Showing 288001 words to 291000 words out of 352722 words

Chapter 97 - GARKUWAAA COMPLTE HAUSA NOVEL

17 Oct 2024

30724

ciki yake cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Ummi ta haihu".
Ita kuma Ummi wani irin zamewa tayi ta zauna bisa kujerar kana tasa hannun tana shafa kan Shatu tare da cewa.
"Allahu Akbar duniya Allah mai iko".

Shi kuwa Sheykh cikin rawan jiki ya fito da yarinyar, zama yayi dirsham a gaban Shatu, tan kwashe sawunshi yayi ya buɗa gariyar jikinsa da kyau, yasa yarinyar da ita kuma taketa cillara kuka.
"Yaray, yaray, inyararray inyararray".
Wani irin Murmushin mai cike da zubda hawaye itama Shatun tayi tare da kallon Sheykh ɗin yadda yasa yarinyar cikin jikinshi, murya na rawa tace.
"Malam Dactor Hamma Yan Sheykh me Allah ya bamu?".
Wani irin matsowa gareta yayi jin yadda ta jero mishi sunayen dake da cikekkiyar ma'ana a gareta gareshi, jawota jikinshi yayi ya ruggumeta gam-gam cikin tsananin jin daɗi yace.
"Aysha Aish Mar'atussaliha my dear sweetheart my everything ɗiya mace Allah ya azurtamu da ita yau jumma'a ɗaya ga watan ɗaya da ƙarfe shida na yamma dai-dai".
Cikin sanyi tace.
"Alhamdulillah Yah Sheykh Allah ya raya mana ita bisa imani ya al'barkaci rayuwar ta, yasa ta kasance mana Jabbo a ahlinmu Allah yasa ta marabci su Yah Giɗi".
Da sauri yace.
"Amin Amin Ameeeeeeen ya rabbil izzati Allah yasa tare da Mamey na, ya Kuma amsa addu'ar da kikayi mata a matsayin mahaifiyarta".

Amin Amin tace tana kallon fuskarshi data yarinyar, cikin sanyi ta koma ta jingina da kujera a hankali tace.
"Alhamdulillah Yah Sheykh da Junainah take kama".
Tayi mgnar tana mai sakin kuka mai cike da raunin ganin an sake hasko fuskokin su Giɗi.
Da sauri ya ɗan ɗago yarinyar ya manna mata ita kan cikinta, kana cikin rauni yace.
"In sha Allah hawayenki zasu dena zuba, Aish da izinin ubangiji zan zame miki GARKUWA keda ƴan uwanki, naji daɗin da ɗiyarmu tai kama da tsatsonki jininki koda ban san Junainah a fuskaba ina zaton dake take kama".
Ina zuwa yanzu bazata iya mgna ba, sabida kukan da take son dannewa.

Shi kuwa Sheykh cikin murmushin hawaye yace.
"Ummi a kawo mana kayan amsar haihuwar masarautar Joɗa zan yanke mabiyar dan ta faɗo".
Cikin tsananin sauri Ummi ta miƙe, kai tsaye wonje tayi.
Shi kuwa Sheykh ronƙo fowa yayi kanta a hankali yasa tafin hannunshi ya share mata hawayenta, kana ya manna mata kiss kan goshinta cikin jin daɗi yace.
"Alhamdulillah Noor Hayat komai naki mai tsabta kalli haihuwarki ma mai tsabta babu jini ko ɗigo, tsabtar zuciyarki ta wadaci komai, ga Babynmu tas da ita ba datti".
A hankali ta buɗe idonta, sosai take jin abubuwa biyu a zuciyarta a lokaci ɗaya tsananin farin ciki da kuma tsananin baƙin ciki da tashin hankali, sai dai farin cikin yana gab da danne baƙin cikin.
Hannunshi yasa ya ɗan ja ƙafarta, ya jawota kusa dashi ta matsa daga jikin mabiyar, cikin sanyi yace.
"Bari a kawo abun karɓar haihuwar masarautar Joɗa, in na yanke cibiyar sai muje Bathroom dan masu irin haihuwarki haihuwar kulle inji hausawa, sukan haihu babu jini, amman bayan kamar mintuna talatin zuwa arba'in jinin zai taho sai dai bai musu zuba da yawa yakanyi dai-dai misali ne".
Cikin nitsuwa tace.
"To Doctor Hamma Sheykh Jabeer".


Ummi kuwa tana fita kai tsaye Part ɗin Lamiɗo ta nufa.
A can babban falon su ta zube gaban Lamiɗo da Galadima da Abba da Gimbiya Aminatu dake dama musu fura.
Cikin kula Lamiɗo yace.
"Bisa alamu dai yau da babban Al'bishir kike tafe".
Cikin zaƙuwa tace.
"Allah rene, Allah hokke sabbugo, Alhamdulillah Aysha matar Muhammad Jabeer ta haihu yanzun nan".
Wani irin miƙewa tsaye Gimbiya Aminatu tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah."
Shima Lamiɗon da Galadima, kusan a tare suka cewa.
"Alhamdulillah masha Allah. Me muka samu?".
Da sauri tace.
"Ɗiya mace".
Murmushi sosai Lamiɗo yayi tare da cewa.
"Allah ya raya mana ita bisa imani ya bawa mahaifiyarta lfyar shayarwa".
Amin Amin sukace.
Gimbiya Aminatu kuwa da sauri tace.
"Taso muje da kayan amsar haihuwa".
Da sauri Ummi tace to kana tabi bayanta, ɗakin ta suka shiga ta dauko wani babban ƙorya ta miƙawa Ummi kana suka juyo suka nufi gidan Shatun.

Murmushi mai yelwa Gimbiya Aminatu tayi ganin yadda Sheykh ke ruggume da matarsa da yartsu a tsakiyarsu wace taketa wawure-wawuren hannunta.
Kusa dasu ta zauna daɓas, kana tasa hannun ta amshi yarinyar tana cewa Shatu.
"Sannu Gimbiya Aysha surkar Gimbiya Aisha mai sunan Maman Lamiɗo, uwa kuma ga AYSHA masha Allah."
Shi dai Sheykh sai murmushi yakeyi
Ita kuwa Gimbiya Aminatu amsar yarinyar tayi,
Kana ta ɗan kamo zariyar cibiyar, ta saita da ƴar ƙaramar yatsarta ƴar ƙuri, wanda hakan yayi dai-dai da kan mahaɗan da alamun kamar ƙari a wurin wanda dai-dai kan ƙarin ta ƙasa tasa zaren ɗinki ta zagaye ta ɗaure cibiyar kana tasa reza ta yanke.
Miƙa Ummi yar tayi tare da cewa.
"Kin amshi haihuwar Babanta tsawon shekaru talatin da lokacin tun kina ƙaramar ki, yau kuma kin amshi haihuwarta, kiyiwa babanta jakadanci itama kiyi mata".
Da sauri Sheykh yace.
"A a kam shiyasa ban bari ƴar ta faɗo a hannuntaba, dan Ummi na ayntacciyace nima bazata min jakadanciba bare ɗiyata, jika ta samu wannan shine tukuicin forko da zanwa Ummi a masarautar Joɗa daga yau wannan sunan Jakadiya ya bar kanta".
Ruggume ƴar Ummi tayi tare da sakin wani irin murmushi mai haɗe da hawaye tana sa yar cikin mayafin nan tana cewa.
"Masha Allah, zuwanki ya iso mana da al'khairai".
Shi kuwa Sheykh cikin sanyi yace.
"Ummi ni wannan al'adarfa ba sonta nakeba, kada asa min ƴa a kwarya".
Da sauri Gimbiya Aminatu tace.
"Jakadiya fita harkar shi ɗauki ƴar ki kaiwa Lamiɗo gashi tafi da mabiyiyar kije ki benneta inda ake binne na ƴaƴan ɗakinsu".
Da sauri tace. To.
Shi kuwa Sheykh a hankali yace.
"Ummi a bari in mata wonka".
Bata kulashi ba ta fita.
Ganin haka ya miƙe ya kamo hannun Shatu.
Bedroom ɗinta Suka shiga, kai tsaye Bathroom Suka wuce, suna shiga ya ajiyeta kan toilet,
ai kuwa sai ga jinin yana zubowa.

Ita kuwa Gimbiya Aminatu tattare wurin tayi kana da sauri tabi bayansu.
Tana zuwa bakin ƙofar tace.
"Kai buɗe ƙofar ka fito".
Cikin nitsuwa yace.
"Wonka zatayi."
Tura ƙofar tayi ta shiga tare da cewa.
"Bani wuri".
Shiru yayi ya koma gefe,
ita kuwa Gimbiya Aminatu a nitse ta juyo ta kalli Shatu dake zaune.
"Yanzu taso kizo kiyi wonka".
Cikin sanyi tace.
"Toh a haɗa min ruwan zafi".
Da sauri Gimbiya Aminatu ta girgiza mata kai tare da cewa.
"A a ai mu al'adar masarautar Joɗa mace in ta haihu bata wonka da ruwan zafi bazataci abinci mai zafiba bazatasha abin sha mai zafiba.
Komai da abu mai sanyi zatayi amfani.
Jaririnma muddin na mijine to da ruwan sanyi za'ayi mishi wonka in macece muke ɗan tarfa na ɗumi kaɗan sabida bamu sai ita ina rabo zai kaitaba".
"Ikon Allah sai kallo waito wasu tsarabe-tsaraben sai yaushe za'a barsune a saki al'ada a kama gsky". Ya hafaɗa yana taimakawa Shatu ta shiga wurin wonkan.
Kana yayi gefe.

Ita kuwa Shatu kasan cewar ta gaji yasa bata ce komaiba.
Wonka tayi kana ta fito.
Suna fitowa Gimbiya Aminatu ta koma falo, shi kuwa a hankali ya jawo hannunta, bakin gado ya akiyeta, kana a hankali yace.
"Ɗan gyara inga ko baby ta ƙaraki".
A hankali ta ɗan kwaɓe fuska, kanshi ya jujjuya alamun kiyi haƙuri.
A hankali ta ɗan zame ta konta, towel ɗin ya ɗan ja, kana ya sunkuyo, da sauri yace.
"Akwai ƙarin amman ɗan ƙanƙanine ɗan kaɗan yanzu kici abinci mu tafi Valli muyi ɗinki".
Ya ƙare mgnar yana gyara mata towel ɗin.
Da sauri Ummi dake bakin ƙofar tace.
"A a ba'a buƙatar ɗinki zai haɗe da kanshi".
Shiru yayi yana kallon Ummi sai kuma ya miƙo hannunsa ya amshi Babyn.
Wacce anyi mata wonka an naɗeta cikin rawanin Lamiɗo.
Murmushi yayi, tare da matsowa gefe ya zauna a bakin gadon.

Ita kuwa Ummi taya Shatu kimtsawa tayi.
Kana tace.
"To zauna bari in kawo miki abinci".
Da sauri ta kwanta tare da lumshe ido kana tace.
"A a Ummi barshi wlh bacci nakeji sai nayi in na tashi zanci".
Jin haka yasa tace.
"Toh."

Har zata fita sai kuma ta tsaye jin yana cewa.
"Uhummm Ayyah Ummi a bani zam-zam da dabino mana".
Da sauri tace. "Toh".
Ba kowa a falon haka yasa taje ta ɗauko danino da zam-zam ta kawo mishi kana ta juya ta fita.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya ɗan malle marfin zam-zam ɗin yasa a bakinshi yasha da kyau.
Kana ya buɗe kwalin dabinon.
"Bismillah". Yace kana yasa dabinon a baki, ya tattaunashi da kyau.
Ya haɗe da damshin zam-zam da yawunshi ya tsastsafo da ruwan zaƙi da ɗan-ɗanon da binon.
A hankali ya sunkuyo ya kawo bakinshi kusa dana yarinyar,
ita kuwa Shatu ido kawai ta zuba musu.
Da sauri ta kalleshi jin an fara kiran sallan magriba.
Shi kuwa bakinshi ya manna kan na yarinyar ya rinƙa tura mata ruwan dabinon, ai kuwa sai gashi tana laluma tana haɗiyewa, murmushi yayi tare da juyowa ya kalli Shatu a hankali yace.
"Uhumm Bubbuga Rumbun Abboi ta haifo bubbuga Rumbun Sheykh dan ke ta gado da ciye-ciye".
Murmushi mai cike da jin daɗi tayi tare da cewa.
"Allah Junainah ce uwar kwaɗayi da kuma Jamil to ta gaji ƙanin ka da ƙanwata".
Murmushi ya kumayi yanaji a ransa yanzu dai sun gama zama abu ɗaya.
Haka yayi ta taunar dabino yana bata ruwan saida ya tauni tabino bakwai.

Amfanin fara bawo yaro dabino a matsayin abinci na forko da zai fara ci a duniya yana da yawa.
Ɗaya daga cikin wanda manyan likitocin duniya sunyi ittifaƙi a kai kuma sun gamsu dashi shine.
Sun gano duk wani abinci da na sha a duniya kab in ɗan adam yaci, sai sun fara zama a ciki uwar hanji ta bambance ta fidda mai kyau da mara kyau kana ya sarrafu ya zama jini kafin nan zuciya kuma ta harba ta rabashi ko wani sashi da saƙo na jikin ɗan adam.
Sai dabino ne abinci ɗaya da likitocin suka tabbatar da cewa.
Shi muddin ka cishi kai tsaye ƙoƙolwar ɗan adam yake wuce, ya wonketa ya in ƙantata.
So bada ruwan dabino ga jariri yana sa yaro ya tashi mai kaifin basira da ilimi da kwarin ƙoƙolwa.
Yayinda mutane kuwa ke cewa.
Yaro zaiji mgnar wanda ya shayar dashi ruwan dabinon da yawunsa fiye data kowa.
Wannan shine bayanin da Sheykh yakewa Shatu yana mai kontar mata da jaririyar kusa da ita.
Murmushi tayi tare da cewa.
"Masha Allah".
A hankali ya ɗan shafa kanta kana yace.
"Bari in tafi masallaci".
Ya ƙare mgnar yana fita.

Ita kuwa ido ta zuwaba ƴar tasu.
Shi kuwa tv ya kashe kana ya nufi falonshi.

Ummi kuwa tana kitchen zabbi take gasawa waya na saƙale a kunneta Umaymah taketa kira tun ɗazu amman bata ɗagawa.


Katse kiran tayi ta kira Juwairiyya tana ɗagawa tace.
"Juwairiyya Shatu fa ta haihu".
Cikin tsananin jin daɗi Juwairiyya dake bisa sallaya tace.
"Kai Ummi Alhamdulillah masha Allah me muka samu?".

"Ɗiya mace".

"Masha Allah bari inyi salla inzo".

Galadima kuwa yana komawa Side ɗinsa ya gayawa matarsa.

Ita kuwa Ummi Umaymah ta kuma kira, bugu ɗaya ta ɗaza da sauri tace.
"Assalamu alaikum al'bishirinki Umaymah".
Cikin dariya mai cike da zallar jin daɗi da farin ciki tace.
"Goro Ummin Jabeer amman Lamiɗo ya rigaki, yanzu yake gayawa Jaddanmu kinsan su Mamma da Aunty Rahma sun zo shekaran jiya, nima tun jiya ina Katsina.
To yanzufa Jadda ya shigo yake gaya mana kai Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!."
Cikin dariyar jin daɗi Ummi tace.
"Eh lallai Lamiɗo yamin shigar saurin".
Sitti ce ta amshi wayar tare da cewa.
"A a kada ki damu goron Al'bishir ɗinki na musamman ne".
Aunty Rahma dake gefene tace.
"Ummi yar da waye take kama".
Da sauri Ummi tace.
"Wlh da Ishma take kama".
Mamma ce ta amshi zancen da cewa.
"Allah sarki yadda take son Ishma haka Allah ya bata mai kama da ita".
Dariyar jin daɗi sukayi dukansu da yake wayar a amsakuwa take".
Daga nan Ummi ta ƙatse kiran ta nufi falon.
Ɗakin Shatu ta fara shiga murmushi tayi ganin Shatun na konce tanata kallon yarinyar tana mata tofi.
Fita tayi ganin bata gantaba.

Ana idar da sallan isha'i suna fitowa Sheykh yayi sauri yabi bayan Abbanshi.
Kana ya bar Jalal Jamil Yah Jafar, Yah Hashim Affan Laminu Sulaiman a bayanshi.
Da sauri yace.
"Assalamu alaikum, Abba".
Da sauri Abban ya juyo wanda Dr Aliyu da Baba Basiru Baba Kamal Baba Nasiru da sauran ƙannen Abban nasu suka tsaya da sauri jin yana cewa.
"Alhamdulillah Aysha ta sauƙa lfy".
Yayi mgnar a hankali ne cike da nitsuwa da zallan farin cikinsa daya kasa ɓoyuwa.
Cikin sauri Dr Aliyu ya juyo tare da cewa.
"A a masha Allah, Masha Allah".
Baba Kamal ma kalmar yake faɗi.
Baba Nasiru kuwa cikin wani irin masifeffen tashin hankali da tsana yace.
"Me aka haifa maka?".
Da sauri Baba Basiru yayi wani irin murmushi tare da cewa.
"Sa ranka a inuwa ƴan macece ba mai gadan mulki aka haifa mishi ba".
Karo na forko a lokaci na forko Abbansu yasa hannunshi ya jawoshi jikinshi ya ruggume shi, gam a jikinshi tare da cewa.
"Alhamdulillah Muhammad Allah ya raya mana ita bisa imani ya bawa mahaifiyarta lfyar shayarwa da bata kekyawar tarbiya, nayi farin ciki mai tarin yawan da jin wannan Magauta zasuyi rabkanuwar aiyukansu".

Ya ƙare mgnar tare da sakeshi.
Tabbas shi kam haihuwar nan tazo mishi da wasu abubuwa manya, wai yau shine har Abbansu ya ruggume shi.
Su kuwa gaba ɗaya tafiya sukayi.


Shima binsu a baya yayi.
Su Jalal kuwa da Yah Jafar da Jamil da Affan da sauri sukabi Yah Sheykh ɗin nasu a baya.
Sabida suna cike da mamakin yadda suka hango Abbansu ya ruggume shi.

Kusan a tare suka kutsa kai cikin falon.

Ummi dake riƙe da babban kular da tasa gasassun zabbin ne ta juyo da sauri, ta kalli Juwairiyya dake bayanta tana cewa.
"Iye gafa Daddyn Baby da Uncles ɗinta".
Da sauri Jamil ya shigo cikin falon yana cewa.
"Kai haba dai My Adda Shatu ne ta haihu?".
Yayi mgnar cikin zumuɗi suma sauran gaba ɗaya ido suka zuma mata jiran amsarta.
Shi kuwa Sheykh murmushi mai cike da yelwa yake, tare da zaro wayarshi a aljihu.

Ummi ce tayi dariyar jin daɗi tare da cewa.
"Wlh kuwa Alhamdulillah Shatu ta haifo mana Kekkyawar ɗiyar fulani fara ƙal".
Kusan a tare Jamil da Affan sukace.
"Yesssss masha Allah Alhamdulillah".
Jalal kuwa wani irin murmushi yayi mai baiyana farin cikinsa a hankali yace.
" A a kai Alhamdulillah Allah mun gode maka, Allah ka raya mana ita bisa imani".

Yah Jafar kuwa da sauri ya juyo ya kalli Sheykh ga mamakinsu babu zato babu tsammani sukaji yace.
"La'ilahaillaha Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam. Alhamdulillah Allah na gode maka, daka c nuna min wannan ranar Alhamdulillah ni Muhammad Jafar Allah na gode maka".
Wani irin juyowa da ƙarfi Sheykh da zai shige falonsa yayi cikin tsananin kaɗuwa da tarin al'ajabi da mamaki da rantsar kokonton shin muryar Yah Jafar ce kuwa da tsawon shekaru 13 baiyi mgnaba yake mgn?.
Jalal kuwa da sauri ya koma da baya ya faɗa kan kujera sabida rawan da jikinsa keyi.
Jamil da Affan da sauri suka matso kusa dashi.
Ummi kuwa da sauri ta saki kular dake hannunta.
Ita kuwa Juwairiyya cikin tsananin kaɗuwa da tsoro ta matso gabanshi bakinshi take kallo tamkar zata cire idonta ta mannasu jikin lips ɗinsa gaba ɗaya sun kasa mgn.

Shi kuwa Sheykh da sauri ya iso gabansa hannunshi ya kamo ya riko gam gam tare da cewa.
"Yah Jafar mai-maita abinda kace Yah Jafar sake mgn inji maimata".
Yayi mgnar da ƙarfi cike da kaɗuwa.
Ga mamkinsu sai ga Yah Jafar ɗin yayi shiru yana kallonsu Tamkar kurma.
Cikin wani irin tsuma da kaɗuwa duk suka zagayeshi.
Cikin tsananin farin ciki Sheykh ya ruggume shi gam-gam a jikinshi murya cike da al'hini da hamdala yake cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!. Yah Jafar kayi mgna ka sake yin mgn dan Allah kayi mgn".
Ya ƙarashe mgnar yana mai janye jikinshi daga jikin Yah Jafar ɗin tare dasa hannunsa bisa kafaɗunsa duka biyu yana jijjigawa.
Itama Juwairiyya cikin rauni murya na rawa cike da kukan hamdala tace.
"Yah ilahi ya mujibadda'awati ya Allah idan mafarki nakeyi ka tabbatar min dashi".
Cikin sauri Jalal dake zaune yace.
"Ba mafarki bane Aunty Juwairiyya".
Affan ne ya matsosu tare da haɗe su duka ya ruggume sai kawai ya saki kuka.
Ummi kuwa cikin shassheƙan kuka tace.
"Sheykh ku barshi mu bishi a hankali tabbas mgn yayi kuma in sha Allah zai kumayin mgn".
Jamil kuwa gaba ɗaya jikinshi kerma yakeyi wayarshi ya zaro Umaymah ya kira tana ɗagawa ya fashe da sassayan kuka tare da cewa.
"Umaymah! Umaymah!!".
Cikin tsananin ruɗani da kiɗima tace.
"Innalillahi Jamil mene! Jamil gaya min meyasa ka kuka".
Da ƙarfi yace.
"Umaymah kukan farin cikine.
Yau Yah Jafar yayi mgna kuma ya maimaita Umaymah farin cikine ya samu kuka".
Cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa Umaymah ta saki wayar tare da juyowa ta kalli Sitti da Jaddansu da sauran ƙannenta da babban yayansu baban Aunty Juwairiyya da Ibrahim kenan.
Cikin wani irin murmushi mai haɗe da hawaye tace.
"Sitti Jadda Jafar ya fara mgn".
Gaba ɗaya salati suka ɗauka a tare, suka direshi da kalmar.
"Alhamdulillah ala kulli halin, Alhamdulillah lallai tabbas dukkan tsanani yana tare da sauƙin."
Kawai sai kuma duk suka matso gaban Jaddansu da ya saki kuka kamar ƙaramin yaro cikin rawan murya yace.
"Ɗaya daga cikin burukana ya cika, kafin mutuwata ko yanzu na kwanta dama nasan bakin Jafar ya buɗu.
Sai dai har yanzu ina da wani babban buri Yah Allah ka bani aron rai da lfy ka ka baiya na min ƴata Aisha ka tsare min ita a duk inda take ka dawo da ita kan ƴaƴan ta al'farmar Annabi da al'ƙur'ani".
Cikin zubda hawaye suka amsa da Amin Amin gaba ɗayansu.


A nan masarautar Joɗa kuwa,
Cikin tsananin tarin farin ciki Sheykh ya kamo hannun Yah Jafar ya zaunar dashi bisa kujera kana da sauri ya juya ya nufi ɗakin Shatu.
Konce ya sameta da alamun bacci takeyi.
Hannunshi yasa ya ɗauki Jaririyar kana da sauri ya juyo ya fito.

Yana fitowa kuma dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima da Abbanshi suka shigo falon.
Cikin sauri ya matso gaban Yah Jafar miƙa mishi ƴar yayi ga mamakinsu sai sukaji yace.
"Bismillahi".
Cikin tsananin kaɗuwa da mamaki Lamiɗo Galadima da Abba suka zauna, Lamiɗo da Galadima da Yah Jafar bisa kan kujeru sauran kuma duk kowa na ƙasa harda Abbansu.
Kallon kallo sukayiwa juna lokacin da suka ga yana shafa kan yarinyar tare da buɗe baki a hankali yace.
"Masha Allah. Allah ya raya mana ke bisa imani yayi miki al'barka".
Zuwa yanzu Lamiɗo da Galadima cikin kaɗuwa suke cewa.
"Jafar".
Da sauri Sheykh ya juyo ya kalli Abbansu da tuni hawaye suke tsastsafo mishi ya kasa cewa komai sai tallabe haɓarsa yayi da hannu bibbiyu yana kallonshi.
A hankali Sheykh ya juyo kamar ƙaramin yaro haka ya iso da rarrafe.
Ya zauna gaban mahaifin nasu ya fuskanceshi da kyau hannunshi yasa ya kamo hannun Abban nasu ya zare mishi tagumin da yayi, kana yasa tafin hannunshi ɗaya ya share mishi hawayen da yakega suna zubo mishi cikin ƙarfin zuciya da tsananin farin ciki kan farin ciki murya cike da girmamawa yace.
"Abbanmu kace


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login