Showing 114001 words to 117000 words out of 352722 words
fari.
Cikin jin daɗi kayayyakin Umaymah tace.
"Kai nako gode naji daɗin kayan miyar nan, dan mu wurinmu suna wuyar samuwa."
Sai kuma ta juyo ta kalli Shatu dake zaune gefenta,
Tayi wani irin kici-kici da fuska babu alamun wal-wala.
Cikin nuna jin daɗi tace.
"Ɗiyata ga kyautan Hajia Mama, komai bibbiyu ne ɗaya naki ɗaya nawa ne, kiyi godiya".
Cikin wani irin kallo mai cike da ma'anoni da sarƙafe-sarƙafe ta gyara zamanta, tare da komawa ta jingina da kujera, ƙafarta ɗaya ta ɗaura bisa ɗaya tare da fara karkaɗa ƙafar cikin fuska a haɗe kana a daƙile ta nuna kayan tare da cewa.
"Bama so, Umaymah Bama buƙata".
Cikin tarin mamaki da al'ajabi duk suka juyo gareta suka zuba mata ido.
Ummi da Umaymah kuwa har suna haɗa baki wurin cewa.
"Sabida me? Akanme zakice bakya so?".
Ba tare da ta kallesu ba tace.
"Ba cewa nai bana soba, cewa nayi bamaso, itama Umaymah bata so."
Cikin tsananin mamaki suka bushe suna kallonta,
Jalal ne ya zuba mata ido cikin haɗe fuska.
Hajia Mama kuwa wani irin kallo mai cike da tsoro da mamaki da al'hini da jin tsanar Shatu cikin ranta, ta rasa me wannan yarinyar take nufi da ita,
ta kasa gano me take gadara dashi.
Cikin tarin takaici da zafin rai tace.
"To kuma baki isa da gidan ba,
Bare ki zana layi a biki, ke in banda rashin sanin darajar manya har zaki gaya min haka, ko gidanku ba manya ne?."
Cikin isa da ɗaga murya tace.
"Yesss! Gidanmu babu manya irinka, Bama so bazamu amsaba ki tattara tarukucenki kije ki bawa wasu can ba dai muba".
Cikin tashin hankali Umaymah ta daka mata tsawa tare da cewa.
"Ke Aysha ki nitsu kisan da waye kike mgna".
Cikin ɗaga murya tace.
"Na sani Umaymah na sani nasan da wacece nake mgna kece bakisan wacece itaba".
Cikin mamaki da sauri Sheykh ya ƙarisa fitowa cikin tamfatsen falon shi.
sabida ya gama shirin jummarsa,
jiyo hayani da hargowane yasa ya nufo falon da sauri.
To jiyo muryar Umaymah ne yasashi buɗe ƙofar falon da hamzari ya fito.
Da sassarfa ya nufo falon.
Dai-dai lokacin daya isone,
Aysha ta miƙe tsaye cikin faɗa da tsawa ta nunawa Hajia Mama da hadimanta da Batool hanya tare da cewa.
"Maza ku tattara waɗannan banzayen tarkacen naku ku tafi dashi, ku ɓace min da gani. Ku fita daga nan! Ku fitarmin gidana".
Ta ƙarishe mgnar da ƙarfi.
Wani irin miƙewa tsaye Umaymah tayi tare da yin sauri tasa hannunta ta....!
By
*GARKUWAR FULANI*
Ta kamo hannun Jalal da ya miƙe tsaye da nufin yarfa mata mari.
Cikin wani irin masifeffen tsana, Hajia Mama takalli Shatu.
Kana da sauri ta juya ta nufi hanyar fita.
Sheykh da tunda ya fito yake tsaye tamkar an dashi ne,
yayi saurin bin bayanta tare da cewa.
"Hajia Mama! Mama!! Mama dan Allah kiyi haƙuri, kizo karki fita Please Mama karki fita, babu wata halitta da zata miki iyaka da sashina, in kin tafi kenan kinbi umarninta."
Cikin tashin hankali yake waɗannan kalaman yana mai binta a baya.
Jamil kuwa miƙewa tsaye yayi ya zubawa Shatu idanu tamkar zasu faɗo ƙasa.
Aunty Juwairiyya kuwa, wani irin kallo mai sarƙafe da ma'anoni takeyiwa Shatu.
Ya Jafar kuwa wani irin kallo mai surke da murmushin jin daɗi yakeyiwa Aysha.
Ummi kuwa tuni jikinta rawa yakeyi da abinda ya faru.
Imran, Ya Hashim, kuwa ido suka zubawa sarautar Allah.
Hibba kuwa kuka takeyi tare da riƙo hannun Shatu tana ja tare da cewa.
"Aunty Aysha ki bari, Mamace fa! Kizo mu tafi ɗaki".
Tanayi tana jan hannun Shatu da ƙarfin tsiya, dole yasa Shatu ta bita a baya.
Umaymah kuwa wani irin tashin hankali da tafasan zuciyane ya dirar mata lokaci ɗaya.
Da wani irin kallo tabi bayan Aysha dashi.
Duk wanda ya ganta yasan tana cikin tashin hankali.
Gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi.
Sun daɗe a haka, da kyar dai
Cikin wani irin tafasan zuciya ta saki hannun Jalal.
Tare da komawa ta zauna.
Da yatsa ta nuna musu hanyar fita daga falon. Murya a hargitse tace.
"Kul kada ka sake tunanin gigin ɗaga kayi nufin taɓa lfyar Aysha, bana so kul.
Maza Ku tafi masallaci".
Sai lokacin suka jiyo sautin muryar Jabeer yana Hudba.
Wanda daga jin muryarsa kasan yana cikin baƙin ciki.
Wani irin numfarfashi Jalal ya sabke tare da yin koffa kana ya juya ya nufi hanyar fita shi matsalarsa meyasa Umaymah na mgn Aysha na mgn Umaymah na hanata abu tanayi.
Haka su Jamil da su Imran da ya Hashim da Ya Jafar suka fita.
Ita kuwa Aunty Juwairiyya wani irin tashi tayi ta fita ta nufi Side ɗin ta.
Ya zama Ummi da Umaymah ne kaɗai suka rage a falon.
Shiru sukayi tamkar ruwa ya cin yesu.
"Uhuhhmmmm". Umaymah ta fesar da wani zazzafan numfashi mai ɗumi.
Hakama Ummi tagwayen numfarfashi masu nauyi ta sauƙe.
Kallon juna sukayi, cikin shiga al'hini wannan al'amari cikin tsoro da karaya Umaymah tace.
"Toh wai meye hakan? Meke faruwa ne? Me hakan yake nufi? Kaina ya kulle. Wani zagon kasan kuma aka shirya tsakanin Shatu da Hajia Mama ko dai dama da zagon ƙasan ne?.
Wake saƙa gadar zare, muna na bi ta kai ya rubta da mu".
Wani numfashin Ummi ta fesar tare da cewa.
"Tabbas akwai babban al'amarin dake faruwa wanda bamu saniba Ni tsorona ɗaya kada a juya ƙoƙwalwar yar mutane."
Shiru sukayi cikin ta'ajjudin al'amarin. A hankali suka miƙe a tare suka nufi ɗakinsu jin har an idar da sallan a masallacin.
Al'wala sukayi kana sukayi salla daga bisani suka, fara tattauna wani abu na sirrin masarautar Joɗa.
A cikin ɗakin Shatu kuwa, tunda suka shiga ta kwanta bisa gado.
Bacci tayi bacci, hakama Hibba.
Sai ƙarfe uku dai-dai Shatu ta tashi.
Cikin kasalan baccin da bai gama isarta ba, ta miƙe ta shiga bathroom.
Wonka tayi tare da al'wala.
Bayan ta fitone, ta tada Hibba, ita kuma ta kabbarta sallah.
Kafin ta idarma Hibba ta fito, gefenta tazo itama ta kabbarta sallan.
Basu tashi bisa sallayan ba, sukaji kiran aallan la'asar.
Haka yasa sukayi sallan. Suna idarwa Hibba ta miƙe ta nufi ɗakin Umaymah.
Ita kuwa Shatu ninke sallayar tayi kana ta dawo gaban dreesing mirror.
Mai ta shafa tare da ɗan murza fauda a fuskarta, kama ta shafa man baki.
A cikin sanyi taje gaban drower'nta,
hannu tasa ta buɗe drower'r, wata tattausar doguwar riga mai masifar kyau ta zaro.
Kalar rigar Black blue mai sheƙi, saman rigar a ɗan tsuke daga ƙasan ƙugunta kuma a buɗe,
yanada wasu duwasu kamar na Daimond daga sama har ƙasan gaban rigar.
Hannunta kuma masu faɗi.
Tayi kyau sosai cikin rigar, dogon gashinta ta haɗa ta tubke wuri ɗaya ta kitse jelar kana ta nannaɗe jelar a ƙeyarta,
sannan tayi rolling kanta da mayafin wanda dai dai inda zai zauna a goshin akwai duwatsun.
Turare ta fesa, kana cikin sanyi da kasala ta nufi, falo.
A falon ta samu, Hibba a kwance tayi shiru.
Ganin bata gan fitowarta banema,
Yasa ta nufi inda take gefenta ta zauna tare da cewa.
"Hibba ɗauko mana awaran".
Cikin sanyi Hibba tace.
"To". Kana ta miƙe ta nufi falon, jin shiru ba kowa a cikine, yasa ta nufi kitchen a hankali-hankali.
Foodflaks ɗin da suka sa awaran da suka soya ta ɗauko.
Tana dawowa ta zauna kusa da Shatu tare da cewa.
"Gashi". Kai ta gyaɗa mata tare da nuna mata kitchen ɗin ta, tace.
"Ɗauko mana plate da roban yajin da Gimbiya Aminatu ta aiko mana.
Kizo mana da ruwa".
Ba tare da tace komaiba ta juya ta tafi.
Bayan ta dawone suka zauna suka fara cin wanda suka zuba.
A can falon Hajia Mama kuwa,
duk mgnar da Umaymah da Ummi keyi, shiru tayi ta zuba musu ido.
cikin sanyi Umaymah tace.
"Addana kiyi haƙuri, kin san yaran sai a hankali, dan Allah kada kisa wani abun a ranki wata ran ko ance tayi miki bazatayi ba".
Murmushi tayi mai cike da ma'anoni kana tace.
"Uhummm ba komai Khadijah jekici gaba da shirin tafiyarki, karki damu kinji".
Ido suka zuba mata domin duk basu gamsu da mgnarta ba, to amman ya zasuyi tunda tace ba komai.
Haka suka tashi suka dawo falon.
Yau su Jalal ma basu zoba.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, tunda aka idar da sallan azahar ya dawo, ya wuce su Umaymah a falon ba tare da yace musu ƙalaba.
koda ya shiga ɗakin ya samu yayi bacci tsakanin azahar da la'asar kamar yadda ya saba, hakan bai samuba.
Sabida abubuwan dake ranshi.
Bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwan sanyi, tare da fara yage towel ɗin dake hannunshi.
haka yake tsaye a ƙasan ruwan har saida yaji an kira sallan la'asar. Nanne ya fita ya tafi masallacin.
Bayan an idar da sallan ne ya dawo gida.
Ganin babu kowa a falon ne yasashi zama, bisa kujerarsa.
Ƙafarshi ɗaya ya ɗaura kan ɗaya.
A haka su Umaymah suka sameshi.
Gefenshi Umaymah ta zauna bisa kujerar dake kusa dashi.
Ummi kuwa gabanshi ta zauna bisa carpet.
A hankali ya buɗe kwayar idanunshi.
Cikin tarin ɓacin rai ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi ina wannan fitsarerren abun da bai san darajar manya ba!?."
Cikin sanyi Ummi tace.
"Allah ya huci zuciyarka tuba takeyi, in sha Allah bazata sakeba, Hajia Mama da kanta ta yafe mata".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"Ummi ko dai kece kika bata dama da matsayin yiwa Mama hakane?".
Cikin sauri tace.
"Wanne ni wlh bani bace".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Umaymah da itama shi take kallo cikin ɓacin rai yace.
"Umaymah har akwai wani abun da zai hana mama shigowa sashina? Har yaushe waccar babyn robar ta samu dama da ikon bada izinin shiga da fita cikin sashina da abinda ya shafi rayuwata?
Me take nufi dani da iyayen nawa."
Kauda ido Umaymah tayi daga kallonshi kana a hankali tace.
"Ba isa bane! Akasi aka samu! Nifa inaga har yau Shatu'n bata gama sanin mutanen masarautar Joɗa da kuma dangantakar makusan tankaba, ayi mata haƙuri a mata uzuri a dai wannan karon".
Juyowa yayi ya kalli Ummi tare da cewa.
"Ummi a kira min waccar abar".
Da sauri Ummi ta miƙa tare da cewa to.
A falon ta samesu, cikin fuskar da babu yabo babu fallasa ta kalli Shatu dake gefen Hibba da alamun ta cire hannunta a cin awarar kanta ta ɗan kauda tare da cewa.
"Kizo Sheykh yana kiranki".
Kai ta gyaɗa tare da cewa "Toh". miƙewa tayi taje Dinning area ta wonke hannunta, kana tazo tabi bayan Ummi.
A gabanshi Ummi ta zauna ganin haka itama ta zauna a gabanshi.
shiru tayi tana kallon yatsun fararen sawunshi. Shi kuwa kanshi na gefe ba tare da ya juyo ya kalleta ba yace.
"Ke ki shiga hankalin ki, kisan abinda kikeyi da wanda zakiyi! Ke har kin kai matakin da isar da zaki ƙaddamar min da iko da isa a cikin gidana? Ko dai ce miki akayi gidan nakine?".
Kai ta gyaɗa mishi alamun eh ance mata gidan natane!.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da ci gaba da mgna dan shi bai ga sanda ta gyaɗa kanba hakama Umaymah, sai Ummi ce kaɗai ta gani, su kuwa sai murmushi sukayi.
Cikin kausasa murya yace.
"In baki san darajar manya da iyayeba, to ki zama kurma bebiya makauniya a cikin giddannan kafin Ubangiji ya zantar da Hukuncin da ikon zamanki da barinshi dan ikone na Allah bana waniba.
Har kin isama Mama tazo ki koreta dan idonki basu da ɗigon kunya.
Ko karen gidannan baki da ikon hanashi abu da sakashi bare Mama.
ke ta bawa abun ne da zakice bakya so.
Kece mai bakin mgn uwar fitsararru ko?".
Sam abinda bai saniba zuwa yanzu hankalinta, tunaninta nitsuwarta, jinta, da ganinta duk suna kan farar ƙamarshi ta dama, da zanen maciji ke liƙe kamar macijin na tafiya.
Wani irin ba hagun numfashin ta sauƙe a hankali,
tare da rufe manyan idanunta da azaban ƙarfi.
Sabida gani takeyi Tamkar macicijin ne ma da kanshi ke manne a jikinshi yana kuma motsa ɗan bindinshi dake saman babbar yatsarshi.
A hankali ta buɗe idanun kana tabi kan rumfar ƙafar da ido, inda take ganin zanen maciyar yabi.
Kasan cewar a zaune yake ya kuma ɗan tattare al'kyabbar jikinshi.
Shi yasa tana iya ganin har ƙarshen rumfar tafin ƙafar nashi.
Inda iya nan jallabiyar jikinshi ta rufe.
da sauri ta ƙara rusunar da kanta wai ko zata ga ci gaban tafiyar macijiyar.
Umaymah ce ta ɗan kalleta cikin wata iriyar murya tace.
"Ki tashi muje ki bawa Hajia Mama haƙuri, ku nemi yafiyarta ki kuma kiyaye gaba, kinji".
Cikin sanyi tace.
"Toh".
Still Bata miƙeba, cikin ɗan ɗaga murya yace.
"Tashi muje yanzu ki bata haƙuri, in ta haƙura kinyi babban Sa'a".
cikin sanyin jiki ta miƙe tsaye.
Shima miƙewa yayi, Ummi kuwa da sauri ta nufi ɗakin Shatu.
Jim kaɗan ta fito da wata kekyawar al'kyabbar matan masarauta ta zuramata.
Bayan ta gama gyrashi ne, tasaka hular.
Shi yayi gaba ita kuwa.
Tabi bayanshi Umaymah da Ummi suka biyo bayanshi.
Suna isa bakin mashigar farfajiyar Side ɗin Hajia Mama,
ta tsaya gis tare da yin ƙasa da kanta.
Ummi ce tace.
"Muje mana".
Shiru batayi mgna ba, jin hakane yasashi juyowa, karon forko kenan da ya zubawa tsawonta ido.
cikin ɓacin rai yace.
"Muje ki lashe aman da kikayi da kanki".
Cikin sanyin sauti tace.
"Ni bazan shigaba".
Da mamaki Umaymah tace.
"Innalillahi wai ke Ayshs wani irin taurin kaine dake? Menene manufarki?".
Murya can ƙasa yana rawa alum zatayi kuka ta kalli Umaymah tace.
"Kiyi haƙuri Umaymah ki gafarceni, amman ni bazanje ba, in kuma zanje to ku ku koma, zanje ni ɗaya zan bata haƙuri".
Cike da al'ajabi Umaymah tace.
"To sabida me bazaki je da muba".
Cikin faɗa Sheykh yace.
"Sabida muna furci mana, ba zuwa zatayi ba, shiyasa zatace sai dai in ita ɗaya zataje, maza wuce muje a gabana zaki bata haƙuri".
Cikin sanyi Umaymah tace.
"Jazlaan barta mu tsaya mu jirata anan in dai zataje ita ɗayan".
Kanshi ya dafe tare da cewa.
"To wai Umaymah mu bayaninta ne da zamu tsaya muna jiranta".
Ummi ce ta mishi alamun yayi haƙuri ya yarda.
Shiru yayi tare da komawa gefen jerin bishi yoyin namiji kwanɗa ya zauna bisa kujerun silver dake zagaye da wurin wanda ko wani side akwaisu.
Itama Umaymah da Ummi zuwa sukayi suka zauna.
Ita kuwa Shatu a hankali ta fara taku ta nufi cikin farfajiyar, suna hangota har ta isa bakin ƙofar.
turawa tayi ta shiga, kana ta maida ƙofar ta rufe.
Bayan kamar 37 minutes ta fito.
Cikin wani irin tafiya mai baiyana tsantsar jin daɗi, fuska cike da fara'a ta nufosu.
A hankali ta isa gabanshi ciki ɗan ɗaga murya tace.
"Na bata haƙuri ta yafe min, ta samin al'barka. Kaima kayi haƙuri ka yafe min".
Da mamaki suka kalleta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wari irin kallon tuhuma yayi mata, kana ya miƙe tsaye tare da cewa.
"In ma ƙarya kikayi, ni ba'amin ƙarya".
Sai ya kuma kalli Umaymah tare da cewa.
"Umaymah kuje ki ƙarisa shirinki bari inje wurin Hajia Mama".
To tace kana taja hannun Shatu suka tafi. Shi kuwa da Ummi suka nufi cikin Side ɗin Mama.
Bayan sallan isha'i, cike suke a falon. Gaba dayansu, Umaymah zaune a tsakiyarsu da jakarta, Sheykh Jabeer na yi mata addu'o'in isa lfy suna amsawa da Amin Amin.
Bayan sun shafa addu'o'in ne ta miƙe tsaye, tare da kallon su baki ɗaya, murya na rawa tace.
"Jazlaan zan tafi, zan bar hankali na, a nan ko na koma banda nitsuwa, kullum ina cikin taraddadin abubuwanda yake faruwa, Jazlaan na sani kaine GARKUWAR yayanka da ƙanneka. Ga wani sabon nauyi ya ƙarun maka.
Aysha baƙuwace bata san komaiba kam al'amuran Masarautar Joɗa, dan Allah in tayi abinda ba dai-dai ba kuyi mata uzuri.
Ita komai a sabon abu zata ganshi abinda bata taɓa ganiba.
Mun rabata da iyayenta yayunta ƙannenta mun kawota tsakiyarmu, mu kasance mata adalan masu masauƙi.
Na sani Jazlaan ka fini sanin haka da kuma haƙƙoƙinta da suka rataya gareka."
Sai ta kuma kalli sauran yaran yar uwarta ɗin tace.
"Jalal, Jamil, Aysha matsayin yar uwarku take, yayarku ce, matar yayanku. Bana son raini especially kai Jalal, ban gamsu da irin mu'amalat ɗin ka da itaba.
Babu wanda yake nuna min yadda nakeso a kanta sai Jafar, a duk sanda ya ganta zaiyi mata murmushi kamar yadda yake min, in yaga bata nan zaiyi ta dube-duben da nasan da yanada baki zai tambayeni lfyarta.
Zan bar Hibba saboda itane, bana son taji kanta a matsayin bare."
Shiru sukayi gaba ɗayansu sabida yadda take kuka da yin mgna tamkar mai bar musu wasiya, ko wacce wani tsohon damuwa ya taso mata.
Sharce hawayenta tayi tare da cewa.
"Ummin Jabeer zan tafi zan barki da sauran aiki, dan Allah ki kula da Shatu da mu'amalarta da Hajia Mama, ki nuna mata uwar miji ba abun rainawa bace".
Sai kuma ta miƙowa Aysha da taketa kuka hannun ta jawota tsaye ruggume ta tayi cikin zubda hawaye tace.
"I dan akaga damuna ana zaton yabanya zatayi kyau, kallon damuna nakeyi miki a cikin ahlin yar uwata.
Ina jin zaki zamo mana haske mai yaye duhun daya maye ganinmu, tun kafin yau ni na sanki a mafarkina Allah ke nuna min ke a matsayin matar Jazlaan ɗin na, kuma Allah yana nunamin abubuwa da dama a kanki a cikin mafarkaina, wasu kuma sunma tabbata na gansu.
dan Allah ki riƙe min Jazlaan amana, ki lura da ƙannenshi yadda zaki lura da naki ƙannen ki kula da Jafar kada ki tsoraceshi bazai cutar da keba ki ɗaukeshi a
Matsayin wa".
Cikin zubda hawaye Shatu tace.
"In Sha Allah Umaymah zan kiyaye zan kuma zamo yadda kike zatonta, koda sanadin haka zan rasa jigo biyu na rayuwata rai da lafiya ta".
Kalaman Umaymah da Aysha kuramen baƙine da su kansu ɗaya bata fahimci abinda ɗaya take nufiba, hakama ɗayar, bare su Jalal dake tsaye.
Jawo Hibba tayi ta haɗa su ta ruggume,
kana ta jawo Juwairiyya tace.
"Ku duk yara nane ku zauna lfy".
Gaba ɗaya da to suka amsa.
Cikin sauri Umaymah ta sakesu kana ta miƙa wa Ummi hannu sukayi musababa, tare da bar mata sallahun yaran.
Daga nan suka fita, gaba ɗayansu.
Sai Shatu da Hibba da suke kuka, ganin hakane Ummi ta dawo ta zauna dasu.
Jabeer da Jafar da Umaymah kuwa Side ɗin Mama sukaje, tayi sallama da ita, suka rabu suna hawaye.
Daga nan Side ɗin Lamiɗo da Gimbiyar shi sukaje.
Nan sukayi sallama dasu kana suka fito, inda suka samu Jamil da Jalal sun kawo musu motoci. Daga nan suka shiga suka tafi Airport tare da rakiyar motocin fadawa guda uku ya zama motoci biyar ne suka tafi kaita Airport.
A gida kuwa, da kyar Ummi ta samu ta lallashi Shatu da Hibba da cewa in basuyi shiruba, zata, sa akai Hibba Airport ta tafi da Umaymah.
jin hakane yasa Hibba tayi shiru. Ita kuwa Shatu dama ba kuka mai sauti takeyi ba, zubda hawaye takeyi.
Ƙarfe tara dai-dai jirginsu Umaymah ya tashi zuwa jihar Tsinako.
A gida kuwa tuni Shatu da Hibba sun shiga