Showing 303001 words to 306000 words out of 352722 words
Allah mun gode Matuƙa Allah ya saka da al'khairi ya kula da ahlinka fiye da yadda ka kula damu".
Cikin jin daɗi yace.
"Amin ya rabbil izzati, amman kuma duk haka ya farune sanadin Sulaiman da aka rufeshi tare daku".
Cikin gamsuwa sakace.
"Ayyah".
Sai kuma Giɗi ya ɗan share hawayen da suka zubo mishi tare da cewa.
"Ayyah bawan Allah yaushe zamu koma Rugar Bani muga Bappa da Inna da Ummey da Shatu da Junnu".
Cikin gamsuwa da tausayinsu Sheykh yace.
"In sha Allah nan kusa amman nafi son sai naga kunyi aski kun ƙara hutawa, gobe zuwa jibi da kaina zan medaku".
Cikin wani irin masifeffen jin daɗi sukace.
"Allah ya kaimu".
"Amin Amin". Yace kana ya musu sai da safe.
Daga nan wurin Abbanshi da Lamiɗo da Galadima yaje suka ɗan yi wata mgnar kana ya dawo.
Ranar dai haka suka kwana gaba dayansu babu wanda yayi isasshen bacci sabida masifar bugawa da ƙirazansu keyi.
A can Rugar Bani kuwa.
Ko abincin dare Ummey bata iya ciba.
Haka nan sai taji zuciyarta na tsinkewa yana bugawa.
Tun abun bai damunta har ta gayawa Bappa, so ya bata ƙarfin guiwa da yin addu'a.
*Ba'ana*
Zaune yake gaban yaransa cikin rauni da yanayin damuwa yace.
"Nanda wata uku masu zuwa zan koma ƙasar Nigeria zanyi yaƙin neman Shatu koda zan rasa rainane, zan koma gareta.
Zan gaya mata ko mutuwa nayi sonta ne ajali na".
Cikin bashi ƙarfin guiwa ɗaya daga cikinsu yace.
"Zama kayi nasara".
A hankali yace.
"Babu tabbas, domin tunda na rasa Shatu nakega nayi rashin babbar nasara".
Sai kuma ya miƙe ya shiga cikin ƴar ƙaramar bukkarsa.
Murmushi Baron yayi tare da katse kiran da yayi Sheykh yana jin duk bayanan Ba'ana.
Dan shi Baroon yanzu ya zama ɗan aikin Sheykh dan tun zuwansa lokacin ciwon hannun Shatu.
Da fari har yasa a kirasa daga baya yasa aka dawo dashi.
Ya biyashi kuɗi masu tarin yawa, yayi mishi duk bayanin ɗaya nema, kana yasashi ya koma wurin Ba'ana kuma ya naɗo mishi rahoto da duk wani motsin Ba'ana yana turo mishi.
Alhamdulillah kuma yanzu duk shirin kama Ba'ana yakeyi.
Washe gari ranar asabar yau babu aiki.
Da misalin ƙarfe goma na safe jirginsu Abboi ya sauƙa cikin birnin Ɓadamaya.
Kai tsaye Salmanu yayi musu jagora zuwa Rugar Bani dan a take suna sauƙa wasu tsala-tsalan motoci guda biyar suka iso wanda dama su tun jiya suka iso.
A ƙasan plate number motocin akwai tambarin hatimin kan shanu a ƙasa ansa Abboi, irin tambarin dake jikin jiragen Abboi kenan.
Suna zuwa kuwa babu ɓata lokacin suka isa har cikin gida.
Inda nan Arɗo Bani da kanshi da sauran dattawan sukazo.
Bayan sun gaggaisane Abboi ya ɗan yi gyaran murya tare da cewa.
"Toh Alhamdulillah lallai komai yayi forko to tabbas yana da ƙarshe, to bayan bincike da bin diddigi dai mun gama fahimtar inane asalin wannan baiwar Allah'n kuma munada yaƙinin daga masararutar Joɗa ta fito.
To yau dai kam ranar data kamata mu shiga da ita ciki da yardar ubangiji tazo.
Kamar yadda muka tsara, yanzu zamu tafi".
Cikin tsananin jin daɗi da kuma fargabar ko ya al'amarin zai kasance Bappa yace.
"Alhamdulillah mu duk a shirye muke, fatanmu Allah yasa ina munje ta tuna baya, ta tuno ita wacece".
Da sauri Arɗo Bani yace.
"In Sha Allah ma zata tuna Malam Babayo".
"Allah yasa haka".
Al'ameen ya faɗa.
Amin Amin sukace kana duk suka miƙe suka fito.
Kana Bappa yazo yacewa Ummey da Dedde su fito.
Nan suka mara musu baya.
Mota ɗaya Bappa da Abboi da Arɗo Bani suka shiga.
Ummey da Dadde da Al'ameen kuwa suma mota ɗaya suka shiga.
Sauran kuma ƴan tsaronsu ne a ciki sai motar Yah Salmanu da Hafsi ƙanwar Shatu a haka suka fito daga Rugar Bani suka nufi Masarautar Joɗa.
A hankali Ummey ta jingine kanta da jikin kujera tare da dafe ƙahon zuciyarta a hankali ta furta innalillahi wa innailaihi rajiun".
Sabida tsananin tsinkewar da zuciyarta keyi Dedde kuwa hankalinta naga makiyayan dake zirya.
A nan cikin birnin Ɓadamaya a tsakiyar Masarautar Joɗa kuwa.
Gaba ɗaya su Umaymah suna falon Shatu.
Aunty Rahma ce da su Sara a kitchin, Aunty Juwairiyya tana part ɗinta da Hibba.
Junainah da Ishma kuwa suna kitchen tare da Aunty Rahma.
Kowa sabgar gabansa keyi.
A hankali Shatu ta miƙe ta nufi ƙofar falon Sheykh da sallama a bakinta.
Shiru ba kowa a falon tray'n breakfast ɗinshi shida Haroon ta ajiye bisa Dinning table.
Ganin ba kowane yasa ta turo kanta cikin bedroom ɗin.
Shiru ba kowa a hankali ta ƙara so ciki tana cewa.
"Salam Yah Sheykh". Ƙofar bathroom ta matso a hankali ta tura ba kowa a ciki komai yana kimtse tsab-tsab.
"Toh ina yaje kuma yau Lahadi kuma ai babu inda zaije".
Shiru tayi tare da juyowa ta matso tsakiyar ɗakin jujjuya kanta tayi ba mutun ba alaman mutun a ɗaki.
Har ta juya zata fita, sai kuma tayi sauri ta juyo tazo bakin gadonshi, abun data hanƙo ƙasan pillow'nshi ne yasa ta sunkuyowa da sauri hannunta tasa ta zaronshi.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Ta faɗa jiki na rawa tare da sakin fuskar robar da Sheykh ake amfani da ita a matsayin Jahan.
Da sauri ta juyo da nufin zata fita, sabida tsoron daya rufeta.
Sai kuma tayi sauri taja da baya tare da zare idanunta dai-dai lokacin da ta iso jikin marfin wodurob ɗin sa
Wanda yayi dai-dai da lokacin da Sheykh ya turo marfi ya fito.
A gigice take jujjuya kai tare da zaro ido.
Sai kuma ta juya da sauri ta kalli fuskarnar da ƙarfi ta buɗe baki tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Yah Sheykh".
Da sauri yasa hannunshi ya kamo nata ya fizgota jikinshi cikin haɗe fuskarsu wuri ɗaya yace.
"Na'am Aysha please kada kiyi ihu tsaya nitsu nine Muhammad Jabeer Yah Sheykh mijinki Abu Afreen".
Cikin yanayi kaɗuwa tace.
"Yah Sheykh kai mutum ne ko al'jan".
Da sauri ya kamo hannunta suka iso gaba durowar.
Buɗe ƙofar yayi, kana a hankali yasa hannunshin ya ture, al'kyabbas ɗin shi dake jere a hanga a saƙale, sai ga wani ƙofa mai kamar glass.
A hankali yace.
"Aysha nitsu ki jini kinji ko".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Toh".
Kanshi ya gyaɗa kana a hankali yace.
"Kinga wannan wurin ko?".
Da sauri tace.
"Eh naga kamar ƙofa ne".
Jawota yayi suka ɗan matso hannunshi yasa ya tura ƙofar da sauri tace.
"Lahh".
Sabida ganin wata ƴar siririyar hanya mai tsawo.
A hankali yace.
"Ni mutum ne Aish yanayin tsarin masararutar Joɗa ne yasa dole nake amfani da wasu ababen.
Kinga wanan hanyar har cikin bedroom ɗin Lamiɗo da Abba na duk akwai su.
Muna haɗuwa dasu a ɗakin Lamiɗo lokuta da dama.
In kina so anjima zan nuna miki, dan yanzu Lamiɗo ya rufe ƙofarsa ne da yanzu zamuje".
Da sauri tace.
"Me kukeyi a ɓoyen".
Jawo ƙofar yayi ya rufe kana a hankali yace.
"Ina wani aikine Aish Kuma aikin sirrine, tsawon shekaru inayi babu wanda ya sani sai Lamiɗo da Abba na da Umaymah sai yau kuma da kika zama ta uku".
Ya ƙarashe mgnar yana jawota suka zauna bakin gado.
A hankali ta sauƙe numfashi ido ta zuba mishi a hankali tace.
"Kai SS ne ko Yah Sheykh?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ba'a faɗa kiyi shiru kada wani yaji kinji ko sirri ne Boɗɗo na".
Murmushi mai cike da jijjina tayi mishi.
Shi kuwa ruggume ta yayi ya koma baya ya kwanta.
Dai-dai lokacin kuwa motar Salmanu dake gaban motocin su Abboi ta kusa kai cikin matsarautar Joɗa bayan an wangale musu gate.
Wani irin rumtse ido da ƙarfi Ummey tayi tare dasa kanta bisa guiwowinta sabida wani irin masifeffen tsarawa da kanta yayi da azaban ƙarfi.
Kai tsaye bakin part ɗin su Sheykh Salmanu ya nufa dasu sai dai Motar Abboi da sauran duk a can baya bakin fada suka tsaya inda Bappa ya nuna musu.
Yadda suke ƙara kusanto Part ɗin su haka sarawa da bugun zuciyar da Ummey keyi yake ƙaruwa.
A can cikin falon Shatu ma, da sauri Umaymah da Mamma Suka kalli juna sabida masifar bugawa da ƙirazansu sukayi.
Sheykh kuwa da ƙarfi ya ruggume Shatu sabida ji yayi tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa ta fito woje.
Jalal da ke Part ɗin Yah Jafar da sauri ya rumtse idanunshi shida Yah Jafar ɗin.
Hakama Jamil dake tare dasu Gaini.
A hankali motocin sukayi parking.
Ummey kuwa wani irin ƙara rumtse idanunta tayi da masifan karfi.
Dedde kuwa a hankali ta buɗe ƙofar.
Ta sako ƙafarsa cikin shigarta ta al'farma.
Shi kuwa Al'ameen da sauri ya zagayo ya buɗe wa Ummey kofar tare da cewa.
"Ummey mun iso bismillah".
Cikin tsananin danne sarawar da kanta keyi ta ɗago jajayen idanunta a hankali ta zuro ƙafafuwan woje.
Ras ras Din dab din dab haka zuciyarta ta bada wasu tagwayen bugu.
Da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta.
Dedde kuwa a hankali ta zagayo inda take.
Shi kuwa Al'ameen a hankali yace.
"Bismillah ku shiga ga ƙofar".
A hankali Dedde tace to kana ta nufi ƙofar.
Ita kuwa Ummey cikin rawan jiki ta ɗaga ƙafarta ta dama ta ɗaura kan barandar tare da ƙara dafe ƙirjinta da rumtse idanunta sabida jujjuyawan da kanta ya fara.
Shi kuwa Al'ameeen bayansu yabi.
Shi kuwa Salmanu a hankali ya kalli Hafsi ƙanwar Shatu dake bin Khadijah.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
"Ko in ɗagaki ne in kaiki".
Cikin jin kunya tace.
"A a Yah Salmanu zan shiga da ƙafata".
Su Bappa kuwa Sarkin ƙofa ne yayi musu iso zuwa cikin fada.
A hankali Dedde ta kai hannunta ta kama handil ɗin ƙofar falon ta murɗa tare da turawa kana tasa ƙafarta ta dama ciki bakinta ɗauke da sallama.
Aunty Rahma dake fitowa daga kitchen Junainah na biye da ita da sauri ta ɗan juyo ta kalli Dedde tare da cewa.
"Wa alaikassalam".
Ta ƙarashe amsa sallamar tana matsowa dan ganin wani irin fitinenne kama da Dedde keyi da Shatu.
Da sauri ta juyo bayanta jin Junainah na cewa.
"Lah Oyoyo Dedde".
Dai-dai lokacin kuma Ummey ta ƙarasa shigowa ciki wanda hakan yayi dai-dai da bugawar da kanta yayi wanda saida tayi sauri sa hannunta duka y ta damƙe kanta da masifan karfi tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Da ƙarfi wanda haka yasa Dedde juyowa ta fuskanceta sanadin juyawar da Dedde tayi kuma ya bawa Aunty Rahma da Junainah damar ganin fuskar Ummey da kyau.
Wani irin sauri Junainah tayi ta nufi inda suke ganin yadda gaba ɗaya jikin Ummeynta yake karkarwa da tsuma.
Aunty Rahma kuwa cikin wani irin tsananin firgita da kaɗuwa ta zazzaro idanunta waje har kamar zasu faɗo.
Wani irin taku mai cike da firgici tayi tana matsowa gaban Ummey dake jujjuyawa tana mai-mai-ta.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil".
Wani irin matsowa kusa da ita Aunty Rahma tayi tare da buɗe baki da ƙarfi tace.
"La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama. Aunty Mamey!."
Ta ƙarashe kiran da azaban ƙarfi da rakaɗi.
Ummey kuwa.
Kiranta da Aunty Rahma tayi yasata ƙara gigicewa.
Karkar haka jikinta ke rawa.
Cikin wani irin gigitaccen murya Aunty Rahma ta fara rabkawa ahlinta kira.
"Umaymah! Mamma Jazlaan ga Aunty Mamey ta dawo da izinin ubangiji Jazlaan, Jafar, Jalal, Jamil, Umaymah. Kuzo ga Aunty Mamey...".
Wani irin azabebben zabura...!
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k ne kacal zaki turo ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Normal group Kuma 300 zaki turo ta asusuna ɗin sai kuyi screenshort na Debit Alert din ku turo min ta whatsApp 09097853276.
By
GARKUWAN FULANI
Cikin zuba mata ido tare da mamaki muryarta da kamanninta suka haɗa baki wurin cewa.
"Wa alaikassalam".
Shatu kuwa da sauri ta miƙe tsaye tare da nufosu cikin farin cike take cewa.
"Oyoyo Allah sarki My Junnu".
Da gudu Junainah ta ƙara sa inda take ruggume juna sukayi suna dariya.
Da sauri Shatu ta ɗan ɗago kanta ta kalli Khadija date cewa.
"Wato ma Junainah kawai kika gani ko Adda Shatu shekara biyu baki ganniba ko ki kulani".
Da sauri ta saki Junainah ta ruggume Khadijah tana dariya tare da cewa.
"Oh Dija ƙorafi".
Ita kuwa Junainah dariya tayi tare da cewa.
"Oh su Adda Dija kishi akeyi dani".
Cike da mamaki da kuma farin cikin ganin Junainah Ummi ta kalli Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa.
"Lalako jaɓɓama mon poi".
Da sauri Shatu ta ture Dija cikin tarin so ta ruggume Aunty Amina da Inna Amarya tare da cewa.
"Aunty Amina Inna Amarya marabanku."
Da sauri suka ɗan juyo jin Sheykh yana cewa.
"Sannunku da zuwa".
Cike da kunyar sirkai sukace yauwa.
Kana sukabi bayan Ummi dake cewa.
"Ku iso mu shiga ciki."
To sukace kana sukabi bayanta itama Shatu tabi bayansu.
Sara kuma ta kwashi kayan duk ta kaisu kitchin.
Ita kuwa Junainah jin muryar Sheykh ne yasa ta juyo da sauri.
Ganinshi riƙe da jaririyar ne yasa ta juyo da sassarfa ta nufi inda yake tare da cewa.
"Hamma Jabeer?".
Tai mgnar tana zubawa Jalal da Jamil ido, da alamun so take taga wanda zai amsa a cikinsu ta gane waye shi.
Cikin sauƙe wata iriyar nannauyan ajiyan zuciya yace.
"Na'am Junainah".
Da sauri ta ƙara so inda yake, tana isa ta ɗan sunkuyo tana kallon Babyn murmushi mai yalwa tayi tare da cewa.
"Ina kwana Hamma".
Yana mai kallon yantsun hannunta data miƙo mishi alamun ya bata Babyn yace.
"Lfya lau Alhamdulillah Junainah ya Bappa".
Da sauri tace.
"Yana lfy yace in gaidaku duka, harda Yah Jafar Yah Jalal da Yah Jamil".
Da sauri ta ɗan juyo jin Affan na cewa.
"Banda ni kenan".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"A a harda kai mana".
Sai kuma ta juyo tana kallon Sheykh tare da yin ƙasa da murya tace.
"Hamma Jabeer me sunanshi".
Murmushi yayi tare da yin ƙasa da murya kamar yadda tayi yace.
"Affan".
Cikin gyaɗa kai, ta ƙara matsowa zama tayi gabanshi tare da miƙa sawunta cikin zaƙuwa tace.
"Hamma Jabeer bani ita mana".
Da sauri yace.
"Junainah zaki iya kuwa inafa tsoron kada ki kada ita".
Da sauri tace.
"Zan iya mana".
To yace kana ya sunkuyo ya ɗaura mata yar bisa cinyarta, yasa hannunshi ya tallabe kan Babyn.
A hankali Jalal yayi wani irin rumtse idonshi da ƙarfi.
Jamil kuwa cikin sanyi ya taso ya taho kusa da ita, matsawar da yayine yasa Yah Jafar hangota.
Miƙewa yayi da sauri ya nufo tsakiyar falon.
Ido suka zuba mishi ganin yadda yazo ya tsuguna gaban Junainah da Babyn da Sheykh ɗin.
Da sauri Junainah ta ɗago kanta ta kalleshi cikin zuba mishi ido cikin ido tace.
"Ina kwana".
Shiru yayi bai amsa ba, sai hannunshi da yasa kan sawunta yatsun ƙafarta ya ɗan kama tare da rumtse idonshi.
Da sauri ta kuma cewa.
"Ina kwana?".
Shiru bai amsaba sai kuma ga hawaye na zubo mishi.
Hakane yasa ta juyo da sauri ta kalli Sheykh cikin rauni ido cike da hawaye tace.
"Hamma Jabeer baya mgn ne? Meyasa yake kuka."
Ta ƙarashe mgnar hawaye na zubo mata.
Da sauri Jalal ya tsuguna gabanta tabbas ta tuno mishi abu da yawa kam Mameynsu sabida masifar kamar da sukeyu.
Haka nan yaji son yarinyar yana ratsa dukkan sasan jikinshi gaba ɗaya.
So irin na ƴan uwataka so irin na wa da ƙanwa
Cike da mamaki Sheykh yake kallon Jalal da yasa tafin hannunshi yana share mata hawayenta.
Wanda ita kuma haka ya ƙara tunzura zubowar hawayen nata.
Cikin rawan murya tace.
"Hamma Jabeer meyasa yake kuka?".
Cikin wani irin yanayi Jamil ya tsuguna shima ya zama sun zagayeta sun sata a tsakiya.
Shi kuwa Sheykh a hankali yasa hannunshin bisa kanta cikin rauni yace.
"Nima ban saniba Junainah wata ƙil yana tsoron kada ki kada Baby ne ko kuma muryarki ce tayi iri ɗaya da muryar Mamanshi".
Cikin shessheƙan kukan da haka nan taji ya kubce mata tausayin mutumin ya rufeta cikin rauni tace.
"A a bazan kada itaba, Ummey na ta koya min yadda ake riƙe yara ai lokacin da mukaje gidan Abboi da yarinyar Maman Idris to Ina Maman nashi".
Sai kuma ta ɗan musukuta ta gyara zamanta tare da gyara riƙon yarinyar.
Cikin sanyi Jamil yace.
"Mamanshi bata nan".
Cikin zubda hawaye tace.
"Ina take?".
Tai mgnar da alamun tausayawa.
Sheykh ne ya ɗan sunkuyo ya kalli ƙwayar idonta a hankali yace.
"Mugayanen magauta sun sabauta rayuwarta sun ɓadda ita".
Kanta ta jingina jikin Jalal dake gefenta cikin sanyi da rauni tace.
"Ayyah Allah ya isan mata, Allah zai saka mana".
Sai ta kuma kalli Yah Jafar ɗin da tsananin kamanninta da Mameynsu ne da kamar murya ya sashi zubda hawaye a hankali tace.
"Kayi haƙuri Yaya zamuyi ta mata addu'o'in, kuna Ummey na zata zama mamanku, kuna so ko?".
Da sauri Sheykh ya gyaɗa mata kai ganin yadda ta ƙarashe mgnar da zuba musu ido".
Affan kuwa gefen Sheykh ya zauna yana mai kallonsu cike da al'ajabin yanayin da suke ciki Especially Jalal da ba kula yara yakeyi ba.
Ummi kuwa a can cikin ɗakin Shatu, tayiwa su Aunty Amina iso.
Bayan sun zauna ne, Sara data kai kaya kitchen ta kawo musu ruwan.
Kana ta fito ta koma Kitchen taci gaba da aikinta Ummi na biye da ita a baya.
A falon ta tsaya tare da zubawa ikon Allah ido.
Muryar Junainah dake iri ɗaya sak da muryar da bazasu taɓa mancewa da itaba a duniya.
Ita kuwa Junainah a hankali ta kalli Ummi data iso gabansu.
Tare da kallon yadda suke a hankali tace.
"Uhm autar Mamey kawo ɗiyar taki in kaiwa su Inna Amarya ita".
Da sauri tace.
"Toh". Ta ƙare zancen tana miƙa mata ƴar.
Jalal kuwa ido ya zubawa Ummi.
Sheykh kuwa juya kanshi yayi yana kallonta yana nazartan kalmarta, itama taga kamar kenan."
Ya faɗi a ransa.
A fili kuwa murmushi suka ga Jafar yayi tare da miƙewa tsaye murya can ƙasa yace.
"Autar Mamey nima haka idona ke sanarwa zuciyata Ummi".
Da sauri suka kalleshi.
To daga jiya zuwa yau dai sun saba da yayi mgn a fizge sai dai bai kuma ƙarayin wata duk mgnar sa za'ayi mishi.
Yana faɗin haka shi kuma ya juya ya tafi.
Da sauri Jalal yabi bayanshi.
Affan kuwa a hankali ya miƙe ya fita ya nufi falon Hajia Mama.
Jamil kuwa sashin Gimbiya Aminatu ya nufa.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya yunƙura ya gyara zamanshi ya koma bisa kujera, kana ya kalli Junainah dake tsaye tana gyara tarhan da tayiwa ɗan kwalin hijab din jikinta.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
"Wannan ɗayar itace Ummey?".
Da sauri ta matso kusa dashi a hankali tace.
"A a Ummeynmu tana gida bata zoba.
Wannan Aunty Amina ce ƙanwar Dedde, ɗayar kuma Inna Amarya ɗayar kuma Adda Khadija ƙanwar Adda Shatu ne. Na fita kyau ko?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa, ke mai zubin larabawa".
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
"Yessss my Hamma ka iya gayan gsky".
Sai kuma ta juya ta nufi falon Shatu tana cewa.
"Bari inje inga Adda na da kyau".
Da ido ya rakata.
Jamil kuwa yana shiga ya gayawa Gimbiya Aminatu cewa wasu baƙi sunzo wurin Shatu da wata yarinya mai kama da Mameynsu.
Tofa wannan al'amari yasa Gimbiya Aminatu sanarwa Lamiɗo haka, da kanshi yace taje tai musu sannu da zuwa.
Yah Jafar kuwa yana shiga, falon shi ya samu