Showing 204001 words to 207000 words out of 352722 words

Chapter 69 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30778

buɗa al'kyabbar shi, ya rufesu ruf, wani irin numfarfashi yake fesarwa da sauƙewa a jere-a-jere.
Cib tayi jin yadda ya mata ƙawanya da jikinshi kana ya sakar mata nauyinshi da yimata garkuwa da al'kyabbar jikinshi.

Buɗe idonta tayi ta zubasu kan kyakkyawan fuskarshi, da take yalwace da.
Hasken addini, ta ƙawatu da kyawun sura da hali da nagartacen haiba da imani.
Gashin girarsa ta zubawa ido,
tana kallo tare da sajenshi.
a hankali ta shaƙi ƙamshin turaren OudKareem dake tashi a jikinsa.
meda idonta tayi ta lumshe da sauri ganin Umaymah ta iso har gaban motar kusa da ƙofarsu.
Mutsu-mutsu ta farayi.
Sam ta kasa zillewa.
Hakane yasa ta ɗago hannayenta, tasa bisa fuskarshi ta tallabe gefen hagu da damanshi ya zama tafin hannunta na kan sajenshi duka biyu.
A hankali ya buɗe kyawawan idanunshi ya zubasu cikin nata.
Da sauri ta janye nata, kanshi ya fara janyewa still dai yana liƙe da lip ɗinta kan harshensa.
da sauri ta turo kanta jin kamar zai tsinke mata shi.
Ɗouhh haka ya saki mata wani sauti mai kashe jiki da zuciya cikin kunnenta lokacin daya saki laɓɓan nata.
Da sauri tasa tafin hannunta tana fifita lips ɗin tare dayin rau-rau da ido tace.
"Zafi! zafi!! Zafeeeh!!!." Hannunshi yasa ya kama tsinin hancinta da yatsu biyu kana ya ƙanƙance idanunsa, cikin wata iriyar fitinenneyar murya yace.
"In kika sake murguɗa min bakin, haka zan miki. In kuma kika sake yimin sherri ko ƙazafi tsinke bakin zanyi".
cikin kwaɓe fuska tana fifita laɓɓan tace.
"Ka tsinke min baki kamar maye".
Kafaɗunshi ya buɗa tare da ɗagasu sama ya taɓe baki kana yace.
"Mayen ne ai ni. In na tsinkasu haɗiyesu zanyi sai kije in sa miki na Aku kinji daɗin yin surutu da kyau".
Ya ƙareshe mgnar yana janye al'kyabbarshi daga jikinta yana gyara shi.
Hannunshi yasa ya jawo niƙabinta daya ɗage ya rufe fuskarta tare da cewa.
"Ki rufe fuskarki kar Hibba tayi miki dariya tace kin zama mai dogon baki dengin jaɓa".
Yana faɗin haka yasa hannunshi ya buɗe marfin motar tare da saƙo ƙafarshi ta dama waje.
Wani irin murmushi mai cike da tarin.
So, ƙauna, shaƙuwa, tausayi, da kulawa. Umaymah tayi mishi.
Hakama Aunty Hafsat.

Ita kuwa Aysha bakin ta ɗan tura tare da cewa.
"Allah ko sai na gayawa Umaymah ka cinye min lips ɗin a".

Juyowa yayi yana kallonta, tare da murmushi a fuskarshi.
Sai kuma ya juyo da sauri jin Umaymah da Aunty Hafsat su ruggumeshi ta baya.
Hannunshi ya miƙo mata tare da cewa.
"To fito ki faɗa kada in rigaki yin nawa sharhin".
Ture hannunshi tayi ta fito.
Shi kuwa tana fitowa yasa hannunshi ya kamo nata tare da jawota bayanshi.
Da sauri Aunty Hafsat ta sakeshi tare da komawa bayanshi hannunta ta jawo tare da Ruggumeta tana cewa.
"Masha Allah diyar kirki".
Da sauri tasa hannunta ta yaye niƙabin.

Umaymah kuwa murmushi tayi cikin tsananin jin daɗin ganinsu take kallonsu cike da so da kulawa tare da cewa.
"Jazlaan naji daɗin ganinku".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Muma haka".
Sai kuma ya juyo da sauri ya kalli Haroon da Ibrahim da suka fito can gaban motar bisa alamu duk Ibrahim ne yaja motar.
Haroon kuwa yana gefen mai zaman banza.
Cikin dariyar tsiya Haroon ya matsoshi tare da ruggumeshi ta gefe, dan su Umaymah duk sun sakeshi sun koma kan Aysha.
Cikin tsiya yace.
"Ur welcome Mr Jabeer Ustazu ƙalilan iya shege kasiran".
wani irin tsare fuska da gira Sheykh yayi tare da watsa Haroon kallon. "Hegen munafurcin sa ido".
Ya faɗa tare da Ruggume Haroon da ƙarfi yadda zaiji zafi.
Da sauri Haroon yasa ƴar ƙara tare da cewa.
"Wayyo Aunty Hafsat zai karyan baya in rasa na amarci".
Dariya sukayi dukansu.

Shi kuwa Sheykh ture Haroon yayi yana mamakin subutar baki irin na Haroon, kwaffa yayi tare da Ruggume Ibrahim murmushi Ibrahim yayi tare da cewa.
"Barka da zuwa Garkuwan Masarautar Joɗa".
Shima murmushi yayi tare da cewa.
"Barka da zuwa, magajin masarautar Leddi julɓe".

Hibba kuwa baki ta tura tare da cewa.
"Aunty Aysha wato kinga su Umaymah ni Ko ki kulani ko?".
Da sauri ta juyo ta ruggume Hibba tare da cewa.
"Oh sorry my Hibba ai ke ta dabance".

Da sauri ta juyo ganin wata kekyawar budurwa kamar Hibba ta gane Azeema ce yar Aunty Hafsat.
cikin bagwariyar Hausa Azeema tace.
"Wato mu bana musamman bane ko Aunty".
Da sauri ta jawo hannun Azeema ta haɗa su ta ruggume.

Da sauri Umaymah ta juyo ganin Ummi ta fito.
Ruggume juna sukayi cikin jin daɗin ganin junasu sun kasa mgn sai murmushi.
Jamil kuwa da sauri yaje ya Ruggume Abudul-azeez da Sadiq ta baya.
Juyowa sukayi suma suka ruggumeshi suna farin cikin ganin juna.

Sheykh kuwa sake Ibrahim yayi ya kalli Sadiq da Abdul-azeez ya shafa kan ƴan matasan.

Umaymah ce ta juya ta nufi cikin gidan tare da cewa.
"Ku shigo, maza ku taho ko".
To sukace kana duk sukabi bayanta.

Wani babban falo mai zaman kanshi wanda yake ɗauke da lumtsuma-luntsuman kujeru set biyu da Dinning table a can babban Dinning area da ƙaton fili a tsakiyar falon.
Suka zauna.
Su Hibba da Azeema sun sa Aysha a gaba.

Haroon da Ibrahim dasu Sadiq kuwa suna ɗaya sashin.

Umaymah da Aunty Hafsat da kansu suka rinƙa kawo musu abubuwan ci da sha.

Bayan sun gaggaisa ne.

Suka ɗan zauna suna hirar Yaushe gamo.

Ummi ce ta ɗan kalli Umaymah tare da cewa.
"Ina Rahma ne ban ganta ba ita".
Aunty Hafsat ce ta amshi zancen da cewa.
"Tab uhum Rahma taji biki ta zauna.
Ɗazu da safe jirginsu ya wuce.
Leddi julɓe, kinsan gobene za'ayi kamu, to taje ita da su Isha dasu Farida, sun haɗu dasu Juwairiyya sunacan suna shiryawa hidindimun da za'ayi".
Ɗan juyowa sukayi suka kalli Azeema da ke cewa Sheykh.
"Hamma Jabeer zamuje da Aunty Ayshan can ko gobe in Allah ya kaimu".
Ba tare da ya ɗago kanshi bare ya kalletaba ya ɗan jujjuya kanshi alamun.
A a, da sauri Azeema tace.
"Ayyah dai".
Umaymah ce ta ɗaga mata hannu alamun tayi shiru.
Ummi da Aunty Hafsat kuwa murmushi kawai sukayi.
Hibba kuwa ƙasa tayi da muryarta tare da cewa Aysha.
"Zamuje ai".
Kai Aysha ta gyaɗa mata alamun eh.

Haroon kuwa juyowa yayi ya kalli Sheykh tare da cewa.
"Yaushe kace zamu tsaida lokacin walimar?".

Kanshi na sunkuye yana kallon wayarshi yace.
"Na gama mgn da Abba, babu wani Dinner'n da za'ayi.
Madadin dinan shi zamuyi waliman".
Da sauri Haroon yace.
"Wannan ai tatsuniya ce".
Ibrahim ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
"Wlh sun gama mgn da Abba, yace tunima ya gaiyaci manyan mutane duk akan walima za'ayi.
An gama shirya komai ma, kuma babban wurine aka kama gefen, maza da matane, za'ayi walima mai kyau da ma'ana.
Yafi akan yin wannan bidi'ar nan da zamuje mu gwamutsu maza da mata a wuri ɗaya a rinƙa kiɗe-kiɗen da bushe-bushen da raye-rayen banza da wofi".
Murmushi Umaymah tayi ganin yadda Haroon ya haɗe fuska kamar zaiyi kuka cikin takaici yace.
"To Ni yau ma zan tafi dan inje mu shiryawa kamun da kyau, duk sauran abokanmu zasu je".
Ya faɗa yana kallon Sheykh, kafaɗarshi ya ɗaga tare da buɗawa kana yace.
"Ya rage naka, Ni nan Muhammad babu inda zanje walimace da ɗaurin aure ya kawoni. Dan dole in jamaka kunne kasan tsarin zaman aure a musulunci ba a yahudance ba".
Dariya sukayi sosai.
Aunty Hafsat ce ta ɗan gyara zamanta tare da cewa.
"In anyi bikin a can, kana in mun dawo nan anyi walima, washe gari ayi fansan ido da daren ranar Lahadi da dare zamuyi mother's day, dan ranar tamuce kuma biki biyune, tunda bamu samu zuwa na Jazlaan ba.
Anyishi babu bikin komai to in sha Allah mu dai iyaye zamuyi namu shagalin wannan umarnine ba shawara ba, bakuma neman iziniba".
Ido Sheykh ya zuba mata cikin sanyi yace.
"Mom".
Hannu ta ɗaga mishi, alamar yayi shiru.
Sai ta kuma juyo ta kalli Ummi tare da cewa.
"Ummin Jabeer kunzo da shiri ko?".
Cikin murmushin Ummi tace.
"Sosai ma kuwa".
Nan dai sukayi hirarsu da tsara yadda abin zai kasance.

Hibba ce taja hannun Aysha, ɗakin Umaymah Suka shiga.
Suna shiga tayi wani irin tsayuwa tana kallon tsarin ɗakin yayi masifar kyau.
Wasu ƴan mata da manyan mata suka samu a zaune.
Cikin murmushin Hibba tace.
"Aunty Rabi'atu ga matar Hamma Jabeer Aunty Aysha da nake faɗa miki".
Da sauri duk suka juyo.
Masha Allah shine abinda suka faɗa kusan a tare.
Ɗan rusunar da kai tayi ta gaidasu.
Murmushi tayi ganin Aunty. Kubra ƙawar Umaymah dake Ɓadamaya.
Motsowa tayi kusa da ita ganin tana miƙo mata hannu cikin kunya tace.
"Aunty Kubra Ina wuni. yaushe kika zo".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah Aysha.
Ni tun jiya nazo, ina ɗan nawa yana lfy ko?".
Murmushi tayi a kunyace tace.
"Alhamdulillah yana falo".
Nuna mata sauran matan tayi tare da cewa.
"Kinga nan duk ƙawayen Umaymah ne yawanci daga wasu garuruwan sukazo.
Kin san Umaymah taku ta jama'ace".
Sannu ta sake yi musu.

Ita kuwa Aunty Kubra miƙewa tayi tare da kamo, hannun Aysha.
"Zo nan". Tace tare suka fita Hibba na biye dasu a baya.
Juyowa tayi ta kalli Hibba tare da cewa.
"Jeki kira min Hafsat kice ina ɗakin can".
Da sauri Hibba tace to, kana ta juya taje falo.
Ta kira Aunty Hafsat kamar yadda Aunty Kubra ta umarceta.

Tare suka juya suka tafi.

Haroon da Ibrahim da Sheykh kuwa miƙewa sukayi suka nufi wanni babban part dake bayan na Umaymah wanda yake da yalwan ɗakuna babban falo sai 3 bedroom sai ƙaramin falo.
Nan suka nufa, wanda akwai wani a gefenshi kuma nanne Haroon zai tare da Amaryarshi Jannart.

Suna shiga suka samu abokansu.

Hunnu sukayi ta bawa juna suna gaisawa cike da fara'a sukeyiwa Sheykh tsiyar yayi auren sirri wato dan baya son suje susha rawa ko.
Murmushi yayi tare da cewa.
"Mazarai sarakunan rawa yanzu ai kun samu wurin rawan ko?".
Dariya sukayi.

Aunty Kubra kuwa suna shiga ɗakin.
Ta jawo wani matsakaicin akwati.
wasu zafafan ɗinkuna ta fara fitarwa. Ko wanne da mayafinshi da takalminshi da jaka ko fosa.
Shigowar Aunty Hafsat ce yasa tace.
"Yauwa Hafsat Ni ina anko ɗin su na ƙawaye da a abokai wanda za'asa a kamun.
Zama tayi gefenta tare da cewa.
"Gashi nan gefenki ɗazu aka dawo dasu daga ɗinki.
Harda na Farida shine fa tun ɗazu ta buwayeni da kira kadafa a manceta".
Jawo ledar tayi ta firfito dasu, kowa da sunanshi a jikin nashi, shiyasa babu wuyan ganewa.

Kala shida Aunty Kubra ta miƙawa Aysha tare da cewa.
"Gashi dana kamu dana walima dana Dina na wuni, ne a nan sai waɗannan kuma kyasasu sanda kikeso".
Aunty Hafsat ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
"Dinar dai mijinta ya hana, gacan Haroon kamar yayi kuka, Jazlaan kuwa ya gama karya zancen a wurin Abban su Haroon ɗin".
Dariya sukayi kana Hibba tace.
"Aunty Aysha zo muje ɗakina, ki gani nida Azeema ce kaɗai a can".
Da sauri ta miƙe da tana jin nauyin sun Aunty Hafsat.


Suna shiga ta zauna bakin gadon Hibba tare da cewa.
"Iye ashe dai my Hibba ba dama wurin tsabta".
Murmushi Hibba tayi cike da jin daɗin yaba mata da Aysha tayi.
Ita ko Aysha numfashin gajiya ta sauƙe tare da cewa.
"Yanzu bari inyi wonka wlh na gaji".
Azeema da yanzu ta shigo ne riƙe da ƙaramin yaron Aunty Safiyya wacce itace ƴar farin Aunty Hafsat kuma itace matar Ibrahim.
Yaron bai wuce shekara Uku bane.
Tace.
"My Aunty kamar tafiyar mota kikayi".
Hannu tasa ta amshi yaron tare da cewa.
"Masha Allah yaron waye wannan mai kama da Jalal".
Hibba ce ta ɗan shafo kansa tare da cewa.
"Aunty Aysha kice kawai mai kama da Hamma Jabeer ko".
Yi tayi kamar bataji Hibba ba.
Azeema kuwa cewa tayi.
"Yaron Aunty Safiyya ce, kin santa ko".
Kai ta jujjuya alamar a a.
Da sauri Hibba tace.
"Itace matar Ya Ibrahim ƙanin Aunty Juwairiyya".
Murmushi ta ɗan yi tare da cewa.
"Ok na gane masha ALLAH".
Tace tana sumbatar goshin yaron.
juyowa suka ɗanyi jin motsin buɗe ƙofa da kukan yaro.
Safiyya ce ta shigo mai kama da Azeema sak.
murmushi Safiyya tayi tare da cewa.
"Iye Aunty Aysha kice kin gane Angon naki kenan".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Angona kuma".
Azeema ce tace.
"Eh ai mai sunan Hamma Jabeer ne."
Kai ta ɗan sunkuyar ta kalli yaron tare da cewa.
"Eyeh kai mun gode kuwa".
Kallonta Safiyya tayi cikin sakin fuska.
gyara riƙon da tayiwa ƙaramin ɗanta, Salim tana bashi nono tace.
"Yanzu muka dawo kasuwa akace min kun iso ko ruwa ban shaba.
Azeema kawo min abinci tun safe muna kasuwa".
Da sauri Azeema ta miƙa taje ta kawo musu abinci.
Bayan ta zubane tace.
"Aunty Aysha sauƙa kuci kema bakici komaiba tunda kukazo".
Zatace a a .
Safiyya tace.
"A a dan Allah kada muyi haka dake sauƙo muci, Ni fa yar uwarkice kuma matar abokin wasanku kinsan ɗan kawuna aka auramin, ni matar abokin mijinki ne kuma Aminiyarki sannan ƙawar mijinki".
Dole Aysha ta sauƙo sukaci abinci tare.

Sannan ta miƙa taje tayi wonka.
Tana fitowa Hibba na shigowa da jakar data amso a wurin Ummi a can ɗakin dasu Aunty Kubra suke.

Fita sukayi Safiyya kuma ta shiga Bathroom ɗin.
Nan ta samu ta kimtsa.

Wani Shadda lace red color sai ratsin white blue a jiki wanda kamar zanen bakan gizo ta saka doguwar rigace
Ta zauna a jikinta ras, tayi masifar kyau, bata wani yi kolliyar azo a ganiba.
Gyalen shi farine ta yafa, bayan ta murza ɗaurin ɗan kwalinta.

Turarenta mai ƙamshi ta fesa.
Kana ta ninke kayan data ciren.
Da sauri Hibba da yanzu ta shigo ta amshisu tace.
"Yauwa bari in kai a wonkesu agoge kadama su tarun miki."
"To". tace, kana ta maida marfin jakarta ta rufe.
Safiyyah na fitowa ta kimtsa itama nan suka zauna suna hira har dai aka kira sallan magriba.
Bayan anyi magriba anyi ishane.
Duk suka fito babban falon.
Sai Umaymah dake can cikin ƙawayenta da matan abokan Abbansu HAROON.

ita kuwa Aunty Hafsat ta Tara zuriyarsu kab sunata hira.

Suna tsara tafiyarsu da za'ayi gobe jumma'a da hantsi, zuwa Leddi julɓe.
Da yamma ayi kamu jibi a asabar ɗaura aure da hantsi sannan su dawo da amarya da daren ranar kuwa ayi walimar washe gari Lahadi kuma ranar wuni ce ayi fansan ido da yamma, da dare kuma ayi shagalin mother's day.
Duk yadda sukaso ayi bidi'a da yawa, Sheykh ya karya musu logo daya samu Ibrahim da Abbansu Haroon da kawunshi Baban Aunty Juwairiyya dasu Ibrahim da amarya Jannart ɗin.
Ya dai tsara yadda yaga dama a bikin.
Haroon kamar ya rinka ihu.
In ya kufula sai Sheykh ya koma gefe yana kallonsa yana taɓe mishi baki.

Shi da Ibrahim dama su sunce sai jibi zasuje asabar zasu sammaka da tawagarsu zuwa ɗaurin aure da ɗaukan amarya.

Washe gari ranar Jumma'a da hantsi jirginsu Safiyya, Hibba, Aysha, Azeema, Aunty Kubra, da wasu ƙawayen Umaymah da ƙannen baban Haroon jirgisun ya isa birnin Jalaluddin.

Sheykh kuwa shi tunda sukazo idonshi ma bai sake ganin Aysha, duk da tana ɗan faɗo mishi a rai lokaci zuwa lokaci sai dai baya bin ta kanta.

Dan hidimomin sun sha kansu.

Suna isa masarautar Jalaluddin.
Kai tsaye suka wuce Side ɗin kakarsu.
Sitti kenan wacce taketa dakon zuwansu dan ganin Aysha matar jikanta mafi soyuwa a ranta.

Suna Shuga babban falonta Safiyya ta fara kiranta.
"Sitti! Sitti!! Sittin Jadda ko dai kina can wurin tsohon zumanki ne".
Dariya tayi ganin Sitti ta fito da sauri.
hannu ta buɗe wa Aysha irin dai al'adar su ta larabawa.
Cike daso tace.
"Iye masha ALLAH Jazlaan ya samu kekyawar mace mai nagarta".
A kunyace fuska ɗauke da murmushi Aysha ta isa jikinta.
Ruggume ta tayi tare da cewa.
"Sannu da zuwa masarautar julɓe, jikata".

Cikin sakin jiki da ita Aysha tace.
"Yauwa Sitti na sameku lfy?".
Alhamdulillah tace.
Tana kallon tsohuwar da kyau tana gani wasu kamannin Ummey a fuskarta.
Jansu tayi har cikin Bedroom ɗin ta.
Duk jikokinta ne.

Safiyya ce ta zaro wayarta ta kira Aunty Rahama tace mata sun isofa.

Aunty Rahma kuwa dake tsuma Jannart da kayan gyara na al'farma Juwairiyya da Jazrah da Saddiƙa na gefenta.
Da sauri tace.
"Gani nan zuwa yanzu kuwa, Safiyya".

Tana katse kiran tace.
"Muje Side ɗin Sittiina.
Su Safiyyah sun iso."

A tare suka miƙa suka nufi ƙofar Sitti.

Tafiyar a kwai yar tazara tsakaninsu.


A can Side ɗin Sitti kuwa, Bayan sun zauna Sitti tasa hadimanta sun kawo musu abin ci dana sha.
Sunaci suna hira.

Ita kuwa Aysha Ishma ƴar Aunty Rahma dake bacci kan gadon Sitti ta zubawa ido.
Duk da bata ganin fuskar yarinyar gaba ɗaya amman ta hango wani irin masifeffen kama da takeyi mata da Junainah.
Shiyasa gaba ɗaya hankalinta na kan yarinyar.

Hibba ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
"Aunty Aysha kici mana, kin tsaya kallon Ishma".
da sauri ta ɗan rusuna ta fara cin Couscous da miyar hanta da Sitti tayi musu da kanta.

Suna shigowa Aunty Rahma ta tsaya tana kallonsu cikin sakin fuska tace.
"To yau duk kamar takuma ta zama ɗaya ina surkar tawa".
Sitti ce ta kalleta cikin son yar autar tata tace.
"Gata nan a gabanki".
Ta ƙarashe mgnar tana nuna mata Aysha dake zaune tana fuskantar gado.
Ɗan juyowa Aysha tayi da murmushi a fuskarta.
Da sauri ta juyo gaba ɗayanta tana kallon Aunty Rahma cike da mamakin tsananin kamarta da Ummeynta, hatta muryarsu iri ɗaya.

Da sauri tayi ƙasa da kanta, jin ta zauna kusa da ita.
Cike da Muryar mamaki tace.
"Aunty Rahama ina kwana".
"Lfy lau Alhamdulillah my surka ya ɗana, Jazlaan".
"Alhamdulillah yana lfy". tace fuska a sake tare da alamun kunya da kuma al'hinin abin da take gani da ji na kamanceceniyar fuska da murya.
Sitti ce tayi dariya tare da cewa.
"Tab lallai kuwa da yana kusa da kinsha tsuka, kin san baya son kina ce masa ɗanki dan yace ya fiki".
Safiyya ce tace.
"Tab ai Hamma Jabeer baya son ace ta fishi, sai yace.
"Dan wata biyun ne wani abun".

Dariya dai sukayi ita kam Aysha.
Ta shiga ruɗani kamannin.
Ƴarinyar da aka kira da Ishma da Junainah sun bata mamaki, sai kuma ga kamannin da yafi bata tsoro ma yanzu kam ko murya da dariyar Ummey nata irin na Aunty Rahma ne.
Ya ilahi ya mujibadda'awati".
Ta faɗa cikin ranta.
Lokacin da Ishma ta taso zaune daga baccin da takeyi, har kamar zata faɗi.
Da sauri tasa hannu ta tare yar yarinyar da bazata gaza shekara biyar ba.
Da sauri ƴarinyar ta manna kanta a jikinta tare da cewa.
"Mommy zansha ruwa".
Da sauri ta sunkuyo kan yarinyar hannunta tasa ta dafa goshinta, cikin sanyi tace.
"To ga ruwan buɗe baki". Ta ƙareshe mgnar tare da ɗaukan bottle water mai ɗan sanyi dai-dai misali, tana buɗe marfinshi.
Juyowa Ishma tayi jin baƙuwar murya.

Cikin sauri ta kalli Azeema tare da cewa.
"Laa Aunty Azeema kalli Aunty Ayshan Hamma Jabeer tazo".
Tayi mgnar da alamun tasan Aysha a hoto.

Murmushi tayi tare da sa mata bakin gorar ruwan a baki.
Cikin mussuke ido ta buɗe baki ta fara shan ruwan.
Aunty Rahma kuwa, kallon Aysha take cike da ƙauna.
Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Aysha cikin yanayin da bazaka gane manufarshi ba tace.
"Sannuku da zuwa yau kam gaki a masarautarmu tushenmu, gaki ga Sitti kakarmu data haifi babana ta kuma haifi Mamansu Sheykh da Ya Jafar dasu Jamil jininmu ɗaya".
Ta ƙareshe mgnar cikin nuna kusanci da dangatakar dasu Sheykh na jinine.
Kai Aysha ta ɗan juyo ta kalleta,
murmushin gefen baki tayi,
dan ta gane manufar Aunty Juwairiyya tana nuna mata cewa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login