Showing 144001 words to 147000 words out of 352722 words
abokansu suka nufa.
Yana dawowa Falon Hibba kaɗai ya samu ta kunna tv tana kallon Film ɗin India kamar zai hanata kuma dai sai ya wuce.
Bayan tayi mishi sannu da dawowa.
Yana shiga ɗakin ya tura ƙofar ɗakin ya rufe ba tare dasa key ba.
Kana yasa hannunshi ya kashe fankar, tare da kashe wutan ɗakin.
A hankali ya iso bakin gadon. Zare Al'kyabbar ajikinshi yayi ya ajiyeshi bisa gadon.
Kana ya zare jallabiyar jikinshi itama ya ajeta kan gadon ya rage dagashi sai 3 qtr da ƙaramar rigar.
Dan sosai yake jin bacci, sanadin ɗan zafin hadarin dake haɗuwa yayi yawane yasa ya ƙara gudun AC kana.
A hankali yayi taku zuwa, gefen gadon agogon hannunshi ya cire ya ajiye a kan Bedside drower'n dake kusa dashi.
Konciya yayi a nan a ƙasa bisa tayis babu shimfiɗan komai bare pillow.
Wannan tsarinshi ne da yakeyi, wanda yanayin hakane dan tuna konciyar ƙabarin da wata rana zai riskeshi.
Wani lokacin ma, harda AC'n yake kashewa.
Yana konciya ya fara tasbihi yanayi a hankali idonshi na rufuwa, wannene yasa yakeyin bacci a lokacin da yaso.
A can cikin masarautar Joɗa kuwa.
Cikin wani irin farin ciki Jalal Jamil suka nufi Side ɗin Hajia Mama jin labarin Ya Affan ya dawo daren jiya karfe biyun dare, a bakin Imran
A falo suka samu Hajia Mama cikin tarin bege da kewar ɗan uwan nasu Jalal yace.
"Mama wai Yah Affan ya dawo?".
Cikin murmushin tace.
"Eh ya dawo".
Da sauri Jamil yace.
"Yesss Jalal zomu tafi tafi Side ɗinshi Aunty Mami an shawo turai an dawo".
Da sauri suka tsaya jin Mama na ce musu.
"Basa nan tunda safe Aunty Mamin naku ta matsa ya kaita gida wai Abban Yusuf ba lfy, to sun tafi can, Aryan ma yazo bai sameshi ba shima ya tafi can duk sun haɗe a can".
Da sauri Jalal yace.
"Muje mu ɗauko shi dan wlh su Hamma Yusuf da Ya Aryan bazasu barshi ya dawo da wuriba".
Cikin murmushin Jin yadda yaran ke son Juna tace.
"Yanzu kuwa zasu dawo, dan kunsansu duka uku da son daba, sun girmama su basu bar hawa doki da tsereba kuma kasan Yusuf zaice suzo wurin uban gidansa Malam Jabeer".
To da hakane suka ɗan gamsu suka nitsu.
A can Dou Gire kuwa samun jikin Abban Yusuf da sauƙine yasa.
Suka shirya suka nufo Masarautar Joɗa.
Ummi ma tayi kolliyar sallanta tayi kyau ta fito falon, inda Hibba take.
Shatu kuwa tana ɗakinta lokacin ta gama yin kolliya tasa wani damdatsen Shadda lace mai masifar kyau, Royal blue ne mai kyau da ɗaukar hankali sai zaren lace-lace ɗin da akayi da red and pink guava mai masifar kyau, sai wani irin sheƙin shaddar takeyi tana fidda maiƙon kyau.
Doguwar rigace inrin fitet ɗin nan na zamani mai ɗan karen kai duk inda sirin yanken fisis ɗin yake an bishi da jerin duwasun shuwa riski masu sheƙin Daimond, cib-cib rigar tayi a jikinta.
Murza ɗauri ɗan kwali tayi irin mai stpes ɗin nan
Kana ta tura ɗan kwalin kaɗan wannan tattausan saje da suman dake konce a goshinta ya fito ras.
Sai ta baya kuma ta tsakiyar ɗan kwalin ta bar rami ta fito da jelan gashinta ya konto har kafaɗanta ba tare da ta kitseshi ba.
Wasu ƴan kunne da sarka na azurfa ta saka a wuyanta,
sai wani kekyawan agogon fata rea ƙirar Gucci ta manna a tsintsiyar farin hannunta da yake, ɗanɗase da zanen jan lalle mai kyau.
Gyale rea color mai masifar kyau ta ɗan yafa a kafaɗunta.
Wasu turaruka kala biyu ta fesa, kana ta kalli muskarta da jikinta a madubin.
Wayarta ta ɗauka ta ɗan kaikaice ta ɗauki kanta hoto ta cikin madubin tayi kyau sosai.
Wasu takalma marasa tudu tasa suma rea color ne.
Tana riƙe da wayarta ta fito falon.
Da sauri Hibba ta miƙe tare da cewa.
"Wow! Wow!! Wow!!! masha Allah Aunty Shatu kin ganki kuwa masha Allah."
Murmushi Aunty Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Kai gsky amaryar Sheykh ta fito da madarar kyau masha ALLAH".
Ita dai sai murmushi takeyi dace musu.
"Ngd".
Cikin jin kunya.
Hibba kuwa duk takun da motsin da zatayi sai ta ɗauke ta hoto.
Daga ƙarshe ta rinƙa yi musu selfi su duka huɗu.
Saida suka gajine kana suka zauna suna hira.
Nan suka kira Umaymah suka sha hira.
Suna cikin hira Ummi ta juyo da sauri jin muryar Affan yana sallama tare da cewa.
"Assalamu alaikum. Ina Umminmu ina amaryar Hamma tuzuru".
Miƙewa da sauri Ummi da Aunty Juwairiyya sukayi tare da cewa.
"La Affan yaushe ka dawo".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Jiya da tsakiyar dare, ina Auntyn nawa".
Ya ƙarishe mgnar yana shigowa cikin tsakiyar falon.
Tafa hannu Ummi tayi tare da cewa.
"Suwa nake gani kamar Yusuf da Aryan".
Cikin dariya sukace.
"Muɗin ne dai Ummi".
Cike da jin daɗi Ummi da Aunty Juwairiyya ke cewa.
"Kai maraba lale lallai yau munada manyan baƙi , oh duniya Yusuf da Aryan kamar ba kuba".
Dariya sukayi tare da zama a kujeru.
Hibba kuwa tuni ta isa gaban Affan lakace hancinta yayi tare da cewa.
"Sakaliyar Umaymah ashe kina nan bana zakiga shagalin sallan Masarautar Joɗa".
Cikin sauri ya kalli Shatu dake ce musu.
"Sannunku da zuwa".
Da sauri ya juyo ya kalli Ummi kana ya kalli Aunty Juwairiyya tare da cewa.
"Wannan ce Auntyn nawa amaryar Sheykh Ustaz Malam Dr Jabeer akarmakallu".
Murmushi Ummi tai tare da cewa.
"Eh itace".
Cikin dariya ya kalli Yusuf da Aryan da suke gaisawa da ita yace.
"Kan bala'i ashe dama Sheykh Hamma Jabeer yana kallon mata kalli yadda ya zaƙulo zankaɗediyar sarauniya".
Yusuf ne ya daki kafaɗarshi tare da cewa.
"Kaifa Affan ɗan iskane baka da mutunci, baiyi aureba kace mishi. Shugaban tuzuran Afirka.
Yanzu yayi auren kuma zakace yana kallon to dama ce maka akayi shi makaho ne?".
Dariya sukayi baki ɗayansu,
Aryan ne yace.
"Bar Affan da shegiyar surutu".
Dariya suka kumayi kana duk suka zauna.
Suka gaisa cikin tsokana Affan ya kalli Shatu dake danna wayarta tana kallon hotunan da sukayi yanzu yace.
"Aunty Amarya Hamman namu yana nan ne, ayi mana iso wurin shi mu kwashi gaisuwa".
Shiru ta ɗanyi tare da kallon Ummi.
Da sauri Hibba tace.
"Eh yana nan yanzu ya shiga".
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
"To Aunty Sayyada ayi mana sallama dashi ace ɗaliban shi ne, Affan, Yusuf, Arya,".
Cikin tsoron kada Shatu ta kuma zuwa ɗakin abun da ya faru jiya ya sake faruwa Ummi tace.
"Ai yana bacci ne yanzu ko".
Da sauri Affan yace.
"No ba matsala in ance masa Yusuf ne, tashi kice muna sallama dashi."
Cikin murmushin jin Yusuf da Aryan sunce.
"Eh gsky gwara mu gaidashi kada ya gammu a wurin sukuwa yace bamu nemi izininshi ba".
A hankali tace.
"To bari a gaya mishi".
Ta yunƙura zata tashine Ummi ta riƙe hannunta tare da cewa.
"Shatu kadafa".
A hankali tacewa Ummi.
"Ba komai fa Ummi".
Ganin hakane yasa Ummi ta sake mata hannun tare da cewa.
"To Allah yasa".
Amin Amin Juwairiyya da Hibba sukace.
Shi kuwa Affan cewa yayi.
"Allah bazaiyi faɗaba in yaji mune".
Kai Ummi ta gyaɗa sabida basu san me take tsoron ba.
Ita kuwa Shatu a hankali ta nufi Side ɗinsa.
Su kuwa hirarnsu sukaci gaba dayi a falon.
A hankali ta tura ƙofar falon nashi ta shiga.
Shiru babu kowa babu komai sai sautin ac dake tashi fuuuhhh.
A hankali ta lumshe idonta kana cikin sanyi ta nufi ƙofar ɗakin nashi.
Tare da cewa.
"Salamu alaikum! Salamu alaikum!! Salamu alaikum!!!".
Shiru babu motsin komai, hakane yasa a hankali tasa hannun hagun ta dafa ƙirjinta dake bugawa.
Kana tasa hannun damanta ta tura ƙofar Bedroom ɗin.
Sai kuma gashi ta buɗu ƙofar.
Wani sassanyan ajiyan zuciya ta sauƙe jin wani irin masifeffen ƙamshi da sanyi daya ratsa mata jiki da zuciya.
Sallama ta kumayi shiru ba amsa.
A hankali ta cusa kanta cikin ɗakinta da yake duhu.
Wani irin bugawa ƙirjinta keyi kana.
Kanta na sarawa da masifan ƙarfi.
A hankali ta juya gefen mashigar ɗakin hannun tasa ta lalubi abin kuna wutan ɗakin danna ɗaya daga ciki tayi,
hakan yasa ƙoyin wutan ɗaya mai kalar Sky blue ya kawo wuta.
Sanadin hakane ɗakin ya kawo wani irin haske mai ƙayatarwa.
Yanayin wutan ɗakin labulayen da kayan jikinta dana jikinshi sukazo iri ɗaya.
Juye- juye tayi tare da cewa.
"To ina yak".
Shiru tayi bata ƙarisa rogowar mgnar ba hangoshi can ƙasa yana konce rigingine yayi pillow'n da tafukan hannunshin.
A hankali tayi taku uku zuwa biyar ta matso kusa dashi cikin sanyin da ya fara yimata yawa ga cikinta dake tsuma a hankali tace.
"Salamu alaikum".
Ko motsi baiyiba bare tayi zaton zai amsa.
Sallama ta kumayi shiru ba amsa.
Ganin hakane ta matso a hankali take takun saɗab-saɗab take taka sawunta a hankali har ta isa kusa dashi.
Da sauri ta zubawa ƙafar damanshi ido.
Ajiyan zuciya tayi mai sanyi tare da mgnar zuciya.
"Uhumm ashe dama yana komciya a ƙasa haka babu shimfiɗan komai ba pillow, da kuma ƙaramar riga da wondo iya guiwa."
A hankali ta iso gab da kanshi,
Cikin yin numfashi a hankali wai karya jita, ta rusuna ta zauna bisa sawunta irin zaman yin tahiyan salla.
Cikin ƙurawa babbar yatsar ƙafar damanshi inda ta rinƙa biyo wannan zanen macijin dake kwance lib a ƙafarshi.
Da ido tabi zanen har kan guiwarshi inda iya nan wondon 3 qtr ya rufe.
A hankali ta ƙara sunkuyowa ta kurawa wurin ido, tare da mgnar zuciya.
"To iya ina wannan zanen tafiyar macijin ya tsaya ne a jikinshi?".
Jim kaɗan tayi kana a hankali.
Ta miƙa hannunta, cikin sanɗa a hankali hankali tasa yatsunta biyu ta kamo bakin ƙafan wonɗon ta ɗan jawoshi a hankali tayi sama das...!
Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 in Kuma special Group kikeso wanda a mako biyu ake gaba part 1 kuma abiyu za'a gama Part two da izinin Ubangiji yimin TRANSFER ɗin 1k ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. sai ki turo screenshot shaidar biyanki ta wannan number 09097853276.
By
*GARKUWAR FULANI*
Cikin sassarfa bisa tsarin addinin yaci gaba da ɗawafin.
Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu.
Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi.
Zuciyarshi nike da mamaki.
Haka yaci gaba da ɗawafin.
Saida sukayi. Kana suka fito.
A hanyarsu ta komawa gidane ya haɗu dasu Jannart da Jazrah da Umaymah da Sitti da kuma Aunty Hafsat ƙanwar Umaymah dake ƙasar Masco.
nan Aunty Hafsat tayi ta sayan kayan tsaraba tana bawa Sheykh wai a kaiwa surkarta.
Dan dole ya amsa sai kuma Aunty Rahma ƴar autar Sitti itama a gaban Aunty Hafsat ta girma.
Kuma sa'ar Sheykh Jabeer ce shiyasa akwai yar tsama a tsakaninsu.
Cikin hausarsu data fara basu wuya tace.
"Ba dai kayi auren sirri ba, in sha Allah zanzo zamuzo auren Haroon zamuga amaryar, inga surkar tawa ya take"
Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Ke tafi daga nan da Allah ki bar manya suyi mgna ba irinki ba".
Murmushi Umaymah da Aunty Hafsat sukayi dan sun san tsamarsu.
Kuma suna masifar shiri.
Ammi suke kiranta ita Aunty Rahman.
Jazrah kuwa hakanan take jin daɗi in ta ganshi.
Shiyasa taketa murmushi.
Haroon kuwa girarshi ya ɗagawa Jannart tare da cewa.
"Wai auren ya kusa ko?".
Cikin jin kunyar Umaymah tace.
"Ban saniba."
Haka dai sukaci gaba da tafiya.
Washe gari da safiya.
Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.
Manya da yara tsoffi maza da mata duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya a ko wani saƙon da suke da musulmai.
Hakace ta kasance a ƙasashen Afrika ma.
Wanda ciki ƙasar Nigeria yake.
Tun daga idar da sallan asuba.
Saratu da Larai sukazo.
Nan suka samu Ummi da Shatu suna kitchen.
Its Ummi fura take kirɓawa mai ɗan karen laushi da ƙamshi yaji sugar.
Ita kuwa Shatu dakkeren Couscous tayi, dambu inji hausawa.
Bayan sun gamane suka killace shi gefe.
Kana ita Shatu. Ta haɗa kajin nan tayi Pepper Checken mai ɗan karen kyau yaji jajjagen taruhu da al'basa mai yawa ga kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi sunji komai yayi maɗau.
Su Sara kuwa robobi ta miƙo musu, suka rinƙa mulmula gumbar nan manya manyan mulmulellen masu kyau sai sheƙi da ƙamshi gumbar keyi, dakkeren kuma a robobi Ummi ta rinƙa zubasu.
Hibba ce data shigo tare da kuloli a hannunta tace.
"Wow Aunty Shatu lallai yau masarautar Joɗa zata amsa sunanta masarautar Fulɓe zata kuma gane an auro mata cikekkiyar ba fulata, gsky tsarin yayi kyau".
Cikin jin daɗi Ummi tace.
"Gsky nima naji daɗin wannan abu.
Dama ace ko wanne yare ranar salla tayi abincin da yarenta keyi ta rabawa maƙota.
Hakan zaisa asan cimar juna, kuma yasa aci abincin salla da marmari, amman kayan haushi duk sai a tafi kan shinkafa taliya masa, da dai ire-iresu.
Su kuma akeci kullum".
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
"Ha Ummi ai yanzuma sai nayiwa su Jalal koda dafadukan taliyace, nasan zasuce wannan ai sai mu".
Da sauri Hibba tace.
"Tab wlh Aunty Shatu karkiyi komai, kinga yanzuma an kawo abincin gidan Barrister Kamal.
Ga kuma na gidan Aunty Juwairiyya.
Sannan kuma Gimbiya Aminatu ma zata aiko".
Cikin sauri tace.
"Allah ko Ummi mu huta kawai kenan?".
Da sauri tace sosaima.
Dan duk yawanci sai an kawo abinci nan wai tunda ke baƙuwace, wannan karamawar masarautar Joɗa akan bago.
Kuma koda kin dade ana aikawa juna abincin salla part 2 part".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Shike nan mu haɗa wannan a kai ko wanne sashin".
Ta ƙarishe mgnar tana rufe ƙatuwar Foodflaks ɗin da ta juye Pepper Checken ɗin.
Bayan ta ɗebawa sashin Ya Jafar da kuma Lamiɗo da Hajia Mama.
Ƙananan robobin da a ƙalla suma nonon dake cikinsu zai kai kwanon sha ɗaya da rabi ta fara firfitarwa.
Kana ta fito da madaidatan ƙoren da zasuci kwanon sha biyu da kaɗan sai manyan da sukaci kwanon sha uku da rabi-rabi.
A hankali ta jerasu kan table ɗin dake tsakiyar kitchen ɗin.
A hankali ta buɗe ƙwaryar forko dake gabanta.
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kunɗirmo ya konta yayi bacci yayi kyau".
Leƙowa Ummi tayi tare da buɗe na kusa da ita.
Nonon yana konce yayi lib ya daskare yayi fari ƙal-ƙal sai alamun maiƙon man nonon da yayi ɗan yellow-yellow kaɗan.
A hankali suka fara bubbuɗe fefeyayen tsakan zaren taburma da aka rufe ƙoren dashi.
Gaba ɗaya duk sun konta sunyi kyai
Yan madaidai robibin da akasa take ɗauka na fura ɗaya na dakkere ɗaya sai na sugar ɗaya kana da ludayin duma. Sai ta jerasu kan fefeyayen da robobin.
Ganin haka yasa Saratu da Laraima suka matso suna taya.
Har saida ta jerasu kab. Gwanin sha'awa.
Manyan ƙore biyu ta maida cikin Fridge.
Kana ta irga sauran tsakanin manya da ƙananan
Ƙoren da robobin su
Talatin da tara
Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
"To Ummi gashi mun gama ki gaya musu duk inda zasu kai.
Zasu isar ko".
Cikin jin daɗi Ummi tace sosaima kuwa harma da sashin bayi zai isa sabida part-part talatin garemu a cikin masarautar Joɗa.
Sai sashin bayi part takwas.
Cikin jin gamsuwa da tsarin Shatu tace.
"Yanzu a kai ƙore biyu sashin Lamiɗo kana duk manyan iyayen Sheykh akai musu kwarya ɗaɗɗaya, sai sashin Ya Jafar kinga manyan ƙoren sun ƙare sai abin na tsakiyan a kai sauran sashin ƴaƴansu robobin kuma akai sashin bayi".
Haka kuwa akayi su Sara suka fara rabawa.
Ita kuwa Ummi ita da kanta da Hibba suka kai na sashin Gimbiya Aminatu.
Kana suka dawo da kuloli har uku na abincin sallan da Gimbiya Aminatu ta basu.
Kana ɗaya daga cikin tace na Sheykh ne a ajiye mishi.
Koda suka dawo samu sukayi su Saratu sun gama rabawa kab.
Kamar yadda Ummi ta tsara.
Har sun tattare ko ina sun gyara sun share sun goge sun tafi.
Zuwa lokacin kuwa gaba ɗaya kan dinning table ɗinsu cike yake da Foodflaks iri da kala abinci kala-kala.
Wani irin kallo Shatu tayiwa kulolin kana tayi murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarsa ta juya ta nufi tsakiyar falon.
A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi.
Ƙarfe tara saura kwata duk suka fito falo.
Tuni lokacin kuma liman har ya fara huɗuba.
Su Jalal, Jamil Ya Jafar suna tsaye cikin shiga ta al'farma.
Karon forko dataga manyan kaya a jikin Jalal.
Sai kamanninshi da Hamma Jabeer ɗin nasu ya fito sak-sak kamar an tsaga kara hatta rashin yawan dariyarsu iri ɗaya ne.
Sai dai shi Sheykh ko yaushe zakaga lips ɗinshi na motsawa yana tasbihi saɓanin Jalal da zaka ganshi baki a tsuke.
Hibba ce ta fito cikin tarin farin ciki da son Jalal yayi murmushi tare da cewa.
"Masha Allah ya Jalal kayi kyau kafisu duka".
Ya Jafar dake karatu kamar ko yaushene ya kalli Shatu da Hibba da sukayi shigar atampa iri ɗaya da manyan hijabai har ƙasa ga sallaya da carbi a hannunsu sunyi matuƙar kyau, murmushi yayi musu kana ya juya yayi gaba.
Jamil ne yace.
"Aunty Shatu sai mun dawo, in munci abinci sai mu sharewa.
Oga, Dr, Garkuwa, Malam, akarmakallahu, Sheykh, mijin Sayyada, ɗin ɗakinshi".
Dariya sukayi dukansu yadda ya jero masa sunayen nashi.
Ummi dake cikin shiga ta al'farma ta miƙa tare da cewa mu tafi.
Suna fita suka rufe ƙofar.
Suka tafi masallacin. Masarautar Joɗa ɗan yin sallan idi.
Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi gefen maza.
Bayan an idar da sallane kuma sai suka zagaya suka shigo ta asalin ƙofar sukayi yadda sunna ta koyar.
Suna dawowa kuwa a falo suka zube nan sukaci suka sha sukayi
haniƙan.
A dai-dai lokacin kuma su Sheykh dama sauran al'ummar Annabi duk an sauƙo sallan idi.
Suna ɗawafin ban kwana.
Sosai Sheykh ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin amman ina hakan bai samuba.
Koda suka fito daga ɗawafin ban kwana.
Kai tsaye gidan Sheykh Abdulkareem suka wuce.
Nan yayi musu addu'o'in komawa lfy.
Kusan duk baƙin gidan a ranar suka bar gidan.
Da su Aunty Hafsat ma ranar suka juya Masco hakama Ibrahim.
Koda suka iso Airport kowa da inda ya nufa.
A nan Ibrahim ya ruggume Sheykh tare da ɗan dukan bayanshi yace.
"In Sha Allah Auren Haroon dani za'ayi".
Shima Sheykh ruggumeshi yayi gam-gam tare da cewa.
"Allah yasa, ina kewar rashinka a ƙasar mu".
Aunty Rahma ne tace.
"Kai jirgifa ba jiranku zaiba oga Sheykh".
Sakin juna sukayi kana kowa ya nufi inda jirgin ƙasarsa yake.
Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ƙasar Nigeria wanda zai sauƙa jihar Ɓadamaya.
A hankali ya zauna.
Ya Hashim na gefenshi.
Kasan cewar yana kusa da window ne, ya ɗan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda jiragan ƙasar su jihohinsu suke.
Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya gani.
Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ƙasar Cameroon suke.
Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ƙugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar da fuskar dattijon da yake hangowa.
A haka dai suka ɓacewa ganinshi.
Kana jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasarmu ta haihuwa.
Ana gida Nigeria kuwa cikin Jihar Ɓadamaya a Masarautar Joɗa.
Zaune suke a falon.
Shatu na waya da Junaidu nan yake ce mata,
Sun samu sauƙi dukansu.
Ance za'a sallamesu bayan salla.
Kuma harda ɗinkunan kayan salla akayi musu.
Bayan