrin makarin sihirurrukan dake jikinshi. Ba'ana mutunne da yake tamkar al'janu sabida yawan ta'ammali da sihiri kai harma da tsafi, Ba'ana riƙeƙƙen tantirin ɓarawone wanda ya buwayi Fulani al'ummar Afirka gaba ɗayanta, da sace-sacen dabbobinshi, muddin ya ƙella ido yaga garken shanunka yayi mishi, to tazarar kilo mita talatin da biyar yake tsayuwa da garken, yayi FITO ɗaya tak, wallahi duk sihirin kafiyar garkenka zai kunce kuma duk inda yayi shanayenka zasu bishi a baya da kuma wannan tazarar, da zaran kasa Hukuma cikin zancen kuma yana burza layar ɓatanshi dashi da dabbobin duk zasu ɓace.

Duk garken da yaga yayi mishi to sai ya kwashesu tsan da wannan ya tara dukiyar dabbobin da shi kanshi baisan adadinshiba babu ƙasar da bashi da makiyayanshi kamar su.
Chadi, Nijer, Cameroon, Ghana, Gabon, Maroco, Senigal, da dai sauran kasashen makusantanmu kuma masu dabbobi, hikimar da yakeyi, muddin ya saci shanayen ƙasar Niger to sai ya cillasu ƙasar Senegal, in kuma makiyayanshi na ƙasar Sanigal sukayi sata to sai ya turo shanayen ƙasar Gabon, haka dai yake banbance mazauninsu.

Sai dai garin zamansa ɗaya ne Rugar Bani, inda nan aka haifeshi mahaifinshi Bukar wanda babarbaren Norba ne saye da sayar da kanwane ya ajiyeshi cikin rugar FULANI shiyasa ya zama dilan saida kanwa, sabida dole duk bafulatani makiyayi yana ta'ammali da kanwa dan ana zubawa dabobbi susha a ruwa ko asa musu a dusa ko harawa yana musu mgni.

Ba'ana ya shiga cikin Fulani ya saje dasu.
Yayinda hakan ya bashi damar da duk duniya ake ɗaukarshi matsayin bafulatani, koda yake hakan baya rasa nasaba, da kallon da mutanen duniya sukewa duk mutumin da akaga shanu, tumaki a gabanshi tofa ko wacce gabilace shi, ya zama bafulatani, wanda kuma sam ba haka abin yakeba.

Mahaifiyar Ba'ana ɗaya daga cikin ƙabilar ɓachama ce,
wacce Bukar ya aura tana a matsayinta na anniya, koda kuwa suka haihu ɗan su. Bukar ya rinjaye ta Ba'ana ya kasance musulmi, sai daifa a baɗini baƙar zuciyarsa da aiyikansa na kafuraine, sata kuwa a wurin babarsa ya gada.

Ba'ana kekyawan mutun ne ajin forko wanda ya gaji wannan kyan ne a kakarshi mahaifiyar babanshi wacce take shuwa Arabce, koda maƙiyinshi yasan tabbas Ba'ana kekyawane.

A duniya kab Shatu ce tasan sirrinshi ciki da woje,
sai daifa bata san yana sataba, amman duk wani abu na asiri da yadda za'a karya asirin da kuma yadda yake juyewa duk ta sani.
To hakanne yasa sam bata fatan ya zama miji a gareta bare uban ƴaƴanta, sai dai babu yadda ta iya. Domin ya mata babbar rana a rayuwarta ya mata taimakon da yasa aka ɗaukar mishi al'ƙawarin aurenta.
Gashi kuma duk wanda yace yana sonta karshenshi mutuwa, kuma yana gaya mata cewa duk wanda yace zai rabashi da ita zai kasheshi Wannan yasa kullum addu'ar shirya take mishi da fatan Allah ya rabata dashi lfy innshi ba mai shiryuwa bane.

Tafiya sukeyi cikin nitsuwa a hankali, murmushi yaketayi cikin so da ƙaunarta yace.
"Mata ya akayi na ganki da ƙaramar jaka?".
Kai ta ɗan gyaɗa mishi tana kallon kekyawar fuskarshi, cikin murmushi yace.
"Kece kika ajiyeni a kasar Kautal a Rugar Bani, kina ƙare karatunki zamuyi aurenmu in ɗaukeki mubar ƙasar, kawai dolece tasa na hakura da batun aurenmu kiyi karatu, dan naga kina son karatun kuma nasan zaki karantar mana da yaranmu, kuma ina son ki zama babbar lawyer mai zaman kanta, sai ki zama lawyer na koda watan-wata rana, rana zata ɓacin min".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Kamar yaune zan kare karatun, Ya Ba'ana".
Kanshi ya rausayar tare da gyara riƙon igiyar jakar da yayi, kana yace.
"Allah ya nuna min wannan lokacin, in sha Allah sadakin aurenki Garken shanu ɗari zan bada".
Cikin mmki ta zaro ido tare da cewa.
"Kai Ya Ba'ana garke ɗari bama shanu ɗariba, ya bana ina zaka samu wannan shanun kaida garken naku ko shanu hamsin bai cikaba".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Allah zai kawosu kafin lokacin auren namu".
A hankali tace.
"Allah ya kawosu".
Amin Amin yace tare da ɗan juyowa ya kalleta, murmushi yayi mata, kana ya miƙo mata jakar tata cikin so yace.
"Mun iso bakin Gari ki shiga.
Ni zan koma baya dama rakoki nazo nayi kar shaiɗanun bakin kogi su cutarmin dake".
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
"Ya Ba'ana lokacin sallah ya kusa fa ai gwara ka shigo sai kayi salla ka koma".
Bakinshi ya ɗan tabe tare da cewa.
"No bar sallan nan sai bayan mako biyu ina ƙara dafa jikinane kuma in nayi al'walan duk aikin zai karye".
Dafa kanta tayi da sauri tare da cewa.
"Wa'iyazubillah Wayyo Allah na Ya Ba'ana ka gane mana wannan abin da kakeyi shirka ne,".
Kanshi ya jujjuya tare da cewa.
"Shiga cikin gari zanzo musha hira da daren".
To kawai tace mishi ta juya ta nufi cikin garin.

Tana shiga ta kama hanyar gidansu, tana gab da shiga gidane ta haɗu da ɗan makotansu Iro cikin girmamawa tace.
"Ina wuni Ya iro".
Fuska cike da fara'a yace,
"A a lale marhabin da ƙanwarmu yar al'barka anyi hutukenan?".
Kai ta gyaɗa mishi sannu da hanya ya mata sannan ta wuce ya wuce.

A gindin bishiyar mangoro dake kofar gidansu gab da zaure ta hango Bappanta yana zaune bisa dakalin dake wurin yana al'wala, da sauri ta nufi in da yake fuska cike da jin daɗi.

Shima Bappa da sauri ya miƙe yana murmushi yake cewa.
"Maraba lale da ƴar al'barka."
Da sauri ta iso inda yake tana murmushi mai nuna tsantsar jin daɗinta tace.
"Oyoyo Bappa na, Alhamdulillah na sameka lfy, ya Ummey na da Innata?".
Dariya yayi tare da matsota yace.
"Duk muna lfy".
da sauri suka juyo ta cikin gida jin muryar yayunta suna cewa.
"Oh wato mu kam bakiyi kewarmu bama ko?".
Da sauri tayi gabansu cikin jin daɗi tace.
"Oyoyo ƴan uwana Ya Gaini, nayi kewarku mana, musamman Ya Giɗi sarkin son girma".
Murmushi sukayi dukansu,
Seyo ne ya kalleta tare da cewa.
"Wallahi yanzuma mgnarki mukeyi da Ummey, har Junainah na cewa wai ai duk munfi sonki".
Dariyar jin daɗi tayi tare da cewa.
"Ayyah ƴar ƙanwaliya tawa mai kishidani".
Murmushi sukayi baki ɗaya kana Lado ya kalleta tare da cewa.
"Shiga gida mu zamu wuce masallaci ne".
To tace kana ta nufi cikin gida tana cewa.
"Yauwa yaya Giɗi dan Allah a kawomin rake".
Kai ya gyaɗa mata kana suka wuce ita tayi cikin gida.

Tana shiga da fara'ar jin daɗi da ɗan karfi ta buɗe murya tare da cewa.
"Assalamu alaikum, gani na dawo, ina Inna ina Ummey, Junainah ina kike?".
Ai kusan a tare suka fito gaba ɗayansu, wani irin tsalle Junainah ta buga tare da rugawa ta nufi kan yayar tata cikin ihu da ɗaga sauti take cewa.
"Oyoyo Addana oyoyo".
Da sauri Ummey ta harateta tare da cewa.
"Ke Junainah magriba cefa, kike irin wannan ihu ke sam baki da nitsuwa".
Ita dai batama jitaba.
Da gudu ta faɗa jikin Aysha, itama Aysha wurgar da jakarta tayi ta ruggume yar uwarta.

Inna da Ummey kam ido suka zuba musu, suna masu jin daɗi irin soyayya da shaƙuwar dake tsakanin yaran nasu.

Dariya sukayi baki ɗayansu, cikin jin daɗi inna tace.
"To yanzu dai lokacin salla yayi ku shigo kuyi salla tukun sai ayita murna dan yau dai kam nasan kwanan zaune za'ayi".
Murmushi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login