Showing 333001 words to 336000 words out of 352722 words

Chapter 112 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

34612

ganinta yace.
"Yauwa Adda Shatu a kawo mana tray'n mana ko plate".
To tace.
Kana taje ta kawo musu tirurruka guda biyu.

Ajiyan zuciya Sheykh ya sauke tare da cewa.
"Wai anya kuwa kunci abincin safe?".
Da sauri Affan yace.
"Bamu ciba".
Murmushi Yah Jafar yayi tare da cewa.
"Koma dai munci ai yanzu hantsi ya duba ludeyi.
Dan haka Affan sa mana".
Allah sarki rayuwa mai daɗi ba girman kai.
Shatu ta raya a ranta.
Shi kuwa Sheykh dariya yayi.

Shi kuwa Affan ludeyin duma yasa ya zuba musu tuƙeƙƙen tuwon nan.
Kana ya zuba musu miyar kasen da yaji nama da kifi banda a saman tuwon.
Jalal kuwa ƙara min tray'n ya jawo.
Danderun ya juye a ciki fiye da rabi.
Ita kam Shatu juyawa tayi ta tafi.

Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Affan, Jamil, Yah Jafar.
Sun haɗa hannu cikin kono ɗaya suna cin abinci cike da gamsuwa da shaƙuwa da ƙaunar juna.

Haka nan yaji wani irin daɗi.
Jalal ne ya ɗan matso gabanshi da tray'n tare da cewa.
"Ni dai Allah ya sani ba cin tuwo zanyiba, Hamma Jabeer muci Danderun".
Jamil ne ya ɗan kalleshi tare da cewa.
"Manyan kuraye ba".
Eh ɗin Jalal yace kana sukaci gaba da ci suna hira.

Ita kuwa Shatu bakin kitchin ɗin ta koma.
Gefen Yah Giɗi ta zauna.

Tare da sa hannunta cikin akoshin abincin da yake cin.
Kana ta kalli Junainah dake gefenshi riƙe da Afreen tace.
"Junnu kaita wurin Ummi kizo muci mana".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ni na koshi naci da Ummey na a ɗaki".
A hankali ta ɗan juyo ta kalli ƙofar ɗakin Bappa jin Sheykh yayi gyaran murya.
Ido ya juya mata, alamun me takeyi.
Cikin jin daɗin yanayin tace.
"Ina cin abinci da Yah Giɗi na".
Murmushi yayi tare da juya kai.

Shi kuwa Yah Giɗi dama ya kaiwa abokan Jalal dake can ƙofar gida zaune kan taburma a gindin bishiya.
Suma sunci.

Haka dai sukaci suka sha sukayi haniƙan.
Kana Shatu ta tattare komai ita da Junainah.

Bayan sun gama ne Bappa ya dawo nan suka sake sabuwar gaisuwa kana suka ci gaba da hira.
Sannan sukaje sukayi sallan azahar a masallacin ƙofar gidan Arɗo Bani.
Kana suka dawo sukaci gaba da hira.

Shi kuwa Ba'ana yana fita.
Ya kalli Babanshi cikin zaƙuwa yace.
"Baba Mata tana Rugar Bani tabbas tazo".
Da sauri Bukar yace.
"A a Ba'ana banji lbrin ba".
Da sauri yace.
"Ga nan zobe na yana gaya min kana cemin a a".
Sai kuma kawai ya juya ya nufi.
Bakin garin inda yasan zai samu Baroon yana zuwa yace.
"Baroon taso muje gidan malam liman indan mun isa ni zan zagaya ta baya kai kuma ka shiga ta ƙofar gida.
Ina da tabbacin yau Mata
na nan kuma yau zan tafi da ita.
Yanzu bari in kira su Droo baki ɗayansu."
Da sauri Baroon yace to.
Kana sukayi maza suka nufi cikin garin.

Shi kuwa Ba'ana ya kira duk sauran yaranshi suka biyo bayanshi.
Ta bayan gidan suka zagaya.
Shi kuwa Baroon ya shiga cikin gidan kai tsaye sabida sanin Sheykh na ciki kuma zaije ya bashi bayani ne.

Yana shiga kuwa Sheykh ya yafi toshi da hannu da sauri ya iso.
Bappa kam ido ya zuba musu jin Baroon nayiwa Sheykh duk bayanin abinda Ba'ana yake shiryawa.
Murmushi Sheykh yayi tare da cewa.
"Yanzu yana bayan gidan nan kenan?".
Da sauri yace.
"Eh dashi da sauran yaran".

Da sauri Sheykh ya kalli Jalal tare da cewa.
"Ka gayawa su Khalid su kula da duk wani dake jikin gidan".
To yace kana ya kira su ya sanar musu.
Nan take kuwa suka miƙe suka fara ɗan zirya

Ajiyan zuciya mai nauyi Bappa ya sauke lokacin da Sheykh yayi mishi duk bayanin abinda ke faruwa.
Ya ƙara da cewa.
"Idan ban kamashi ba bazai daina bibiyar rayuwar Shatu ba, kuma zai iya ci gaba da yiwa mutane illa in ya rasata".
Cikin sanyin jiki Bappa yace.
"Hakane".

Dai-dai lokacin ita kuma Shatu ta fito cikin ɗakin.

Randunansu ta nufa.
Dai-dai lokacin kuma Ba'ana yana ta wurin ta bayan danga.
Tasa hannu zata ɗebo ruwa kenan taga zoben yatsarta ya kawo wani haske.
Da sauri ta miƙe tsaye.
Jin muryar Ba'ana cikin raɗa da leƙota ta tsakankanin karan da akayiwa danga a madadin katanka.
Da sauri ta dafe ƙahon zuciyarta jin muryarshi ras cikin kunneta murya cike da rauni yace.
"Mata! Mata!! Mata!!!".
Ta sani duk duniya mutum ɗaya rak ke kiranta da wannan sunan.
Murya na rawa tace.
"Yah Ba'ana".
Cikin rauni yace.
"Mata ina kika shiga kika mance dani.
Mata kika barni cikin ƙunci da ciwon rai da zuciya na rashin ki Mata wlh zan iya jure komai amman bazan iya jure rashin kiba".
Kar-kar haka jikinta ya fara rawa.
Da sauri ta juya, da nufin zata koma ɗakin Ummey sai kuma ta tsaya tare da rumtse idanunta da ƙarfi.
Ganinshi ya ɓace ɓat ya dawo gabanta.
Cikin rauni yace.
"Ina zakije? Tafiya zakiyi ki barni!".
Ya ƙare mgnar da rauni yana kuma ƙoƙarin kai hannunshi zai kamo nata.
Cikin tsananin ruɗani tace.
"A a, Yah Ba'ana kada ka taɓani ni matar aurece".
Sai kuma ta kauce.
Da sauri shima ya kauce ya bita.

Cikin tsoro tace.
"Dan Allah Yah Ba'ana ka bar fito min".

Da sauri Sheykh ya miƙe tsaye cikin tsananin tashin hankali jin furucin da Shatu keyi tare kuma da kakkaucewan da takeyi alamun ana binta.


Su Jalal ma kab miƙewa tsaye sukayi.

Shi kuwa Sheykh da sauri ya nufi inda take.
Dai-dai lokacin su Ummey ma kab Suka fito sabida karan da Shatu tasa.
Sabida riƙo hannunta da Ba'ana yayi ya fara ja.
A zahiri ita kaɗai ake gani amman a badini shike janta.
Cikin rawan jiki ta tashin hankali tace.
"Bappa Yah Ba'ana ne yake jana wai zai tafi dani.
Yah Sheykh zai tafi dani".
Ta ƙare mgnar da ƙarfi da kuma sakin kuka.

Shi kuwa Ba'ana shima kukan yakeyi cikin rauni da tsananin so yake cewa.
"Mata yanzu wani kike cewa yazo ya ceceki ya rabaki dani.
Shin bakya so nane?".

Dai-dai lokacin kuma Jalal ya iso gab da ita.
Da sauri duk suka buɗe baki tare kallon yadda Jalal yayi sama ya faɗi ƙasa tib sabida wani irin azabebben naushi da Ba'ana ya kima mishi.
Wanda su ba ganinshi sukeyi ba.
Cikin wani irin tafasan zuciya irin na sojojin Jalal ya miƙe tsaye tare da nufosu.
Jin Shatu na cewa.
"No Jalal kada ka iso zai illa taka".
Ina bai kulaba sabida ranshi ya gama tafasa.

Ai kuwa kamar da fari, suka sake ganin Jalal yayi sama-sama yayi ƙasa har saida Ummey tayi kansa da gudu hannu tasa ta dagoshi.
Tare da juyowa tana kallon gaban Shatu cikin sanyi tace.
"Ayyah Ba'ana kayi haƙuri kada ka cutar min da ahlina nasan kai mai al'khairi ne a gareni.

Bappa ne ya matso shima a hankali hakama su Affan da Yah Jafar.

Shi kuwa Sheykh jingina kanshi yayi da jikin bishiyar Ceɗiya dake gefenshi.
Hannunshi na dama yasa ya tallabe haɓarshi yana mai bin inda Shatu take da wani irin kallo.
Sabida da fari zatonshi ko makaranta ne suka dawo.
So yanzu ya fahimci ba makaranta bane.
Hatsabibancin Ba'ana ne,
Nazari yakeyi yadda zai fito mishi ta sigar da dole ya karya lagonshi da takwabin addu'a.

Da sauri su Ummi duk sukace.
"Innalillahi".
Sabida ganin Ba'ana ya baiyana kansa garesu.
A take kuma ya ɓace.

Sai ya kuma sake baiyana ya kuma bace, saida yayi haka sau uku kana ya ɓace sai muryarsa ke tashin cikin rauni yace.
"Baroon kaci amanata ina sane na Barka.
Nayi hakane dan ka jawo shi wannan mai jajayen kunnuwa ya kawo min ita har nan.
Ku a zatonku tarkonku na faɗa baku san cewa nawa tarkon kuka faɗa ba sa'ansu ɗaya nayi tuba na gaske bazan sake kashe raiba."
Sai ya kuma bayyana still hannunshi riƙe da hannun Shatu cikin rauni murya na rawa tace.
"Ayyah Yah Ba'ana dan Allah ka sakeni kada ka rabani da ƴan uwana da ƴata".

Wani irin jujjuya kai yayi tare da cewa.
"Bappa kun kasa cika min al'ƙawarin da kukayi min ko.
Kai kuma Baroon kaci amanata ka muna furceni.
Shatu ke kuwa kin yiwa soyayya ta ta gsky riƙon sakainar kashi.
Wani abu kuke tunanin zaifi min ciwo da zafi sama da rabuwa da Shatu".
Sai kuma ya kalli Sheykh daya zuba mishi ido yana takaronto addu'o'i babu ƙaƙƙautawa ido cikin ido ya tsare Ba'ana da ido.
Shi kuwa Ba'ana murya a mace yace.
"Ko na bar barun a raye kaima watan wata rana zai ci amanarka tabbas zaici amanarka maci amana kuwa gubane".
Cikin sauri suka juyo kan Baroon daya saki wata iriyar gigitaciyar ƙara tare da komawa bayan Sheykh.
Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa inda Shatu take tana nufoshi alamun Ba'ana na matsowa inda yake.
Da sauri sojojin dake wojen suka shigo da gudu

Lokaci ɗaya mutane suka fara tururuwan shigowa gidan sabida ihun da Baroon yakeyi yana kiran sunan Ba'ana yana bashi haƙuri.

Jalal kuwa da sauri ya kuma nufo inda Shatu take wanda da ita suke gane inda Ba'ana yake.
Cikin tsoron kada ya cutar da Sheykh ya nufosu.
Gib ya kuma ture Jalal tare da cewa.
"Ummey ki gayawa wannan yaron zan illatashi fa ya dena matsowa inda nake".
Gaba ɗaya tsoro ya rufesu jin furucinsa.

Jalal kuwa hatsala iya hatsala ya hatsalo allurar ta motso to amman kuma faɗa da Ba'ana tamkar faɗa da iska mai kaɗawa ne ko kuma duhu.
Da sauri Ba'ana ya juyo kawai sai ya fara dukan sojojin nan baki ɗayansu.
Ya bugi wannan ta nan ya bugu wan can ta can.
Kana ya haɗa da shaƙo wuyan Baroon.
Kurma ihu da kakarin mutuwa Baroon yakeyi da ƙarfi.
Wanda yasa gaba ɗaya gidan ya cika da mutane.
Harda su Arɗo Bani.
Bukar da Bugulu kuwa gefen Bappa suka tsaya suna kekrketa dariyar mugunta.

Junaidu kuwa gefen Junainah dake ta kuma ta tsaya yana bata baki.

Gaba ɗaya hankalin mutane ya tashi.
Su Bappa da Arɗo bani da sauran dattawan Rugar Bani duk sai haƙuri suke bawa Ba'ana sabida ganin yadda yaketa dukansu Jalal ba sauƙi.

Ita kuwa Shatu da gudu ta faɗa jikin Sheykh sabida saketa da Ba'ana yayi.

Ganin ta nufi wurin Sheykh ne ya sashi sakin wuyan Baroon tare da barin dukan su Jalal.
Ya nufo kansu Sheykh da Shatu.
Cikin tsananin ruɗani Shatun ke cewa.
"Yah Sheykh mu gudu zai maka illa".
Jamil kuwa tuni ya fara aikinshi.
Affan kuwa da Yah Jafar Kara matsowa kusa da Sheykh suke gudun kada a cutar dashi.
Aunty Juwairiyya da Ummi da Sara da inna Amarya kuwa gaba ɗaya jikinsu rawa yakeyi.

Shi kuwa Sheykh murmushi yayi jin Shatu tace.
"Wayyoooooooo Allah Yah Ba'ana ka sakeni".
Hakane yasa ya fahimci Ba'ana na kusa dashi.
Ido ya lumshe tare da ɗago hannunshi kana a hankali yace.
"Bismillahi".
Yana faɗin haka yaji hannunshi ya sauƙa kan hannun Ba'ana kuma ya baiyyana kowa na ganinshi.
Cikin nitsuwa Sheykh ya fara karanto Ayatulkursi'u yana mai kallon Ba'ana ido cikin ido wanda a take ya karya duk wani sihirin da Ba'ana ke tutiya da tinkaho dashi da ayar Allah. (Haske ya kori duhu)

Da sauri Shatu ta koma bayan Sheykh ɗin.
Shi kuwa Sheykh juyowa yayi ya kalli su Jalal daketa haki cikin haki da tsananin tafasar zuciya suka nufosu.

Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Ba'ana ganin yadda yaketa fiffizgewa da buga ƙafarshi ta dama da ƙasa amman ina ya kasa ɓacewa.

Cikin sanyi yace.
"Jalal ku kamashi da sunan Allah bazai sake ɓacewa ba har abadan da izinin ubangiji".

Ai kuwa da sauri Jalal yasa hannunshi ya damƙo wuyan Ba'ana tare da cewa.
"Bismillahi".
Ai kuwa bai ɓace ɗinba.

Cikin wani irin tafasan zuciya da zafin yadda Ba'ana yayi ta libgarsu kamar shine sojan sune masu laifi cikin takaicin.
Yayi mishi wani irin azabebben shaƙa tare da kima mishi naushi a cikinsa tare da kalmar "Bismillahi".
Wani irin azabebben ihu mai rakaɗi da baiyyana azabar da yaji yace.
"Wayyoooooooo Allah na rana,".
Cikin haki Jalal ya kuma haɗa mishi wani naushin tare da cewa.
"Kasan Allah ne kafurin banza matsafi".
Dai-dai lokacin kuma sauran abokanshi sojojin suka rufe Ba'ana da azabebben duka da ammaton sunan Allah wanda hakan ke ƙara kwance duk wani ɗaurin sihirin dake jikin Ba'ana.

"Ya ilahi ya mujibadda'awati."
Mamey da Ummi ke faɗi sabida wani irin dukan zaban da su Jalal keyiwa Ba'ana.

Ita kuwa Shatu cikin tsananin tsoro da kerma ta ɗan leƙo.
Dai-dai lokacin Khalid ya murɗe hannun Ba'ana ɓas ya bada sautin karyewa.
Da sauri ta rumtse idanunta tare da sakin wani irin kuka mai ciwo a rai.
Da sauri Sheykh ya juyo yana kallonta.

Bappa kuwa dasu Arɗo Bani dasu Yah Jafar kab Bukar da Bugulu suke kallo wa ɗan da suke wani irin kuka mai cike da tashin hankali.
Jamil da Affan kuwa sarawa su Jalal sukayi.

Mutanen Rugar Bani kuwa kab suna tsaye wasu tuni hawaye na zubo musu.

Da ƙarfi Ba'ana yayi wani irin azabebben ihu da kururuwa sabida taka hannunshi da Khalid ya karya.
Wanda Umar yayi ɗaya sojan ya murza tare da buga mishi naushin da saida yayi birgiman kule ya iso har gaban Sheykh.

Cikin rauni da azabar raɗaɗi murya na rawa yace.
"Mata! Mata zasu kasheni!".
Cikin wani irin rauni da tsananin tausayi wani irin masifeffen kuka mai ƙarfi yan kwacewa Shatu.

Da sauri ta zame har ƙasa ta durƙusa.
Sabida wani irin azabebben tokara da guiwa da Jalal yayi mishi bisa tsakiyar bayanshi.
A take sai ga jini ta hancinsa da bakinsa.

Murya na rawa cike da rauni Shatu ta ɗago kanta.
Ta kalli Jalal dasu Khalid kana ta kalli jinin bakinshi daya ɗan tsallo ya taɓa farin gyalen jikinta.
Wani irin kukane mai cike da tsananin tausayi rauni ta fashe dashi tare da cewa.
"Ayyah Jalal dan Allah ku barshi kada ku kasheshi ku barshi dan Allah".

A hankali Jalal ya ɗan tsaya yana maida wani irin azabebben numfashin haƙi.

Sheykh kuwa wani irin kallo mai cike da azabebben kishi ya watsawa Shatu.
Tare da sa tafin hannunshi ya tallabe haɓarshi.
Kana ya jingina kanshi da jikin bishiyar yana mai kallonsu.

Mamey kuwa itama zamewa tayi tanamai sakin kuka.
Ummi, Inna Amarya, Aunty Juwairiyya, Sara, dama duk sauran matan dake wurin wasu irin hawaye ne masu zafi suka tsastsafo musu.

Junainah kuwa zuwa tayi ta durƙushe gaban Ba'ana gefen Shatu cikin wani irin azabebben kuka mai cike da rauni tace.
"Wayyo Yah Ba'ana Dan Allah Adda Shatu ki hanasu dukanshi."

Da ƙarfi Junainah ta faɗa jikin Shatu lokacin da Jalal yayi wani irin juyi ya kifawa Ba'ana wani irin masifeffen mari da tafin ƙafarsa.
Tare da cewa.
"Wato kai gaka shege har zaka sa hannu ka daki jamin soja".
Wani irin azabebben karkarwa jikin Ba'ana ya farayi tamkar mazari.

Wani irin kuka mai azabar ciwo da cin rai Bukar da Bugulu suka saki sabida ganin yadda hukuma ke azabtar da Ba'ana tamkar zasu ɗauke ransa.

Cikin rauni murya na rawa ido na zubda hawaye Mamey tace.
"Jalaluddin ku bar dukanshi".
A hankali Jalal ya koma baya ya zauna bisa dakalin ƙofar ɗakinsu Giɗi.
Sabida yasan muddin Mamey ta kirashi da sunanshi kai tsaye to abu ya ta'azzara gareta.
Domin Babana take kiranshi, sai gashi yau full name ɗinshi ta kira bama Jalal kawai ba.

Sai kuma ta kalli su Khalid kana ta juyo ta kalli Sheykh murya na rawa tace.
"Muhammad ka hanasu dukanshi".
Cikin wani irin yanayi Sheykh ya ɗagawa su Khalid hannu.
Haka yasa suma suka koma gefen Jalal suka zauna suna haki da maida numfashi.


Shi kuwa Sheykh ido ya zubawa Shatu dake kuka tamkar ranta zai fita.

Gaba ɗaya wurin babu wanda rauni bai darsu bisa zuciyarsa ba.

Yah Jafar da Bappa kuwa tuni hawaye suke zubdawa.

Bukar da Bugulu kuwa da rarrafe suka iso gareshi.

Shi kuwa Ba'ana wani irin dogon numfashi mai cike da azaba rauni nadama ya fesar a wahalce kana a hankali ya fara yunƙurin tashi zaune.
Amman Ina ya kasa ganin hakane yasa Bukar yin sauri yasa hannunshin ya tallaboshi ya ɗagoshi.
Ya jingina bayan Ba'ana nan da kirjinsa.
Ya zama suna fuskantar Shatu dake kuka tamkar ranta zai bar gangar jikinta gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Cikin wani irin rauni murya na rawa yace.
"Mata!".
Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta ɗaurasu kanshi.
Wanda haka yasa ta saki wani sabon kuka, Junainah ma kukan ta saki da ƙarfi.
Shi kuwa Ba'ana hawaye na kwarya yana ƙore jinin hancinsa da bakinsa murya can ƙasan maƙoshi yace.
"Mata".
Murya na rawa kuka na kumbe mata tace.
"Na'am Yah Ba'ana".
Wani irin murmushi mai rauni yayi kana a hankali yace.
"Mata Ranar da nake tsoro tazo, ranar da na gaya miki zata iya ɓaci zata zo, gata yau tazo".
Sai kuma ya ɗago ɗaya hannun nashi mai lafiyar ya sharce hawayensa, cikin sanyi ya jujjuya kanshi dake masifar mishi ciwo.
Ido ya zuba mata ganin yadda take kuka har numfashin ta na fizga.
A hankali yace.
"Shatu kin san son da nake miki gsky ne?".
Cikin kuka tace.
"Na sani Yah Ba'ana na sani son da kake min gsky ne".
Wani dogon ajiyan zuciya mai nauyi ya sauƙe tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ga hawaye shar-shar bisa fuskarshi.

Cikin rauni yace.
"Ke kuma kin taɓa sona a ranki da gsky?".
Kanta ta fara ɗan bugawa da ƙafar Sheykh dake gefenta.
Tare da cewa.
"Eh eh eh Yah Ba'ana na soka so na gsky na soka so irin wanda naso mu gudu tare mu tsira tare nasoka irin son da nake yiwa Yah Al'ameen sabida bana son irin wannan ranar tazo mana".
Kanshi ya jujjuya kana cikin rauni yace.
"Shatu haka ƙaddarar rayuwata take."

Sai kuma ya kalli Junainah a hankali yace.
"Junnu me yasa kike kuka, bakya son a kashenine".
Cikin kuka tace.
"Bana son a kasheka Yah Ba'ana. Ina sonka kamar yadda nake son sun Yah Giɗi".
A hankali ya sunkuyar da kanshi tare da sakin wani irin raunataccen kuka wanda saida Affan ya zubda hawaye.

Cikin sanyi yace.
"Mata ina ƴarmu?".
Cikin wani irin rawan jiki hawaye na kwarya.
A hankali tasa hannunta ta amshi Afreen dake hannun Ummi.
Kana ta juyo da rarrafe tamkar ƙaramar yarinya ta iso gabanshi cikin rawan murya tace.
"Gata nan Yah Ba'ana".

Wani irin murmushi mai yelwa yayi wanda saida fararen haƙoranshi suka fito ras.
Da idonshi ya nuna mata cinyarshi.
Cikin kuka ta sunkuyo ta kwantar mishi da Afreen bisa cinyarshi.

Kana ta kife kanta cikin cinyoyinta ta saki kuka.

Shima kukan ya saki mai rauni.
Kana yasa tafin hannunshi ya shafi kan tattausan suman gashin Afreen hawayenshi na kwarya suna ɗiga kan goshinta.
A hankali yace.
"Masha Allah, Allah ya raya mana ita bisa imani al'farma Annabi da al'ƙur'ani Allah yasa mahaddaciyar al'ƙur'ani ce, ya azur tata da miji na gari".
Karo na forko da Sheykh ya motsa lips ɗin shi a hankali yace.
"Amin ya Allah". Sabida daɗin Addu'ar da akayiwa ƴarshi.

Itama Shatu cikin kuka tace.
"Amin thumma Amin".
Sai kuma ta ɗago kanta a hankali jin yana cewa.
"Naji lbrin Ummey ta tuno baya ta gane ahlinta ance min ma wai ɗan ta ne ya aureki ko?".
Ina ta kasa mgn sai kuka,
Ummeyn ce ta sharce hawayenta a hankali tace.
"Eh Ba'ana na tuno baya, na gano ahlina Allah ya saka da al'khairi ya biyaka da mafi kyawun sakamako".
Cikin rauni yace.
"Amin Amin Ummey".
Sai kuma ya kalli Bappa dake ta kuka a hankali yace.
"Bappa kana kukan baka cika min al'ƙawarin da kayi bane?".
Da sauri Bappa ya gyaɗa kai alamar eh.
Kai ya jujjuya kana a hankali yace.
"Ba laifinka bane, ƙudirin ubangijine ba gashi yanzu Ɗiyar Shatu ce a cinyata, wani bazai haifi ɗan wani ba ai. Ni na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login