Showing 210001 words to 213000 words out of 352722 words
ta ko yana raye ko ya amsa kiran Ubangiji.
Shi kuwa Sheykh lokaci ɗaya yanayin fuskarshi ta sauya cikin muryar dake nuna dafin zafi da tiririn da ke cikin zuciyarsa yace.
"Uhummm Jadda taimakon Ubangiji na mahaliccina masanin zahiri da baɗini kawai nake nema, shi zai haskamin hanya in riski haskena.
Zanyi ta roƙonshi kuma da fatan ya baku aron rai da lfy har sanda burinmu zai cika.
Ina addu'o'in Allah ya bawa magautanmu lfy da rai har zuwa lokacin da gsky zatayi halinta".
Tuni Safiyyah da Sitti sun fara sakin Shessheƙan kuka.
Wanda sam Aysha ta gaza gane dalilinsa kalaman Jadda da Sheykh kuwa sunyi mata ɗaurin talala a ƙoƙolwarta, ta gaza gane bakin zaren haka yasa ta tattare yawun bakinta cikin kukan da taji yana son kubce mata tace.
"In sha Allah Jadda zan kula da amanarka iyakar iyawata.
Zan kuma tayashi da addu'a koda bana yankin da yake.
Tabbas watan-wata-rana gsky zatayi halinta".
Sai ta kuma kalli Sitti da Safiyyah tare da cewa.
"Sitti kiyi haƙuri du ban san zafin me kikeji a zuciyarki ba, amman kukanki yamin kama da kukan uwar data rasa ɗanta, kiyi haƙuri".
Da sauri Sheykh ya miƙe ya fita, hakama Ibrahim.
Safiyyah kuwa hawayenta ta share kana ta kamo hannun Aysha tace.
"Jadda mu zamu tafi kada dare yayi mana".
A hankali Yace.
"Bazaku tsaya kuyi sallan la'asar ba".
Sitti ce tace.
"Sai dai suyi a hanya naga yadda Sheykh ya fita bazai dawo cikiba".
Kai ya jinjina kana yace.
"To Allah ya kaiku lfy ya tsare hanya.
Aysha Allah yayiwa aurenku al'barka".
Kusan a tare sukace Amin.
Kana suka miƙe suka fita.
Shi kuwa Jadda ya kira Sarkin dogarai ya bashi umarnin a haɗa motar dogarai hudu suyiwa jikokinsa rakiya.
Biyu a gaba biyu a baya tasu Sheykh a tsakiya.
Wacce Sheykh da Aysha suna baya.
Ibrahim da Safiyyah suna gaba, Ibrahim ke jan motar.
A haka suka bar masarautar Jalaluddin suka nufi jihar Tsinako.
Tafiyar mai yar tazara ce.
Shiru cikin motar Ba maiyin mgn, Sai sautin Radio da suka kunna.
Jingine yake da kujerar yayi shiru, idonshi a lumshe sai lips ɗin shi da yake motsawa alamun yana tasbihi kamar ko yaushe.
Ita kuwa Aysha sosai ta faɗa duniyar nazari.
Ibrahim kuwa ya maida hankali kan tuƙin.
Safiyyah kuwa bacci nema ya saceta a motar.
A ƙalla tafiyar awa ɗaya sukayi, kana suka fita jiharsu Jadda suka fara tafiya cikin dajin jiharsu Haroon.
A hankali ya buɗe idonshi.
Jin Ibrahim na cewa.
"Tab lallai Abban Haroon da Sarki Ahmadu suna ji da wannan walimar da za'ayi.
Kajifa duk gidajen rediyon Tsinako, gaiyatar walimar akeyi ba ƙaƙƙautawa kaji ko zasu sakeyi."
Meda kunnuwansu sukayi kan abinda ake faɗin.
"A madadin iyalan mai girma sarki Ahmadu suna farin cikin gaiyatar walimar auren. jikokinkin mai Martaba Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Joɗo da matarsa Aysha Aliyu Garkuwa.
Da kuma Haroon Abubakar Ahmadu. Da amaryarsa.
Jannart Umar Jalaluddin
Za'ayi walimar ne a wurin babban filin taron al'ummar musulmi na Tsinako, ana gaiyatar ɗaukacin al'ummar musulmai wurin walimar wanda za'ayi yau misalin ƙarfe takwas na dare zuwa goma da izinin ubangiji, in da sanan malamin nan Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda shima angone kuma shi zaiyi nasiha ga mauratan.
Saƙon gayyata daga Mai martaba Sarkin Ahmadu. Allah ya bada ikon zuwa Amin...".
Gajeren tsaki Sheykh ya ɗan ja tare da cewa.
"Kai tsoffin nan fa sunada matsala, ji wani dogon sharhi iya sunayemmu ya ishi a gunduri mai sauraro".
Murmushi Ibrahim yayi tare da cewa.
"Kuma wlh tallatar tayi armashi."
"Sosai ma kuwa". Safiyyah tace, cikin jin daɗi.
A gogon hannunshi ya kalla kana yace.
"Tsaya nan garin muyi salla la'asar tana gab da wucewa".
To Ibrahim yace, kana sukaci ga da tafiya.
Tafiya kaɗan sukayi suka isa.
Wani masallaci mai kyau wanda dama dan matafiya akayishi.
Gefen mata da ban gefen maza da ban.
Bayan duk sunyi parking ne fadawan, suka fara fitowa.
Da sauri sukazo suka buɗe musu mota.
Ibrahim ne ya fara fita kana Safiyyah.
Juyowa yayi ya ɗan kalleta ganin ta gyara zamanta ta kishin giɗa tare da lumshe idanunta.
fuska ya ɗan yamutsa kana yace.
"Fitowa zakiyi muje muyi salla. Ba gyara zama zakiyi ba."
Shiru batayi mgna ba, haka yasashi haɗe fuska ya kuma maimaita mgnar.
Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
"Ni nayi".
Idonshi ya zubawa fuskarta na daƙiƙu biyar.
Uhummm yace kana ya sa ƙafarshi ya fita.
Bayan sunyi sallan ne kana suka dawo sukaci gaba da tafiya.
Ƙarfe biyar dai-dai suna cikin masarautarsu Haroon.
Suna shiga fadawan suka wuce masauƙinsu dan sai gobe zasu koma.
Su kuwa Sheykh da Ibrahim Side ɗin Abban Haroon Suka nufa sabida kiransu da yayi a woya.
Aysha da Safiyyah kuwa Side ɗin Umaymah suka wuce.
Suna Shiga Hibba tace.
"O oyoyo My Aunty's Umaymah gasu Aunty Aysha sun iso".
Da sauri Umaymah da Aunty Hafsat da Rahma suka fito.
Cikin kula Umaymah tace.
"Allah sarki Ɗiyata sukayi muku wayo suka dawo a jirgi ku suka barku da gajiyar mota ko".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai tace.
"Ina wuni Umaymah Aunty Hafsat barka da yamma".
Murmushi sukayi suka amsa cike da kulawa.
Aunty Rahma ce tace.
"Yaseen kuwa Umaymah ba wayo mukayi musuba Ibrahim ne yace mu barsu zasu dawo tare tun randa mukaje hutasa bayi shirin dawowa dasu a jirgiba".
Ta ƙare mgnar tana kallon Aunty Juwairiyya da Jazrah da suka shigo yanzu.
"A Safiyyah sai yanzu kuka iso".
Jazrah ta faɗa tana ƙin kallon inda Aysha take.
"Eh ba kun musu wayo ba".
Aunty Hafsat ta faɗa.
Murmushi suka ɗan yi.
Cikin kula Umaymah tace.
"To Safiyyah yanzu dai kuje ku ɗan huta, kafin ku fara shirin zuwa walimar."
To tace kana suka nufi ɗakin Hibba dan yau Side ɗin Umaymah cike yake maƙil da taron al'ummar Annabi.
Suna shiga Aysha ta wuce Bathroom da hand bang nata a hannunta.
Meda ƙofar tayi ta rufe tare da sauƙe ajiyan zuciya.
Dan tana son kimtsa jikinta sabida larurarmu ta mata da take tare da ita.
Allah yasa ma ita in tana fashin salla bata yawan fitsari.
A wuni bazai fi sau biyu zata zagaba, dan fitsari sai dan ko kimtsa jikinta, shima kuma baya mata wawan zuba, a bisa tsari yake zubo mata sai dai tana yawan bacci in bata salla.
Wonka tayi kana ta kimtsa jikinta da kyau, kana ta fito ba kowa a ɗakin sai ɗan Safiyyah dake bacci.
Akwatinta ta buɗe ta zaro wata doguwar riga mara nauyi ta zura.
Tana rufe akwatin Hibba da Aunty Rahma Suka shigo da Foodflaks a hannunsu.
Ishma biye dasu da plate and spoons.
A tsakiyar ɗakin suka ajiyesu bisa carpet.
"My surka ina Safiyyah".
juyawa sukayi jin muryar Safiyyah a bakin ƙofar shigowa tana cewa.
"Gani Aunty Rahma naje nayi wonka a wancan ɗakin ne".
"Ok to ga abinci zo kuci".
Cewar Rahma to tace kana ta shigo.
Aunty Rahma da Hibba kuma suka juya zasu fita Ishma na biye dasu.
Cikin yanayin gajiya Aysha tace.
"Ishma na zo mu zauna mana".
Cikin sanyi tace.
"Mommy tace in barki ki huta".
Fuskar Rahma ta kalla tare da cewa.
"Aunty bar min ita".
Sake hannun Ishma tayi tare da cewa.
"Ai shike nan gata in ta buwayeku da surutu Safiyyah ta korata".
Da sauri ta dawo ta zauna bisa cinyar Aysha kana su kuma suka fita.
Safiyyah ce ta zuba musu abincin.
Bayan sunci sun shane.
Aysha ta koma kan gado sabida har yanzu tana ɗan jin ciwon cikin kaɗan-kaɗan duk da tasha mgnin ta.
Kwanciya tayi tare dasa Ishma a gaba.
Ganin kamar bacci zatayi ne yasa Safiyyah fita, ta koma can cikin ƴan uwa nan sukaci gaba da hirarsu.
Saida aka kira sallan magriba ne duk suka tashi duk sukayi al'wala sukayi sallan magriba da yawa basu tashi bisa abin sallaba saida sukayi sallan isha kafin suka tashi.
Nan suka fara shirin tafiya walimar.
Aunty Hafsat Maman Safiyyar kenan wacce suke kiranta da Mamma ce ta nufi ɗakin Hibba tana cewa Safiyyah dake bayanta.
Yauwa zo ki kaiwa Jannart nata kayan da zatasa a walimar, gana Aysha kuma."
Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom ɗin Hibba.
A hankali ta ƙarasa cikin ɗakin.
Kana a hankali ta juyo ta kalli Safiyyah cikin yin ƙasa da murya tace.
"Har tayi bacci ne ma?."
"Ai tun dazu ma tayi baccin, bari in tasheta".
Safiyyah ta faɗa tana nufar gadon.
Da sauri Mamma tace.
"A a kada ki tasheta da ƙarfi ba'a son tada mai ciki daga bacci ta sigar da zata firgita".
Aunty Rahma dake shigowane tayi saurin ƙarasowa tare da cewa.
"Kai Aunty Hafsat haba dama ni na lura kamar ciki take dashi naga tana yawan bacci".
Juyowa sukayi suna kallon Safiyyah daketa dariya ƙasa-ƙasa cikin dariyar tace.
"Au ku dama kallon mai ciki kukeyi mata ashe.
To wannan kam yanzuma bata salla, kuma dama wasu in suna al'ada suna yawan bacci inaga ita hakane".
"Kai Safiyyah wannan tsarabe-tsaraben naku na Nurses baya gaya muku gaskiya wasu lokutan".
Mamma ta faɗa da iya kar gskyar ta.
Ita dai Safiyyah dariya tayi kana ta fara kiran Aysha.
Ita kuwa Aysha tun mgnar Mamma na forko ta farka daga baccin ta dai ci gaba da rufe idonta ne kawai sabida karta katse musu hirarsu.
A hankali ta buɗe idonta tare da yin salati kana ta miƙe zaune.
Cikin kula Mamma tace.
"Sannu ko tashi kiyi salla ki shirya dan har an fara kai mutane wurin walimar".
Cikin sanyin bacci tace.
"To Mamma".
Daga nan ta miƙa ta nufi Bathroom.
Ita kuwa Mamma miƙawa Safiyyah ledar kayan Jannart tayi kana ta ajiyewa Aysha nata a bakin gado tare da cewa.
"In kin fito ga kayan da zakisa a cikin jakar nan a bakin gado".
"To ngd Mamma".
Tace tana rufe ƙofar Aunty Rahma kuwa hannu tasa ta ɗauki Ishma dan zataje ta kimtsata.
Safiyyah kuwa da sauri ta kaiwa Jannart nata kayan ta dawo.
Tuni ƙawayen Umaymah manyan mata da matan abokan Abbansu Haroon matan sarakuna Da ƴaƴan sarakuna duk anata kaisu wurin da aka tanada dan yin walimar.
Manyan mutane dattawa maza masu karamci da mutunci yan kasuwa da yan siyasa da sarakuna duk sun cika maƙil a babban hall ɗin.
Katon hall ne wanda a ƙalla zai iya ɗaukar mutune dari takwas zuwa ɗari dubu ɗaya.
An gyara wurin an ƙawatashi.
Ansa wani labule mai zaman kanshi an raba wurin biyu, kasan cewar dama ƙofofin shigowan biyune, haka yasa aka tsara wurin yadda mata zasu zauna a gefe ɗaya maza a gefe ɗaya bazama su ga junaba.
Sai can sama akayi wani ɗan dandamali wanda sai ka taka steps huɗu ana biyar zaka hau.
Shine wuri na musamman wurin zaman malami.
Ƙasa kaɗan dashi kuma wani ƙawataccen table ne mai kujeru shida, inda nanne wurin zaman angwaye da amare.
Can gefen inda malamin zai zaunama akwai ƙofar da ta nan zai shigo.
Tako ina ka cilla idonta haskene ras tamkar rana, wurin yayi kyau gwanin ban sha'awa.
Gaba ɗaya wurin mata da mazan ya cika maƙil duk manya-manyan baƙin sun samu isowa.
Hatta Sarki Ahmadu da tawagarsa da Abbansu Haroon da tawagar abokanshi duk sun iso.
Hakama Umaymah da da mutanenta hakama Mamma ta iso da Hajia Mama da Ummi da Aunty Juwairiyya da Hibba da Azeema.
Isowar Sheykh Jabeer da Ango da amaren kawai ake dako.
Madadin zama shurun sai akasa, sautin karatun al'ƙur'ani mai girma.
A can gida kuwa, Ibrahim, Haroon Sheykh da ne tsaye a harabar farfajiyar Side Umaymah, suna cikin wata iriyar fitinenneyar shiga mai masifar kyau da ban sha'awa.
Shigar fararen jallabiyar ƙirar Pakistan irin mai riga da wonɗonan ne kalar Sky blue mai azabar kyau da taushi da sheƙi.
Sai wasu tattausan al'kyabbar farare ƙal tamkar madara, al'kyabbar sun irin mai shara-sharan nanne haka ya bawa kolliyar tasu damar zama kamar adon sararin samaniya.
Sai hiramin dake kansu ne ya banbanta na kan Haroon da Ibrahim farine tas.
Sheykh kuwa nashi farine sai ɗigo-ɗigon Sky blue, hakama takalminshi hafl cover suma fararene sai ɗigon Sky blue.
Sai kekyawan zoben Daimond mai ɗigon Royal blue mai masifar kyau sai wal-wal yakeyi.
Sai ƙamshi sukeyi da sheƙi.
Ibrahim ne ya kira Safiyyah a waya tare da cewa suyi maza su fito mana.
To tace kana ta kalli Aysha dake cikin shigar doguwar riga mai masifar kyau da tsada, rigar iri ɗaya ce da Tata data Jannart.
sai dai tafi kama jikin Aysha sabida ta fisu faɗin ƙasa da sama.
Sunyi kyau sosai sunyi rolling kawunansu da gyalullukan suka fito tamkar yammatan larabawa.
Cikin sauri ta fesa turare kana ta kalli Safiyyah tare da cewa.
"To na gama mu tafi ko".
Murmushi Safiyyah tayi tare da cewa.
"Masha Allah kinyi kyau. Mu tafi".
Da haka suka fito.
A falo suka samu hadiman Umaymah nata gyara gidan.
Suna fitowa Aunty Rahma da Jannart suma suka iso.
Da sauri Ibrahim ya buɗe motarsa ya shiga, Safiyyah ta shiga gefenshi.
Aunty Rahma da Ishma suka shiga baya.
Haroon kuwa kama hannun Jannart yayi suka shiga bayan motarsa direbanshi na gaba.
Sheykh kuwa a hankali ya buɗe motarshi dasu Sulaiman da Ya Hashim suka zo da ita, kuma su tuni an kaisu can wurin walimar.
Kasan cewar babu mai janshi ne yasa ya shiga ya zauna a mazaunin gireban.
A hankali tabi bayanshi ganin tuni Ibrahim yaja motarshi hakama motar Haroon.
Cikin takun nitsuwa ta iso gab da motar, hannu tasa zata buɗe baya ta shiga.
Jin marfin a rufe yake yasa ta ɗan matso kusa da inda yake tare da cewa.
"A rufe yake".
Ƙwayar idanunshi ya juya mata tare da mata alamun ta zagaya ta shigo can gefenshi.
Kasan cewar yana latsa wayarshi haskenta ya haska fuskarshi yasa ta gane manufarshi.
Zagayawa tayi ta buɗe ta shiga kana ta maida marfin.
A hankali ta juyo ta ɗan kalleshi jin yace.
"Bismillah". Kana ya tada motar yaja suka bar harabar wurin.
Kasan cewar wurin babu nisa sosai da masarautar.
Tuni su Haroon sun isa har sun shiga sun zauna yanzu isowar Sheykh kawai ake jira.
Suna isa harabar wurin. Bayan yayi parking, suka fito.
Suna isa suka samu tarin fadawa a bakin ƙofar.
gaba yayi ya nufi ƙofar da zai shiga ta wurin.
Ita ma binshi a baya tayi.
Suna shiga, tayi maza ta kange fuskantar da bayanshi sabida. Tarin mutanen da ta gani sun firgitata, sam batayi zaton yawan mutanen ya kai haka ba.
Fahimtar hakane, yasashi yin gaba ita kuma tana biye dashi.
Har inda su Haroon suke. Kujerar dake gefen Jannart ya nuna mata.
Ai da sauri ta zauna.
Shi kuwa sunkuyowa ya ɗanyi kan Haroon kana yace.
"Ka nitsu da kyau ka saurari abinda Allah da Manzonsa suka ce a tsakanin ma'aurata".
Cikin murmushin dake bayyana zallar jin daɗi da zumuɗin amarci Haroon yace.
"To Sheykh".
Daga nan ya juya ya koma inda aka tanada domin shi.
Yana zama wani ɗan agaji ya dawo bayanshi ya tsaya.
kana ya miƙo mishi abin mgn.
Amsa yayi kana ya saƙalashi a bakin al'kyabbar jikinshi.
Gyara zamanshi yayi da kyau kana ya fuskanci taron al'ummar baki ɗaya.
Ɗaya daga cikin ƴan agajin ne yasa hannunshi ya katse sautin karatun Alqur'ani dake tashin.
Cikin nitsuwa kamala haiba da ilimi ya ɗanyi gyaran murya tare da fara bude taro da bimilla da addu'a da sallama.
"Bismillah rahmanirrahim. Assalamu alaikum warahmatullahi wa barka tuhu.
Innal hamdalillah nahmaduhu wanasta inuhu wanastagfiru wana uzubillahi min shururi am fusina wa sai'yi ati amalina. Manyahadillahu fala mudillalah, famanyuddul fala hadiyala wa asshahu'alla'ila'ha'illalahu wahdahu lasheri kallah, wa asshahadu annamuhammadan abduhuwarasulu.
Ya ayu allazina amanuttaƙullaha haƙƙa tuƙatil wala ta mutunna illah wa antum muslimun ya ayu hannasu taƙu rabbakum.
Kalakum min nafsin wahida, wa kalaƙa minha zaujaha wa bassa minhuma rijalan khasiran wa nisa'ah wattaƙullah lazitasa'aluna bihi, wal'arhama innallaha kana alaikum raƙiba, ya aiyu allazina amanutaƙullah wa ƙulu ƙaulan sadidah yuslahlakum amalakum wayagfirlakum zunuba kum, waman yuɗillah wara sulahu, faƙadfaza fauzan azeema ambaduhu fa inna'asdaƙal hadisi kitabullah wa'ahsanal hadi hadiyu Muhammadin (S.A.W) wa sharal umuri muhdasatuha fa innakulla mudasatin bidi'a wa kulla bidi'atin balala wa kulla balaltun finnar."
Dogon nufamshi ya sauƙe mai ɗan nauyi sabida jan dogon numfashin da yayi, kana ya kalli Side ɗin dasu Abbansu Haroon suke yace.
"Alhamdulillah kamar yadda muka sani, walimace ta farin cikin auren ƴan uwanmu, kana kamar yadda kowa ya sani walima shine aci asha kana a watse.
To a madadin muyi zaman da ci da sha kawai ya dace mu haɗa da ambaton sunan Allah, dayiwa ango da amrya taƙaitacciyar nasiha akan tsarin aure a musulunce da haƙƙoƙin ma'aurata ga junansu da addu'an zaman lafiya."
A hankali yayi gyaran murya.
Kana ya muskuta ya gyara zamanshi da kyau ya fuskanci taro al'ummar Annabi dake gabashin.
Manya da yara maza da mata.
Especially matasa, yatsarshi manuniya yasa gyara zaman siririn farin gilashin dake manne a fuskarshi.
Ɗan sunkuyar da kanshi yayi.
Dai-dai inda abin sautin mgnar ke saƙale a wuyan al'kyabbar jikinshi.
Gaba ɗaya hall ɗin yayi tsit bakajin motsin kowa sai sautin numfashin mutane dana A/C.
Cikin tattausan lafazi muryarshi ta ratsa kunnuwan duk wanda yake wurin inda yace.
*AURE*
Ma'anar aure a musulunce shine. Sunnan Allah a wojen halittar Allah daya halitta ya haliccemu ne a jinsi guda biyu macce da namiji.
Kamar yadda Allah (S.W.A) ya ce, a Suratul Zariyya aya ta 49:-
(WA MIN KULLI SHA'I'IN KHALAƘNA ZAUJAINI LA ALLAKUM TAZAKKARUM)
"Kan ko wa wane abu Allah ya halice shi namiji da mace don ku yi tunani a kansa.
Sannan Allah maɗaukakin sarki a wata ayar ya sake cewa a Suratul yashin aya ta 36:-
(SUBHANALLAZII KHALAƘAL AZWAJA KULLAHA MIMMA TUMBITUL ARDU WA MIN AMFUSIHIM WA MIMMA LA YA ALAMUN)
"Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicci ma'aurata namiji da mace, dukkansu daga abinda ƙasa ke sirarwa, kuma daga ko wannensu kuma da ma abin da basu sani ba!."
Kanshi ya ɗan ɗago ya kalli gefen maza, idonshi ya ɗan lumshe sabida gamsuwa da nitsuwarsu data tabbatar mishi, zantukanshi na ratsasu.
Idonshi ya ɗan tsaida kan fuskar Haroon ango mai jiran gado.
Sai kuma ya janye idonshi yaci gaba da cewa.
"Tabbas da wannan tsarin na auratayya ne. Allah ya zaɓa mana ya zama hanyar da zamuyi ta haife-haife muyi ta karuwa a bayan ƙasa.
Domin shi aure wata muhimmiyar igiyace wadda idan aka ƙullashi zai bawa ma'aurata daman saduwa tsakaninsu ba tare da wata ƙyama ba, kuma ta hakane ma'aurata zasu zama sutura ga junansu kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a Suratul Baƙara aya ta 187:-
"Su mata suturane gareku maza, sannan kuma maza sutura ne garesu-su matan.
Saboda haka zamu tabbatar lallai akwai al'ƙawari da amana mai ƙarfi a tsakanin ma'aurata, kuma Allah ya al'barkaci aure kuma yana son tabbatarsa , yana kuma ƙin ɓacinsa ba tare kwakkwaran larura ba.
Shi aure sunnace daga cikin sunnonin da ɗan Adam ya sami kansa a ciki, sannan kuma larurace daga cikin larurorin rayuwar ɗan Adam domin da aurene mutun zai kiyaye dangantakarsa, kuma ya ƙididdige ƴaƴansa wanda ya haifa kuma da shine zai kiyaye mutuncinsa, martabarsa dama dukkan dangantakarsa ga sauran ƴan uwansa da jama'a baki ɗaya kamar yadda Allah (S.W.A) ya faɗa a Suratul Furƙan aya ta 54:-
( WA HUWALLAZII KHALAƘA MINAL MAA'I BASHARAN FAJA ALUHU NASABAN WA SIRRAN WA KANA RABBUKA